Showing 1 words to 3000 words out of 105783 words
[3/8, 5:34 PM] Salma😝: CAPTAIN SADIQ
👮🏼
written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Blood sister deejah
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM 🐄
follow me on wattpad username: salmamasudnadabo
1_2
Yarinya ce yar shekara 10 na hango, tana tafe tana rusa kuka kamar anmata mutuwa, fara ce sosai ita ba siriri ya ba, ita ba lukuta ba, d'ankwallinta ne a hannu hakan ya sa na kalli gashin kanta, bak'i ne sosai amma saboda tsabar datti yayi jawur, kallo d'aya na mai na gane mai laushi ne, rashin kullawa ne yasa yayi haka, Hancin ta yayi jaga-jaga da majina, gata da manyan ido,tana tafe tana kukan, dan ba dainawa tayi ba, dai-dai wani madaidaicin gida ta tsaya chak, gidan kasane natallakawa sosai, dan ko k'ofar gidan bata samu ishashiyar kofa ba, Ihu ta Kara saki kamar an watsa mata ruwan zafi, inna da ke kurya d'aki ta fito tana gyara zani, inda sabo to ya kamata ta saba da halin fatuha, amma ba yadda ta iya dole ta fito inba fitowa tayi ba to wallahi sai dai maqota su fito, ganin inna ta leko yasa fatuha tuma a k'asa tana ihu.
inna ta gyara tsayuwa. ta ce, "ohni fatuha nabani yau kuma wakika tsokana kika ci duku, fatuha ciki murya tsiwa irin na yara masu wayau masu rashin ji ta ce "inna wallahi tallahi kwarankwatsi dubu bani na tsokane shi ba inna" ta k'ara rushewa ta saban kuka inna ta san halin ta sarai shiyasa ta ja bakin ta tayi shuru can kuma ta ce, "to fatuha waya bige ki?
"wallahi inna Rabi'u ne ya bigeni har da taka min ruwan ciki" ta k'ara rushewa da saban kuka kuma inna billahilazi ba zan yarda ba" ta inda zancan tana katse majina hancin ta saboda inna ta san karya irin ta fatuha tasan ba yarda za'ayi rabi'u ya bige ta har ya taka mata ruwan ciki, sai dai in laifi ta masa kuma ko bugun ta yayi bai taka mata ruwan ciki, qila ma satan mangwaro taje ya kamata Inna ta ce, "yi hakuri fatuha ki kyale shi kin ji kuma kiga Rabi'u ba sa'an ki bane kin ji diyar baffan ta"
"kambuuuu..! ta zaro manya idanuwan ta "qur'an inna ban hakura..!
"haba fatuha yi hakuri Zan baki biyar kin ji" washe baki tayi kamar ba ita ke ihu da koke-koke ba ta ce, to inna na hakura kwarankwatsi" Inna ta washe baki fatuha ko ba wai har cikin zuciyar ta ta hakura ba, dan ta dau alwashi sai ta rama dukan da Rabi'u ya Mata haka ta bi inna cikin uwar d'aka tana matse kwalla da katse majina .
Misalin karfe hudu na yamma fatuha ce zaune tsakar gida wadda take share kwal, ba dati ko d'aya da yake inna akwai san tsafta duk yadda ta so ta gyara fatuha da ta fita zata dawo kamar almajira ko sabuwar mahaukaciya saboda tsaban rashin ji ko wanka sai anyi da gaske, inna ke samu ta dirje ta fura take sha hankali kwance daga gani fura na kai mata karo dan sai rausaya kai take kamar kadangaruwa, inna ce ta lek'o daga uwar d'aka ta ce, "fatuha yi sauri ki shirya ki tai makaranta allo.! baki ta turo gaba kamar zata tunkud'i birji ta ce, "gaskeya yau inna ban zuwa, na gaji qur'an kullun Malam d'alha sai ya bigeni" ta inda zancan tana matsar kwalla"
"to fatuha in baki je makarantar ba inaa zaki sauke? baki so na siya maki shanun a yanka ranar sauka? washe baki tayi ta ce, "to inna zani wallahi ko dan ki yanka min shanuwa babba tafi tasu fatsima kwarankwatsi"
"yawa yar albarka maza ki shirya" hijabin ta dake saman igiya ta janyo ta zura ta fita da gudu inna ta girgiza kai ta dau kwanan fura ta Kai madafi ta aje.
