Showing 108001 words to 111000 words out of 145791 words

Chapter 37 - Sakatariya Ta Book One Complete Hausa Novel

Azizat   

01 Nov 2025

330

ta sani idan har Sabreen za ta auri wani ba Najeeb ba to ba abinda zai sa ta baro chan ?asar su ta zo nan ta zauna da niyyar wai ta zo gyaran jiki. Mi ke shirin faruwa?

Ranan har yamma ba ta kuma fitowa ba. ZazzaSi ne ma ya rufeta. Tana nan haka Najeeb ya shigo Wakin da sallama.
Ba ta kulashi ba har ya gama abinda zai yi ya zo ya kwanta gefen ta. ?anshin jikinta na ratsa duk wani jijiyar jini a jikin sa.

"Mi ya faru na ga ko sannu da zuwa ba ki min ba"

Idonta da su ka yi ja ta Wago ta kalleshi ta ce "mi Sabreen ta ke yi a gidan nan?"

?an dafe kan sa yai yana danne dariyar da ta taso ma sa.

"Oh sorry" ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce "i'm going to marry Sabreen, rana Waya za a Waura mana aure da su Anas. You see Aysherh ki na da kyau kuma kin min abinda ba zan taSa mantawa da ke a rayuwata ba. You'll always be my first wife amma kuma Sabreen will always be my first love"

Dariya Farida ta fara dan maganar Najeeb bai kama hankali ba kwata-kwata.

"Wasa ka ke yi Najeeb, kuma ba na son irin wasan nan, zuciyata za ta iya bugawa"

"I'm serious Aysherh. Na san Sabreen ta yi ba dai-dai ba a baya amma yanzu ta chanja. She loves me"

"Da Sabreen da soyayyar ta sun ci kutumar uban su. Wai Najeeb me ka Wauke ni ne. Shashasha ko? Wallahi ba zan yadda ba. Yau ko mata uku za ka auro ka auro amma banda Sabreen. Wai tukunna kan ka Waya kuwa. Sabreen fa, Sabreen da ta gudu ana saura kwanaki a Waura mu ku aure, Sabreen da ta shiga harkan film tana she?a ayarta yadda ta ke so, Sabreen da kana kwance baka da lafiya ta shure ?afa ta tafi ta barka wai za ta je ta yi film da Kwano Reeves ne ko Keanu Reeves ne ma..."

"I know, na san komai Aysherh but kin san soyayyar farko ba ta taSa gushewa"

Hawaye fal a idon ta ta ce "ni tawa soyayyar fa? Duk son da na ke nuna ma ka a banza kenan, ba ka Wauke shi a bakin komai ba ko?"

"Aysherh i have feelings for you amma kin san Sabreen..."

"Ya isa haka!" Ta daka ma sa tsawa.

"Ni ba zan zauna da kai ba matu?ar za ka auri Sabreen. Idan ma ba za ka iya zama dani ni Waya ba, ka nemi wata mana. Ko acikin cousins Winka ka aura amma banda Sabreen. Wallahi ba zan zauna da Sabreen ba"

"Aysherh please, na yafewa Sabreen ke ma ki yafe mata" ya faWa yana kamo hannunta. Tureshi ta yi ta tashi ta je wajen closet ta fara haWa kayan ta. Zan bar ma gidan ka, zan bar rayuwan ka, ka zauna da Sabreen ita kaWai tunda matacciyar zuciya gareka"

"Kin san ina bu?atar ki, Kamfanina tana bu?atar ki. Please Aysher"

"Kai wanni irin mutum ne Najeeb. Ba ka sona, ba ka tausayina, ni dai kawai na zauna da kai saboda amfanin kamfani"

"Ba haka ba ne Aysherh please ki fahimceni"

Tsugunnawa ta yi a wajen tana kuka. Zuwa yai zai rarrasheta ta buge hannun sa ta ce ya bar wajen ta. Yana tsaye a gefe har ta gama kukan ta ta tashi ta shiga banWaki ta jima a banWakin dan a?alla ta kai kusan minti talatin kafin ta fito. Direct gado ta je ta hau ta kwanta ta rufe dukkan jikin ta...

