Showing 66001 words to 69000 words out of 145791 words

Chapter 23 - Sakatariya Ta Book One Complete Hausa Novel

Azizat   

01 Nov 2025

356

means, za ki iya saka hijabi ko mayafi babba tunda ki na da aure"

"I see, amma ka sani ko nawa mijin bai damu da sa hijabina da rashin sawata ba"

"Still Mrs Jibo, ya kamata..."

"Shhhhhh, Sir Najeeb our relationship is strictly professional" ta kwaikwayi muryan sa.

Ya Wan ji zafi a ran sa amma ya dake da ce wa "ok get back to work"

Har ta buWe ?ofa idon sa na kan bayan ta. Irin kayan da ta ke sawa ne tun da, amma ya rasa dalilin da ya sa yanzu bai son ganin ta da wannan kayan...


Tana zaune tana typing Anas ya zo zai shiga office Win Najeeb sai kuma ya tsaya su na gaisawa. Labarin marukan da Najeeb ya sha a kan ta ya fara yi ma ta wanda ya sa ta fara dariya. Dai-dai lokacin kuma Najeeb ya fito, ba yau Anas da Farida su ka fara hira su na dariya ba amma yau gani yai dariyar ta yi yawa.

"Ango wajen ka na ke son zuwa amma tunda za ka fita barin jira ka a nan, idan ka dawo sai mu yi maganar"

Najeeb bai ce komai ba ya fita, bai yi nisa ba sai ya dawo, har lokacin magana su ke.
Yai gyaran murya ya ce "Mrs Jibo ki tuna min ina da meeting ?arfe goma"

Ba tareda ta kalle shi ba ta ce to.
Ya sake fita amma ko taku biyar bai yi ba ya dawo.
"Mrs Jibo follow me"

"Ina zuwa"

"Follow me, now!" ya daka ma ta tsawa. Shi kam Anas ya gane kishi ke ran sa, tun Wazu da ya fito ya ga irin kallon da ya ke ma sa kaman zai mangareshi.

Farida ta tashi da sauri ta ce " ina zuwa Yaya na"

Sai da su ka fita Anas yai dariya ya ce "muje zuwa Najeeb, da kan ka za ka hanata aikin nan"










*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




0?? 2?? 6??



*wannan labarin na kuWi ne, dan Allah kar a fita da shi*




Har su ka isa second floor bai ce ma ta komai ba. Bin shi kawai ta ke yi amma har su ka dawo ba abinda ta ma sa. Su na dawo wa ta ce "Sir Najeeb dama ba abinda zan yi shi ne ka hana mazauna na su samu hutu"

"Dama hutu ki ka zo yi ne?"

"Sir Najeeb its not fair, ina zaman-zamana kawai ka zo ka tasheni ,na yi ta bin ka kaman wanda aikin bodyguard ka Wauke ni"

Kafin ya ba ta amsa wayarta ya fara ringing.

"Your Ray?"

"To ba shi ba ne, Yakubu ne" ta faWa tana picking call Win ta yi waje.

Shi ma Win Waukan waya yai ya kira Anas. Lokacin da Anas ya zo ya ce "ango-ango, ka gama yawo da amaryar ta kan. Can we discuss business"

Najeeb ya Wan gyara zama ya ce "wannan Architect Yakubu Win whats his surname?"

"Yakubu Musa Wase"

"Ok"

Anas ya kalli reaction Win Najeeb ya kwashe da dariya yace " ba dan ka ma sa ?wace ba da yanzu shi ne angon Farida"

"Kar ka ?ara cewa na yi ?wace. You and Dad force me into this marriage"

"Ayya! Ashe abinda ya faru kenan ko. Sorry Najeeb angon Aisha"

"Cut this bullshit, ya ake ciki?"

"Dama maganar hutun ?arshen shekara ne, ta ya za'ayi a gama duk wasu major project da mu ke da su a ?asa kafin lokacin?"...

Tana duba wasu takardu sai ga mutum ya shigo ma ta office da sallama. ?agowar da za ta yi sai ga Rayyan.

Ta mi?e tsaye da sauri. "Rayyan lafiya?"

