Showing 102001 words to 105000 words out of 145791 words

Chapter 35 - Sakatariya Ta Book One Complete Hausa Novel

Azizat   

01 Nov 2025

342

kafin ya ce "abun aure"

"Abun aure ai dayawa My Champ. Wanne a ciki?"

Ya marairaice ido ya ce "please Aysherh. Kin san abun da na ke nufi fa"

DaWi kashe ni. Abin da zuciyarta ya faWa kenan, wai Najeeb na hira da ita, hiran ma irin hiran su ta da.

"I'm serious Aysherh"

"Abubuwan aure ai dayawa My Champ. Akwai cin abinci tare, wanka tare, wasa da dariya tare, akwai kuma abubuwan da ake yi da dare, ko kuma ayi abun idan Waya ya ji abu sai ya ta?ali Wayan sai a haWu ayi abubuwa. So wanne aciki ka ke tambaya?"

Maganan nan ya tuno ma sa da wassu abubuwa amma har yanzu bai iya tuno ko sunyi abun da shi ya ke tambaya ba.

"So, we did everything that couples do?"

"Mun yi komai hadda gyara"

Zaro ido yai lokaci guda kuma ya sa hannu yana tare gaban sa.

Farida ta fashe da dariya tana faWin "to na nawa kuma. Bayan angama ganin komai"

Har lokacin bai Waga hannun sa ba ya ce " you're lying"

Tana cikin dariya Anas ya shigo.

"Wannan dariya haka, Farida ko dai ya tuno komai ne?"

Farida ta girgiza kai. As usual ya kawo ma ta wasu documents ne ta duba.

Anas ya gaida Najeeb wanda har lokacin yana kare gaban sa da hannu.

"Abokina ya dai? ko wani abu ya samu wajen ne?"

Pillow ya jawo ya sa a wajen kafin yai wa Anas wani mugun kallo.

"Mutumina ka godewa Allah da ya ba ka jarumar mace. Ba dan ita ba da kamfanin ka ta samu matsala"


"Ko a wanni duniyan ne secretary ta ke zama Oga oho?"

Ya kalli Farida da ido ya ce "what did you know Miss Salihu?"

Farida ta zaro ido, shi kuwa murmushin ya?e ya mata ya maida hankalin sa kan Anas.

Abubuwa dayawa ne ke yawo a cikin ?wa?walwarta. Kenan Najeeb ya tunata, komai ya tuna? ko kuma dai ba komai ba.

"Alhamdulillah mutumina. Ka tuna Miss Salihun ka, the stubborn Miss Salihu"

"Ko ba Miss Salihu ba ne ta sa min superglue a seat?"

Anas ya kwashe da dariya. Ita kuwa Farida jikinta ne yai sanyi.
Najeeb ba wai ya tuna abin ba ne da kan sa. Ranan ne Najdah ta nuna ma sa video Win da Anas ya nuna mu su ranan birthday Win sa, yana gani kuma wassu abubuwa su ka dinga dawo ma sa gameda Farida, musamman lokacin su na office...

Bayan Anas ya tafi, Farida ta ce " My Champ ka tuna komai ne?"

"The last time i remember ba da wannan suna ki ke kirana ba. What changed?"

Da gayya ya gaya ma ta haka, shima rama abinda ta ma sa Wazu yai.

"Saboda..." sai kuma ta kasa magana.

Ranan gaba Waya gwiwarta yai sanyi. Duk yadda ta yi dan ta fahimci ko ya tuno komai na rayuwar su amma ta ka sa. Sai ya dinga gwaleta idan ta tambayeshi...

Washe gari da safe ?arfe goma sai ga Lukman. Bayan ya yiwa Najeeb ya jiki sai ya ke faWa ma sa cewa gaskiya ya ri?e Farida da kyau domin ta ma sa abinda ba ko wacce macce ne za ta iya yi ba.

"Oh! and how do you know?"

Lukman ya ?a?aro murmushin dole ya ce "saboda na gani da ido na"

"Nagode da gaisuwa, Dr Lukman right?"

Lukman ya gyaWa ma sa kai tareda barin Wakin, chan ?asan zuciyarsa kishi na cin sa...


