Showing 87001 words to 90000 words out of 145791 words

Chapter 30 - Sakatariya Ta Book One Complete Hausa Novel

Azizat   

01 Nov 2025

329

?aramin zabgewa yai ba, to ba dole ba shalelen Wan sa yana kwance a asibiti shi da mai mutuwa banbancin su kaWan ne.

"Aisha ya aikin?" Ya katse shirun na su

"Alhamdulillah Daddy"

"Allah ya taya ki ri?o" ta amsa da amin.
"Ki na cin abinci kuwa? na ga kin rame"

"Ina ci tareda Sir Najeeb mu ke ci"

Daddy yai shiru bayan yai addu'an Allah ya bawa Najeeb lafiya.

"Aisha, Anas ya zo wajena Wazu da rana kuma ya min wassu bayanai, na saurare shi kuma na fahimce shi. A wani Sangaren kuma ke ma na fahimci inda ki ka dosa. Alhamdulillah dukkan ku manufar ku Waya ne, sai dai ra'ayin ku ne ya banbanta kan yadda za ku cimma wannan manufa"

"Daddy zan ha?ura idan ka ce na ha?ura amma gaskiya ba zan cigaba da zama a matsayina ba bayan hakan"

" ba zan ce ki ha?ura ba amma ina da tambaya. Idan da ace Najeeb ne a wannan yanayi ki na ga zai shiga gasan nan ko ba zai shiga ba?"


"A sanin da na yiwa Sir Najeeb Wallahi zai shiga gasan nan"

Daddy ya Waura ?afa Waya kan Waya ya ce " ki je ki yi abinda ki ka ga Najeeb zai yi, Allah na tareda ke. Idan ki na bu?atan taimakona ko shawara kan wani abu feel free ki min magana yadda Najdah ta ke matsayin 'ya ta haka na Wauke ki"

Godiya ta ma sa sannan ta tashi ta shige Wakin su. ?akin na nan yadda ya ke abu Waya ya rasa shine mazaunan ciki.

Tana tsaye gaban mirror ta rage kayan jikin ta tana kallon yadda ta rame ta yi ba?i.

"Aysherh ba na son ?azan ta" ta ji muryan Najeeb a bayanta. Ta juyo ta Wan harareshi ta ce "ni ba ?azama ba ce"
Sunkuyo da kan sa yai ya shinshina gashin ta sannan ya Wago yana fifita hanci yana faWin " kin san ba na son wari Aysherh"

Ta juyo a harzu?e zata fara masifa ta ga wayam ba kowa. Dama idon ta ke ganin kamar Najeeb na wajen, abinda ke sa ta nishaWi kenan saboda ganin Najeeb da ta ke yi a idon ta, koyaushe yana tare da ita.

Da sauri ta wuce banWaki ta fara wanke gashin ta wanda rabon shi da ya ga proper wanki tun zuwan ta Jos. Ta shampooimg kanta tana dirje dattin gashin da na scalp Win ta. Da ta wanke kumfan sannan ta saka instant conditioner yai minti biyar kafin shima ta wanke, sai a sannan ta fara wanka da shower gel Win Najeeb mai shegen ?amshi.
Lokacin da ta fito ita kan ta sai kan ya ma ta sa?ayau. Bayan ta drying na shi da hand dryer sannan ta shafa ma sa leave in conditioner. Zama ta yi ta yiwa gashin twist manya guda takwas. Ta kalli kan ta a madubin ta ga ta yi kyau saboda rabon da gashin ya ga gyara tun tana Jos. Cikin ran ta tana faWin ai dole Champ ya ce ba ya son wari, kan ta cikin wata biyu ban da ruwan alwala da kuma ruwan wankan tsarki bai ga ruwan wanki ba. Tana shiryawa Tasallah ta zo ta tambayeta ko ta kawo ma ta abinci ne yanzu. Ta ce ta haWa ma ta za ta wuce da shi asibiti...

Lokacin da ta je asibitin ta samu likita na duba Najeeb.

"Ya jikin na shi?" Ta tambaya lokacin da ta ?araso.

Likitan ya amsa da sau?i

Sai da Farida ta samu waje ta zauna sannan likitan ya juyo ya kalleta bayan ya gama duban na'uran da ke kula da Najeeb.

