Showing 99001 words to 102000 words out of 145791 words

Chapter 34 - Sakatariya Ta Book One Complete Hausa Novel

Azizat   

01 Nov 2025

334

assessment ko excercise sai abin ya dinga sa ta kuka. Hatta juya kai sai da aka koya ma sa.
In every theraphy section da aka yi ma sa Mom da Farida su na manne da shi. A kwana na sha uku aka fara koya ma sa tsayuwa. Sai a bashi abu ya dafa ya tsaya idan ya daWe sai a zaunar da shi kafin a kuma Waga shi a haka ake yi har sai an ga ya gaji kafin a bar shi haka nan.

Ranan da aka fara bashi abinci, amai ya dinga kwarawa ?arshe jikin sa ya fara jijjiga da ?yar aka samu jikin sa ya dawo normal. Sai da ya kwana biyu ana bashi maganin da zai sa shi iya cin abinci kafin da ya ci bai amayar ba. Mom ce ke bashi abincin amma yana ci kaman wani Wan koyo.

A rana na goma sha tara ya fara magana. Mom na sallah ita kuma Farida na zaune a kujera tana karanta ma sa labari taji kaman magana. Maganar ta fito kaman mai koyon magana ko na ce irin maganar wawaye.
"Yuu a yuu?"

Ta yi saurin ajiye littafin ta kai kunnen ta saitin bakin sa dan ta ji da gaske Maganar yai.

Maganar ta sake fitowa kaman ta da. Da farko ba ta gane me ya ce ba sai a na biyu da ya maimaita ta gane cewa "who are you" ya ce.
Dam ta ji ?irjin ta ya buga.
"Sir Najeeb ba ka gane ni ba?, Aisha Farida, Miss Salihun ka"

Mom ta dafa kafaWarta ta ce "Aisha ki kwantar da hankalin ki, kin ji dai mi likita ya ce" sai a lokacin ta ji zuciyarta ya yi sanyi.

"Whhhhere...Whhha" sai yai shiru saboda maganar da ta ma?ale ma sa.

Mom ta fara shafa kan sa tana cewa " its ok son, a hankali maganan zai fita"

Da therapist Win da ya ke ma sa rehabilitaion theraphy section ya zo su ka gaya ma sa ya yi magana. Sai ya fara ma sa wassu tambayoyi, wassu ya amsa da ?yar wassu kuma shiru yai.

Tambayar farko sunan sa ya tambaya. Bawan Allah Najeeb kam da ?yar ya iya furta "YaaJeeb" Najeeb Win ya ke son faWa amma saboda bakin sa da be koma dai-dai ba maimakon N to Y ne ta fito.

A kwana na ashirin da shida ya fara gwada tafiya da taimakon sanduna biyu. Yanzu maganan sa ta Wan fara kyau ba kaman ranan da ya fara magana ba...

Fiskar Daddy Dr Kenneth wanda ya ke shi ne rehabilitation therapist Win sa ya nuna ya tambaya ko ya gane shi.

"Dad" ya faWa a hankali.

Ya nuna Mom ya tambayeshi, ya jima yana kallon ta kafin ya ce "Mom"
Hawaye da Mom ke ?o?arin Soyewa ne su ka fara zubowa. Shekara nawa rabon da Najeeb ya kira ta da wannan sunan.
Najdah aka nuna ita ma ya furta "baby"
?irjin Farida bugawa ya ke da ?arfi-?arfi yadda ka san zuciyar ta ne zai fito.

A karo na uku ya sake tambayar shi ko ya san Farida amma bai yi magana ba. Najma ya nuna ita ma ya kira sunan ta Najma.

Wannan karon hawayen da Farida ke Soyewa kan su ke zirya a idon ta.
Najeeb ya zuba ma ta ido yana son gane a ina ya san ta amma ya kasa, kuma idon na ta ya ma sa kama da idon da ya ke yawan gani cikin baccin sa.

Hannu ya Waga ya nuna Farida da yatsa ya ce "who is she?"






*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0?? 4?? 0??




