Showing 132001 words to 135000 words out of 170905 words

Chapter 45 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

628

Sarki ya kalli Zahrah da ke xaune daga kasa kusa da shi, sannan ya kalli Junaid yace "Kasan yarinyar nan?" Junaid ya daga kai yana kallon kwayar idonta, Sunkuyar da kai tayi da sauri ta dalilin faduwa da gabanta yayi, sai da sarkin ya kuma nanata tambayar sannan ya gyada kai kawai, Hajja da ko k'adan bata gane Zahrah ba ta yo waje da ido tace "A ina ka santa don ubanka?" Kallonsa kawai sarkin ke yi, a ransa kuwa tunani yake anya shi din El-ameen ya basa labari jiya, da irin fadin ran nan ya taimaki 'yar sa kenan, A fili kuwa cewa yayi "Toh a ina ka santa Ahmad?" Kallon El-ameen Junaid yayi yace "Shi ma ai ya santa, ya ma fi ni saninta" Hajja ta mike tace "Atoh a hankali gaskiya dai xata bayyana don ni nasan jikana bai santa ba sai dai abokinsa" Aminin sarki ne yace "Ahmad kake koh? Toh kasani ba karamin mutum bane nan gaban ka, am repeating this, you go straight to the point and answer his questions right away, takanas ya taso tun daga bauchi domin ka don haka kar ka maida mu kananan mutane" Mumy ji tayi ta kasa tsayuwar ma, da kyar ta samu waje ta xauna tana kallon ikon Allah, Junaid kam dama ba direction dinsu yake kallo ba, Sarki ya nisa yace "Ahmad, ni ne Mahaifin Zahrah, ka kuma min abinda har karshen rayuwata baxan taba mancewa da kai ba, ka dawo min da farin cikina ka fitar da ni kunci lokaci daya, ashe har yanxu akwai sauran mutanen kirki a duniya? ashe akwai masu xuciya irin taka a duniya, kaf rayuwata ban taba jin na kaunaci mutum kamar yanda naji kaunar ka daga jiya ba, da kai na kwana a raina jiya Ahmad....." Hajja sai wuwwulla ido take tana jiran jin me yayi ma sarkin, Sarki yace "Xan so ka ban labarin yanda ka ga Zahrah har ixuwa jiya Ahmad" k'in dagowa Junaid yayi da farko can ya dago suka hada ido da sarkin sai yaga yayi masa kwarjini, da kyar ya iya cewa "Nayi xaton El-ameen ya fadi maku ranka shi dade" Sarki yayi murmushi yace "Ehh, amma xan so sake jin labarin daga bakin ka" Junaid ya shafa kansa ya kalli Abba dake kallonsa, sannan ya dauke kai, xaunawa Hajja tayi tana jiran jin labari ita ma, Kamar baxae ce komai ba sai kuma cikin sanyin murya yace "It all happened on a faithful tuesday evening....." Lumshe ido yayi ya bude ya shiga ga bada labarin tun daga ranan da ya fara ganin Zahrah a gefen titi, bbu abinda ya canxa daga wanda El-ameen ya fadi ma sarkin jiya, yanda ya kama mata gida da farko daga karshe kuma suka koma gidan El-ameen, irin hidima da wahalhalun da suka yi shi da El-ameen a kanta, da yanda suka boye ma iyayensu, mama jummai da suka dauko.... kai bbu abinda ya boye har gida da ya kawota da nufin aurenta da yanda iyayensa suka gane ba mai hankali bace..... Bbu wanda jikinsa bai yi sanyi ba a parlon, Hajja ta rushe da kuka tace "Ae dama nasan jikana yaron kirki ne, Allahu Akbar, xaka aikata fiye da haka ma don k'akan ka ka gado " sunkuyar da Kai Junaid yayi ya kasa ci gaba don dama yanda yake bada labarin kamar bai son yi, Aminin sarki ne yayi Encouraging dinsa da ya ci gaba don sarkin kasa cewa komai yayi banda ido da ya tsura masa, Zahrah kam banda kuka babu abinda take jikinta yayi sanyi ba kadan ba, ita kanta Mumy hawayen ne ke sakko mata, cikin sanyin murya junaid ya ci gaba yace "I had to take her away..... muka bar gidan and....." shiru yayi kafin ya fadi yanda suka yi hatsari bayan barinsu gidan wanda shi ne dalilin dawowan hankalinta sai dai kuma tayi losing memory ta mance komai, bai boye yanda ya janye jikinsa daga lokacin bisa umarnin da iyayensa suka basa, ya fadi yanda ya bar ta da El-ameen bai kuma bi ta kanta ba, El-ameen kuma ya kai ta gidan Course mate dinsa tayi kusan wata biyu a can, a watannin ta biyu a gidan sau daya yace yaje daga nan kuma bai sake komawa ba, har aka yi aurensa da Humainah, ya fadi shawarar da El-ameen ya basa da yanda ya