Yana jin kukan ta a ransa, he wants to tell her it was all a trick amma ya san halin ta, idan ya gaya ma ta komai za ta nuna rashin damuwa, hakanan kuma abinda ya shirya ba zai tafi dai-dai ba dan Sabreen za ta iya ganewa.




*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0?? 4?? 4??






Ba baccin daWi Farida ta yi ba, bacci ne ta yi na wahala. Da huturun sanyi aka tashi da asubahin ranan. Da ?yar ta tashi ta shiga banWaki ta yi alwala. Sanda ta farka Najeeb ya fito kenan yana shirin fita masallaci.
Tana idar da sallah ta nemi wata ?atuwar rigan sanyinta wanda a?alla ya yi shekara shida da ta ke amfani da shi. Rigan sanyin doguwa ce mai hula, dan idan ta sa yana wuce gwiwanta. Ko lokacin tana Jos idan ana tsananin sanyi idan ta sa shi ta sa dogon wando da socks shikenan ta yi maganin sanyi. Tana son rigan saboda Ummi ce ta siya ma ta...

Daga sallaya gado ta koma, kan ta ke wani mugun sara ma ta, ga cikinta da ke ta kukan yunwa.
Ba bacci ne a idon ta ba, asali ma jiyan ba ta kwanta da wuri ba. Yadda cikinta ke juyawa ya sa ta tashi dan ta sha gestid ko za ta ji sau?i duk da kuwa ta san ciwon cikin ba na magani ba ne na yunwa ne. Tana tsaye a wajen dressing mirror tana shan maganin Najeeb ya shigo.
Ta yi kaman ba ta ganshi ba, maimakon 10ml da za ta sha sai ta ?ara wani 10ml ya zamo 20ml, tana tsayen ma wani jiri-jiri ta ke ji.

Yana tsaye yana kallon ta. Har ta ajiye maganin ta je ta hau gado. Bai ce ma ta ?ala ba, zuwa yai ya buWe fridge ya Wauko apple guda biyu da su ka saura a ciki. Dama shi kam bayan ruwa to fruits kawai ya ke sawa a ciki.
Sai da ya zauna gefen ta sannan ya ce "Aysherh tashi ki ci apple, bai da ce ki sha magani ba tareda kin ci wani abu ba"

Shiru ta yi ba ta ce komai ba.

"Aysherh"

A harzu?e ta tashi ta na masifa "ina ruwan ka da ni, na ce ina ruwan ka dani. Na ci abinci, ban ci ba, wannan ba matsalar ka ba ce"
Juyawa za ta yi ta kwanta ya ce "Aysherh amma rigan sanyin kin nan gwanjo ce ko? As in Okrika, fairly used cloth..."

"Eeh shi ne, gwanjo ne, amma ka san me? ta fi designer cardigans Win da ka ke sawa. Tunda shekara da shekaru tana min maganin sanyi"

"Oh really, kinga banbancin ki da Sabreen kenan. Sabreen ba za ta taSa saka irin wannan kaya ba"

"Mugu, butulu, ka bi ka damu mutane da Sabreen Sabreen, daWin abin ma karuwa ce. Karuwa mai lasisi ma. Idan ita ba ta sa gwanjo ni a ina sa gwanjon ka ganni ka Sata min aure saboda ka aure ni. Ka ga gwanjo kuwa sun min rana"

Sake mi?a ma ta apples Win yai wannan karan ta wafce a hannun sa.

Sai da ya ga ta fara ci sannan ya ce " Sabreen ta tuba Aysherh. Kuma Allah Gafurun Rahimun ne zai gafarta ma ta"

"Allahu Akbar, Ashsheikh Najeeb Adam Jibo Rahimahullah. Aje dai a ?arata da ragowar kafirai" fa faWa tana hararar sa

"Yawwa Uwargida na, Aysherh mai gwanjo"

Dundu ta fara kai ma sa da apple Win a hannunta tanayi tana kuka, dayaga abin na yi ne ya tashi a gadon da sauri yana dariya...

...............................


?arfe shaWaya ta fito dan ta maida plates Win abinci kitchen. Sabreen ta gani da tawagarta a falo su na duba wassu jewelries.

"Aishah" Sabreen ta kira sunan ta.