"Shi kuma wannan daga ina ya ke?" Ya tambaya yana tsare Farida da ido

Ba tareda ta kalli idon sa ba ta ce "he's my ex husband"

"Ashe ma bazawara na aura ban sani ba"

?ago rinannun idanunta ta yi tana ma sa wani kallo. Abinda ma zai ce ma ta kenan wai bazawara. Anya za ta taSa samun matsayi a wajen Najeeb musamman yanzu da bai gama gane kan sa ba...

...............................

Bayan anyi sunan Wan Maijiddah da kwana uku AbdulWahab ya koma Lagos. Bai samu Aneesa a gida ba, dama ta ce ma sa Abuja za ta je. A washe garin ranan da ya dawo ta dawo. Ita ba ta ma san ya dawo ba...

Tana zaune a falo tana kallo tana cin pringles sai ga kiran wata ?awar ta.

Bayan sun gaisa ?awar ke tambayarta ya kishiyar ta.

" shegiyar fa haihuwa ta yi, namiji kuma"

?angaren ?awar ta ke ma ta faWa akan ta yi sake da har ta bari Maijiddah ta haihu a gidanta.

"To ya zan yi Binta, kwanan baya har cikin ?arya na ce ina da shi dan na samu attention Win AbdulWahab kuma na samu a lokacin. Daga baya na mata sharri akan ta tureni cikin ya zube. Da farko ya yarda daga baya ya ?aryata zancen. I really dont know what to do again..."

Ko mi ?awar ta ce oho. Aneesa dai cewa ta yi "ni kin san ba na son shige-shigen nan. Ka je ma duk su ci kuWin ka a banza ba biyan bu?ata"

Jayayya su ka fara yi da ?awar akan zuwa wajen Boka, daga ?arshe Aneesa ta kashe wayan tareda cewa za ta yi tunani akai.

"Nonye....Nonye"
Ta fara kiran mai aikin ta. Jin shiru ya sa ta mi?e tsaye, ai kuwa da sauri takoma ta zauna daSas tana ri?e baki.

"Sweetheart" ta faWa baki na rawa.

Yana tsaye ya harWe hannuwan sa a ?irji yana kallon ta, idon sa yai wani irin ja.

"Aneesa why? Why? Ki rasa abinda za ki yi sai ?arya"


"I can explain AbdulWahab, please" ta faWa tana haWa hannuwan ta biyu.

"Wajen Boka ko, ki je Allah ya bada sa'a" yana faWin haka ya haura sama.

Jikin ta na rawa ta tashi ta bishi da sauri...

Buga ?ofar sa ta ke yi amma bai kulata ba balle ya buWe, ta zauna a bakin ?ofar tana ba shi ha?uri tana hawaye...

Kwanaki uku su ka gifta amma kalma Waya ba ta ji daga bakin AbdulWahab ba. Ta yi kukan ta bada ha?urin amma bai ma kulata ba balle ta san ko ya yafe ko bai yafe ba.
A rana ta biyar ya ce ma ta idan har ta zaSi zama da shi to za ta ajiye aikin ta ta zauna ta kula da shi da kuma yaranta, amma idan ta zaSi aikin ta to zai sawwa?e ma ta.

It was a very tough decision for her. Tana son AbdulWahab tana kuma son aurenta. Duk da dai ta san ba ?aramin asara za ta yi ba idan ta ajiye aiki amma kuma ba za taSa zama bazawara saboda aiki ba. Ta kira Mama neman shawara, inda Maman ta ce ma ta ta zaSi abinda ta ga ya fi ma ta, amma ta sani ba za ta taSa samun wani miji kamar AbdulWahab ba musamman ma a shekarun da ta ke yanzu.
?arshe dai shawaran da ta yankewa kanta shine ta ajiye aiki...

Duk da ta ajiye aiki hakan bai sa AbdulWahab ya koma ma ta kamar da ba. Cewa ma yai ta je ta bawa Maijiddah ha?uri. Girman kai ba zai bar ta ba, ta girmi Maijiddah sosai, kusan shekara shashida ta bata. Da ta ga uwar bari dole dai sai da ta kira Maijiddan a waya ta ba ta ha?uri. Maijiddah kam ta yafe tuntuni tunda mijinta ya gane gaskiya kuma ya yarda da ita ai an wuce wajen... kafin Aneesa ta samo kan mijinta sai da ta kai wajen wata Waya...