*jiya na ga comments Win ku na kuma sha dariya. Princess Salma shugaban 'yan team Farida, ina mai ban ha?uri=??. No brain injury is the same haka healing process Win ma ba Waya bane. Normally waWanda su ka farfaWo daga coma su na shiga wani yanayi da ake cewa traumatic brain injury. Ya danganta idan aka gwada mutum a samu ko mild ne ko acute ko kuma severe. Ko da wanda aka yiwa induced coma ba sa farfaWowa a take su dawo normal. Wassu idan su ka farfaWo manta komai su ke tundaga magana zuwa tafiya zuwa duk wani abu da su ka iya da. A hankali-ahankali ana sake koya mu su sai brain Win su ya dinga picking da sauri, waWansu abun ma kafin a nuna musu sai su tuna da kan su. Najeeb ya fara tuna 'yan uwansa ne saboda sun fi kusa da shi. It will be odd ace daga farko-farko ya gane Farida tunda ba wai sun jima tare ba ne. Koda ya ke Najeeb Wan duniya ne zai iya ganeta ma ya waske=?? i dont know, ba ri mu bi su mu ga ya za ta ?are*


Najdah ne ta yi saurin cewa "she's your secretary" Daddy ya buge bakin ta.
Najeeb cigaba dai da kallon Farida yana son fahimtar miye ma'anar secretary da kuma dalilin da ya sa ita wannan secretary Win ta ke tareda shi koyaushe.

Dr Kenneth ya ce "za ka tunata a hankali. Yanzu ka tuna ya aka yi ka zo nan?"

Najeeb ya girgiza kai still idon sa na kan Farida da idon ta ke cike da hawaye amma tana ta dannesu kar su zubo.

"Ba ka san ya aka yi accident Win nan ya faru ba?" Najeeb ya sake girgiza kai.

"Ka tuna wani abu a iya kasancewar ka cikin yanayi na coma?"

"I dont know, there was darkness, then voices then her eyes" ya faWa yana nuna Farida

"Za ka iya tuna voice Win da ka ke ji?"
Najeeb ya girgiza kai.
Dr Kenneth ya mi?a ma sa wani littafi ya ce duk abinda ya tuna ya rubuta a ciki.

Kafin Dr Kenneth ya fita sai da ya tabbatar mu su da kada su dinga damun sa da tambayoyi, su bari a hankali zai dinga tuno komai. Za dai su iya dinga yi ma sa labarin abinda ya ke so ko kuma su dinga nuna ma sa abubuwan da zai sa ?wa?walwar sa ta yi saurin dawowa dai-dai...

Najeeb ya buWe littafin ya fara zane. Idan akwai abinda ya farayi bayan ya fara iya ri?e biro to zane ne. Dan har yanzu ma rubutun sa bai dawo dai dai ba.

Dukkan su su ka zuba mishi ido su na ganin yadda ya ke zanen wani gida. Duk da freehand sketch ne hakan bai hana gidan ya fito da kyau ba. Da ya gama sai ya zana wata mace a bakin gidan tana murmushi wanda yanayin fiskar ya Wan yi shige da fiskan Farida.

Farida kam ba zanen ta ke kallo ba tana tsaye ne amma ta yi nisan kiwo. Tunanin ta bai wuce ya za ta ji idan aka ce kwata-kwata Najeeb ya manta da ita kuma ya kasa tunowa da ita.

"Aisha" mom ta faWa tana dafa kafaWarta. Ta Wanyi firgigit ta kalli Mom, Mom ta nuna ma ta Najeeb.
Idon ta ya sauka akan Najeeb da ke mi?a ma ta takarda. Hannu na rawa ta karSi takardar. Duban zanen ta yi sai ta fashe da dariya wanda ya sa hawayen da ta ke ta Soyewa su ka samu damar saukowa.
Shima Najeeb Win murmushin yai.

Ba abin da ya fi Waukan hankalin Farida irin abinda ya rubuta a ?asar zanen *Plz smile*

"Allah sarki yanajin ta ajikin sa ne fa" Daddy ya faWa yana shafa kan Wan na sa.

Najdah ta cika ta yi fam, tana ta hararan Farida ta gefen ido.

