Showing 135001 words to 138000 words out of 145791 words

Chapter 46 - Sakatariya Ta Book One Complete Hausa Novel

Azizat   

01 Nov 2025

340

amma idan ka ma ta magana wallahi ba za ta ?i maganar ka ba"

" Son kenan, wannan tsakanin ka da iyalin ka ne ba ni da wani hurumi a ciki. Ka bata lokaci kaWan za ta sauko, she went through alot saboda kai dan haka ka bi ta a hankali"

Najeeb ya haWa rai dan bai ji daWin maganar Dad ba, maimakon ya supporting Win sa sai ya ke maganar wai ya amince da hukuncin da ta yanke...



Lokacin da su ka dawo ma haka ta wuce shi, yana magana ko uhum ba ta ce ma sa ba ta haura sama.

"Sabreen please help me talk to her" ya faWa yana haWa hannu.

Kaman Daddy itama cewa ta yi ya ba wa Farida lokaci.

?akin su ya wuce ko zai samu daman magana da ita amma ya samu ta kulle Wakin.

"My Queen please ki bari na ganki ko na minti Waya ne"

Tana zaune akan gado tana jin magiyar sa amma ko ajikinta duk da chan ?asan ranta tana son kasancewa da shi amma ba za ta janye ?udirinta na son horashi kaWan ba. Haka ya gama magiyar sa ya bar wajen....

Bayan kwana biyar da haukar Naomi Pastor ya bada shawaran a je a bawa wanda ta yiwa magani ha?uri saboda idan su ka yafe hakan zai sa Naomi ta samu sau?i.
Mrs Comfort, Pastor Chukwudi da Saint Janet suka je gidan su Najeeb. Maigadi ne ya sanar da su Farida tana gidan au Najeeb, su ka karSi address a wajen shi su ka wuce chan...


Mrs Comfort kuka ta dinga yi wiwiwi a gaban su Farida tana ro?on su gafartawa Naomi. Daddy ya ari bakin Najeeb da Farida ya ce sun yafe, Najeeb ya haWe rai dan shi plan Win shi ma sai Naomi ta je jail.

Pastor ya mu su godiya sannan su ka tafi. Duk da wannan yafiya da aka yi bai sa Naomi ta warke ba. Kwana biyu da dawowar su daga gidan su Najeeb ta tsere daga gidan Pastor ta shiga gari. Wasa-wasa aka baza neman ta amma har sati guda ba labarin inda ta ke...


.........................


Shirye-shiryen bikin Sabreen ake yi duk da kuwa Sabreen da Lukman Win sun amince akan ba za ayi hidima ba amma Mom da Farida sun ?i. Wata guda aka saka har yanzu kuma saura sati uku.

Fitowarta kenan daga wanka ta kalleshi zaune akan gado. Mantawa ma ta yi ba tarufe ?ofan ba.
"Ni fa ba na so ana shigo mini Waki ba izini"

A hankali ya taso ya zo ya tsugunna gaban ta ya kamo hannunta biyu ya ri?e gam. Kallon sa ta ke yi yadda idon sa yai ja.

"Aysherh I cant, ba zan iya ba. Kafin 3 months Win nan zan iya mutuwa idan ba kya tareda ni. Please ki manta da komai ki dawo gida mu cigaba da rayuwar mu. I promised to make it up to you, ba zan sake Waukan sakatariya ma ce ba, yalla yarinyace ko tsohuwa. Zan dage da addu'an dare saboda kar wata ta kuma samun galaba a kaina. Zan yi duk abinda ki ka ce amma please come back to me. I love you"
Ya kai hannun ta kan kirjin sa ya ce " My heart beats for you Aysherh, only for you. Ki taimakeni ki taimaki zuciyata kar rashin ki kusa da ni ya min illa. Na Wauka zan iya jurewa amma Wallahi ba zan iya ba, its being 2 weeks amma gani na ke kamar 2 years ne. I miss you Aysherh, I miss us. Please my Queen..."


*team Farida kun karSi ha?urin Najeeb ko ya?*




Skt 57


"Ka yi ha?uri amma ba zan koma yanzu ba" ta faWa a hankali duk da kuwa maganganun sa sun karya ma ta zuciya.

