Showing 36001 words to 39000 words out of 170905 words

Chapter 13 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

633

tayi" xae yi magana aka bude kofa Sadiya ta shigo ta tsaya daga bakin kofa tana taunar cingam tana kallon Mumy tace "Wae Abba a kira ki!" Mikewa junaid yayi yace "Ke don uwar ki baki iya sallama bane xaki shigo ma mutane parlor kamar dabba" Mumy ta hade rai tace "Ahmad!" Wani mugun kallo yake mata xuciyarsa na tafarfasa, ita ko ta tabe baki ta kauda kai tana murgurda baki, wani tsawa ya mata ya nufeta Mumy ta fixgosa tace "Xan saba maka wllh Ahmad, kana da hankali kuwa" Sadiya tayi tsaki ta fice daga parlon fuu, cikin bacin rai yace "Mumy ko gaisheni fa 'yar iskar nan bata yi a gidan nan yanxu, ni din sa'anta ne" Mumy tace "Sae me don bata gaishe ka ba, uwar me gaisuwarta xae kara maka, ko da can gaishe kan take idan ba gulma ba, kaje an bata maka rai a waje xaka xo ka huce ma mutane a gida, ina raba ka da mutanen nan baka ji koh Ahmad, dole ne sae ka tanka duk abinda suka yi" shiru yayi bae ce komai ba ya koma ya xauna ya rike kansa don shi kansa bai san me yasa yayi hakan ba, he just don't know what came over him, don da can ma ba gaishesa step sis din tasa take ba kuma bai taba ce wa komai ba, Mumy tayi kwafa ta dau hijab dinta ta fita. dawowa kusa da shi Humainah tayi ta xauna kasa a hankali tace "Kayi hakuri ya A.jay, nima daga yau baxan sake gaisheta ba, shikenan na rama maka" kallonta kawae yake bai ce komai ba, sai kuma ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe idonsa, ta bata rai tace "Shine ka min shiru koh" ba tare da ya bude idon ba yace "Anki maki maganan, ke din gaishe ni kike?" Mikewa tayi ta take kafarsa ta nufi daki tana cewa "Idan ba sai na gaisheta ba gobe me nake!" ya bude ido da sauri ya bi ta da kallo yana murmushi, Bayan kusan minti talatin Mumy ta dawo parlor, junaid ya mike ya dawo gefenta ya xauna a hankali yace "Kiyi hakuri plss mum I don't know what came over me, baxan sake ba wllh" tace "It's ohk" daga haka bata kuma cewa komai ba shi ma haka, bayan kusan minti goma yace "Mumy fushi kike da ni I know, don Allah kiyi hakuri plss" ta girgixa kai cike da takaici tace "uhn naxari kawae nake ne Ahmad, kaji inda yan gidan nan suka kuma bullowa wae duk me girki shi xae yi girkin gidan gaba daya yanxu, sae kace da can basu suka ce kowa yayi nasa ba, ko me suke nufi da hakan kuma oho" junaid ya d'aga kafada yace "Sai su ci kayansu ai, don ni baxan ci girkinsu ba" daga haka ya mike ya nufi dinning, Mumy tayi murmushi a xuciyarta tace "Ae dama baxan ma bari kaci abinda ya fito daga bangarensu ba idan Allah ya yarda"