Mom ta ajiye album a gaban sa ta buWe tana faWin duk wanda ta tuna a ciki ya faWa. Hoton baby tana jinjira ne a farko, ya fi minti biyu yana kallon hoton kafin ya ce Baby. Gaba Waya sai su ka sa dariya.
Hoto na gaba kuma na shi ne yana Wan shekara huWu anyi hoton a wani amusement park ne yana cikin motan wasan yara. Wannan kam bai Wau lokaci ba ya nuna kan sa. Hoto na uku hoton shi da Sabreen ne lokacin da Sabreen ta yi graduation Win gama high school. Ya jima yana kallo, ya gane ta amma sunan ya ma?ale ma sa. Kusan minti huWu ya ce "Sa Sa Sabreen"...

Har lokacin da Farida ta zame jiki ta bar Wakin ba su ankara ba. Tafiya ta ke amma ba abinda ke yawo a ?wa?walwarta irin sunan da Najeeb ya ambata.
Wato ya iya tuna Sabreen amma ita bai tuna ta ba, Sabreen fa!...

Hoton Aisha aka buWe ma sa lokaci guda idon sa ya fara kawo ma sa hoton ta kwance cikin jini. Dafe kan sa yai yana numfashi da ?yar nan kuma seizure ya kama shi ya fara jijjiga. Su Najma su ka fita kiran likita, bayan seizure Win ya tsaya Dad ya gyara ma sa kwanciya ya maida shi kwance ta gefen sa...


...................

Tana zuwa Wakin su gado ta hau, kukan ma da ta ke son yin ma ta kasa. ZazzaSi ne ya rufeta tun tana rawan sanyi har bacci ya tafi da ita. A ?alla ta yi awa uku tana bacci kafin ringing Win wayar ta ya tashi.

Ta Wau wayar tana mai goge gumin da ke goshinta da Waya hannun.

"Aisha ki na ina?"

"Ina gida Mom"

"Yaushe za ki dawo?"

"Sai dare"

"Ok"

Sai da ta ajiye wayan ta tashi da ?yar. Ko'ina a jikin ta ciwo ya ke a haka ta shige banWaki dan ta yi wanka...


Da dare da ta isa ta tarar da abun mamaki. Mom na tsaye gaban Najeeb tana hawaye tana bashi ha?uri, shi kuma ya kauda kai gefe.
Daddy baya nan dan ya bar asibitin tun da yamma. Najdah ne a wajen bayan Mom, itama Sallah ta ke yi.

Mom ta zagayo gaban Najeeb ta tsugunna har ?asa. Da gudu Farida ta ?arasa wajen tana ?o?arin Waga Mom.
"Mom so ki ke ki ja ma sa bala'i. Bai kamata ki tsugunna ma sa ba"

"Ki bar ni Aisha, ya tuno abinda na yi ya ce baya son ganina. Plz ki ce ya yafe min, ba zan iya rayuwa ba tareda ina kusa da shi ba"

Farida sai da ta tabbatar ta Waga Mom kafin ta sa hannu ta fara goge ma ta hawaye.
"Dan Allah ki dena kuka, kukan ki masifa ce a gareshi"
Da ?yar Mom ta iya haWiye kukan ta yi shiru.

Farida ta juya ta kalli Najeeb da ya ?ura ma ta ido, cikin Waga murya ta ce "kai Sir Najeeb, ka kiyayi fushin mahaifiyar ka. Kar ka ga dan kana cikin wannan yanayi ana tausaya ma ka ka maida mu bamu san mi mu ke ba, ka sanni sarai zafi gareni, kuma idan ba ka shiga taitayinka ba duk abinda ke cikin ?wal..."

"To kashe ma na shi. Munafuka, kin san yana cikin wani hali amma ba za ki bari hankalin sa ya kwanta ba, kashe shi tunda abinda ki ke so kenan, dan ki gaji dukiyar sa ko"


"Najdah!" Mom ta daka ma ta tsawa.

