Showing 141001 words to 144000 words out of 145791 words

Chapter 48 - Sakatariya Ta Book One Complete Hausa Novel

Azizat   

01 Nov 2025

339

sha ya fita har ya kusa kai wa bakin ?ofa ya dawo ya manna ma ta kiss a goshi ya ce " sai na dawo"

Sai alokacin Farida ta saki ranta ta ce " Allah ya kiyaye hanya ya dawo da kai lafiya" ya amsa da amin sannan ya fita...

Shiru- shiru har ?arfe uku Najeeb bai kira ba bai kuma turo text ba. Ina Kano da Kaduna ace tun bakwai saura da ya tafi bai isa ba. Da farko ta Wauka ko dan maganar jiya ne amma yanzu kam hankalinta ya tashi dan duk faWan da su ka yi ko text zai tura ma ta ya ce ya isa.
Ta fara kiran numbar sa switch off, ta kira numbar Abdullahi dreba shima switch off. Nan jikinta ya hau rawa ta shiga kiran Mom. Tambayar Mom ta yi ko Najeeb ya kirata ta ce ma ta a'a.
Cikin kuka ta ce "Mom ki tambayamin Daddy ko sun yi magana da shi"...


Zaune su ke a falon kowa yai jugum saboda rashin sanin halin da Najeeb ya ke, da shi da dreban sa duk wayoyin su a kashe.
Daddy dai baya nan dan ya fita kai report ko zai ji labari ko anyi hatsari hanyar Kano to Kaduna.

Najma na jijjiga Wan ta Bobo da ke kuka wayar Farida ta fara ringing Farida ta yi saurin tashi ta Wau wayar da ke kan centre table. Ganin My Champion ke kira ya sa ta fara murmushi.

"My Champ saura kaWan na mutu yau, ina ka shiga? Are you Ok"

"Yana nan lafiya idan har kun amince da sharuWWan mu" muryan wani ?ato ya doki kunnen ta.

"Waye, mi kuka yiwa mijina? Ina mijina?" Tambayoyin da ta fara jerowa kenan.

Jin maganarta ya sa Mom tashi da sauri ta amshi wayar ta sa a speaker tana faWin " ina Najeeb?, mi ku ke so"

Mutumin yai wata mahaukaciyar dariya sannan ya ce " Najeeb Adam Jibo yana nan lafiya until kun fanshi ran sa a wajen mu"

" what do you want?" Mom ta faWa tana danne hawayen ta.

"200million" ya faWa a ta?aice.

"Ka bawa Wana mu yi magana"

Mutumin ya sawa Najeeb waya a kunne.

"Mom i'm ok, ku kwantar da hankalin ku." Jin kukan Farida ya sa shi cewa " My Queen dan Allah ki dena kuka"

Mutumin ya ?arSe wayan ya ce " kun ji shi dai yana raye, nan da 24hrs idan ba mu ga kuWi ba za mu aika shi lahira" daga haka ya kashe wayan.

"Hello Hello" Mom ta faWa amma shiru, sake kiran numbar ta yi amma ta ji shi a kashe.

Farida ta dafa kafaWan Mom tana faWin "Kashe shi za su yi ko? Kashe min shi za su yi ko?"

?o?arin faWuwa ta ke yi Mom ta ri?ota tana kiran sunan ta amma....



*Jirgin SAKATARIYA TA yana shirin sauka jama'a, jirgin ya yi wata Waya da 'yan kwanaki yana lulawa a sararin samaniya kuma Alhamdulillah yana daf da sauka da daren yau Insha Allah. Da fatan Team Najeeb da Team Farida za su yi cincirindo a filin jirgi su ga saukan mu sannan su bamu masauki mai kyau. Wanda su ka supporting Wina by paying to read this novel Jazakumullahu khairan. Wanda su ka karanta ta bayan fage kuma...*




Skt 60


Haihuwa ne ya taso wa Farida gadan-gadan bayan sun kaita asibiti wurjanjan. Ba ?aramin wahala ta sha ba kafin ta haihu dan sau biyu tana suma a wajen. Lokacin da 'yar ta fito gaba Waya ta gama galabaita jinin ta ya hau sosai, ga azabar haihuwa ga kuma tashin hankali.