.................................


Yau aka sallami Najeeb daga asibiti bayan kwanaki hamsin da huWu da yai da farfaWowa. A report Win da su ka bayar sun nuna cewa ba shida matsala, a hankali zai dawo da dukkan ?arfin sa, haka kuma bisaga tambayoyi da kuma shaidar 'yan uwansa sun tabbatar da cewa ya tuno kaso tamanin na rayuwar sa ta baya kuma a hankali zai ?arasa tuna komai...

Gefen sa na dama Farida Wayan kuma Najdah a haka su ka fito daga asibitin Daddy da Mom kuma na gaba farinciki yana nan tattare da fiskokin su. Motar Farida su ka shiga, yadda Najdah ke ma?alewa Najeeb ba dan su Daddy na wajen ba da ta gaya ma ta maganar banza.

Maimakon Najdah ta bi motar su Daddy sai ta shiga tasu motar.
Su uku ne a baya sun sa shi a tsakiya.
"Dan Allah ki fita ki bamu waje, mata da miji suna son ganawa da junan su"

"Wayaga mata. Ba inda zan je. Yaya na son kasancewa da ?anwar sa"

"Tunda sirrin miji da mata ki ke son gani, Bismillah" ta faWa tana hawa kan cinyar Najeeb, kafin ya ce wani abu ta haWe bakin su, yana so ya tureta daga jikin sa saboda Najdah da ke motar amma gangan jikin sa ya betraying Win sa. Maimakon ya tureta sai ma ?ara matseta yai a jikin sa, yayinda kuma hannunsa duka biyu su ka fara yawo tsakanin bayan ta zuwa hips Win ta.

"Dreba tsaya zan fita" Najdah ta faWa tana jan tsaki.
Sun fito daga gate Win asibitin kenan ko nisa ba su yi ba.
Ya samu waje yai parking

"Karuwa kawai" ta faWa tareda banko mu su ?ofar motar.
Abdullahi dreba ya fara dariya ?asa-?asa yana faWin "to kema miji ya kwanta a asibiti tsawon watanni ba lafiya, yanzu ya samu lafiya ki zo ki li?e ma sa, ai duk abinda ki ka gani ke ki ka jawo"


Lokacin da ta ji Najdah ta fita ta fara ?o?arin janye bakinta.
"My Champ" ta faWa cikin sar?ewan numfashi tana nuna ma sa ?eyar dreba wanda bawan Allah kam kiWa ma ya sa a motar ya ?ure volume sosai, dan kar kunnen sa ya jiyo ma sa ba dai-dai ba.

Kallon-kallo su ka fara yiwa junan su, idon Najeeb yai wani ja guguwar sha'awa ta bugeshi.
Ya san a mota su ke amma kuma duk wani ?o?arin hana jikin sa aikata wannan abu ya ka sa, jikin sa har rawa ya ke yi. ?o?arin tashi ta ke yi daga jikin sa gaba Waya. Ya maidata da sauri, "My Ch..." Najeeb bai bari ta ?arasa ba ya jagoranci wannan kiss Win, wannan karan da zafi zafin sa ya ke yi, ya cire Wankwalin ta ya sa hannun sa cikin gashin ta yana shafawa. Kafin ta ankara yai wani juyawa da ita sai gashi tana ?asa yana samanta still bakin su haWe da na juna. Ta san glass Win motar tinted ne amma kuma ko da Abdullahi dreba bai juyo ya le?a su ba, ya san dole su na aikata wani abu a bayan motar.

?o?arin zuge zip Win doguwar rigarta ya ke ta yi saurin ri?e hannun sa. "A mota mu ke My Champ" ta faWa lokacin da bakin su ya rabu. Ya jima yana kallon idon ta kafin ya tashi daga kan ta. Itama Win tashi ta yi ta Wau Wankwalin ta tana Waurawa. Tunda ya juyar da kam sa gefe bai sake juyowa ya kalleta ba, numfashi kawai ya ke saukewa da sauri sauri. Ita kan kwantar da kanta ta yi a kafaWar sa tana ayyana abubuwa dayawa a ranta...