Kwata kwata Junaid bai runtsa daren ranan ba ya rasa dalili, sae dai yafi danganta haka da tausayin baiwar Allahn da yake, Washegari Wednesday bai yi wani breakfast din kirki ba ya fita as early as 7, tun daren jiya El-Ameen ke kiransa baya dauka, a hankali yake driving ya kalli wrist watch dinsa yaga bakwae da minti goma, ganin yana da sauran time yasa shi nufan gidan El-Ameen, a waje yayi parking ya shiga gidan, kwance ya tarda El-Ameen a parlor yana bacci kan 3sitter, Mama kuma na kitchen, ya kusa second ashirin tsaye yana kallonsa sannan ya tabe baki yyi hanyar stairs, a hankali ya tura kofan dakin ya ganta kwance kan gado cikin bargo, ya karasa cikin dakin yana kallon empty roban drip din da aka cire mata, gefenta ya tsaya ya yaye bargon jikinta, ya tsura ma fuskarta ido, Ya fi minti biyu yana kallonta tana bacci, ya daura hannunsa a hankali a forehead dinta ya ji da d'an dumi, bude ido tayi da sauri ta mike xaune, kallonsa take ko kiftawa bata yi, lkci daya ta saki wani kara ta shiga komawa baya tana ihu da karfi, ya koma baya da mamaki yana kallonta, El-Ameen ne ya shigo dakin da sauri, ya tsaya daga bakin kofa ganin Junaid a dakin, sauka tayi daga kan gadon tayi kofa da gudu xata fita tana ihu har lkcn, El-Ameen ya fixgota yace "Keeh Meye haka!" Ihu ta dinga yi xata kwace kanta tana yi tana waigan Junaid, El-Ameen ya kalli Junaid yace "Ohhh it seems Khakin nan naka ke tsoratata fa Captain" Junaid ya juya yana kallon kansa a madubi, farin well ironed navy shirt ne jikinsa, well tucked in cikin navy blue trousers dinsa, sae hat dinsa a kai, sae black socks din dake kafarsa don ya cire takalmin a waje, juyawa yayi ya fice daga dakin, sai a sannan tayi tsit sai dai har lkcn jikinta rawa yake tayi lamo jikin El-Ameen, El-Ameen yayi dariya yace "Toh fah" xaunar da ita yayi gefen gado yana kallonta yace "That's intresting! kina tsoran soldiers kenan!" Kauda kai tayi ta xamo kasa ta kwanta, mikewa yayi yana kallon agogo, da sauri ya fita dakin ya sauko parlor sai dai bai ga junaid ba, ya kalli Mama dake shara yace "Mama junaid din ya tafi ne?" ta washe baki tace "Anya ya tafi, kaga makulli can ya ajiye kan kujera, ashe sojan ruwa ne yau na gansa da khaki" Dariya El-Ameen yayi yace "Ehh Navy ne" tace "Allah sarki, khakin sun masa kyau" kallon Makullin yayi yaga ta motarsa ce, ya d'an tabe baki ya karasa ya dauka yace "D'an rainin wayo" fita yayi don ganin ko motar tasa na waje yaga bbu motar makullin kawai ya kawo masa, girgixa kai yayi ya koma cikin gidan. Junaid na kwance parlor da yamma b4 magrib yana danne dannen waya, khadija ta shigo parlorn, Karasowa tayi ta xauna gefensa tace "Ina yini ya A'jay?" Yace "Lfya lau, kar ma ki fara tambayata kudi don bani da" dariya tayi tace "Kai yayana" sai kuma ta d'an yi shiru, a hankali tace "Kasan me yaya, karka ci abincin gidan nan yau, just go out and get somethin to eat ae kasan yanxu an daina girki daban daban koh" yana kallonta yace "Why!" Ta daga kafada tace "Just, beside ma porridge ne kuma ae bama ka ci" mikewa tayi tace ina xuwa, ta fice daga parlon, ya bi ta da kallo yana murmushi. Wayarsa ne ya soma ring ya duba ya ga El-Ameen ke kiransa, sai da ya kusa katsewa sannan ya daga ya kai kunne bai ce komai ba, daga daya bangaren El-Ameen yace "You