Showing 36001 words to 39000 words out of 145791 words

Chapter 13 - Sakatariya Ta Book One Complete Hausa Novel

Azizat   

01 Nov 2025

352

banban duk da kuwa sunan su Waya....



***

Aisha Mustafah Jibo ta taso cikin soyayya da kulawar iyaye da 'yan uwanta. Kasancewarta kurmiya bai rage ma ta komai ba na jin daWi a wajen iyayenta. Gata kam tana samu tun daga kan Alhaji da yayyanta ga uwa uba uwar da ta shayar da ita wato Hajiya Mama.

Karatu mai zurfi Alhaji Mustafah ke so Aisha ta samu saboda ya zamo ma ta gata ko ba sa raye, wannan ya sa ya turata ?asar waje karatu wajen yayanta Adam. Komai cikin sau?i Adam ya nema ma ta tundaga dreba zuwa ma su kula da ita a gida saboda shi da Nabilah ba zama su ke ba. Sabo mai ?arfi ya shiga tsakanin Aisha da yaran Adam musamman Najeeb wanda ke da shekara tara a lokacin. Kamar wata babbar yayarsu su ka Wauketa hakanan itama ta kan zama yarinya acikinsu duk da ita Win ma ba wai ta girme su da yawa bane dan shekararta goma shabakwai.
Yaran da sun dawo daga makaranta su na ma?ale da ita, za ka gansu da biro da takarda suna hira da Aisha ko kuma suna wasa. A hankali har su ka iya maganan kurame ya zamo idan za su yi magana ba sa bu?atar su rubuta sai dai su yi yaren kurame.
Shekaru biyu kenan da komawar Aisha wajen Adam. Duk hutun ?arshen shekara ta ke zuwa gida amma su Alhaji da Hajiya Mama su na kawo ma ta ziyara lokaci zuwa lokaci. A wannan ?arshen shekaran da ta je ta tarar Alhaji ba lafiya. Nan ta tubure akan ba za ta koma America ba sai dai ta zauna kusa da Baban ta.

Adam daga Belgium ya taho dubiyan Alhaji saboda a lokacin an maida shi chan. Zuwan sa kuwa ya tarar jikin Alhaji yai tsanani. Shi da su Sulaiman su ka fara yun?urin yadda za a yi su turashi ganin likita a ?asar waje sai dai shi Alhajin ya ce ba inda zai je. Ana gobe Adam zai koma Alhaji ya nemi alfarma a wajen sa duk da alfarmar ta zo ma sa bazata amma Alhaji ya fi ?arfin haka a wajensa dan haka ba tareda ya ja ba ya amince. A yammacin ranan aka Waura auren Adam Usman Jibo da 'yar uwar sa Aisha Mustafah Jibo. Washegari ya koma saboda jikin Alhajin ya fara sau?i dan an sallamoshi daga asibiti.
Kwana uku da tafiyar Adam, Alhaji ya rasu mutuwar da ta girgiza 'ya'ya da 'yan uwansa musamman Aisha.

Sai da aka yi da gaske kafin Aisha ta yarda ta koma karatu duk da kuwa ta san da auren Adam a kanta dan Alhaji ya gaya ma ta kafin ya rasu.

Larabawa da shegen ba?in kishi, tunda Adam yai wa Nabilah bayanin aurensa da Aisha sai ta tuSure ma sa ta ce ita ba ta san zan ce ba. Sosai abin ya jawo rikici tsakanin su.
A da ba ta shiga harkan Aishan dan ba ta da lokacin ta amma tunda ta zamo matar Adam sai abin ya chanja, kullum cikin tsangwamarta ta ke. Ta kori dreba da mai kula da ita da Adam ya Wauka ma ta, ta hana yaranta kulata amma Najeeb bai daina ba sai ma ?ara jin son Aishar da ya yi.
Lokaci guda Aisha ta chanja kullum sai ta yi kuka a Soye saboda indai Najeeb ya ganta cikin Sacin rai to sai ya yi ta tambayar ta dalili haka shima ranan ba za a gane ma sa ba.
Allah-Allah Aisha ta dinga yi ta gama makaranta ta bar mu su gidan ta koma Nigeria.
Shi Adam a nashi Sangaren duk lokacin da ya zo yana ?o?arin ganin komai ya tafi dai-dai sai dai ita Aisha ba ta nuna ma sa tana cikin matsala haka nan Nabilah ma tana nuna komai na tafiya dai-dai.
Ganin ba abinda ya ke shiga tsakanin su ya sa Nabilah ta Wan saki ranta kaWan, sai dai shi a nashi Sangaren ganin Aisha na karatu ya sa ya bari har sai ta gama tukunna ya tare da ita.