Najdah kiran Mom ta yi akan su dawo su Wauketa, da ke motar su ta riga ta yi nisa.
Cikin Daddy da Mom ba wanda ya tambayi dalilin da ya sa ta sauka a motar su Farida. Tunda dama tun farko bai kamata a ce ta shiga ba. Ta zauna a gaban mota sai tsaki ta ke yi tana ?ara jin tsanar Farida. Ita fa tun day one da ta ga Farida yarinyar ba ta mata ba, balle yanzu da ta ke jin ina ma tanada yadda za ta yi ta raba Najeeb da Farida saboda tsanar da ta ma ta...






*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0?? 4?? 2??






Motoci ne cike ma?il a compound Win gidan lokacin da su ka shigo.
"Ya na ga gidan ya cika haka?"

Juyowa ya yi ya kalleta kallon irin kin fini sani ai.

Wayarta ta Wauko ta kira numbar Mom.

"Mom gidan a cike sosai kaman wanda ake biki?"

"Dear, Walima ce za'ayi"

"Oh"

"Gamunan ma mun iso"

Katse wayan ta yi tana jira motar su Daddy ta shigo.

"My Champ" ta kira shi a hankali

?aga ma ta gira yai.

"Wai an shirya ma ka Walima. Yadda aka cikan nan na san za ayi hayaniya, ko mu wuce kawai ka je ka yi wanka ka kwanta?"

Girgiza ma ta kai kawai yai.
Sai da Mom ta zo ta ?wan?wasa mu su window kafin su ka buWe ?ofa su ka fito. Yana fitowa daga motan ya fara kallon gidan na su. Tabbas ya tuna gidan, hakanan kuma ya tuna cewa shi ya zana gidan, lokacin ma yana degree Win sa na farko ne.

Wannan karon Daddy ne ya kama hannun sa su ka nufi hanyar garden inda aka shirya Waliman.
Farida kam cikin gida ta wuce bayan sun yi musayar harara ita da Najdah.

Tana shiga ta tadda ba?i sun cika falon ?asa, kusan ba zai fi mutum biyu ta gane a ciki ba sauran duk ba?in fiska ne a wajen ta. A tsanake su ka gaisa kafin ta haura sama.

Wanka ta yi da ruwan zafi saboda jikinta da ke ma ta ciwo. Bayan ta fito ta shafa mai ta Wau wata atamfar ta riga da skirt ta sa. Dariya ta farayi lokacin da ta kalli kan ta a madubi ta ga yadda kayan ya ma ta ruwa. Gaskiya yanzu kam ta yarda ta rame sosai. Cire kayan ta yi ta je ta Wauko wani Anarkali gown kalar abin cikin ?wai, zanen adon flowers da ke jikin kayan kuma ja. Ba wani kwalliya ta yi ba powder ce kawai da kwalli, sai ta Wan goga jan lipstick kaWan a lips Win ta. Tana yafa gyalen tana murmushi. Ta ya ba za ta yi farin ciki ba, taya fiskarta ba zai zamo ma'abocin murmushi ba akoda yaushe. Kaman yau fa ta ke cikin nishaWi saboda first kiss Win su, gashi duk da matsaloli da su ka fiskan ta, duk da ?addara da ta afka mu su. Allah ya sake dawo da wani ranan da su ka sake sharing kiss. Akwai lokutan da ta ke jin kaman ba zai tashi ba amma sai ta dake ta dinga maimaitawa kanta cewa ita da Najeeb akwai rayuwa mai tsawo a gaban su, rayuwa mai tarin farinciki da annashuwa, rayuwa da za su ga 'ya'ya da jikokin su.
Wani abu ta tuno da ya sa ta rufe fiskan ta tana murmushi. Tana kuma fatan Allah ya sa wannan rana ta iya jurewa ta daure ta faranta ma sa rai sosai...
Kiran Ummi ne ya katse ma ta dogon tunanin da ta tafi.

"Mun iso gidan na ku ki fito ki shigo da mu"

"Ummi na yaushe a gari? Shi ne ba ki ce za ki zo ba"

"Ba na son surutu ki fito yanzu, ba ni Waya ba ne harda su Baaba Sabuwa"

"Yeeeeh, ganinan zuwa"...


