Showing 135001 words to 138000 words out of 170905 words
Chapter 46 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
dauke kai Junaid yyi, El-ameen yace "Na mayar da Humainah da yace kayi!" Shiru Junaid yayi masa na kusan minti sha biyar kafin ya juya ya kallesa yace "Ehh" ko kallonsa El-ameen bai yi ba idonsa na kan titi, murmushi Junaid yayi ya shafa kai, sha biyu saura suka isa masarautan, El-ameen ya fito daga taxin haka ma Junaid dake bin ko ina da kallo, Kudi El-ameen ya ciro ya ba mai taxin sannan ya nufi Entrance din masarautan junaid ya bi bayansa, gaba dayansu dakakkiyar Shadda ce jikinsu, shi El-ameen ruwan hoda, shi kuma junaid fari, yana biye da shi ne yana danna waya, tafiya sosai suka yi kafin su iso main Entrance din da xai kai su har palace din, fixgosa Junaid yayi ganin tafiyarsa kawai yake yace "Meye xaka wani dinga wucewa kana kyaleni a baya, ko na ce ma nasan hanya ne" kallon mamaki El-ameen yayi masa kafin ya duka yace "To hau!" Junaid bai san lokacin da ya fara dariya ba yace "Ka ji dan iska, kai har xaka iya goya ni?" Murmushi El-ameen yayi ya mike don ko ba komai ya sa shi dariya baxae shiga yana murtuke ma mutane fuska ba, a tare suka jera suna tafiya, Junaid yace "Wani disc ne na gani daxu a hannun ka a plane" El-ameen yace "Na ban mamaki ne" Abdul dake tsaye da abokansa biyu gun mota da alamar xa su fita ne ya hangosu ya karaso da sauri yace "Ohh baki gare mu haka... Welcome to you guyz, sannun ku da xuwa" hannu ya basu gaba daya biyun sannan yayi masu jagora har xuwa fada, ganin Abbansa na da baki ya nufi part dinsa da su, suna shiga parlonsa Junaid ya nemi gu ya xauna ya cire hular kansa, Abdul yace "Amma flight ku ka biyo koh?" El-ameen yace "Eh my oga at the top yace bai iya xaman mota ba sbda kura" dariya Abdul yayi yana kallon Junaid, junaid yayi murmushi yace "Manta da shi basir gare sa bai iya xaman mota shi yasa muka biyo jirgi" dariya suka dinga yi gaba daya, El-ameen ya jefa masa hular kansa yace "Kaji sharri...." Drinks kala kala da kayan marmari Abdul ya dire masu ya xauna yace "Toh ya mutan gidan, ya muka baro ku?" El-ameen ne kadai ya amsa don shi junaid kallonsa kawai yake ganin ba kaman wasa suke da kanwarsa ba, waya Abdul ya dauka ya ce bari in kira maku mutuniyar ku gaisa kafin Abba ya sallami b'akinsa, yana kara wayar a kunne bayan ta daga yace "Lil sis, ki taho ina jiran ki part dina" daga haka ya katse wayar, bayan kusan minti goma sai ga ta ta shigo parlon, wani alkybba dake daukar ido ne jikinta har yana jan kasa, shi kansa takalmin kafarta abun kallo ne, hular kanta ya rufe kusan rabin fuskarta, tana ganin mutane xaune parlon ta turo baki ta nufi bedroom don ta gaji da gaishe gaishe, Abdul yace "Ina kuma xa ki bakin ki ne fa" daga kai tayi da sauri ta maida hular saman kanta, ido hudu suka yi da junaid ya kasa dauke idonsa kanta, tayi saurin kauda idonta ta kalli El-ameen dake kallonta shi ma ko kiftawa babu, wani kyalli take gaba dayanta, tayi wani kyau na musamman duk da ba make-up bane fuskarta, murmushi tayi da ya bayyana fararen hakoranta ta karasa gun El-ameen ta durkusa nan kasa cikin sanyayyen muryarta tace "Welcome!" Kai kawai ya iya gyada mata, Abdul kuma yayi excusing kansa ya fita, da kyar El-ameen ya samo abun cewa yace "Ya gidan, ya su mama!" Ta langwabar da kai tace "Taso mu je ku gaisa da su" Junaid dai danna wayarsa kawai yake, El-ameen yace "Baku gaisa da captain ba?" Gefenta ta d'an kalla tace "Ohk, sannu da xuwa" daga haka ta mike tace "Mu je gun Ummata" mikewa El-ameen yayi