"Aisha, ki cigaba da addu'a amma halin da Najeeb ke ciki komai zai iya faruwa. Wassu kan Waukan shekaru ma su tsawo ba su farfaWo ba wassu daga haka su ke mutuwa, wassu kuma idan sun farfaWo ma za ka ga sun samu matsala da ?wa?walwar su ko kuma ka ga sun..."


"Na sani likita, tunda Najeeb ya shiga wannan halin na fara karance-karance akan wanda su ka shiga hali irin na shi kuma na gane komai. Ina da ya?inin cewa mijina zai tashi nan ba da jimawa ba. Zai tashi mu yi rayuwan aure mai cike da soyayya da ?auna, zai tashi mu haifi 'ya'ya kyawawa kaman sa, zai tashi ya kirani Mrs Jibo, zai tashi na nuna ma sa yadda na ke tsananin son sa" hawaye ya ?wace ma ta.

"Ki yi ha?uri Aisha, Allah ya na tareda ke. Akwai wani likita da ke zuwa visiting doctor a nan kwanan nan ya dawo Nigeria kuma gaskiya ana yabon ?wazon sa. Yana aiki ma da Dr Sajid so inaga idan ya zo gobe zai duba mijin ki. Mu ji wanni shawarwari zai bayar"

"Na gode Doctor amma idan ya zo ka kirani, zan so na ji mi zai ce da kunne na"

"Insha Allah zan kiraki" daga haka likitan ya fita.

Farida ta taso ta ?arasa gadon Najeeb. ?ankwalin ta ta cire ta kai gashinta dai-dai hancin sa ta ce "my champ na wanke gashin baya wari yanzu, ka ji ?anshin sa. Do you like it?"

Ta sumbaci idon sa da ke rufe ta ce "ko za ka mutu a haka ba zan gujeka ba, zan jira ka. Zan cigaba da jiran ka har iya ?arshen rayuwa ta. I love you, I love you so much. Ka tashi ka ji, ka tashi mu yi abubuwa, saboda kanada abubuwa ma su saka abubuwa kuma nima inada abubuwan da za su saka yin abubuwa. Ka tashi ka kissing Wi na irin na ranan, ka tashi kamin tafiyar ka mai Waukan hankali Win nan. Ka tashi ka min dariyan ka mai daWi"...

.........................

Washe gari ta zo ta tarar da abun mamaki, tana office Mrs Comfort ta shigo wai Anas yana kiran ta ana meeting a conference room.
Ba tareda Sata lokaci ba ta wuce hall Win. Tana zuwa ta tadda an cika, duk wani mai babban matsayi yana wajen, abun takaicin ma har da Sabreen.

Anas ne ya raising motion kan ?in amincewa da yai da shiga gasar da Farida ta sa.
Zaro ido tai lokacin da ya ce ko ta janye gasan nan ko kuma ya ajiye aikin sa.

"Ya Anas ya za ka min haka?" Ta faWa idon ta ya ciko da hawaye. Ba ta Wauka abin zai kai haka ba. Jiya sun rabu da Daddy akan zai yiwa Anas magana to mi kuma ya faru.

Sabreen ta ce Anas ba zai ajiye aiki ba idan ya ajiye kuma za ta cire shares Win ta. Ta sake cewa Farida ta ajiye aikin ko kuma dukkan ma'aikata su yi yaji.

"Its your lost Farida, dont destroy my Noory's company"

Sunkuyar da kai ta yi tanajin maganganun su. Ta jima a haka kafin ta Wago, ga mamakin ta sai ta ga Najeeb yana kallon ta yana murmushi.

"Its not easy ko?, haka nima na ke fama da su, but you have to be strong, you have to stand by what you believe. Kin san ya akayi na gina wannan kamfani cikin shekara bakwai ta zama haka?"
Farida ta girgiza ma sa kai

"Saboda idan na sa abu a raina sai na ga na cimmaci na ke ajiyewa. Na gaya miki mi za su yi idan ki ka janye gasar nan?"
Ta Waga ma sa kai

"They will consider you weak and incompetence. Za su ce ki sauka daga matsayin ki za su ce ba abinda ki ka iya. Anas is good amma yana da tsoro da rauni???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?. But you" ya nunata da yatsa "My Miss Salihu My Mrs Jibo My Aysherh ba ki da tsoro ba ki da rauni"

Firgigit ta yi lokacin da Anas ya ce " muna sauraren ki Aysherh"

Tashi tsaye ta yi tana shanye duk wani damuwa da ke ranta.