Ya cize leSen sa na ?asa yana huci, bayan 'yan da?i?ai ya mi?e tsaye ya ce "tunda abinda ki ke so kenan zan jira ki"...

Ba ta iya Waga ido akan sa ba har ya fita daga Wakin.
Anya ta ma sa adalci kuwa? Ta tambayi kan ta. Sai dai kuma ta rasa gane amsar da za ta bawa kan ta...

Yinin ranan sai sintiri ta ke tsakanin falo da Waki amma Najeeb bai dawo ba. Washe gari ma bai zo gidan ba...

Su uku ne a dining su na cin breakfast lokacin da Najeeb ya shigo. Kwana biyu kenan bai zo gidan ba.
Wajen Mom ya je ya gaisheta, ta shafa gashin sa tareda ma sa peck a goshi.

Ya duba Sabreen ya ce "amarya ya shirye-shirye"

Sabreen ta yi murmushi ta ce "shiri ai sai su Mom da Ayshah, su ke ta komai"

"Allah ya kaimu lokacin"

Mom ta amsa da amin yayinda Sabreen ta sunkuyar da kai tana murmushi.

"Zan wuce Abuja, i'll be there for two days"

Mom da Sabreen su ka ma sa addu'ar Allah ya kiyaye.
Farida tunda ya zo ta ke binsa da ido amma bai ko kalli wajen da ta ke ba.

Ganin ya juya zai tafi ya sa ta yi saurin sake mug Win tea da ta ri?e, Mug Win ya faWi kan tile ya Wan fashe.

"Ouch...Ouch ... Wayyo zafi..." Farida ta faWa saboda tea Win ya Wan fetsu ma ta.

"Sannu Ayshah, sannu, ba ki ji ciwo ba ko?" Mom ta faWi tana ?o?arin ri?e hannun Farida.
Farida kam idon ta na kan Najeeb wanda ta ke tunanin zai zo da gudu ya dubata. Sai taga saSanin haka tsayawa kawai yana kallon ta.

?an gyaran murya yai ya ce " na tafi"

Farida na jin haka ta fashe da kuka.
Sabreen mi za ta yi banda dariya. Mom ma dariyan ta ke son yi amma ta gimtse.

Har ya fita Farida bata dena kuka ba. Sabreen ta ce "someone is missing her husband"

Farida ta kalleta ta galla ma ta harara. Mom kam yi ta yi kaman ba ta san sunayi ba, Adama ma ta kira akan ta zo ta tattare wajen da Mug Win ya fashe...

?arshe haushi ya sa Farida tashi daga wajen ba tareda ta gama cin abincin ba...


...........................

Tana jiran kiran sa ko text amma shiru. Ba?in ciki ya tokare ma ta ma?oshi, kowa ma haushin sa ta fara ji a gidan. Sabreen kuwa indai su ka haWu sai ta tsokaneta akan Najeeb.

Ranan da zai dawo ta samu Mom a Wakin ta da su ka gaisa ta ce "Mom zan je na Wau wassu kaya a chan gida"

Mom ta yi murmushi dan ta gano Ayshah na son komawa gidan ta ne. Ta ce " 'yata ni inaga horon ya isa haka, Son zai cutu idan ki ka cigaba da zama a nan"

"Amma Mom..."

Mom ta katseta da cewa "ki yi ha?uri ki koma kin ji"

Farida ta yi ajiyar zuciya ta ce "shikenan zan koma saboda ke"

Mom ta ce na gode. Sai da Farida ta fita sannan Mom ta yi murmushin manya...


Farida ta kira Adama ta tayata haWa kaya, da su ka gama ta kai ma ta su cikin mota. Da ta shirya ta je ta yiwa Mom sallama sannan ta shiga Wakin Sabreen. Waya su ke da Lukman lokacin da ta shigo, tana kallon ta da jaka ta sa dariya har da hawaye.

"Ni ba na son gulma, Mom ce ta ce na koma" Farida ta faWa tana haWa rai.

Sabreen ta ce " to Allah ya kiyaye hanya sai mun zo karSan tsaraba"...