"Kin ?i Waukan waya ta Farida kuma na ji labari kin fito aiki"

"Wato stalking Wina ka ke yi?"

"Farida ki zauna ma na mu yi magana"

"Wanni maganan za mu yi?, ni fa matar aure ce Rayyan"

"Exactly, matar Rayyan ya kamata ki zama ba ta Najeeb ba. Duk abinda yai ya yi ne da sanin kan shi dan ya raba mu. Idan ba rashin sanin darajan mace ba, ta ya zai auri mace kamar ki just one week ya dawo da ke aiki, aikin secretary"

"Rayyan dan Allah ka tafi. Ka ga miji na na nan"

"Miji? My Farida miji fa ki ka ce. Ina ki ka saka al?awurran da mu ka yiwa junan mu. Tun yanzu har kin fara cin amana ta kenan"

"Yau na ga ta kai na, Rayyan duk al?awarin da na ma ka ba wanda na saSa aciki, Na yi al?awarin mallaka ma ka zuciya ta da duk soyayyata idan mu ka yi aure. Kuma ba mu yi aure ba mi ya kawo maganar cin amana a nan?"

"Saboda yana da kuWi ko?"

" yes, saboda ina da kuWi"

Su ka jiyo muryan Najeeb a bayan su.


"DaWin abin ma sai dai mutum ya bi gefe yai zagon ?asa amma bai isa ya tunkari mace ya nemi soyayyarta ba" Rayyan ya faWa yana yiwa Najeeb kallon banza.

Najeeb ya ?araso kusa da shi ya Wan buga kafaWar sa ya ce " mutumina ka Wan je ka Wauki darasi a kan virtual reality ka ji"

Ya mi?awa Farida hannun sa guda Waya ya ce " Mrs Najeeb Jibo shall we"

Farida ta haWiye miyau saboda kan ta ya Waure amma indai dan ta yi abinda zai sa Rayyan ya fita a rayuwar ta ne to za ta yi. Duk da ta so Rayyan a baya, amma yadda ya shure watannin da su ka yi tare ya fasa auren ta ana saura kwana biyu Waurin aure ya sa tana jin ko da akwai burbuWin son shi a tareda ita to za ta kaWe shi ta huta. Ko da ba ta auri Najeeb ba Rayyan ya dawo, to ba za ta iya auren sa ba bayan ya riga ya watsa ma ta ?asa a ido.

Ta sa hannun ta cikin na Najeeb tareda matsowa ku sa da shi, maimakon ya tsaya a haka sai ya jawo ta jikin sa sosai. Ya kalli Rayyan da yai mutuwar tsaye a wajen saboda kishi ya ce " please feel free to visit Najeeb constructions some other time, yanzu Mr and Mrs Jibo za su huta. So get out"

Yadda ka san an sace balon-balon (balloon) haka gwiwar Rayyan ta yi sanyi. Yana son Farida sosai tun ranan da ya fara ganin ta a Keke kuma har yau yana son ta, hotunan da ya gani su suka birkita ma sa tunani ya rasa gane kan sa, musamman da ya kasance dama mahaifiyar sa ba son Faridan ta ke ba, ta dai ha?ura ne a lokacin dan ba yadda za ta yi.

Juyawa yai zai fita dan bashida ta cewa a wajen. A yadda ya ke ganin su zai iya sha?e Najeeb a wajen.

"One more thing, dont ever call Mrs Jibo again"
Rayyan ya ji wani abu ya suke shi a ?irji. Ya haWiye miyau da ?yar sannan ya sa kai ya fita.

Rayyan na fita Najeeb ya ture Farida gefe.

Ta Wan yi ?ara ouch.

"Sir Najeeb za ka karya min ?afa"

Fiskar nan ba wasa ko kaWan ya ce " kar ki sake kawomin tarkace office"

Ta gyaWa kai saboda yadda ta ga ya ci serious.

Har aka tashi ranan Najeeb ba shi da walwala. Tana ganin ya fito zai wuce gida ta yi saurin bin bayan sa. Bai ma ta magana ba har su ka isa gida itama ba ta ce komai ba dan yunwa ta ke ji.