"Ya Anas za ka iya ajiye takardar a wajen sakatariya ta, za ta shigo min da shi office. Sauran da za su shiga yajin aiki kuma Bismillah sai na ji ku. Ma su son bin bayan ya Anas kuma takardan ajiye aikin ku duk ku ajiye wa sakatariya ta"

Ta maida kallon ta ga Sabreen ta ce "ke kuma zan fi kowa farin ciki idan ki ka cire shares Win ki a wannan kamfani"

"Ga wanda ya goya min baya wajen ayi gasa kuma. Zan sa a ajiye box a ?asa kowa ya jefa ?uri'ar sa ciki. Ba suna za ka saka ba ko matsayi, kawai ka Wau takarda ka rubuta *i support* ka jefa ciki. Na barku lafiya"
Daga haka ta Wau wayar ta ta fita. Anas dai mutuwar tsaye yai a wajen. Hall Win ya kaure da kace na ce.


Ko zama ba ta yi ba Sabreen ta shigo. " ba ki isa ki yi haka ba. Ba ki da matsayin da za ki kafa doka ki ce dole sai an bi ba"

Farida ta sa dariya ta ce " na samu matsayi tun ranan da aka Waura aure na da Miji na Najeeb. Love of my life, my heartbeat, my champion, my handsome.." mari Sabreen ta kai ma ta Farida ta ri?e hannun.

"Ka da ki kuskura ki taSa ni, ko kuma na sa a yanke mi ki hannu. Duk wanni matsayi da ki ke da shi outside Nigeria ya ke da tasiri. This is Nigeria ba wanda ya damu da wata karuwar Hollywood a nan. Ki tattara ki koma inda ki ka fito ko kuma idan na waiwayeki ba za ki ji daWi ba" ta tura hannun gefe.

Yadda ta ke magana da masifa ya sa Sabreen ta Wan ji tsoro.

"Now get out of my office"
Yadda ta yi tsawan tamkar Najeeb ne ke wannan tsawa.

Sabreen ta ce " we'll see" sannan ta fita.

Daga fitan ta Yakubu ya shigo.

"Haba Farida, ta ya za ki yiwa Anas haka. Anas ya mi ki halacci ta ya za ki ma sa haka?"

Wayar ta ne ya fara ringing ta duba ta ga Doctor Sadiq ta Wauki kiran tana faWin to gani nan zuwa. Tana gama wayan ta kalli Yakubu ta ce.

"Barinje na yi magana da likitan mijina, duk wani ?orafin ka zan saurara idan na dawo"

Yakubu yai galala da baki yana kallon 'yar uwartasa yadda ta koma Najeeb sak.

Jaka kawai ta Wauka ta fita ta barshi a office Win...

............


Kai tsaye Wakin Najeeb ta wuce lokacin da ta iso. Ba kowa a ciki dan haka ta kira likitan ta gaya ma sa cewa ta iso. Kusan minti goma sai ga doctor Sadiq ya shigo tareda wani likitan.
Idon sani ta gani, idon da ba za ta taSa mancewa ba.

"Dr Lukman ga matar patience Win na mu" ya kalli Farida ya ce "Aisha ga Dr Lukman wanda na miki maganar sa jiya"

"Green eyes" ta faWa bakin ta na rawa...



*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




0?? 3?? 5??





"Kin san shi ne?" Dr Sadiq ya tambaya. Ba ta bashi amsa ba sai kawai kallon Lukman da ta ke, bai chanja ba ya de Wan ?ara ?iba da kuma gemu amma bayan nan yadda ta sanshi haka ya ke.
Lukman ya katse shirun da cewa " ka san na zauna a Jos, itama 'yar Jos ce"

Dr Sadiq ya ce ok barin barku. Sai da ya fita sannan ya kalli Farida da kyau. Although kayan jikin ta sun nuna tana cikin jin daWi amma yanayin fiskarta ya nuna saSanin haka.