Wani hutu, Nabilah ta Wau Najeeb da Najma ta wuce da su Bahrain wajen iyayen ta. Sai aka bar Aisha a gida.
Aisha tun tana tsoro har ta dena, kwana uku da tafiyar su Adam ya zo ya Wauketa ya wuce da ita Belgium.
Ya kira Nabilah ne sai Najeeb ya Wauka ya ke shaida ma sa ai sun bar Aisha ita kaWai a gida kuma itama ta gama jarrabawarta.

A Brussels babban birnin ?asar Belgium su ka sauka. Ba su tsaya ko'ina ba sai gidan shi. Ha?uri ya dinga ba ta na barinta da aka yi ita kaWai.
Da dare ya zo dubata a Wakin da ya sauketa sai ya samu tana kuka. Hankalinsa a tashe ya ce " Aisha mi ya same ki?"

Ya Wauko biro da takarda ya ma ta rubutu. Ya mi?a ma ta biron akan ta rubuta ma sa amsa. Ta amshi biron ta rubuta " ina so na je wajen Mama"

" ba kya son zama da ni ne? Kin tsane ni ko? Saboda ba na zama ina kula da ke" ta yi saurin girgiza kai bayan ta karanta.

Jawota jikinsa yai ya rungumeta sosai ya na Wan bubbuga bayan ta a hankali har bacci ya saceta...

Wannan sati ukun da ta yi a Belgium cikin gata da kulawa ta yi su. Adam yana tare da ita koyaushe, harta office mafiyawancin lokuta da ita ya ke zuwa. Har 'yar ?iba ta yi saboda kwanciyar hankali.

Da hutun ta ya ?are ya maida ita lokacin su Nabilah sun dawo. Ita da ta dawo ba ta ga Aisha ba, ta Wauka Nigeria ta wuce sai da ta ga Adam ya dawo da ita hankalinta ya tashi. Ta san yadda ta gansu akwai abinda ya shiga tsakanin su nan da nan ta nuna sai dai Adam ya rabu da ita ba za ta iya zama da kishiya ba ko kuma ya rabu da Aisha.

Rikici sosai su ka yi har ya ma fi na farkon lokacin da ya ce ma ta ya auri Aisha.
?arshe ta ce za ta shigar da shi ?ara a raba auren tunda ba zai saketa ba. Ta chanja gida ta Wau yaranta amma Najeeb ya gudo ya koma wajen Aisha.

Abu sai ?ara rikicewa ya ke, wata rana da ta zo Waukan Najeeb sai ta lura da ciki ajikin Aisha, wannan ya sa hankalinta ya kuma tashi. ?arshe ta shigar da Adam ?ara, ganin ya ba da ha?urin ta ?i ha?ura ya sa ya ma ta saki Waya dan mutum mai matsayi irin na sa ace yana hayaniya da matarsa a kotu ba dacewa bane...

Ma su aiki biyu Adam ya Waukawa Aisha dan su dinga kula da ita lokacin cikinta ya girma.

Lokacin da cikin ta ya shiga wata na takwas Hajiya Mama ta ce za ta zo ta zauna da ita, ta shirya zuwa sai aka ma ta rasuwa Babban yayan su ya rasu sai ta Waga tafiyar zuwa wa ta sati....



***

"Sir Najeeb, Sir Najeeb"

Muryan Farida ya dawo da shi daga dogon tunanin da ya ke.

"Sir ka na da meeting ?arfe tara"

"Ok" kawai ya faWi ya mi?e tsaye.

Yanayinsa kaWai ya nuna ma ta akwai abinda ke damun Najeeb, kuma koma minene to yana da girma.



*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0?? 1?? 4??


Tana zaune a office Faru? ya kirata wai gashi a kamfanin su. Kwatancen office Win ta ta ma sa sannan ta ajiye wayar tana cigaba da aiki. Minti biyar kacal sai ga Yakubu da Faru? sun shigo.