Farida ba ta juya ba, ta dai tsaya.

Sabreen ta taso ta zo gaban ta ri?e da sar?a. Ta kai hannu za ta gwada sar?an a wuyan ta Farida ta buge hannun.

"Kar ki taSa ni!" Ta faWa da tsawa.

"I wanted to give it to you Ayshah, i mean no harm"

"I dont want anything from you, you whore" ta faWa tana barin wajen.

Sabreen ta yi murmushi dan ta san kishi ke cin Faridah...


Daga kitchen Wakin Mom ta wuce. Mom Win ma jewelry box ta buWe tana ware jewelries da za ta bawa Najdah da wanda za ta bawa Farida.

Da sallama Farida ta shigo, ko gaisuwa babu ta tsugunna a gaban Mom ta Waura kan ta a cinyarta tana kuka.

"Miya faru?, Aishah talk to me, miya same ki?" Dan ta tsorata da yanayin ta.

"Mom dan Allah ki ce Najeeb kar ya auri Sabreen, Mom mutuwa zan yi idan ya aureta. Mom dan Allah"
Tana maganan tana kuka.

"Farida, Najeeb yana son ki. He loves you so much"

"Mom ?arya ne baya sona, idan yana sona ba zai ce zai auri Sabreen ba. Mom yaushe ma ya samu lafiya da har zai yi zancen aure. Wallahi idan har ya aureta ba zan zauna da shi ba" ta sake fashewa da kuka

"Farida sai ki barwa wata mace mijin ki, mijin da ki ke tsananin so"

"Mom ba zan iyaba, mutuwa zan yi, Mom please ki ma sa magana"

Tausayin Faridan ne ya kamata. Tsoron ta kar garin neman gira a rasa ido. Ya sa ta yanke shawaran gaya ma ta gaskiya.

"Barin gaya mi ki abinda ke faruwa, amma ba na so ki nuna kin sani"

Farida ta girgiza kai tana share hawayen da ke shimfiWe a fiskarta...


...........................

Bisa shawaran Mom ta fara attending class Win da Miss Jean ke yiwa Najdah. Ranan da ta zo kunya ne ta cika ta, da ?yar ta iya ?arasa class Win. Baturiyar matar nan ba kunya ba komai ta ke bubbuWe mu su abubuwa, tun daga sizes na girman abun zuwa yadda su ke idan suna cikin aiki. Bayan an gama bayani aka koma kan su mata. Da Faridan da Najdan dukkan su ashe shatara su ke cikon ishirin. Sun Jahilci abubuwa dayawa gameda jikin su da kuma yadda za su sarrafa mazajen su saboda kar a samu matsala...

A ranan lecture na biyu Jean ta fara nuna mu su different sex positions. Farida ganin abun na wuce gona da iri ya sa ta tashi za ta fita, sai ga Sabreen ta shigo.

?an dariya ta yi ta ce "you're still a virgin? You mean Noory never ..." sai ta sake kwashewa da dariya.

Haushi ya cikata har wuya, ba dan ta san gaskiya ba, da yanzu ba abinda zai hanata marin Sabreen.

"Dont be shy Ayshah. Na san kin fi Najdah bu?atar lectures Win nan. Domin sai kin yi da gaske kafin ki samu kan Noory idan mu ka yi aure"

Farida ta cize leSen ?asa tana huci. Sabreen zuwa ta yi ta gayawa Jean sa?o sannan ta fita. Sai da ta fita Farida ta koma ta zauna, duk da dai tana jin kunya haka ta daure tana ?aruwa da bayanan Miss Jean...

Najeeb kan bai fahimci komai ba saboda Farida ba ta nuna ma sa ta san plan Win shi ba. Har yanzu ba ta sake mishi fiska, maganan kirki ba ta shiga tsakanin su...

Wasa-wasa ranaku su ka dinga tafiya har ya saura kwana huWu ayi aure. Gidan na su ya fara cika da mutane. Da ke Najeeb ya cewa Sabreen baya son hayaniya shiyasa ba ta nuna za?ewa kan wassu lamuran ba. Dama itama ta ce tanason auren ne a sirrance dan kasancewarta celebrity idan maganar auren ya fito fili za ayita cecekuce, tafiso ko da za ayi gulma to ya zama bayan auren ne...