Saloon ta fara wucewa aka ma ta gyaran gashi da lalle sannan ta wuce gida. Ko'ina na nan tsaf-tsaf saboda Tasallah ba ta wasa da gyaran gidan.

Lokacin da ta shiga Waki wanka ta yi ta feshe jikin ta da turaruka.
?arfe biyar na yamma Abdullahi ya faWa ma ta zai je ya Wauko Najeeb a airport yanzu kuma ?arfe huWu da kwata.
Gyara Wakinta ta yi kafin ta wuce na shi Wakin. Yana nan a gyare amma sai da ta cire zanin gado ta sake sa wani sannan ta shiga banWaki dan ta wanke...


Tun ?arfe biyar da kwata ta ke tsaye jikin balcony na falon sama tana jiran dawowarshi amma Abdullahi bai shigo gidan ba sai ?arfe shida saura minti goma. Tana ganin ya fito daga motan ta yi saurin barin wajen. ?akin sa ta shiga ta fara gyara arrangement na turaruka da mayukan sa...

Ta ji shigowar sa amma ta dake ba ta kulashi ba ta cigaba da gyaran har da faWin " duk an bar Waki a hargitse. Komai gashi nan ba tsari kaman ba mutum ke kwana a Wakin ba"

Yana tsaye yana kallon ta bai ce komai ba duk da farin cikin da ya mamaye zuciyar sa.

Ya ajiye jakar sa ya shige banWaki ba tareda ya ce ?ala ba. Tana binsa da wutsiyar ido har ya shige banWakin.

Ta Wan yi ?aramar tsaki ta ce " koma ya nuna ya gannin nan"
Ta zauna bakin gado tana jiran sa. Ya jima a banWakin kafin ya fito sanye da bathrobe fari.

"Ni fa kar mutum ya ga na zo ya nemi yi min wala?anci Mom ce ta ce na zo."

Shiru Najeeb bai ce komai ba. Ta Waga ido ta kalleshi yana tsaye gaban mirror yana shafa jikin sa da mai.

"Allah na gani sai na tafi tunda ba a son ganina, dama ba wai da son rai na na zo ba"

Najeeb ya ajiye man da ke hannun sa ya je ya buWe ?ofar Wakin ya ce " a gaida Mom da su Sabreen. Allah ya kiyaye hanya"

"Kuturun Uban chan. Au'uzubillahi har ka sa ina zagi"
Ta tashi fuuuu ta ce " zan tafi Win koma ba za ka sake ganina ba"

Sai da ta zo shigewa ta ?ofan ya ri?e hannun ta.

"Ni ka sake ni in tafi, ka sake ni na ce"

Ya jawota jikin sa yana kallon ?wayar idon ta. Itama Win kallon sa ta ke ?irjin ta na bugawa da sauri-sauri ba abinda jikinta ke muradi irin tajita kwance kan faffaWan ?irjin sa.

"My stubborn Mrs Jibo. Na san duk maganan nan cika baki ne kawai, you miss me, i see it in your eyes"

"Ba wani. Ni dama taimakon ka zan yi tunda Mom Allah Annabi ta ro?eni akan na dawo"

"Oh really?" Ya faWa tareda sunkuyo da kan sa, ganin yana matso da bakin sa kusa da nata bakin ya sa ta lumshe ido tana jiran haWuwar bakin su.

Maimakon kiss a baki sai ya kissing kumatun ta. Ta buWe ido a hankali gaba Waya ta yi laushi saboda wani mugun sha'awar sa da ke taso ma ta.

Murmushi ya ma ta ya sake matsowa da bakin sa wannan karan kam tuni ta yi saurin matsawa da nata bakin, bakin su ya haWe waje guda...
Sun jima suna aikawa junan su hot kiss kafin ya jawota zuwa kan gadon. . Wata Waya da 'yan kwanaki rabonta da shi, ba ?aramin missing Win sa ta yi ba. Yadda ya ke sarrafata haka itama ke mayar ma sa da martani, sun jima su na gogar junan su saboda an jima ba a gamu ba...

Bayan komai ya kankama da su ka yi wanka Najeeb ya ce " ki shirya na maida ki wajen Mom na ha?ura ki huta a chan"
Duka ta kai ma sa ya goce yana dariya...


..........................