Shi ne ya fara shigewa ciki ita kan zuwa ta yi ta Webi abinci kafin ta haura sama da tray a hannunta.

Tana shiga ta gan shi tareda Najdah, Najdah na nuna ma sa hoton abu a wayarta wai ya zaSa ma ta.

Sallama ta mu su amma ba ta ji an amsa ba, ko da kuwa an amsan to aciki su ka yi.

"Amsa sallama yana daga cikin ha??in musulmi akan Wanuwansa musulmi"

Najdah ta Waga ido ta kalleta sai kuma ta sauke ido. Shi kam Najeeb bai ce komai ba ya san fitina ta ke nema and he's not ready for that.

Ta ajiye tray ta shiga banWaki ta watsa ruwa, lokacin da ta fito Najdah ta fita. Ba ta san mi ya sameshi ba amma ta ga ko kayan jikin sa bai cire ba ya mi?e akan gado yana kallon sama.

"Sir Najeeb ba ka da lafiya ne?" Shiru

"Sir Najeeb ka tashi mu ci abinci"

Ta gama duk surutun da za ta yi amma bai ce komai ba sai daga baya ya tashi ya shige banWaki...

.....................


Sati Waya kenan da fara zuwa aikin ta, ba za ta ce komai na tafiya dai-dai ba ba za kuma ta ce akwai matsala ba. Yawanci ma Najeeb ba ya zama a office ya kan fita supervising ayyukan da kamfanin sa ke yi kuma ya ke so a ?arasa kafin hutun ?arshen shekara.

Safiyar yau da ta shiga kitchen ta samu Mom na decorating wani chocolate cake, sai ?anshi ya ke yi.
"Mom wa ke birthday?" Ta tambaya.

"Ya kamata a ci taran ki tunda ba ki san birthday Win waye gobe ba" Mom ta faWa tana murmushi.

"Najdah?"

Mom ta girgiza kai, Farida ta le?a cake Win ta ga shekarun da aka rubuta "wai-wai ashe na babban mutum ne"

Mom ta yi murmushi ta ce " he likes chocolate cake"

Farida ta ce "Ayya, cake Win ya yi kyau kuma"

"Akwai surprise family dinner da za ayi gobe da yamma. But dont tell him, idan ya sani ba zai zauna a gida ba"

"Allah ya kaimu gobe Mom"

....................

Safiyar asabat bayan ya iddar da sallah bacci ya koma. Haka kawai ta tsinci kan ta da kallon kyakykyawar fiskar sa, ta jima tana kallon sa, she cant believe he's 35yrs. Gaskiya jindaWi da hutu na Soye shekarun mutum...

Da ta Wan tattare Wakin sai ta fita dan ta taimakawa su Adama da aiki.

Lokacin da ta dawo Wakin kusan azahar ya riga ya fita. Ta buWe akwatin kayan ta tana duba kayan da za ta sa. Mom ta ce iyalen gidan Uncle Sulaiman za su zo ga su Hajia Fatima, dole ta yi shigar da ba za a raina ta ba. Tana cikin duba wannan ta ajiye ta sake dubawa ta ajiye aka ?wan?wasa ?ofar Wakin,
Ta je ta buWe ta ga Mom ne.

"Mom ki shigo"
Mom ta mi?a ma ta wani paper bag ta ce "ki sa wannan and please wear the dimond necklace"

Ta amshi bag Win tana ma ta godiya...
Ba ?aramin kyau gown Win ciki ya ma ta ba tareda takalmi da purse wanda su ka shiga da kayan.

?arfe huWu ta fito bayan ta shirya cikin doguwar riga pink da Mom ta ba ta. Lokacin gidan an fara hayaniya, ta sauko ?asa tana gaisawa da su Hajia Fatima...