Saboda yadda ta rikice dole sai da su ka ma ta allurar bacci.
Tun a asibiti Mom ta kira Daddy ta sanar da shi halin da ake ciki daurewa yai ya ?araso asibitin dan hankalinsa ya mugun tashi.
Lokacin da ya iso Mom na Wauke da jaririyar da ke kama da uwar ta sak. Ya karSi jinjirar yana ma ta addu'a...

Bayan an tabbatar ma sa da lafiyar Farida ?alau sannan ya bar asibitin saboda ya je ya sanar da jami'an tsaro...

Wannan karan waWanda su ka kama Najeeb da Abdullahi ba ?ananun kidnappers ba ne domin duk yadda ake ?o?arin gano inda su ke abin ya faskara. Washe gari Daddy ya je bank aka fara ?o?arin cire kuWi, abu da manyan mutane cikin abinda bai fi awa uku ba aka gama haWa 200million...


......................


Ummi ce ke zaune gefen Farida tana ri?e da baby tana Wan shafa bayanta saboda kuka da ta ke yi. Yarinyar ba dai kuka ba, ga shi uwar ta ko ta kan ta ba ta yi, damuwar da ke ranta ya isheta.

"Farida ki karSe ta ki ba ta nono dan Allah. Ba ta da wani ?wari fa"

"Ummi idan su ka kashe shi mutuwa zan yi, ba zan iya rayuwa babu shi ba" ta faWa hawaye na bin kumatunta.

"Ba na son kina magana kamar wacce ba ta da imani. Rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah ya ke kuma zai kuSutar da mijin ki Insha Allahu. Tashi ma za ki bata nono dan Allah"

Da ?yar Farida ta iya mi?ewa zaune tana jin duk gaSoSin jikinta na ma ta ciwo, ta amshi jinjirar daga hannun Ummi ta fara ba ta nono har lokacin ba ta dena zub da hawaye ba.
Ummin ma tausayin 'yartata ne ya cika ta amma dole ne ta dinga ?arfafawa 'yarta gwiwa saboda halin da ta ke ciki...

A kwana na uku da haihuwar aka sallameta su ka dawo gida. Yau Win ne kuma kidnappers Win su ka ce za su sake Najeeb dan jiya aka aika mu su da kuWin su. ?arfe goma Mom, Farida da Ummi su ka iso gidan wanda ke cike da 'yan uwa. Kowa a wajen yana jimamin abinda ya faru ne ana kuma jiran dawowar Najeeb...

A hankali Mom ta taimaka ma ta ta zauna a bakin gado, har yanzu ba wai tana da ?arfin jiki ba ne kawai dai dauriya ta ke yi.

"Mom zan sha ruwa" ta faWi tana ?o?arin kwantawa akan gadon.
Mom ta ce tana zuwa. Ummi ta kwantar da baby a gefen Farida tana faWin "ta ma yi bacci ashe"


Tun safe ake jiran dawowar Najeeb har yamma shiru.
Ihun da gidan ya karaWe da shi ne ya farkar da Farida da ke bacci. A hankali ta buWe ido tana maida hankalin ta ga abinda ta ke jiyowa. Jin ana kabbara da faWin Alhamdulillah ya sa ta mi?e tsaye zumSur ta fita da gudu duk da kuwa yadda jikin ta ya ke very weak.


Tun daga stairs ta hango shi yana murmushi, an yi cirko-cirko ana kallon shi ana kabbara, gefen sa Daddy ne ri?e da hannun sa Waya, shima Win fiskar sa Wauke da murmushi. Tun da ta gan shi ta rage saurin da ta ke yi ta koma saukowa a hankali. Hajiya Fatima ce ta fara kallon ta ta ke cewa " Farida Alhamdulillah kin ga sun sake shi ko"

Tsayawa ta yi tana ?arewa mijin na ta kallo, kayan jikin sa ne tun na ranan da ya fita, kayan sun Wan yi bututu, akwai tabon ciwo a goshin sa da gefen bakin sa. Sai duhu da yai da alama bai ga ruwa ba a 'yan kwanakin nan.