Rayuwan masoyan gwanin sha'awa, kullum su na manne da juna. Duk dare sai sun tashi sun gudanar da sallah sun ro?awa junan su addu'an samun zaman lafiya da kuma samun 'ya'ya ma su albarka. Duk Jumu'ah Farida ba ta fasa yin sadaka ba...

Ranan Asabat aka Waura auren Sabreen da Lukman. Daddy ne ya zama alwalin Sabreen 'yan uwanta sun zo ba laifi, wannan karan har mahaifiyarta sai da ta zo. Anyi walima kuma anyi family dinner a gida. Washe gari Sunday kuma aka wuce da Sabreen Abuja. Farida ta so zuwa amma Najeeb ya hana saboda yanzu ta yi nauyi.

Duk cikin 'yan uwanta babu wanda ya nuna damuwar sa da asalin Lukman, su daWin su ne ma Allah ya shirya mu su Sabreen har kuma ta yi aure hankali kwance...


.......................


Wanda su ka kawo Sabreen mutum huWu ne Mom ce da Najdah sai Aunt Mouna da wata cousin Win Sabreen Win Nihaya. Ba su fi awa biyu a gidan ba suka koma bayan sun yiwa Sabreen 'yan nasihohi.

?arfe biyar Lukman ya shigo gidan na su. Cike da farin ciki, finally shima ya zama ango...

?arfe takwas saura su ka gabatar da sallan Isha tareda sallar godiya sannan Lukman ya gabatar ma ta da kazarta. Tare su ka ci kazar su ka ?oshi sannan Lukman ya tattare wajen...

Kunyar Lukman ta ke ji, ta sani ita ba irin matar da ta dace da Lukman ba ne. Ya fi ta daraja da kima duk da kuwa ta fishi asali.

"Ka yi ha?uri ba nida abin da kowane ango ke farin cikin samu a rana irin ta yau. Na yi rayuwa marar daWi a baya, na zubda mutuncina a idon duniya, na Wauka rayuwa mai kyau na ke yi, rayuwa ta 'yan ci da jin daWi amma a gaskiya rayuwar ?unci na yi a baya. Ka yi ha?uri dan Allah. Ina godiya da Allah ya bani kai. Ba ka dubi yawan shekaruna ba, ba ka dubi rayuwar bariki da na yi a baya ba amma ka amince da ni ka amince na zamo sashen rayuwar ka. Thank you Lukman"


"Shhhhhh" ya faWi tareda haWe bakin su...

Sabreen ta sha gyara sosai, duk da ta saba amma Lukman ya bata mamaki saboda yadda ya birkitata da salon sa, sai takejin ba ta taSa tarayya da wani da yai kusan sa a iya sarrafa mace ba....



Skt 58


*ina ro?on duk wanda ya karanta wannan shafin yai wa Mijin Maman Durratu addu'a, Allah ya ji?an sa da rahama, ya haskaka ?abarin sa, ya gafarta ma sa ya kuma bawa iyalen sa ha?uri da juriyan rashin sa, Amin. Wanda su ka rigamu gidan gaskiya Allah ya ji?an su da rahama, muma idan tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani amin*



Yau tun safe ta ke jin ta ba dai-dai ba. Ta dai daure ta cigaba da ayyukan da ta saba. Yana fitowa daga wanka ta riga ta cire ma sa kayan da zai sa. Ita ta shafa ma sa mai sannan ta taimaka ma sa ya shirya. Tana gyara mi shi tie Win ya ce "my Queen lafiya? You look dull this morning"

"Just ?afafuwa na ke ciwo" ta faWa dan kawai kar ta tada ma sa hankali

"Ko za mu je ki ga likita?"

"No, zai yi sau?i zuwa anjima"
Ta Wan bugi ?irjin sa kaWan ta ce " mijina ka ga yadda ka yi kyau. Dan Allah ban da dogon hira da mata, banda lumshe mu su ido, ban da yi mu su murmushi, ka ji nawan"

Ya Wan ja kumatunta ya ce "na ji your highness zan kiyaye duk abinda ki ka ce" light kiss ya manna ma ta a baki kafin ya ja hannunta su ka bar Wakin...