Ya na gidan sa Dad ya kirashi akan maza-maza ya zo gida. Ya san ?ila surprise party su ka shirya ma sa. But he has no choice ba ya iya yiwa Dad mu su. Haka ya rufe gidan ya shiga mota ya dawo. Tundaga motoci da ya fara cin karo da su ya san hasashen sa ya tabbata.
Da sauri ya haura sama yana avoiding wata ?aramar cousin Win sa 'yar shekara biyar da ke cewa ya Wauketa.
Zuwa yai ya shirya a gurguje dan text Win Najdah da ya gani akan ya zo Garden su na jiran sa a wajen.
Komai sauri-sauri yai tun daga wanka zuwa sa kaya. Yana buWe ?ofa ya gan ta a bakin ?ofa. Daga sama har ?asa ya kalleta, she look beautiful, ga dimond necklace da ta sa da ya ?ara fito da ita.

"A ka ce na zo na kira ka"

* a surprise page gobe for team Najeeb*




*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......
'*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




0?? 2?? 7??



Da farko ya shagala da kallon ta amma tunda ya ?yalla ido ya ga sar?an da ke wuyan ta sai ya janye idon sa yana cewa "matsa na wuce"

"Sir Najeeb Happy birthday"

Bai amsa ba kawai wucewa ya yi. Ta bi bayansa tana cewa " Dan ma ka samu na wishing na ka Happy Birthday Win" yana takun sa na ?asaita ta na bin sa a baya, da ke heel ta sa sai ya zama ba ta iya sauri ba sai ta Wan sa gudu-gudu sauri.

Sai da su ka kusa isowa wajen sai ya tsaya, tana iso shi sai yafara tafiya a hankali ta yanda za su jera tare.

Su na shiga wajen aka sa tafi. Wani cikin cousins Win sa ya ce " ka ga salon soyayyar manya. Har ta tafiyar su iri Waya ce"

Najdah ta zo ta kama hannun Najeeb ta ma sa jagora zuwa inda zai zauna. Yana zama itama Farida ta zauna gefen sa.

"Happy Birthday babban yaya" Uncle Sulaiman ya faWa yana kallon Najeeb da ke kujeran su na opposite.

Daddy ya ce " kar ka kumbura ma sa kai, wannan taron domin 'ya ta aka yi ba shi ba"

Najdah ta Wauko cake ta kawo gaban sa. Ta kissing goshin sa ta ce " Happy birthday sweet Bro"

Murmushi yai sannan ya amshi wu?ar yanka cake Win ya sa zai yanka.
Aminu babban Wan Uncle Sulaiman ya ce " ka yanka tareda amarya ma na mu san yanzu kam ka bar tuzuranci"

Juyowa yai ya kalli Farida wanda itama shi ta ke kallo.
" he's right, 'yata help him cut the cake" Daddy ya faWa yana kallon yadda Najeeb ya haWa rai.

A hankali Farida ta Wau hannun ta ta Waura akan na Najeeb. Ido ya ?ura ma ta ita ma cikin idon sa ta ke kallo. A haka har wu?ar ya nitse cikin cake Win. Sai da aka fara tafi sannan su ka cire ido cikin na junan su.
Da ya yanka ma cewa aka yi Farida ta sa ma sa cake Win a baki bayan ta sa aka ce shima ya ba ta, relunctantly dai ya sa ma ta.

Ba a jima ba aka fara serving abinci ana yi ana taWi ana dariya. HaWa kujeru aka yi da table sai ya zama kaman a dogon table ake cin abinci. Sun jeru straight akan kujerun.

Anwar Wan Hajia Fatima ya tashi ya ce " aga aga?"

Aka amsa ma sa da aga

"Aga waye yai aure @35yrs?"

Aka nuna Najeeb.

Aminu ya tashi "Aga Aga" aka amsa da aga

"Aga waye yai ?wacen mata?"

Aka nuna Najeeb, wassu na dariya ?asa-?asa.

Wani kallo ya watsawa Aminun dan ya girmeshi kusan shekara shida amma shi ya yi aure harda yarinyar su Waya.

Aminu ya zauna yana dariya.

Anas ya tashi ya ce "aga aga?"

Da aka amsa ma sa ya ce "aga waye yai auren soyayya da sakatariyar sa?"