Ba wassu 'yan uwa ba ne su ka zo daga Sangaren Sabreen mahaifinta ma tun zuwan sa Walimar Najeeb da ya koma ciwon sa ya tashi, yana chan London ana kulawa da shi. Sabreen independent woman ne. Da 'yan uwa, ba 'yan uwa za ta yi aure ba abinda ya shafeta. ?anin Mahaifinta ne ya zo sai kuma yayan Mom da yayar Mahaifiyar Sabreen...

Daddy ya ce baya son hayaniya saboda albarkar aure ake so ba komai ba. Najdah ta so ayi dinner amma Daddy ya hana. Shi Daddy tun ciwon Najeeb yai wa kan sa karatun ta nitsu wajen almabazzaranci da kuWi. Da da ne ba ?aramin bidiri za ayi a bikin ba, dan ko lokacin auren Najma ansha shagali sosai...

Daddy bai san mi Najeeb ke shiryawa ba sai da ?anin Baban Sabreen ya ma sa maganar sadakin Sabreen. Abun ya Waure ma sa kai, a take a wajen ya kira Najeeb.
Da Najeeb ya zo ha?uri ya bayar tareda nuna mu su cewa ya yi hakan ne saboda ya kowa wa Sabreen hankali.
Daddy ya rufe shi da faWa yayinda Hajj Khalid Abu Nasir ya fahimci Najeeb Win. Tunda shi kan sa ya san lokacin da aka kashe ma?udan kuWi wajen shirya bikin su amma Sabreen ta gudu ta bar su da abun kunya. Hakanan bai taSa goyon bayan shiga film da Sabreen ta yi ba...


Ranan Jumu'ah bayan an yi sallar Jummu'a aka Waura auren *Architect Anas Ali Almustafah da Najdah Adam Jibo* biki ya samu halartar manya-manyan mutane...

Sabreen wani farin wedding dress ta saka wanda ta aje ma?udan kuWi aka designing purposely saboda ita. Ta sha ado na dimond da gwalagwalai. Hakanan make-up artist da ta zo da ita Arfa ta rangwaWa ma ta kwalliya, ba ?arya ta yi kyau sosai.

Wanda su ka dawo daga wajen Waurin aure ne su ka fara labarin yadda taro yai taro. A wajen Mouna yayar mahaifiyar Sabreen ta ji aure Waya aka Waura, auren Najdah da Anas. Mamaki ya sa ta wuce Wakin Sabreen wanda ke ta Waukan selfie cikin kayanta na aure kafin su zo su yi hoto da angonta...

Maganar da Mouna ta gaya ma ta ne ya sa jikinta ya fara rawa. Waya ta Wauko da sauri ta kira uncle Win ta wanda ya ?ara jaddada ma ta auren Najdah kawai aka Waura ban da na ta. Wayar hannun ta ya suSuce ta yi dur?ushe a ?asa kanta na ma ta wani nauyi, zuciyarta na cigaba da bugawa da ?arfi-?arfi kaman wanda zai bullu?o...



* ku wanke idon ku da kyau gobe za'ayi abubuwa*






*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0?? 4?? 5??




Duk yadda ta daure ma zuciyarta ta ka sa saboda wani ?unci da ya cika ma ta zuciyar.
"Ahhhhhhhh" ta fashe da kuka

"Noory dont do this, dont do this to me plz" sunbatun da ta farayi kenan tanayi tana kuka.

"Mahlan yaa Sabreen, Mahlan binti" Mouna ta faWa tana Wan bubbuga bayan ta.

Lokaci guda ta yi wuff ta mi?e tsaye tareda tattare rigarta da ya baza waje ta fita da gudu, su Mouna su ka bi bayan ta...

?akin Mom ta shiga ba ta nan dan haka ta sauko ?asa da gudu tana kiran Noory.

A falon ?asa ta yi kiciSus da Najma. Najma cikin rashin sanin miya faru ta fara tambayan lafiya, Noory kawai ta iya furtawa.
Najma ta ce bayanan. Sabreen ta fita da gudu tana kiran Noory...