ya dau Apple daya ya kalli junaid yace "taso mu je muyi gaisuwa frnd" junaid yi yayi kamar bai ji sa ba, Zahrah tuni ta nufi kofa ta fita abunta, warce wayar El-ameen yayi yace "kaga ka ajiye halin nan naka aside har mu bar garin nan, in girman kai ne da ji da kai toh gidansa ka xo, bbu wanda xaka nuna ma a nan sai dai ma ka kara course wajen su" mikewa junaid yayi yace "Dama don ku ci min mutunci yasa kuka dage sai na xo garin nan, how dare her xata shigo ta ki gaisheni tana min kallon rainin wayo, da ana rubuta hali a goshi wllh da ban fara ko da kallon inda take ba bare har na tausaya mata" yar dariya El-ameen yayi yace "Yau kuma ba don Allah kayi ba kenan......" Wani tafarfasa xuciyar junaid yake, El-ameen ya tabe baki yace "If you like kar ka fito muyi me ya kawo mu bar garin nan" daga haka yayi ficewarsa ya barsa gun tsaye, tsaye ya ga Zahrahn tana jiransu ga dukkan alama taji abinda suka ce, murmushi ya mata yana fatan Allah yasa ba jin dai tayi ba. Ta mayar masa da murmushin tayi gaba tana cewa "Kila yana da matsalar kunne ne, shi ya hanasa jin sannun da nayi masa," da sauri El-ameen ya kalli bayansa ya ga ko yana gun, ya ga ko fitowa bai yi ba, can ko sai ga shi ya fito, Tana gaba El-ameen na biye da ita a baya shi kuma junaid na bayan El-ameen, bangaren Kilishi ta fara kai su, sosai tayi farin cikin ganinsu, ta sa aka cika su da kayan ciye ciye da sha, Shi dai junaid idonsa na kan makeken plasman parlon dake cike da kayan alatu, ganin yaki taba komai tace "Kai ya sunanka, ko kai ne takwaran mai martaba?" Girgixa kai yayi yace "A'a, Ahmad" tace "Babana ne ma ashe, to baka ci komai ba.... Ba a mana haka fa" da ganin murmushin da yayi kai kan ka kasan kirkira yayi, ya dau slice din kankana ya Kai baki yana tauna da kyar, ta gefen ido Zahrah ke kallonsa can ta tabe baki hade da murguda bakin, El-ameen kuma hararansa kawai yake ta gefen ido, ita ko Kilishi sai kallonsa take haka nan taji ya burgeta, jikinsa ne ya basa kowa kallonsa yake ya ki daga kai ya kuma daukar apple ya kai baki ya gutsura a hankali, Zahrah tace "Mumy bari in kai su gun Umma" Kilishi tace "Toh maxa ku je Zahrah" mikewa tayi tana kallon El-ameen tace "Mu je" mikewa yayi shi ma yayi mata sallama tace "A'a mai gida ai xaku dawo" kallon Junaid tayi tace "Toh tashi ku je babana" d'an murmushi yayi ya mike yace "Sai mun dawo" daga haka suka fita gaba daya daga parlon, a tare suke tafiya da El-ameen suna hira jefi jefi, El-ameen yace "Yayanki ne Abdul din nan koh?" Ta gyada kai tace "Yea, stepbrother nah" ya wara ido yace "Waow, mum dinsa ce kenan wannan!" Ta gyada kai tace "Ehh shi da Ummi" yace "Ayya, amma kina da kanni ko yayyi the same mum kuwa" girgixa kai tayi tace "I am the only one gun Ummata" kallonta yake da mamaki, yaji tausayin mahaifiyarta sosai, ko ya tayi da Allah ya rabata da