Wassu su ka nuna Najeeb wassu kuma wanda ba son auren Najeeb da Farida su ke ba, su ka fara hararan Farida, irin su Najdah da Afrah wanda tunda ta dawo daga weekend ta tarar da auren Najeeb ta tattara ta koma gidan Uncle Sulaiman.

"Barin nuna wani short video clip na wannan masoya, there first fight and probably there first love"

Idan da yadda Najeeb zai yi ya je ya make Anas a inda ya ke tsaye da ya je. Dan wani mugun kallo ya ke aika ma sa daga inda ya ke zaune.

Anas ya Waga Tab Win sa sama ya playing video Win. Video compilation ne na wajen da Farida ta fara zuwa aiki har ta hana Najeeb shiga office, da wajen da ya koreta ta ?i tafiya har ta rungumeshi lokacin da ya kira security. Sai wajen da Najeeb ya zo ya zauna akan superglue. Tun a clip na farko aka fara dariya, Daddy har da tari tsabar dariya. Wassu da ke gefe su ka dawo wajen da za su ga video Win da kyau.
Lokacin da video Win ya ?are Anas ya ce " Thanks to CCTV footage na kamfani mun samu wannan video na masoya mai cike da tarihi"

Najeeb ya rintse ido ya cize leSen sa na ?asa. Wannan embarrassment Win da me yai kama. A gaban su Daddy da ?annen sa, dan duk wajen idan ka cire iyayen to ya girme mu su.

A lokacin aka fara cewa ya tashi ya duba kujeran da ya zauna ko akwai superglue a kai. Wa su kuma su na kwaikwayon maganar Farida su na "Sir Najeeb ya dai?"

Farida kam idon ta na ?asa saboda ta ji kunya. Duk uban mutanen da ke wajen nan sun ga asirin ta.

Uncle Sulaiman yana dariya ya ce " kai gaskiya Alhaji ka iya matchmaking. Ka haWa Najeeb da dai-dai da shi"

Aminu ya ce " ai yanzu da take gidan sa idan yai mata laifi da ruwan borkono zai yi tsarki"

Anwar cikin dariya ya ce " sai ya zama tsuliyar Big B is on fire kenan"
Gaba Waya wajen kowa dariya idan ka cire Najeeb da ya cika yai fam.
Farida ma da ta sunkuyar da kai Wan dariyan ta yi...

Ana cin abinci ana sake gulman abinda aka gani. " Hajia Fatima har da cewa immediately Anas ya tura ma ta video za ta forwarding wa Najma da su Uncle Abubakar da ba sa nan...

Daddy ya ce " kar ku sa 'ya ta a gaba. Idan Sera na sata to daddawa ma na wari"


Yadda hannun Najeeb ke shaking, Farida da ke gefen sa sai da ta tsorata. Ta le?a ta ga hannun sa Waya da ya sa akan cinyar sa ya tamke shi kamar mai shirin kai dundu amma still hannun na rawa, Waya hannun da ya ri?e tsokali da shi kuwa yai wa sokalin ri?on makami ne.

Ana cin abinci amma Najeeb ba ya ci. Farida ma tunda aka playing video Win nan ta ka sa cigaba da cin abincin.

Lokaci guda hayaniyar da ake ta tsaya chak. Wanda su ke opposite da su Najeeb su su ka ga matar da ta doso wajen da ake taron ita da Adama da ke ri?e da tray za ta kawo wani nau'in abincin.

Jin shirun yai yawa kuma su Daddy sun ?urawa mai zuwan ido ya sa wassu daga cikin wanda ke zaune layi Waya da Najeeb su ka juya, cikin su har da Aminu.
Muryan Aminun ne ya fitar da sunan wacce ta doso wajen cikin takun ta na ainihin celebrity, yadda ta ke catwalking kamar a kan redcarpet ta ke za ta je karSan Oscar award.

*"SABREEN"* ya faWa da sigar mamaki

Jin sunan ya sa sauran su ka juya duk da ma ba kowane a wajen ya san Sabreen ba, balle labarinta. Idan ka cire Najeeb da Farida duk sauran sun juya.

Najeeb na zaune, takaicin abinda Anas yai ya cika shi, chan ?asan ran sa yana tsara irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login