Fatuha da ke tafe tana yan surutai wanda ko ni (salma) bajin ta nake ba chan ta tsinkayo muryar malam dalha taja birki ta tsaya tana raba ido dan tasan kashin ta ya bushe, dan ba k'aramar makara tayi ba, Malam d'alha ne ya juyo sukayi ido 4 da fatuha ya kwallo ido waje ya ce, keeeeeeeee!! fatuha dan uban ki yanzu ne lokacin zuwa makaranta shegiya mai Kama da mayu, duk kauyan nan kin raina uban kowa" yana huci ya cigaba da cewa, "yau zaki ci gwafar ubanki wallahi" fatuha dake ta raba ido ta duqa da niyar rarumo takalmin ta ta ruga muryar Malam d'alha ce ta tsinke mata tunani "wallahi kika ruga sai na sa basiru ya dauko min ke akai" kasancewa tasan basiru Ba k'aramin kato bane yasa taja ta tsaya chafka d'aya Malam d'alha ya mata yana muzurai kuka ta farayi tana yarfe hannu tana bashi hakuri Allah annabi amma yayi biris ya fisgota ya fara kila kamar an aiko shi, ihu take jera mai da Allah ya isa bugun ta yake amma bakin yaki mutuwa dan kan shi ya gaji da dukan ta ya hakura, fatsima da ke gefe sai matsar kwalla take tana yimai daquwa ta hijabi ta, lalla6owa gefan fatuha tayi Malam D'alha be ganta ba ta ce, "yi hakuri fatuha kin ji Allah sai ya saka maki" fatuha dake matsar kwalla ta turo baki gaba ta ce, "billahilazi sai na rama fatsima, ba yana zuwa gidan qilu zance ba da yamma ba, kwarankwatsin dubu sai nayi maganin shi fatsima"
"Kai fatuha ki kyale shi dan wallahi ki kai mai iskanci har gida zai biki dan Malam D'alha ba wayau garashi ba, ya hadaki da baffa"
"yo nima wayau ya isheni? ta karashe zancan tana washe baki fatsima taja bakin ta tayi shuru haka suka cigaba da karatun su dai-dai gwargwado fatuha na da k'okari sai dai bata jin magana ko kad'an, ba wanda bai san ta akauyan su ba.
Mayan motoci ne kira bentley guda 5 suka nufi wani katafarin gate kallo d'aya nayi ma motocin na hadiye miyau dai-dai katafarin gida motocin suka kunna Kai wurin parking suka nufa suna gama parking da sauri wasu sojoji guda 4 suka foot daga ciki motar gaba at the same time sojojin 4 na cikin motor baya suka nufi motar tsakiya ahankali d'aya daga cikin sojojin ya bud'e mai murfin motar tsakiya wani had'addd'en kafa nagani mai sanye da booth yana cikin kakin shi na sojoji karfafen namijine kyauwan sa ya isa wow fari ne Sol idanu sa manne da glass fari wadda ya fido da zala kyan shi da qwarjinin shi dogo ne sosai jikin shi murd'e yana da fad'and'an kirji gashin kanshi mai laushi ne duk da gashi na cikin hula shi na uniform hakan be hana gashinshi bayyana ba, ga sajan shi kwance hanci shi kamar pencil dan tsini briefcase din shi ya amsa hannu daya daga cikin yaran sa, fuskarsa murtuke Ba alamar dariya kamar an aiko mai da wahayin mutuwa, (na ce ohni Salma da guy dinan zeyi dariya da ba k'aramin kyau zaiyi ba) haka yaran suka bashi guri ya wuce Kai tsaya main palour ya nufa wow fad'i tsaruwar palour bata lokaci ne saboda ba karamin haduwa yayi ba baba jummai da ke gafe cikin washe baki ta tsugunna tana kwasar gaisuwa cikin isa kamar mai koyan magana ya amsa tare da cewa, "mom fa?