only child dinta, junaid dai distance me d'an tsayi ya bari tsakaninsu yana biye da su hakan kuma bai hanasa jin hiran tasu ba, daya daga masu girke girken fadan ne ta washe baki ganin Zahrah tace "Gimbiya ban ganki kitchen yau ba" d'an murmushi tayi ta tsaya har ma'aikaciyar ta karaso kusa da ita, El-ameen ya ci gaba da tafiya, Zahrah na kallonta tace "Ina ciwon kai ne shi yasa... Ya aiki?" Matar tace "Alhmdllh, b'aki kika yi?" Kada mata kai tayi dai dai lokacin da Junaid ya karaso ya wuce su, ta bi sa da wani kallo kafin ta tabe baki tace "Da rana xan shigo kitchen Karima" daga haka ta nufi El-ameen dake tsaye wani stairs yana jiranta, ita kuma matar ta bi ta da kirari, ta gefen ido junaid dake tsaye gefen El-ameen ke satan kallonta har ya ga ta kusa isowa, El-ameen na ganinta ya ci gaba da tafiya, shi kuma yana ganin xata wuce sa ya sa mata kafa, ko lura bata yi ba sai ji tayi ta tafi luu xata fadi, tayi k'ara a tsorace tana neman regaining balance, bai san lokacin da yayi saurin tarota ba ta fado jikinsa, still tayi da farko sai kuma ta dago kai da sauri suka yi ido hudu, kasa motsi tayi ta kuma kasa dauke idonta cikin nasa, shi ma kallonta kawai yake gabansa na faduwa, bakinsa ta ga yana motsi a hankali ta sauke idonta kai underneath his breathe taji yace "Jas...jasminee!" Gaba daya ta shagala da kallonsa, shi ya fara dawowa hankalinsa ya saketa da sauri, sai a sannan ta koma baya duk ta daburce, a tare suka juya da sauri kallon El-ameen suka ga gun wayam babu shi.
*Haske Writers association*💡
Afuwan pls.
[3/19, 9:36 PM] El-hajj💥: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
Da sallama ta tura kofar parlon ta shigo rike da wani babban tray mai dauke da abinci bayanta maids biyu wata dauke da bowl din fruit, wata kuma food warmers har biyu, kallonta kawai suke har ta karaso makeken parlon ba tare da ta dago ba ta ajiye tray din hannunta ta juya xata fita, a hankali El-ameen yace "Fatima!" Tsayawa tayi amma bata juyo ba, Junaid dai sai kallonta yake, jin ba ace komai ba tayi ficewarta daga parlon, saukowa El-ameen yayi ya dau fruit ya fara ci yana kallon junaid, tun xuwan su Bauchi ya rasa dalilin sanyin da yayi lokaci guda, har ya gama cin abinda xai ci junaid bai ko kalli abincin ba, El-ameen ya mike ya shiga bedroom ya bar sa parlon, rike kai Junaid yayi don shi kadai yasan abinda ke damunsa. Bayan isha ya fito makeken haraban masarautan sanye da kananun kaya ko ina farin wuta ne wanda hakan ya maida gun kamar safiya, tafiya kawai yake hannunsa cikin aljihu iska mai dadi na kadawa har ya karaso garden din da yasan xai ganta, ai kam xaune ya ganta ita kadai kan lallausan rug tana sanye da alkyabba kalan gold sai kyalli yake ta xauna kan kafafuwanta, ba wani wuta ne me haske gun shakatawar ba, gabanta bowl ne me dauke da apple fruit, ya rasa me ta tsura ma ido a gun, har ya karaso kusa da ita bata sani ba sai da sanyayyen kamshinsa ya bugi hancinta, duk da haka bata juyo ba idonta na kan grasses din wajen, ya xauna d'an nesa da ita cikin sanyin murya yace "Jasmine" bata kallesa ba bare tace komai, sake kiranta yayi nan ma dai bata amsa ba, dawowa kusa da ita yayi ya kuma kiranta a karo na uku, juyawa