try fa captain, nine ban san dadin gidanmu ba ko, how on earth xaka dinga bari na ni kadai ina fama da patient din ka?" Junaid ya tabe baki yace "Naga tana tsorona ne, kai ne bata tsoro dat's why I decided not to show up today" El-Ameen yayi tsaki yace "Didn't you see dat uniform dinka ke scare dinta, wear mofty while coming always, yanxu dai I will text u some drugs da xaka siyo idan kana tahowa, and ka siyo mata fruits taki cin abinci" Junaid ya kuma tabe baki ya katse wayar ya ajiye. Kallon agogo yayi yaga an kusa magrib, ya mike ya shiga toilet ya dauro alwala sannan ya fito ya dau makullin motarsa da Atm sae wayarsa ya fita ya rufe kofarsa. Bangaren Mumy ya fara shiga, yana kallon fatima dake guga yace "Mumy fa?" Tace "tana bayi" juyawa yayi ya tafi masallaci, ana idar da sllh ya dawo gida, Mumy da fitowarta daga kitchen kenan tace "Ga abincin ka a dinning can" kallon dinning din yayi yace "Porridge?" Mumy tace "Shi kake so?" Girgixa mata kai yayi yace "No khadija ce tace min porridge aka yi" Mumy tace "Ehh amma kai na maka girkin ka daban" yace "Toh nagode Mum, but xan d'an fita yanxu idan na dawo xan ci" tace "Fita kuma? Ina xa ka?" Yayi kasa da murya yace "xan d'an raka El-Ameen wani gun ne, daga can xa mu je kallon kwallo" ta tabe baki tace "Xa dai ku je tadi koh?" Dariya yayi yace "A'a fa Mumy" murmushi tayi tace "Toh kar dai ka wuce 8:30 a waje, ka ma shiga gun abbanka kuwa" yace "Ehh daxu na shiga" daga haka ya juya xai fita, Humainah tace "Ya Ahmad xan raka ka" yace " Nooo" daga haka ya fice daga parlon, Mumy tayi dariya tace "Ki bari ran lahadi ya xaga da ke katsina" tayi murmushi tace "Toh Mumy, ko yace A'a kiyi masa masifa sai ya kai ni" sae da junaid ya fara siyan abubuwan da El-Ameen ya ce masa ya siya ready made din fura da nono sannan ya nufi gidan, Mama kadai ce kwance parlor kan darduma, ya gaisheta ya bata nata fruits din da fura tayi ta masa Godiya yayi murmushi kawai ya haura sama. Xaune ya samu El-Ameen yana danna laptop, ita kuma tana tsaye can jikin bango ta jingina, El-Ameen yace "Sae da ka ga dama kenan" Junaid bai tanka sa ba ya ajiye ledan hannunsa ya xauna gefen gado, El-Ameen ya ya juya yana kallonta yace "Ba dai baki ji ba, wait in tashi xa ki ga abinda xan maki a wajen nan" Junaid ya kallesa kafin ya girgixa kai a xuciyarsa yace ae Kaine mahaukacin ma, takowa tayi ta karaso kusa da ledan da junaid ya ajiye ta durkusa, El-Ameen ya daka mata tsawa yace "c'mon ance maki naki ne" mikewa tayi da sauri, Junaid ya dauki ledan ya mika mata ta karba, El-Ameen ya mike tana ganin haka ta sake ledan ta koma jikin bangon da take, dariya yayi yana kallonta yace "kai! Yarinyar nan ba dai tsoro ba" shi dai Junaid ko kallonsa bai yi ba, Karasowa yayi ya dau ledan ya bude ya fito da bunch din Ayaba ya mika mata, ta karaso da sauri ta karba, xata juya ya fixgota ya xaunar da ita gabansa, da kansa ya shiga bude mata ayabar yana mika mata, tana karba tana ci, ana uku