?ago ido da zai yi ya kalleta tsaye ta zuba ma sa manyan idanun ta. A hankali ya cire hannun sa daga jikin na Daddy ya taka zuwa wajenta yana zuwa ya rungumeta tsam ajikin sa kamar zai shigar da ita ?irjin sa ne. Sun jima a haka kafin Farida ta iya cewa "it's a girl, your princess is born"

"Alhamdulillah ala kulli Haal" ya furta ya na sauke ajiyar zuciya.

A?alla sun yi minti biyu rungume da junan su. Hawayen da ya gani a fiskarta ne ya sa shi sa hannunsa duka biyu yana goge ma ta su yana faWin "Queen ba na son kuka please" sake shigewa ta yi jikin sa tana murmushi...

.......................

Su na shiga Waki ta sa key ta kulle. Kafin ma ta gama kullewa ya je wajen gado ya Wau 'yar sa da ke kwance tana bacci. Ya kissing goshin ta yana yi ma ta addu'o'i.

"She's beautiful, just like you"
Ya faWa yana kallon Farida. Ganin ba shi da niyyar ajiye yarinyar ya sa ta amshi 'yar a hannunsa ta ce mu je na ma ka wanka. Ta maida yarinyar kan gado kafin ta ja hannunsa su ka shiga banWaki. Ita ta sa hannu ta cire ma sa duk kayan jikin sa wanda ta san daga yau sun gama aiki dan ?ona su za ayi. Yana tsaye yana binta da kallo ta fara murza ma sa shower cream a jikin sa tana dirje dukkan jikin sa da shi. Da ta gama ta kunna shower ya wanke duk kumfan. Ta tsiyayi shampoo ta sawa gashin sa tana dirza ma sa especially scalp Win sa, Wan rankwafowa yai da kan saboda ta samu daman wankewa da kyau cause ya fi ta tsayi. Sai da ta wanke shi sau biyu a bakin shower kafin ta tara ma sa ruwan zafi a bathtube ta ce ya shiga ciki. Ya ji daWin ruwan zafin da ya shiga dan dama jikin sa na ma sa ciwo.

"I'm sorry my Queen" ya faWa ganin hawaye da ta ke yi.

"Ni ce zan ba ka ha?uri miji na. I'm sorry you are married to a crazy woman"

Dariya ya fara yi yana faWin "and i love my crazy wife"

Dariya itama ta yi tana cigaba da yiwa kafaWun sa massage...


..........................


Duk ?o?arin 'yan sanda ganin an kama wanWanda su ka kidnapping Najeeb abin ya ci tura. Kidnappers dai sun tafi da miliyan Wari biyu wanda biya kam sai dai a lahira.

Ranan suna anyi ?asaitacciyar walima, duk da anyi shagali amma bai kai lokacin sunan Yaman ba. Ko dan saboda abinda ya faru, oho.
Yarinya dai ta ci sunan Mom, an raWa ma ta *Nabeelah Zafreen*

Wannan karon a gidan Daddy aka yi suna, infact sai da aka yi sati uku da sunan ma kafin su ka koma gidan su.


.........................


Yau Monday ta fara fita aiki bayan Zafreen ta cika wata biyu a duniya. Tana duba wassu takardu Zafreen da ke kwance a gadon yara da ke office Win ta hau kuka.

"Kayya 'yar nan Allah ya miki albarka, shegen kukan kin nan ban san ya zan yi da ke ba." Ta faWa tana Waukan yarinyar.

Wayar office Win aka fara kira ta Wauki kiran.

"Hajiya, Architect Fauziyya na son ganin Ki" muryan Kabiru sakatare ya doki kunnen ta.

Kabiru ?anin mahaifiyar Anas ne. A ?alla zai kai shekaru talatin da takwas zuwa da tara. Sakandare kawai ya karanta, yana aikin masinja a wata makaranta kafin Anas ya ma sa maganar aiki a Najeeb constructions tunda Najeeb ya rufe Waukan sakatariya ma ce. Wata Waya ana ma sa training na aiki kuma ya Wauka sosai gaskiya, kafin ya fara yi mu su aiki.

Farida ta ce "ka ce ta shigo"...

Najeeb ba ya gari ya tafi Lagos wani taro.