"Farida haka yaron nan ya zama lu?e?e. Kin san da farko ban ganeshi ba"

"Kai ma ka faWa ai, wannan sai ya goyeni yai yawo da ni duk faWin garin nan bai gaji ba"

"Haba Anty, Wan ni Win nan" Faru? ya faWi yana dariya

Yakubu ya fita ya basu wuri, dama wajen Anas zai je ya haWu da Faru? Win.

'Yan uwan biyu su ka zauna su na taWi, su na yi su na dariya.


Wayar Farida ya ?arSa ya na duba hotuna. Ko ba a gaya ma sa ba ganin hotunan selfie da Farida ta yi da wani saurayi ya tabbatar ma sa shine Rayyan.

"Sis, wannan shi ne sirikin na mu ?"

"Kai ba na son gulma"

"Wallahi ba ku da ce ba, wannan ai kin fi ?arfinsa. Hmm ina tausaya ma sa wallahi, aka yi auren nan mijin ta ce zai koma dan ba zai iya da masifar ki ba"

"Buuuuyagi" wafce wayan ta yi tana faWin " ka ji min rainin hankali, wato dai ni ka ke zagi ko" ta maki kafaWar sa ta ce " Faru? yaushe ka raina ni haka?"
Yarfe hannu ta farayi shi kuma ya fara dariya. " jikin ka kamar wani katako, wai yaushe ka girma ne haka? Faru?"

"Serious Anty Farida ba k???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i dace da shi ba, kin ga lokacin Lukman..."


"Faru?!" Ta faWa da ?arfi.

Ya haWa hannu ya ce "afuwan Anty na ta kai na"

HaWe fiska ta yi ta tsume.
Faru? ya sa hannu ya fara tattaSa kumatun ta yana tsokanarta kaman yadda yake yi lokacin suna yara.
"Anty kumatu, Anty Kumatuttu"

Ba ta san lokacin da dariya ya kuSuce ma ta ba.
"Yaron nan ka mugun raina ni wallahi"

Yai dariya ya ce " na tuna da, lokacin idan na ce mi ki Anty Kumatu har ma?ota sai anji faWar mu"

Ta fara dariya sosai harda kama ciki.

Faru? ya cigaba " lokacin tunda na gano bakya son sunan sai na samu abun tsokala. Kin tuna lokacin da ki ka kwaWa min tukunya har goshi na ya fashe?"

"Ai ranan Ummi ta zane ni kamar ba gobe" ta faWa cikin dariya. Suna cikin dariyan kakkausan muryan Najeeb ya doki kunnen ta.

"Miss Salihu"

"Sir" ta faWi tana mi?ewa tsaye.

"To my office"

Ya jima tsaye yana kallon su tun daga lokacin da Faru? ya ke shafa mata kumatu. Zuciyar sa ta yi ba?i haka nan idon sa ya kaWa yai ja, a take ?wa?walwarsa ta tariyo ma sa sunan da ya gani ranan *My Ray*
Ta ya za ta kawo saurayinta har office tana iskancin da ta ga dama. Enough is enough dole ya taka ma ta birki. Abinda zuciyarsa ta tsayar kenan dai-dai lokacin da Faridan ta shigo.

"Ga ni Sir" ta faWi a hankali

Da ?arfi ya fara masifa "Miss Salihu yaushe ki ka maida office wajen soyayya da iskanci?. Listen young Lady, idan ba ki san yadda za ki kama kan ki ba go and get married. Ki dena mayar min da office wajen karuwanci. And i..."

"Sir Najeeb ba fa ni na kar zomon ba balle a bani ratayar sa. Daga ?ani na ya kawo min ziyara sai ka maidashi wani zancen banza wai karuwanci. Ba Karuwanci ba a'a Kwartonci"

Kalmar *?ani na* da ya ji shi ya sanya duk wani masifar da ke cinsa ta washe, cikin Wan ?an?anin lokaci kamar kiftawar ido, muryar sa da yanayin sa su ka chanja. Cikin sanyin murya ya ce "Miss Salihu, da ?anin ki da saurayin ki, nan ba wajen ziyara ba ne"

Haushin sa da ta ji kaman ta makeshi takeji sai dai yanzu ba ta son samun matsala da shi dan ankusa biyan albashi, ?aramin aikinsa ne ya cire mata wani kaso a ciki.