"Mom ki ga abinda ta ke ma sa fa, anan Wazu ya shiga wani hali saboda wani abu ya tuno amma yanzu ta dinga ma sa masifa kaman wani Wan ta"

Shikan ido ya ke bin su da shi. Yadda Farida ke masifa haka ya dinga ji ?wa?walwarsa na tuno ma sa wassu masifan da ta yi a baya. Abin ya confusing na shi, domin yana ta ?o?arin gano a ina abubuwan nan su ka faru kuma yaushe su ka faru.

"Ki tafi ki bamu waje zamu iya jinyar sa" Najdah ta faWa tana kallon Farida ido cikin ido.

"Yarinya kenan, ki je ki yi aure za ki fahimci minene tsakanin miji da mata. Jinya kuma ko uwar da ta haifeshi ba ta ma sa Wawainiyar da na ma sa ba."

"Mom kin ji maganar banzan da ta ke yi ko?"

Mom ta ce "gaskiya ta faWa. Babu wanda yai wa Najeeb hidima kaman ta, kuma ba abinda za mu saka ma ta da shi sai addu'a. She's the only one that never stop believing in him kuma na tabbata da ya yi shekaru a haka to a hakan Faridan za ta jira shi"

Najdah haushin maganan Mom da ta ji ya sa ta je ta Wau jakan ta fuuuu ta fita ko sallama???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? babu.


"Koyaushe haka ki ke da faWa?" Najeeb ya tambaya yana kallon Farida

"Haka na ke, a haka ka sanni dan haka idan za ka tuno ka tuno, idan ma ba ka tuno ba to zamu cigaba daga inda mu ka tsaya"


"Son please forgive me" Mom ta faWa tana haWa hannun ta alamar magiya.

"Ka san Allah Sir Najeeb ba inda za ta je sai ka ce ka yi ha?uri"

Dariya yarinyar ta bashi.
"A matsayin ki na wa?"

Confidently ta ce "a matsayina na matar ka"

"Mata na?" Ya tambaya looking confused

"Yes ni matar ka ce" ...


.........................

Bai gama yadda da maganar Farida ba sai da Washegari da Najdah ta zo ya tambayeta ya aka yi ya auri Farida ba Sabreen ba. Da ke tana jin haushin Farida ba ta faWi laifin Sabreen ba, sai ta ce Daddy ne ya aura ma sa Farida kuma ba son ta ya ke ba.
Maimakon ya bibiyi miya faru. Sai zuciyar sa ta fara kawo ma sa soyayyar sa da Sabreen, take kuma tausayin Sabreen ya kama shi. Sai dai kasancewa bai gama gane abinda ya faru da shi ba ya sa yai shiru...

Duk da ya tuno abinda ya haWa su da Mom amma tundaga ranan da Farida ta ma sa masifa sai ya dena Waure ma ta fiska amma dai still ya kasa sake jiki da ita.

A kwanan sa na talatin da bakwai da farfaWowa sai ga Sabreen. Shi da Farida da therapist Win sa ne a chan wani fili, yana gwada tafiya da walking stick Waya maimakon biyu da ya ke amfani da su da.

Najdah da Sabreen ne su ka nufo su. Sabreen na ?ara tabbatar wa idon ta ga Najeeb nan a raye kuma yana tafiya ta yanka da gudu ta je ta faWa jikin sa.

"Noory you're back, i miss you Noory, i miss you"

Ji ta yi an dam?i gashinta da ?arfi, dama Wan gudun da ta yi ya sa gyalen da ta yafa ya faWi.

"Ah Ah...Noory help" Sabreen ta faWa tana ?o?arin ?watan kan ta. Amma ba ?aramin dam?a Farida ta yiwa gashin ba.

"Wallahil Azim ko ki koma inda ki ka fito ko na lahira ya fiki jin daWi. Idan ma hauka ke kan ki to nawa sun fi na ki"

Ganin yadda idon Sabreen ya firfito, goshinta yai ja, jijiyinta su ka mimmike ya sa Dr Kenneth ya fara bawa Farida ha?uri akan ta sake ta za ta illata Sabreen.

Najeeb kam tsayawa yai a gefe yana kallon ikon Allah.
Da ?yar Farida ta ha?ura ta sake Sabreen wanda ta faWi ?asa tana numfashin wahala, har da hawaye.