Tafiyar Najeeb office da awa uku Farida ta fara na?uda. ?anliti sabon dreban ta ya wuce da su asibiti. Tun a hanya Tasallah ta kira Mom ta gaya ma ta. Su na zuwa asibitin ko minti arba'in ba ta cika ba ta haihu.
Abin ya zo ma ta da sau?i gaskiya, kuma Alhamdulillah ba wata matsala...

Tana kwance an kaita Wakin hutu Mom na gefe tana kallon jaririn mai kama da uban sa. Cikin zuciyarta ta ke godiya wa Ubangiji da ya sa ta ga Wan Najeeb.
Mom ta mi?awa Farida jaririn tana faWin "he look just like his father"

Farida tana kallon jaririn tana godiya bisa wannan ni'ima da Allah ya ma ta...

Bayan minti talatin da haihuwar kafin Najeeb ya iso asibitin. He cant believe it sai da ya ga jaririn, Mom ce ta kirashi ta ma sa albishir da haihuwan. Bai kawo haihuwa ba tunda ya bar Farida lafiya gashi kuma EDD Win ta saura kwana shida. Sai dai al'amari na Allah yafi gaban kowa.

Ya Wau yaron yana murmushi tareda kissing goshin yaron. Alhamdulillah ya ke ta maimaitawa a fili, bakin sa ya ?i rufuwa saboda farin ciki.

?arfe huWu da rabi aka sallame su daga asibitin su ka dawo gida. Kafin dare gidan na su ya cika da Jama'a. Kowa na zuwa ganin babyn Farida.


................................

Gidajen biyu sun kasance cikin farinciki bisa wannan ?aruwa da aka samu. Da farko Mom ta so Farida ta dawo wajenta amma gogan sam bai ba da dama ba.

Mom za ta je gidan su tun safe sai dare ta tafi. Ita ke yiwa Farida wanka. Ummi ma kullum sai ta zo duba Farida da jikar ta.

Kafin ranan suna gidan an cika shi da tarkacen yara. Wassu abin ma jaririn kafin ya iya amfani da su sai ya shekara uku amma an siye su tun yanzu.

Ranan suna yaro ya ci sunan *Muhammad Yaman*
(Finally Farida an zama Umm Muhammad>??)

Mutane ba kaWan ba su ka halarci waliman wannan suna, tun daga mutanen Gombe zuwa na Wase da Jos kowa ya karkaWe jiki ya zo. Sabreen da Lukman ma saura kwana Waya suna su ka dira a Kano. Yaro ya samu kyaututtuka ba adadi.
Sorveniers sa aka raba ba za su irgu ba. Saboda gudun evil eye, sunan yaro kawai aka sa babu hoto. Washe gari aka yi abincin sadaka aka kai Iskalin Almajirai sunfi ishirin...


Rayuwa ta cigaba da tafiya hakanan soyayyar Najeeb da Farida tana tafiya gwanin sha'awa. Baby Yaman ba ?aramin gata ya ke gani a wajen iyayen sa ba, ga uwa uba kakannin sa. Kowa son Waukan sa ya ke idan aka fita da shi, amma miskilin yaro ba kowa ya ke yarda ya Wauke shi ba. Ko Tasallah da ?yar ya Wan saba da ita ya dena kuka idan ta Wauke shi...

Kamfanin Najeeb sai daWa bun?asa ta ke yi, yanata samun buWi ta ko'ina...

Wannan zuwan Farida gida lokacin Yaman yana Wan wata huWu ta lura da cikin Ummi. Ko ya akayi ma ba ta lura da shi ba sai yanzu oho dan a?alla cikin zai kai wata shida.

"Ummi dan Allah ki haifo mace na samu ?anwa nima"

Ummi ta ma ta da?uwa, Farida ta sa dariya, dan ta gane Ummi kunyar cikin ta ke ji...


....................


Aneesa da Maijiddah sun saita kan su, sun dena kishin hauka. Aneesa ta yadda duk makaman ya?inta, sosai ta ke kula da miji da yaranta tunda yanzu ba inda ta ke zuwa. Ciki ma ta ke da shi amma ta kasa sanar da Abdulwahab dan kar yai zaton ?arya ta ma sa irin wancan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login