Fauziyya ta gaida Farida a ladafce kafin ta ce " Ma ya jiki?"

"Da sau?i" Farida ta faWa fiskarta a sake dan yanzu ta yi wa kan ta faWa. Dama cikin Zafreen ne ya sake tunzura ta.

Fauziyya ta fito da IV daga jakarta ta mi?awa Farida. Farida ta amshi IV Win tana karantawa. Ta Wago ido da sauri ganin sunan da ke jiki.

Fauziyya ta yi murmushi ta ce " Ma, you have every reason to be jealous, ko ni na ke auren Sir Najeeb ba ?aramin kishin sa zan yi ba. He's handsome, rich and successful. Amma ki sani ban taSa son mijin ki ba, tun kafin na fara aiki anan an riga an ba da ni, lokaci kawai mu ke jira and now the wedding is in 12 days"

Cike da kunya Farida ta ce " ba dai za ki bar aiki da mu ba"

"No, i love my job, kuma dear ya amince na yi aiki anan matu?ar za a maida lokacin tashi na ?arfe Waya ko biyu"

"Kar ki damu za a rage miki. Wannan kamfani yana bu?atar ma su ?wazo irin ki"

Fauziyya ta mi?e tana faWin " na gode Ma"

Farida ta ce " dan Allah ki yi ha?uri abinda ya faru baya"

Fauziyya ta ce ba komai ya wuce...


..........................

Tun da su ka dawo daga sunan Zafreen ta ke jin jikin ta ba daWi. Ba ta son gayawa Lukman saboda kar hankalin sa ya tashi. Ciwon kai idan ta ce tana ji ranan za ka ga Lukman ya rikice yana ?o?arin ba ta kulawa na musamman. Yana son ta sosai yana kula da ita, she's really lucky da ta aure shi. Ya iya soyayya ga iya kula da mace, ba shi da zafi kwata-kwata. Cikin zaman auren su za ta iya irga lokutan da ta ga ransa a Sace hakanan ana Waukan wassu awowi za ka ga ya sauko ya koma normal. Itama Win ba ?aramin tattalin sa ta ke ba, cikin 'yan kwanakin nan ma tunanin samun haihuwa ta ke dan ta san shine kaWai abinda za ta yi ta sa Lukman farin ciki, ga shi har yanzu shiru. Wani lokaci sai ta ga ko dan shekarun ta ne, amma kuma ai mata na haihuwa har a fifties na su balle ita da ke talatin da biyar.

Ta tuno da lokacin da ake tsakiyar shooting wani film hajijiya ya kwashe ta ta faWi, da aka kaita asibiti aka ce tana da ciki. Ba?in cikin da ta ji a lokacin ba zai misaltu ba. Bayan kwana uku ta sayi wassu pills ta sha ranan ta yi bleeding kamar jinin ta zai ?are. ?arshe sai da ta yi jinyar sati biyu a asibiti Ta rintse ido tana hawaye....

Lukman na fitowa daga asibiti ya haWu Da Dr Jennifer wanda ta koma Dr Aisha. Ta jima da barin aiki da asibitin da ya ke, few months bayan ta yi aure.

Gaisawa su ka yi sama-sama har zai tafi ta tsayar da shi akan tana son magana da shi.

"FaWi maganar ki da sauri dan my wife na chan gida tana jira na"

Jikinta yai sanyi da jin kalaman sa amma ta daure ta shiga koro ma sa bayanin yadda mijin ta Dr Faisal ya wala?antata ya hana ta aiki ga shi ba ya wani kula da ita, ga matan sa da su ka sa ta a gaba akan ita yare ce kuma kafira wacce ta gama yawon titi. Wala?anci dai iri-iri, yanzu gashi ko wata shida ba ta cika da haihuwa ba ya saketa.

"Sorry ko, ya sunan babyn?" Lukman ya faWa cikin halin ko in kula.

"Fatima amma ta rasu few days bayan sunan ta"

Lukman ya ce " Allah ya sa me ceto ce amin. Barin je gida kar wife Wina ta jini shiru"

Ya wuce ya bar Dr Aisha cike da tarin nadama, yau da Dr Lukman ta aura ta tabbata ba zai taSa wala?antata haka ba, he'll love her and cherish her for the rest of his life, sai ga shi ta ?i auren Wan shege ta auri Wan asali kuma tana nadama...