"Zan iya tafiya?"

Yai ma ta nuni da hannu. Sai da ta fita ya sauke numfashi. Cikin zuciyarsa yana cewa to ma miye ruwansa idan ma saurayinta ne?.


Tana zama ta yi tsaki " shi komai masifa, yai wa mutum kyakykyawar fahimta ba zai yi ba"

"Sis Ogan kin nan ya burgeni fa. Saurayi da shi amma ya mallaki babban kamfani kamar wannan, gaskiya na jinjina mi shi"

"Ko za ka je ya baka aiki ne. Nan za ka san wannan saurayin zuciyar dutse gareshi"

"Oh really"

"Hmm ai ni ma ba dan bana barin hau ta hauni ba da tuni an jima da fatattaka ni"

"Kai Masha Allah, wa su kam Allah ya basu duniya, ga shi handsome, ga kuWi, ga class..."

"Zan make bakin ka Faru?u"

Dariya yai ya ce " Jiya na yi mafarkin kin auri wani millionaire. Wai gamu a wani haWaWWen mansion, wai nan ne gidan ki"

"To Sayyadi Sheikh Umar Faru?, ma su mafarkin waliyyai"

"Da gaske fa Anty Kumatu"

Ta Wau wani littafi za ta buga ma sa ya kauce yana dariya...



...................


Wannan karan ba ta yi garajen barin wajen aiki ba dan ta san yana Waya daga cikin babban dalilin da ya sa Najeeb ya rage albashinta a watan farko da ta fara aiki. Ranan Laraba ta tambayeshi leave Win kwana biyu ya ce ya bata kwana Waya. As usual sai da ta yi ?orafi amma bai kulata ba.
Wannan karan bayan Walima ba abinda za'ayi. Baffa yai iya ?o?arinsa wajen yiwa Maijiddah kaya, duk da bikinta ya zo ma sa cikin matsi.
Ranan Alhamis aka je yi ma ta jere, su Farida ne 'yan gaba-gaba wajen ganin komai ya tafi dai-dai. Gidan yana da kyau sosai, tana da Wakuna biyu na ta sannan an ware ma ta kitchen daban sai dai store ne za su haWa da Aneesa...

Gidan ya cika saboda gobe ne walima jibi Asabat kuma a Waura aure. Farida tun da su ka dawo daga wajen jere ba ta samu zama ba, shiga ta yi cikin ma su haWa kayan waliman gobe ana aiki da ita.
Cikin ma su aikin cupcake ta ke ana yi ana hira. Chan wata 'yar uwar su wanda ita kan ta Faridan ba ta san takamaimai ta ina su ka haWu ba ta ce " Ikon Allah, kaman ba yau aka yi hidiman bikin Farida ba, na tuna cake Win da aka yi ranan mai daWi, su Talatun Haruna ne su ka yi cake Win nan ko?"

Farida ta fusata da wannan zance. Ta mi?e tsaye " Inna Tabawa ki ke ko wane. Wallahi ki ri?e girman ki, na ga take-taken ki tun awajen jere. Ba zan miki da daWi ba"

"Daga magana. Ni na ce kiyi sosayya da Wan shege" Taas Farida ta wanke ta da mari ai kuwa matan kowa ya tashi wasu su ka ja Farida gefe wasu kuma su ka tsaya da Inna Tabawa da ta ke ta zage-zage...

Kai tsaye falon Baffa Ummi ta shige da ita bayan an kawota wajen Ummin.

"Mi ye haka Aishah?, zafin kan ki har ya kai ki mari mace kamar Tabawa"

"Ummi so ta ke ta ci mutuncina cikin jama'a. Tun a wajen jere ta ke ta min habaici ina shareta. So ta ke wanda ma ba su san abinda ya faru ba su sani"

" shikenan?" Ummi ta faWi ranta a Sace

Farida ta kalli mahaifiyarta da mamaki ta ce "Ummi maganan Lukman fa"

" da ta yi maganan akwai abinda ya ragu ko ya ?aru a jikin ki ne?"

Farida ta girgiza kai.