"Aisha ya ki ke ya mai jikin?"

Da ?yar ta haWiyi miyau ta ce " lafiya Alhamdulillah"

?arasawa yai gadon Najeeb duk da ma dai kafin zuwan Faridan shi da Dr Sadiq sun shigo sun duba shi, sai dai Wazun rashin sanin ko waye ya sa bai damu da kallon ya patient Win ya ke ba. Masha Allah ya faWa chan ?asar zuciyar sa lokacin da ya ?are ma sa kallo.

"Yaushe ka dawo?" Farida ta tambaya tana matsowa kusa da shi.

" shekara Waya da ya wuce"

"Ok"

"Sai dai tun lokacin da na dawo ban je Jos ba gaskiya"

Farida ba ta ce komai ba sai bin hannun sa ta ke da ido yadda ya ke tattaSa jikin Najeeb.

"Kinga Allah ya amsa addu'a ta ko? He's handsome"

Maimakon ta bashi amsa sai ta ce "ka na ga zai tashi nan kusa?"

"Na duba records Win sa kuma na ga cewa ya taSa motsa hannu sau Waya which is good news gaskiya. Insha Allah zai farfaWo Aisha, dole ma ya tashi ya kula min da ke"

Sai alokacin Farida ta yi murmushi...

Daga asibiti dreba ya mai da ta kamfani. Tana zuwa sakatariyar ta ta mi?a ma ta resignation letter Win Anas. Har ga Allah ta Wauka Anas ba zai yi haka ba. Dama so ta ke ya gane da gaske ta ke ba za ta janye ?udirinta ba. Amma sai gashi ya Wau abin da zafi.

Yakubu ta kira akan ya zo office Win ta. Bayan ya zo dai faWa ya fara ma ta kan abinda ta yiwa Anas ga shi yanzu ta sa Anas ya ajiye aiki.
"Sai mu ga yadda za ki kula da kamfanin ba tareda Najeeb ko Anas ba"

"Akwai Allah Yakubu, da Allah na dogara kuma shi zai taimakeni"

Tashi yai zai bar office Win ta ce ya tsaya.

"Yakubu ka na tareda ni?"

"Farida zan ba ki goyon baya akan wani abu amma ba wannan ba"

"Ba ka yadda da ni ba ne kenan?" Ta faWa tana matse hannayen ta.

"Mi ki ka sani gameda wannan gasa?"

"Ban san komai ba amma idan kuka min bayani zan fahimta"

"Farida abu ne mai wuya..."

"Dan Allah kar ka gujeni kamar yadda Ya Anas yai" ta faWa tana narai-narai da ido. Ajiyar zuciya yai sannan ya ce...

..........................


Washe gari da ta ke tunanin za'ayi yajin aiki shiru ka ke ji kamar shaho ya ci shirwa. Kowa ya kama aikin gaban sa. Ba ta jima ba Sakatariyarta ta kawo ma ta box Win da aka ajiye tun jiya wanda ke cike da takardu.

"Ki je ki ware min wanda su ka supporting da wanda ba su yi ba ki gayamin percentage Win"

Mrs Comfort ta amsa da to ta fita.

Bai fi minti talatin ba Mrs Comfort ta dawo da result
"Madam, 65% sun supporting sauran 35% kuma ba su yi supporting ba"

" 'yan iska kawai, na gode Mrs Comfort. Yanzu ki je ki aikawa Mr Ogonna sa?o kan cewa na janye suspension da na ma sa kuma ya resuming aiki gobe"

Mrs Comfort na fita ta cigaba da duba wani littafi da ta ke ganin Najeeb na yawan dubawa lokaci zuwa lokaci idan baya aiki. Sai yanzu ta fahimci Najeeb mutum ne mai tsari. WaWannan wa su details ne na yadda ya cimma wa su manyan projects na shi...

"Ina shegiyar ta ke?" ta jiyo muryan Najdah tana daka wa sakatariyarta tsawa.