"ah mai gida tana sama" K'ara d'aurewa yayi dan wannan suna k'ona mai rai yake a hankali yake taka matatakala cikin isa.
Kai tsaye d'akin mom ya shiga had'add'an d'aki ne mai kyau sanyin AC sai ratsa d'akin yake hajiya da ke zaune saman kujera dressing mirror tana shafa turare tasha had'add'en leshin ta mai kyau, fara ce bafulata na kallo d'aya zaka mata kasan hutu ya zauna mata, ahankalin ya k'araso yayi huging nata cikin fara'a ta juyo dan tasan ba mai mata haka se son, kiss ya sakar mata a kumatu ya ce, "Mom I miss you..!
"miss u more son welcome back dear, baby ka k'ara girma kamar ba Kai ba" turo baki yayi ya langwabe Kai alamar shagwaba ya ce, "Kai Mom ni dai gaskiya ban girma ba"
"AI ka ji da shi, yanzu dai kaje kayi wanka ka dawo your food is ready a dinning area"
"ok Mom..! ya fice yana murmushi kamar bashine Wanda ke d'aurewa d'azu ba...!
VOTE
COMMENT
[3/8, 10:06 PM] Salma😝: CAPTAIN SADIQ
👮🏼♂
written
by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
blood sister deejah
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
Follow me on wattpad: salmamasudnadabo
3_4
Kaitsaye bedroom nashi ya wuce komai na bedroom d'in golden colour ne wani makekyen gado ne atsakiyar d'aki wanda ke kama da ba a kwanciya a saman shi, dan komai na d'aki very neat ne dressing mirron din shima abin kallo ne kayan shafa ne kamar suyi magana dan yawa, perfume kam ba'a magana da man gyara gashi tsayawa lusafa maku haduwar d'akin 6ata lokaci ne, kayan shi ya fara cirewa
ya shige toilet, wow toilet d'in ma abin kallo ne dan ya had'u iya had'uwa baifi 30 minutes ba ya fito d'aure da towel a qugun shi d'aya kuma yana goge gashin kanshi da shi dressing mirror ya nufa ya shafe jikinsa da mayuka masu kamshi tare da gyara sumar sa da sajan shi wardrobe nashi ya bud'e, wow wardrobe din ma abin kallo ne saboda kaya ne a ciki kamar gurin saida kaya suit kala2 da uniforms d'in shi na sojoji kamar suyi magana da yake shi mutun ne ba mai yawan sa manyan kaya ba, dan haka k'ananan kaya sunfi yawa hannu yasa ya ciro T-shirt din shi white mai gajeran hannu da 3quarter black, ba k'aramin kyau yayi ba haka yasa kyan shi ya bayana sosai agogo ya mak'ala ma hannu shi mai tsada silver na azurfa har ya kai bakin kofa phone nashi ya fara ringing wayarsa kira iPhone 7 white chak ya jaa ya tsaya hannu ya kai saman dressing mirror nashi sweet Mom ne rubuce a screem d'in phone din ahankali yasa hannu ya d'auka ya ce, "hello Mom..!
"son na d'auka bacci ya d'auke ka?