Taro ne da ya haWa manya-manyan mutane, 'yan uwa da abokan arzi?i. Wanda aka gayyata da wanda su ka zo gayyar soWi duk an cika garden Win ma?il. Manya manyan tents huWu aka kafa amma sun cika ma?il har ma wassu ba su samu wajen zama ba.
Abinci kam Masha Allah domin anyi varieties kala-kala, caterers aka Wauko su ke serving mutane abincin.

Malami aka kira ya fara buWe taro da addu'a kafin Daddy ya yi jawabin godiya da kuma farinciki da ya ke ciki a yau. Daddy yai hawaye lokacin da ya ke bayyana halin da su ka shiga da Najeeb ya shiga coma, tun ana irga kwanaki da satuttuka aka koma irga watanni, daga ?arshe ma da Allah ya tada shi sai da aka yi kusan wata biyu cur kafin ta kai har yau yana tafiya normal, yana magana yana kuma gane mutane, gaskiya abin godiya ne. Bayan ya gama jawabi aka kira Najeeb. Najeeb ya karSi mic yai ta?aitacciyar jawabi wanda godiya ce ga dukkan wanda su ka taya shi da addu'a da kuma wanda su ka dinga ware lokutan su mai muhimmanci su na zuwa dubashi a asibiti bayan sun san ba ganin su zai yi ba balle ya ji su. Har ya mi?awa MC mic Win sai kuma ya ?arSa ya ce "Aysherh Farida Salihu should please come here"

Farida na zaune kusa da su Ummi ta ji abinda ya ce. Dama tunda ya fara magana hankalin ta ke kan shi.

"Mrs Jibo" ya sake kira.

Du?ar da kan ta ta yi tana ?o?arin danne hawayen da ke shirin zubo ma ta.

"Farida ba za ki je bane?" Muryan Ummi ya doki kunnen ta.

"Mrs Jibo please come out" ya sake maimaitawa.

A hankali ta ke tafiya kan ta a ?asa, ba wai kunyan mutanen wajen ta ke ji ba. Abubuwan da su ka faru ne su ke mata zirya a ?wa?walwar ta.

Tana isowa wajen da ya ke ta Waga ido ta kalleshi, shi ma Win ita ya ke kallo. Hannunta Waya ya kama ya jawota kusa da jikin sa sosai.

"Ga wanda ba su san wacece wannan ba, ko su ke tunanin minene ala?ata da ita. To dai Aysherh Farida Salihu sakatariya ta ce"

Wurin ne ya Wau hayaniya, domin dayawa sun san Farida matar sa ce.

?an murmushi Najeeb yai wanda ya ?ara bayyana kyaunsa.
?irjin Farida ya fara bugawa da sauri-sauri.

"Then she became my wife. Auren mu bai cikata wata biyu ba na yi hatsari na shiga coma, i was unconcious for months. Kun san mi ta yi?"

Aka haWa ba ki aka ce a'a

"Ta jira ni, ta kula min da gida da dukiya, ta aiwatar da duk wani responsibility da mata za ta yiwa mijin ta. Ba ta gujeni ba, ba ta ?yamace ni ba, ba ta kuma nemi rabuwa da ni ba in my vulnerable state. Ba ko wace mace ba ce za ta iya abinda Aysherh ta yi. Ina so ku sani cewa Aysherh jaruma ce, she always fight and she always win"

Ya kalli Farida da ke kallon ?asa idon ta na hawaye, ya sa hannu Waya ya goge ma ta hawayen da ke fiskar ta.

"Thank you Aysherh, Thank you for everything"

Fashewa ta yi da kuka me haWe da dariya, Ya jata jikin sa ya rungumeta. Gaba Waya wajen aka sa tafi...

Anyi ruwan hotuna kam kamar ba gobe har sai da Najeeb ya gaji da tsayuwa. ?arshe da ya ji hajijiya na kama shi ya excusing kan sa ya bar wajen.

Yana ?o?arin shiga gida sai ga Sabreen ta biyoshi.

"Noory"

Juyowa yai ya kalleta yana jin haushinta na taso ma sa tun daga ?asan zuciyar sa.
Lokacin da ta iso ya yi ?o?arin sake fiskar sa ya ce "Sabreen"

"Noory na san na yi laifi a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login