"To ni banga abin Waga hankali ba anan. ?addarar ki ce ta zo da haka. Kuma Alhamdulillah Allah ya chanja mi ki da mafi alkhairi sai ki yi ta gode ma sa, ki share 'yan gulma da gulmar su"

"Amma Ummi..."

"Kul. Ba na son jin wani magana, ki je ki nemi abinci ki ci ki samu ki huta"...


?akin su Yakubu ta shiga ta ke cin abincin, ba wai daWin abincin ta ke ji ba sai dai saboda Ummi ce ta takura sai ta ci. Gaba Waya zuciyarta na ma ta Waci. Duk yadda ta so ta basar da abin ta ka sa, kawai sai hawaye. Ta ya za ta manta da wannan rana a rayuwarta, ranan da ya kamata ace ya zamo ranan farin ciki amma kuma komai ya zo ya dagule, ya zamo ranan shine rana mafi ba?in ciki a tarihin rayuwarta. Sai da ta yi kuka mai isarta kafin ta share hawaye ta tattara kwanukan ta fita...

...................


Anyi Walima lafiya, sai dai duk yadda Farida ta ci burin ganin anyi komai da ita abinda ya faru daren jiya ya kashe ma ta jiki. Da farko ma shiri ta yi kawai za ta wuce office amma amarya Jiddah ta hanata.
"Dan Allah Anty Farida kar ki tafi, ki taimakeni ki tsaya ayi komai da ke. Ke ce support Wina Anty"

"Na san kin ji abinda ya faru jiya, ba na son tsayawa anan wata ta gayamin maganan banza mu kwashi 'yan kallo. I dont want to ruin your day"

"Anty dan Allah ki mance da komai, Allah ina bu?atar ki kusa da ni fiye da kowane lokaci"

Da ?yar Farida ta ha?ura ta tsaya. An ci kuma an sha sannan an kira Malami ya yi wa'azi.

Washe gari Asabat ?arfe shaWaya aka Waura auren *Hauwa Maijiddah Musa Wase da AbdulWahab Bello Hassan Kachako*

?aurin auren da ya samu halarcin manya-manya mutane, ta Sangaren Alhaji Bello Kachako da shi kan sa AbdulWahab Win.
Da dare aka kai amarya gidan ta wanda kwana biyu kawai za ta yi su wuce Lagos...


Gidan Amarya Maijiddah kam bayan kowa ya tafi aka bar amarya da halayenta.
Tun safiyar yau ta ke gudawa saboda tsoro da fargaba.
Akwai mafiya yawancin mutane da idan su na cikin damuwa ko tashin hankali ko tsananin farin ciki ko ba?in ciki za ka ga yanzu-yanzu cikin su zai hautsine su fara ziryan banWaki.
Maijiddah was nervous tun wayewar garin yau, abu ne da ta jima tana ro?o sai gashi ya tabbata, wai ga ta amarya. Ta sha Flagyl kam har ba adadi duk dan ta samu sau?in wannan abun amma kaman tunda Maghriba ta do so abin ya fara ?aruwa. Yanzu haka kafin Farida ta tafi sai da ta tabbatar ta sha magani amma yanzu da ta ke ita kaWai sai ta ke jin cikin ta na ?ugi yana kuma murWawa.

Tana cikin wannan yanayi wanda ta kira da ?arshen kunya aka shigo Wakin. BuWe ?ofar Wakin yai daidai da kukan da cikinta yai "?ululululu"

A hankali ya tako wajen da ta ke ya ajiye ledar hannun sa akan drawer sannan ya tsugunna gaban ta ya sa hannu ya Waga gyalenta sama yana mai yin Bismillah.
Jikinta rawa ya ke, sai zufa ta ke haWawa. Na farko saboda tsoro na biyu kuma saboda yanayin da ta ke ciki.

"Alhamdulillah, finally Gimbiya Allah ya nuna ma na wannan rana"

Duk maganan da ya ke yi sama-sama ta ke jin sa. Kamar ta saki ihu ta ke ji saboda kunya da haushin kan ta. Ta ya za ayi daren farkon su ace ta Sarke da gudawa, wannan abin kunyan har ina.

Hannunta ya kamo yana wasa da yatsunta bayan ya zauna kusa da ita.
"Bari mu yi sallah sai mu ci abinci,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login