"no mom yanzu zan fito"
"ok.. datse kiran tayi daga dayan bangaran cikin isa yake saukowa daga steps hannu sa d'aya cikin aljihu Jidda dake dining ce ta rugo da gudu ta rungume shi ta ce, "daddy welcome back..! d'aga ta sama yayi yana mata wasa tana dariya har suka qaraso dining tana rik'e a hannu shi Mom sai murmushi take ita tayi serving d'in su shinkafa ce da miya wadda taji kaji da namomi da ganyaye cikin kwanciyar hankali suke cin abincin, wadda sadiq da kanshi yake feeding Jidda itama tana feeding nashi yarinya ce wadda baza ta wuce 4 years ba chocolate Colour ce mai kyau da ita gashin kanta yasha gyara sanye take da gwon pink mai dan siririn hannu, yadda sadiq ke bata kulluwa hakan zai gwada ma ba k'aramin ji yake da ita ba, Mom dake zaune tana Kallan su sai taji tausayin Jidda ya kamata, da shi kanshi d'an nata Jidda ce ta katse shuru da cewa, cikin muryar ta mai tsamin, "daddy Ina tsaraba na? kallan ta yayi yana murmushi ya lakace mata hanci ya ce, "sweetheart ki bari daddy ya gama lunch mana" baki ta turo gaba ta ce, "Uhm daddy na k'osa naga tsaraba ne"
"Uhm na sani swetheat bari mu gama tukun" Mom ce ta washe baki ta ce, "ke dai baki gajiya duk san da yayi tafiya fa sai ya maki tsara"
"to ai grandma Ina so ne" ta ida zan can tana turo baki
"ke ko Allah ya shirye ki" cewar Mom duk hiran da suke idan sadiq nakan little daughter d'in shi wadda ya ke jin ta har cikin ranshi sadiq ya ce, "oya cigaba da cin abinci sweetheart mu gama na baki tsaraba ki, sannan muje shan ice cream ko dear"
"yes dadd.! haka cikin wayau ya samu yayi feeding nata.
*******
Fatsima da fatuha ne tafe antaso daga makarantar allo suna tafe suna tsoka dan wannan ya zamar masu jazaman, in antashi daga makaranta sai sunyi tsokana san ransu suke komawa gida, wata Rana da kuka wata rana da gudu suke komawa gida yau kam a guje suka koma gida, fatsima ta shige gida fatuha ta shige gidan su baffa ne zaune bisa tabarma Inna na gefe tana zuba mai ruwa abuta saboda magrib ya kusa, fatuha ta kunno kai tare da sallama ta yarda hijabin ta k'asa baffa ya bita da kallo, washe baki tayi ta ce, "baffa sannu da gida"
"yauwa yar albarka, an dawo daga makaranta kenan?
"eh baffa"
"yauwa ya karatun"
"lahiya lau baffa" taje ta amshi buta da ke hannu inna ta kawo ma baffa yayi alwala ya wuce masallaci bashi ya dawo ba sai bayan isha'i, inna da fatuha na zaune suna cin tuwan dawa ta miyar kubewa wadda tasha man shanu baffa ya shigo da sallama, fatuha ta ruga da guda ta rungume shi "ah'ah zaki karya ni fatuha wai ke baki san kin girma ba" baki ta turo ta ce, "gaskiya baffa ban girma ba"
"to naji" ya ja hannu ta suka zauna bisa tabarmar da Inna ke zaune murmushi inna tayi ta tashi ta shige madafi ta d'auko kwana abinci Malam ta aje mai yana samata albarka bayan sun kamala cin abinci fatuha ta kwashe kwanikan ta dawo ta zauna kusa baffa ta ce, "baffa..!