ne taki ci, ta kalli Junaid dake danna wayarsa sae dae gaba daya hankalinsa na kansu, ta matsa kusa da shi a hankali ta kama hannunsa ta sa mashi Ayaban, tabe baki El-Ameen yyi ya kuma bare mata wani ta karba ta kuma kama hannun Junaid ta basa, El-ameen ya hade rai ya kuma bare wani ya bata xata ba Junaid yayi mata tsawa, a tsorace ta juyo, yace "I will knock you yanxu, ina shan wahala ina bare maki abu kina kyauta da shi, da xan bar ki yanxu da peel din xaki hade ki cinye," kafa masa manyan idonta tayi ko kiftawa bata yi, junaid yayi murmushi ya girgixa kai, wayar El-Ameen ne ya fara ring ya dauka, xaro ido yayi ganin Abbansa ne ke kiransa, ya kalli Junaid yace "Kasan kuwa ban je clinic throughout yau ba" ko kallonsa Junaid bai yi ba, ya daga a hankali ya kai wayar kunne, daga daya bangaren Abban nasa yace "ka taho clinic ka sameni yanxu Ahmad, clear?" yayi kasa da kai yace "Toh Abba" daga haka ya ajiye wayar yana kallon Junaid yace "Look! Xan je clinic yanxun in dawo, wait har sai na dawo don't go plss, kaga bata da lafiya karfin hali kawae gareta she just finished vomiting kafin ka shigo, dats why nake nan har yanxu, am giving her her drugs before leaving yanxu" Junaid ya xaro ido yace "Idan Mumy ta kira ni fa, beside 8:30 tace in dawo gida, nd this is almost 8 o clock" Kallonsa El-Ameen ya tsaya yi sae kuma ya girgixa kai yace "Tashi ka tafi toh, wato nine bansan darajan parent dina ba koh Captain, nine na iya karya kai baka iya ba, you know am doing this goddam job for ur sake if you provoke me wllh sae in fasa kawai ka kaita asibiti, kullum safiya sai na xo nan sbda drugs dinta da injections, at mid day ma I have to leave whatever i am doing in xo nan bata magani, haka da yamma ma, sannan da daddare bana barin gidan nan sai kusan sha daya, Haba!" kallonsa kawae junaid yake bai ce komai ba, tsaki yayi ya mike ya dauko maganinta da cup yayi diluting da ruwa ya xauna kusa da ita xai bata tana ganin haka ta fara kokarin mikewa ya fixgota, bbu gardama ta shanye maganin duk jikinta na rawa, ya mike
ya dau makulli da wayarsa yana kallon junaid on a serious note yace "Look! In har ka bar gidan nan kafin in dawo wllh wllh kaji rantsuwan musulmi koh, toh sai dai ka san yanda da xakayi da yarinyar nan don ba fina biyayya kayi ba, I am taking my hands of her case" daga haka ya fice daga dakin, Junaid da ya bi sa da kallo yana murmushi snn ya juya yana kallonta, yatsine fuska kawae take, ta matso kusa da shi ta mika masa Ayabar hannunta, a hankali ya sauko daga kan gadon ya karba ya kai mata baki yana kallonta yace "Eat!" Ta kauda kai da sauri, kallon Ayabar yake yana son ci amma ya kasa, ajiyewa yayi ya dau Apple ya mika mata, Kin karba tayi, yayi murmushi ya ajiye shi ma, a hankali ta kwanta nan gefensa, ya tsura mata ido, kamar warce aka tsikara ta mike xaune da sauri, ya koma baya yana kallonta.

*Haske writers Association*
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

18.....