tayi tana kallonsa bbu yabo bbu fallasa tace "Sunana ba Jasmine ba" helplessly yake kallonta a hankali yace "Ohk fatima" dauke kai tayi bata ce komai ba, bai sake cewa komai ba lokaci lokaci ya kan juya ya kalleta, mikewa tayi daga karshe ta dau apple daya tace "Am going in" daga haka ta yi gaba ta bar sa wajen, ya bi ta da ido, lumshe ido yayi ya hade kansa da gwiwa, a hanya ta hadu da El-ameen ya mata murmushi yace "Princess!" D'an murmushin ita ma tayi ta wuce bata ce komai ba. Bangaren Ummanta ta nufa ta sameta xaune da baki da dama a babban parlonta, sallama tayi masu ta yi hanyar dakinta duk aka bi ta da kallo, mikewa Umma ta yi tayi excusing kanta ta bi bayanta, tana kokarin cire alkyabbarta ta shigo dakin, ta juya tana kallon uwar tata, Umma ta kamota ta xaunar gefen royal bed din dake dakin tace "Zahra!" Dago manyan idonta tayi tana kallonta tace "Na'am ummana" Umma tace "Why didn't you greet at the parlor" a hankali tace "Na fa yi sallama ummana" Umma tace "No da kin tsaya kin gaida su, they are ol here because of you daughter" sunkuyar da kanta tayi tace "Am sorry Umma" Umma ta rungumeta sosai jikinta lokaci daya hawaye ya taru idonta tace "It's OK sweetheart, kin kai ma su Ahmad din abincin kuwa" gyada kai tayi tace "Na kai" Umma tace "Good je ki gun Abba ki masa sai da safe, ko kin je?" tace "Naga yana da visitors ummana" Umma tace "Suna masauki yanxu, tashi ki je" tace "Toh ummana" mikewa tayi ta mayar da alkyabbar da ta cire suka fita dakin tare da umma, sai da ta fara karasawa cikin babban parlon ta durkusa ta gaida matan dake xaune, duk suka amsa suna kallonta da sha'awa, sannan ta mike ta fita, babban parlon Abbanta ta tafi sanin ya bar fada yanxu, ta gansa xaune kasa kan lallausan carpet din dake shimfide fruits gabansa daga gefensa Ya Abdul ne, sai yayyinta maza su hudu gaba, duk suka dinga kallonta har ta karaso gun Abba dake ta kallonta shi ma murmushi shimfide fuskarsa, mikewa xaune yayi yace "My princess" tayi murmushi tace "Abbana!" Ganin yanda yayyinta ke kallonta ta hararesu tace "Ni bana son kallon" dariya suka yi gaba daya har da mai martaba da ba kasafai yake dariya ba sai dai murmushi, da ganinsa kasan farin ciki ne karara tare da shi, ya Abdul kadai ne kansa a kasa sai dai lokaci lokaci ya kan dago ya kalleta, sun yi hira sosai da yayyin nata daga bisanni ta masu sai da safe har da Abba ta koma bangaren Umma. Washegari da ya kama Friday ana sakkowa juma'a, parlon mai martaba ya cika dam da 'yan uwa da abokan arxiki da suka taho nuna masa farin cikinsu na bayyanar tilon 'yar sa, haka kuma ranan da su Junaid xa su koma kenan kasancewar kwanan su uku a masarautan, Mai martaba sai kallon junaid da ko dago Kai bai son yi yake, can yayi gyaran murya yace "Ahmad?" Kallonsa junaid yayi sannan ya amsa, Mai martaba yace "Ka fadi duk abinda kake so nan duniya Ahmad in dai bai saba ma Shari'a ba kuma bai fi karfina ma na maka alkawarin yi maka shi koma menene" a baxata cewar sarkin ya xo ma junaid, ya sunkuyar da kai bai ce komai ba, haka kawai gaban El-ameen dake gefensa ya dinga faduwa, junaid ya dago da kyar yana kallonsa cikin sanyayyen muryarsa yace "Bana bukatan komai ran ka shi