Yana wajen reception Najma ta kira shi akan ga Sabreen tana ta kuka tana neman sa. Ya san za ayi haka, hankalin sa kwance ya ce a bashi 30mins yana zuwa. Shi yadda ya tsara ma baya so ta gano shi har sai dare idan ya zo da niyyar zai Wauki amarya. A yadda ya sharara ma ta ?arya cewa yai shi zai zo ya Wauketa su je gidan sa inda anan za su ci amarcin su. Ai raka amarya ?auyenci ne, ita kuma Sabreen ba 'yar ?auye ba ce...


Zuwa yanzu kusan kowa agidan ya san abinda ke faruwa. Sabreen tana zaune tana kuka, fiskar nan duk ya chaSe, kwalliyar da aka wa idon duk ya zazzago sai idonta ya zama kaman wani horror.
Sai lallashinta ake, wanda ba su san mi Sabreen ta yiwa Najeeb ba su ka fara zagin Najeeb, wassu har cewa su ke ?ila ?wa?walwarsa ce ta motsa tunda ance tun rashin lafiyan da yai ?wa?walwarsa ba ta dawo dai-dai ba. Ka ji mutane fa...

Farida tun da sassafiya da su ka tashi ta fara wani tsumewa ita a dole yau za a mata kishiya. Da Najeeb ya Wau wanka ya sha manyan kaya zai tafi ta ce ma sa "Allah ya taimaki angon Sabreen"
Yai dariya kawai ya fita. Kwanciyar ta ta yi, sai ?arfe goma sha Waya ta tashi. Bayan ta yi wanka ta shirya sannan ta fito. ?asa ta sauka dan ta nemi abinci dan tsayawa sai Adama ko Tasallah sun kawo ma ta har Waki ba adalci ba ne dan ta san aiki ya sha mu su kai..
Bayan ta karya Mom ta kirata, da ta je kaya ne ta bata wanda za ta sa a yau Win, ta karSa tana godiya...
Tana Waki ta idda sallar azahar kenan ta ji ihun Sabreen. Jin hayaniya ya fara yawa ya sa ta sauko dan kar ayi show Win ban da ita...

Ba ?aramin cika aka yi a falon ba. Kowa da abinda ya ke cewa zuwa yanzu Sabreen ta dena ihun kuka. Hawaye ne kawai ke zuba a idon ta...

Har lokacin kayan da ya sa ya je Waurin auren ne a jikin sa amma babu malun-malun Win. Bai yi mamakin ganin yadda mutane su ka cika falon ba dan yasan mata da gulma. Najma da Mouna ne ke gefen Sabreen su na ?ara lallashinta.
"Ga Najeeb Win" Najma ta faWa lokacin da ya shigo.
ZumSur ta mi?e ta nufe shi.

"Noory why? Why?" Ta faWa tana dafe ?irjinta da ke ma ta zafi.

?an murmushi yai sannan ya ce "Why? Sabreen ki na tambaya na Why?. The same why da ki ke tambaya shi na yi ta tambayan kai na 9yrs ago. We were inlove remember, we made so many promises. Sabreen why? Abinda na yi ta tambayar kai na kenan. It took years kafin na amince wa kai na cewa ni ko soyayyata ba komai ba ne a wajen ki. That being an actress ya fi ni muhimmanci a wajen ki. That having a role in a movie ya fi aure na a wajen ki, That the love we shared was fake, that everything about you is fake"

Sabreen ta tsugunna a ?asa tana ?ara danne ?irjinta saboda gani ta ke idan ta cire hannunta ?irjin ne zai fito saboda yadda ya ke bugawa da ?arfi.

"Kina ji kaman zuciyar ki za ta fashe ko? Thats exactly how i felt and even more, na tsani kowa na tsani komai, na zamo tamkar mahaukaci. Sai da na yi watanni bana cikin hayyacina Sabreen. Ba na iya bacci sai na sha magani ba na iya cin abincin kirki. Years went by and i couldnt love again, kyawawan mata, mata ma su matsayi da ?asaita fiye da ke sun nemeni amma idona ya rufe, ba na kallon kowa sai ke. In those 8years da na yi ta yawo da dakon soyayyar ki not once ki ka waiwaiye ni, not

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login