"na'am fatuha"
"Baffa Ina so gobe na bika gona dan Allah"
"makaranta fa fatuha" baki ta turo gaba ta ce, "ai gobe litinin baffa ba ta sahe" inna da ke gefe ta ce, "toh fatuha kin san sai 5:00 Malam ke dawowa ki bari sai ranar alhamis ki bishi kin ji" kwalla ta Fara matsewa baffa ya ce, "yi hakuri ki shirya goban sai muje ko" washe baki tayi dan ita akwai abinda take san daukowa a gona shiyasa zata bishi inna ce ta katse mata tunanin da cewa, "haba Malam wai me yasa kake biyewa fatuha dan Allah, taita sangarcewa"
"kinga ladingo bana san haka haba dan Allah, Allah ya bamu yarinya sai baza mu faranta mata ba, mun dad'e muna san yara Allah bai bamu ba sai yanzu, yanzu kuma ya bamu sai muki faranta mata, gaskiya bazaiyu ba ladingo, ke ma kin fara d'aukar maganar mutanan waje Kenan, toh yayi ni dai ba maimatsa ma d'iyata akauyan nan" kyale shi ladingo tayi ya ida zan can tare da d'aukar fatuha wadda tuni bacci ya kwashe ta inna ta bishi da ido tare da kwashe tabarmar tsakar gida.
****
After dinner mom da sadiq ne zaune a palour suna kallan news Jidda na kwance jikin shi, da alama tana wasa bacci ya d'auke ta Teddy's d'in ta a baje cikin palour baba jummai ce ta leko daga d'akin ta ta zo ta fara kwashe kayan wasan tana kaiwa d'akin jidda dakine mai kyau fadi tsaruwa dakin 6ata lokaci ne sai da ta gama kwashewa ta zo d'aukar jidda dake mak'ale da baban ta sadiq ya ce, "ah baba barta yau tare zamu kwana"
"to shikenan maigida bari na mata wanka nasamata kayan bacci"
"to shikenan" ya miqa Jidda Mom ta juyo ta kalle shi tana sanyin magana amma ba tasan 6acin ran son shiyasa taja bakin ta tayi shuru, can ta ce, "ni ko baby aikin da baba jummai take bai mata yawa ba, gashi ba yarinya ba ce"
"haka ne Mom tunda Mary ta tafi ba a kawo wata ba, ni wallahi Mom tsoran d'aukowa sweetheart wata yar aikin nake duk basu iya komai back wallahi" ya ida zancan yana 6ata fuska Mom ta ce, "ya zamuyi dole a samo wata saboda aikin ya mata yawa"
"to shikenan duk yadda kukayi ki fad'a min"
"to.. kun koyi waya da abban ka"
"yes munyi jiya lokacin yana airport yace sai yayi 2weeks zai dawo"
"eh haka kasan har yanzu suna magana kan kwangillannan ne"
"eyya to Allah ya taimaka"
Mom ta ce, "amin gobe kai da Jidda in ka dawo daga wajan aiki ka kaita gidan sister ka ya kamata ka leka, ka bama su hanan tsaraba su ko"
"tam bari mu gani idan na dawo da wuri sai muje" sai ga baba jummai dauke da Jidda ya amshe ta yayiwa Mom sai da safe..
CAPTAIN SADIQ
👮
written
by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
blood sister deeja
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
5_6
ASUBA TAGARI
fatuha ce ta tashi tunda safe ta fito daga d'an akurkin d'akin ta wanda ko lafiyaya katifa bai samu ba, inna dake gefe ta na hura wuta Fatuha ta gaishe ta tare da d'aukar tulun da ke kusa ta inna, ta fice zuwa d'iban ruwa rafi gidan su fatsima ta wuce kai tsaye dai-dai bakin kofa suka ci karo da Fatsima ta washe baki ta ce, "kai fatsima qur'an na d'auka baki tashi ba da billahilazi na higo ruwa zan heqamaki"
"aiko da anyi heqa-heqa" suna tafe suna tsokana magidanta da suka fita siyaya safe har su qarasa rafi, yan'mata ne da sa'anin su birjik suna d'iban ruwa haka suma suka qarasa, duk yarinya data gansu indai sa'ar su ce sai ta matsa saboda tasan hali in bata matsa ba ta ci na jaki, fatsima ce ta hango Rabi'u shi da larai suna tad'i fatsima ta zuguro fatuha ta