Lukman na zuwa gida ya samu Sabreen na kela amai a banWaki. He's being suspecting pregnancy 'yan kwana biyun nan amma saboda rashin samun isashshen lokaci ya sa bai damu ya tsaya ya tabbatar da zargin sa ba. Bayan ya taimaka ma ta ta gyara jikin ta sannan ya fara duba ta. Daga idanun ta zuwa tafin hannunta kafin ya Waga rigarta yana sa hannu a mararta da cikin ta.

"What is it?" Sabreen ta tambaya ganin taSe-taSen yai yawa.

With excitement a fiskar sa ya ce " Lets confirm first"

Sai da ya tabbatar ta samu ?warin jiki kafin ya fita ya je ya siyo PT strip. Da ya dawo su ka gwada.

?aukan ta yai sama yana juyi da ita yana dariya bayan ya ga reading Win strip Win ya bada positive...

..........

Kwanci tashi cikin Sabreen ya cika wata tara inda ta sha wahala wajen na?uda ?arshe aka ce ba za ta iya haihuwa da kanta ba aka cire ma ta kyakykyawar jaririyar ta. Yarinyar sak ubanta hatta green eyes Win sa sai da ta Wauka, idan ka Webe farin Sabreen da ta Wauko ba abin da ta bari na Lukman.

Murna wajen Lukman ba a magana. Finally shi ma ya samu 'ya, 'ya ta sunnah.

Kwana biyu kafin suna Najeeb da Farida su ka dira a Abuja, tareda yaran su Yaman da Zafreen wanda ?iriniyar yarinyar yafi ?arfinta. Yayinda Yaman ya ke so quite ita wannan tun aciki ta ke sa uwarta masifa da ta fito ma tun tana 'yar jinjira ta ke nuna iya shegen ta balle yanzu da ta fara wayo. Idan mutum ya Wauketa ba ta so har cizo tana yi.

Ranan suna gaskiya anyiwa Sabreen da Lukman kara domin kuwa an zo dayawa, 'yan uwan Lukman ta Sangaren mahaifiyar sa duk sun zo, ga 'yan uwan su Najeeb da su ma su ka cika wajen.

Tsakanin ma'auratan su ka yanke shawaran sunan da za a sawa yarinyar. Farida kam ba ?aramin mamaki ta yi ba da Najeeb ya kira ta daga masallaci yana faWin sai ta kawo kuWin suna domin an samu *little Aisha Farida*

Bayan sun gama waya ta je ta Wauki 'yar tana ma ta addu'a. Sabreen da ke kwance sai murmushi ta ke yi...


..........................


Rayuwa na cigaba da tafiya shekaru sun fara ja domin kuwa an samu haSaka na arzi?i da iyali.
Najdah da Anas sun sake haifan mace inda su ka sawa 'yar su sunan *Aisha Amira* aka yiwa marigayiya Aisha takwara.

Farida ta sake haihuwan namiji bayan Zafreen ta cika shekara biyu su ka yiwa Daddy takwara *Adam * suna kiran sa da *Aasim*

Sabreen ma ta sake haihuwa bayan Little Farida, shima Win CS aka ma ta dan ance da wuya ta iya haihuwa da kan ta. Sun samu *Muhammad Mubarak*

Baffa Musa da iyalen sa na zaune lafiya kowacce ?o?arin faranta ran Wan tsoho ta ke. Amma alamu sun nuna Amina ta ci galabar sace zuciyar wannan tsoho, ilimi da wayewa sun sa duk abubuwanta sun banbanta da na sauran matan. Ba ta ganin tsufan sa kwata-kwata, duk ranan girkin ta haka ta ke birkitashi da salon ta na matan zamani wanda ya ke sa ya ji ina matan sa su ka shiga lokacin da sauran mata ke koyan dabarun sarrafa miji. Abubuwan da ya ke yi yanzu da wanda Ummi ke ma sa ko lokacin yana matashi bai samu wannan gatan ba.

Yakubu ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login