"Ohooo! so wuyan ki yai ?wari har za ki ce Ya Anas ya ajiye aikin sa? Who are you? Mi ki ka Wauki kan ki ne. Idan akwai wanda ya dace ya ri?e kamfanin Big B to Ya Anas ne ba ke ba. Gold digging bitch"

Farida ta yi juyi kan kujera sannan ta ce " idan kin gama haushin na ki dan Allah a gaida min Daddy dan ban samu zuwa gida jiya ba. Miji na baya so na bar gefen sa"

Najdah ta harzu?a ta je gaban Farida ta sa hannu ta fara janta. Wallahi ki tashi a kan kujeran nan, ba ki dace da shi ba..." saukan mari ta ji a fiskarta wanda ya sa ta yi saurin ri?e gefen fiskan ta.

"You slapped me!"

"Idan ba ki fita harkata ba Najdah sai na sa an zane min ke. A kan ki aka fara auta ne da za ki bi ki rena mutane. Ni sa'ar ki ce? Na ce ni sa'ar ki ce?"

Farida ta koma ta zauna da kyau sannan ta ce " ki rufe min ?ofa idan kin fita...

Najdah was so shocked da ?wa?w?waran motsi ta kasa. Ta jima tsaye kafin ta fita daga office Win... sai da ta fita Farida ta kalli wani hoton Najeeb da ke kan table Win ta ce "My champ ka ga za su haukata ni ko, Ina zaman zama na su ka ce na karSi wannan matsayi kuma yanzu na karSa ana min mugun kallo"...

"Najdah is my favourite sister mi ya sa ki ka mareta?"

"Ka na ganin rashin kunyar da ta min fa, dama tun ba yau ba ta ke gayamin maganganun da ta ga dama ina shareta"

"Ohooo ni da ki ke min rashin kunya kullum na taSa marin ki?"

'Yar dariya ta yi ta ce "Haba my champ ni yaushe na ma rashin kunya, faWi gaskiya dai" zuwa yai gaban ta ya ja hancin ta da ?arfi.

" ouch! My champ da zafi fa" ta faWa tana hararan sa...

"Madam na gama aikin" muryan Mrs Comfort ya dawo da ita daga duniyar tunani.

...........................

"Daddy she slapped me fa. Daddy ka yi wani abu please"

"Na san idan ba ki ma ta rashin kunya ba ba abinda zai sa ta mareki. Ki fita a maganan kamfanin Najeeb. Karatu ne a gaban ki yanzu"

"Daddy abinda za ka ce kenan, mu zuba ma ta ido ta Sata komai ko? I will never do that" ta tashi ta bar falon da sauri.

Waya ya janyo ya yiwa Farida text akan ta zo idan ta tashi...

Anas ne ya fara zuwa kafin Farida ta zo. Ta samu Daddy yana mishi faWa kan ajiye aiki da yai, dan shi bai gaya ma sa ba Wazu Najdah ke gaya ma sa da ta kawo ?aran Farida...

"Ni ban amince da wannan ba Anas. Idan ku ka raba kan ku kuna ga kamfani zai cigaba ne? Ka koma aikin ka, idan ba za taimaka ma ta har ayi gasan ba, ka cigaba da kula da sauran harkokin ai"

"Daddy ka yi ha?uri dan Allah. Kawai dai..."

"Ba na son jin wani ?arin bayani. Gobe idan Allah ya kaimu ka koma aiki"

"Insha Allahu Daddy"
Juyawa yai kan Farida ya ce.

"Ku haWe kan ku Aisha, saboda a samu cigaba mai inganci. Allah ya shige mu ku gaba" ta amsa da Amin...

Tana cikin yiwa Najeeb taWi sai ga Lukman ya shigo da sallama. Ledar hannun sa ya ajiye wanda ke cike da fruits.
"Barka da yammaci Aisha" ya faWa lokacin da ya ?araso wajen ta.

"An wuni lafiya?"

"Lafiya, ya mai jiki?"

"Da sau?i Alhamdulillah"
Shiru ne ya ratsa Wakin na 'yan mintuna kafin Lukman ya ce " zan wuce Abuja gobe amma Insha Allah zan dinga neman ki na ji ya mai jikin"

"Na gode" ta faWa tana maida kallon ta ga Najeeb...

Bayan ya fita ta kalli Najeeb sai ga hawaye ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login