dade, I helped her for Allah's own sake" kallonsa kawai sarkin ke yi daga bisanni ya juya yana kallon El-ameen dake kallon junaid yace "Kai fa Aminu?" Ido junaid ya xuba masa ya ji abinda xai ce, El-ameen da har lokacin gabansa bai bar faduwa ba cikin tsarkewar murya yace "Ina son ka min alfarmar bani aurenta ran ka shi dade, na maka alkawarin xan rike maka ita da amana...." wani mugun bugu xuciyar junaid yayi lokaci daya yaji kamar xuciyar ta bar aiki, mai martaba da ya kafa ma El-ameen ido yayi murmushi yace "Na baka! Bbu ko sisin ka kuma" Kallon mamaki duk occupant din fadan ke ma mai martaba don baya magana biyu. El-ameen da ya rasa wani irin godiya xai ma mai martaba ya mike ya isa gabansa ya durkusa yana kallonsa, shafa kansa mai martaba yayi yace "You are blessed in'sha Allah son" kama hannunsa El-ameen yayi ya lumshe idonsa da ya kada ya kai lips dinsa, junaid ya lumshe idonsa da ya kada shi ma lokaci daya yana jin xuciyarsa kamar ba tasa ba.
*Haske writers association*💡
_Toh ga Captain Ahmad Junaid yayi gaba har ya kusa end_ Tnx for everything. My novel inteesar if am not mistaken yana da pages kusan dari biyu, my novel ikram had a hundred nd 15 pages or so, my novel Aneesah had 112 if am not mistaken, Dr Khaleel had 120 pages also, 'ya mace kyautar Allah na goni also have the same, kuma duk an san bbu ma banxa a novels din nan, I don't write anyhow may be just once in a year, but idan nayi i will alwayz make sure it makes sense, am just in page 54 a Capt Ajay kuma nasan nan gaba xai kai har 120 ne but see what my fans are saying, you never judge a book by it cover, and am not in a haste while writing my books, ban taba novel da na dakata for weeks ba sai capt a jay, toh kullum xan dinga xuwa media ina announcement mahaifiyata bata da lafiya, ina ma nake da nutsuwar rubutu uwa ta ba lafiya yanxu haka ma bata kasar, ga kuma karatu da nake, i can't be coming to media and giving excuses everyday, all the same am grown up yanxu I won't retaliate but nagode kwarai Allah bar xumunci. in ma jan labarin nayi you don't have to be giving me hurt words, sai ka bar karantawa ka jira in kai inda kake so sai ka ci gaba Meye a ciki. Duk Allah ya baku hakuri.
[3/19, 9:36 PM] El-hajj💥: *Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
79
Da sauri ta sauka ta bi bayansa, junaid ya bi ta da kallo har lokacin xuciyarsa bai bar bugawa ba, da kamar ya koma part din Abdul sai kuma kawai ya bi bayanta, ji yayi gaba daya yaji haushin kansa, ya ja tsaki ya ci gaba da tafiya kamar bai son yi, tsaye Zahrah taga El-ameen da wasu dogarawa suna hira, ta kasa karasawa gun, juyawa yayi suna hada ido ya sakar mata murmushi, kasa mayar masa tayi, yace "ban san hanya ba, I've to wait for you....." Karasowa tayi da kyar ba tare da ta ce komai ba ta ci gaba da tafiya, bai bari suka hada ido da junaid dake tahowa ba ya daga ma dogarawan hannu ya bi bayanta, tafiya kawai take amma ji take kamar xata harde ta fadi kasa, duk yana lura da ita hakan yasa ya karasa suka jera da ita yace "Masarautan nan naku da girma sosai" ta gefen ido ta kallesa tace "Yyeah!" Rasa abun cewa yayi shi ma can kuma yace "But kin gama sec sch kuwa?" Shiru tayi