Amai ta shiga kwararowa a gurin, ya mike yana kallonta har ta gama ta koma xata kwanta yayi saurin riketa, kara ta saki ta turasa da karfi xata kwanta gun aman yaki saketa, nan ta shiga kokuwa da shi ita sai ta kwanta, ya rike ta gam yace "Wait Jasmine..." ta kuma sakin wani ihun da ya tsorata shi, ae da ta turasa sai da ya kusa faduwa ba shiri ya saketa, ta yi kwanciyarta nan kasa, ya sauke ajiyar xuciya ya nufi toilet, mop da bucket ya dauko ya dawo dakin, rasa ta inda xae fara gyara wajen aman yayi, ya ajiye ya fita don kira Mama jummai, tare suka shigo dakin, ta karaso kusa da ita da sauri cike da tausayinta ta dagota tana mata sannu, ihu ta sakar mata ita ma ta kwace kanta ba shiri ta saketa ta koma ta kwanta tana mayar da numfashi, girgixa kai mama tayi ta mike ta shiga gyara wajen, tana gamawa ta kuma gwada d'aga ta a kasan tiles din still taki tashi, kyaleta tayi ta fita, Junaid ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito jin kiran isha, a nan dakin yayi sallah, yana xaune kan darduma ya ga tana juye juye a kasan da take kwance. Kallonta kawae yake cike da tausayinta don da ganinta kasan tana jin jiki, ta mike xaune a hankali ta dawo inda yake tana kallonsa ta kwanta kusa da shi, dagota yayi murya can kasa yace "Sorry Jasmine" lumshe ido tayi ta kwanta nan kusa da shi lkci daya bacci ya dauketa, ya mike ya koma can jikin gado ya xauna, har Karfe tara El-Ameen bai dawo ba, duk ya kagu ya dawo ya wuce kafin Mumy fa kirasa, tara da rabi kiran Mumy ya shigo wayarsa, k'asa d'agawa yayi don bai ma san me xai ce mata ba har sai da ya kusa katsewa sannan ya daga da sauri, Mumy tace "Where are you Ahmad" kallon dakin yayi kafin a hankali yace "Mumy, am am with El-Ameen" strictly tace "You are very stupid, within the next 10 to 15 mins ka tabbatar kana cikin gida if not xaka ga bacin raina, in kuma kaya ku ka kasa a titi ku ke saidawa da daddaren nan xaka gaya min" kamar mai shirin kuka yace "Kiyi hakuri Mumy xan dawo" katse wayar tayi, ya rike kansa, layin El-Ameen ya shiga nema yana ta ring bai d'aga ba, ya lumshe ido ya jingina jikin gado, he just don't know wat to do, haka yayi ta kiran El-Ameen bai daga ba, Shivering yaga tana yi daga kwancen da take kan darduma, ya mike ya karasa inda take ya dago ta ta bude ido da sauri, kan gadon dakin ya kwantar da ita ya rufa mata bargo, ta cire xata sakko ya riketa da damuwa yace "You are shivering Jasmine" ba shiri ya saketa a dalilin kara me karfi da tayi masa a kai, ta sauka nan kasan dakin ta kuma kwanciya. Har goma El-Ameen bai dawo ba, Junaid ya rasa me ke masa dadi shi da bae taba yi ma Mumy musu ba, yasan kuma fushi tayi shi yasa bata kara kira ba, da yayi niyar tafiya sae ya tuna abinda El-Ameen yace masa, ya kuma san xai aikata, shine xaune har sha daya, Mama jummai ta shigo tace "Kai xaka kwana yau a nan kenan junaid?" D'an murmushi yayi yace "A'a ina jiran El-Ameen ne yace xai dawo" tace "Toh tafi daki can ka kwanta inda yake kwana xan kula da ita" Junaid yace "yana kwana nan ne?" Tace "Eh wani lkcn yana kwana can dakin don akwai alluran da yake mata da sassafe, toh duk ran da xai mata alluran a nan yake kwana, ni kuma tare muke kwana da ita saboda shiga bayi da daddare" Junaid ya gyada kai yace "Bari in jira sa a nan Mama ni ba kwana xan yi ba ai" tace "Toh" sannan ta juya ta fita. Lumshe ido yayi ya jinginar da kansa jikin gado, wani bacci ya ji na fixgarsa ya bude ido yana kallon agogo yaga sha biyu, kallonta yayi ya ga ta canxa position, a hankali ya mike ya isa inda take xai dagata ta bude ido da sauri, birginawa tayi ta bar gun ta juya masa baya, ya mike ya koma ya xauna kan gadon, xuwa yanxu kam ya gama sanin iskanci El-Ameen yayi masa, dole ko yaki ko ya so a nan xai kwana hakan ba karamin bata masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login