Cikin zuciyar sa ya ke tunanin ashe Najdah ta yi gaskiya da ta ce ma sa Farida is mentally not stable.

Zuwa yai zai taimakawa Sabreen ta tashi. Farida ta ri?e shi " inka Waga ta na mutu kafira"
Bai Waga tan ba sai ma Dr kenneth ne da Najdah su ka Waga ta...

Ranan dai Sabreen ba ta sake dawowa ba sai washegari.
Duk zuwan ta gaishe shi sai dai ta zo da Najdah dai-dai lokacin da Mom ko Daddy ke wajen sa. Shegiya ta ji dam?an manya=??...

Har yanzu dai bai gama tuno komai ba, yadda memory Win ke dawo ma sa tsilla tsille ne ba direct ya ke tuno abu ba. Wani lokaci sai anyi magana sai abinda aka faWa ya triggering ma sa wani memory.

Yau ma magana ya ke da likitan sa a office likitan ya excusing kan sa yana amsa waya. Juyawar da zai yi ya kalli Tv da ke Wakin likitan sai ga Sabreen a cikin TV. A church su ke ana Waura ma ta aure da wani, bayan priest ya ce you may now kiss the bride sai ga shi Waya actor Win ya kama waist Win Sabreen su na kissing. Najeeb ya rintse ido wassu abubuwa na dawo ma sa....





*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0?? 4?? 1??





Dafe kan sa yai yana jin wani irin zogi. Komai ne ke son dawo ma sa lokaci guda. Likitan ne ya lura da yanayin sa.

"Are you Ok?"

Da kyar Najeeb ya Wago kan sa idon sa sun yi ja.

"Mr Najeeb ka dinga yi a hankali, kar ka takura wa kan ka, ahankali za ka tuno komai"

Najeeb ya gyaWa kai...


Tun bayan abinda ya tuno gameda Sabreen ?o?ari ya ke ya tuno ya su ka yi zaman auren su da Farida. Although Najdah ta gaya ma sa ba auren soyayya su ka yi ba, he still wants to remember something gameda auren su. Yawancin abubuwan da ya ke Wan tunowa gameda ita time to time bai wuce aikin su tare a office ba. Tun ranan da ya tuno abinda Mom tayiwa Aisha ya ke ?o?arin Soye wasu abubuwan da ya tuno. Ko ranan da ya tuno accident Win da yai bai gaya mu su ba, he pretends bai tuna ba.

Farida ce bashi abinci, su biyu ne a Wakin. Duk da yanzu yanada ?arfin jiki sosai zai iya cin abinci da kan sa amma Farida sam ta hana. Dole sai dai ita ta feeding Win sa, su yi ta daru akan rashin son cin abincinsa. Yana cin kaWan idan ya ce ya isa Farida za ta hau shi da faWa. Wani lokaci idan ta takura ya kan ?ara kaWan amma ma fi yawancin lokutan kau da kai gefe yakeyi ya ?i ci.

Yau ma Win ita ke bashi abinci.
"Aysherh" ya kira sunan ta. Ranan da ya fara kiranta da wannan suna ya ga farinciki da Woki tattare da fiskar ta, har da cewa "My Champ sake kira dan Allah"

Lokacin da ya tambayeta ko ya ya ke kiranta da kafin wannan abu ya sameshi ?in gaya ma sa ta yi, tace ya kira ta da Aishern kawai. Shi kam sai ya ke ji kamar ba Aysherh ya ke kiranta ba. Sunan a bakin sa ya yi daban, like there's more to sunan Aysherh da ya ke kira.

Yayi gyaran murya ya ce "Ehm Aysherh...Ehm....did we?" Ya sake gyaran murya
"Have we.....?"

"Ina jin ka mijina" ta faWa tana goge ma sa baki da tissue.

Wannan karan daurewa yai ya ce "lokacin da mu ka yi zaman aure da ke muntaSayin wani abu?"

Dariya ne ya cika ta amma ta gimtse ta ce "wani abu kuma?"

Sai da yai gyaran murya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login