amince ya maidata gidansa da xama gaba daya ya kuma sa ta a islamiyya, bai boye irin matsalolin da suka dinga fuskanta da Humainah a kanta, ya kuma fadi dalilin sa na sakin Humainah, bai rufa komai ba kan irin xaman da suka yi da Zahrahn bayan barin Humainah gidan har ya kai karshen labarin da fadin dalilin dawowar memory dinta, sai da idon kowa ya kawo a parlon, ya kusa minti biyar kansa a kasa kafin ya dago a hankali, hawaye ne cike idonsa ya mike ya isa gun Mumy ya durkusa ya daura kansa a kafarta a sanyaye yace "Ki gafarceni Mumy, nasan nayi disobeying din ki, na kuma boye maki abinda nayi which I wasn't suppose to ko da kuwa baxa kiyi supporting dina ba shi yasa komai bai tafi min dai dai ba, forgive me plss Mumy....." Hawaye kawai Mumy take bata iya ta ce masa komai ba, ya mike ya isa gun Abbansa shi ma ya durkusa gabansa hawaye na sakko masa yace "Ka yafe min Abba, I know I... I failed you....."Jin Abba bai ce komai ba yasa shi mikewa a sanyaye, tashi sarki yayi ya taka har gabansa ya dafa sa sai kuma ya rungumesa yace "They will all forgive you in'sha Allah son, sannan ina me umartarka da ka mayar da matarka ka nemi gafararta....." Daga haka ya sake sa ya isa gaban Abba yace "Ina neman alfarmar ku yafe ma Ahmad duk abinda ya maku a kan Zahrah...." Murmushi Abba yayi ya mike yace "Bai min komai ba mai martaba, Allah ya basa ladan abinda yayi, ina alfahari da kasancewarsa d'ana, yasan ba lallai in sauraresa ba a lokacin shi yasa yayi komai gaban kansa, Allah ya biyasu gaba daya da abokin nasa, is good thing sun riketa amana, ta kuma samu lafiya ta dalilin su, I am proud of them....." Mikewa Mumy tayi a sanyaye xata fita Sarki yace "Toh Hajiya bamu ji kin ce kin yafe masa ba, ina nema masa wannan alfarmar don Allah" murmushi kawai tayi, Hajja da baki ya ki rufuwa tace "Yo wa ya sani ko bakin ciki take masa kamar yanda matan ubansa ke masa, ni dama tun ran da Amadi ya kawo yarinyar gidan na daura ido na kanta na ji ta kwanta min toh tunda yan gida suka ce mahaukaciya ce basu san xance ba ina ni ina magana ace don ba ni na haifesa ba" kallonta kawai junaid yake haka ma El-ameen dake murmushi, sarki yayi murmushi shi ma yace "Da fatan mun kafa xumunci kenan har illah maa'sha Allah" Hajja ta mike da sauri tace "toh ni makka xaka kai ni, shekarana uku rabona da can wllh" 'yar dariya sarkin yayi yace "Kina da kujeru biyar wannan shekarar Idan Allah ya yarda" shewa tayi tace "Allah yayi maka albarka...... Sai mu je tare da Humainah da kawayena Uku" kofa junaid ya nufa xai fita daga parlon sarki ya kirasa, juyowa yayi yana kallonsa, sarkin yace "Ina gayyatar ka masarautar mu tare da El-ameen, ur labours will not go in vain" Shiru Junaid ya d'an yi sai kuma yayi kasa da kai yace "Sai na dau excuse gun aiki idan Allah ya yrda" Kai kawai sarkin ya gyada masa, Satan kallon Zahrah yayi ya juya ya fice, kamar warce aka tsikara ta mike ta bi bayansa da sauri.

*Haske Writers association*💡
[3/19, 9:36 PM] El-hajj💥: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

77......

Bin bayansa Zahrah tayi, ya ki tsayawa ita ma bata ce ya tsayan ba ya nufi part din Mumy, yana bude kofar ta ja ta tsaya tace "Amm... Ahmad Junaid!" Lokaci daya ya juyo ya sauke idonsa kanta yace "Yess!" Wani mugun kwarjini ya mata ta kasa cewa komai sae kallonsa take, daga kasa har sama ya kalleta sannan ya juya yayi shigewarsa parlor, still tayi gun kamar warce ruwa ya cinye, duk wannan abun El-ameen na tsaye balcony yana kallonsu, juyawa tayi suka hada ido da shi, hawaye ne ya ciko mata ta sauka daga balcony din da sauri ta nufi gunsa tana kallonsa lokaci daya hawayen idonta ya silalo tace "kaga abinda yayi min koh?" Murmushi El-ameen yayi ya buda ido yace "Yea! Haka nan yake! but idan ya sauko xa ki ga he is the sweetest guy you never expect.... He's still angry at you ne shi yasa" a sanyaye tace "But he shud have listen to me..... He's a sadist I notice" dariya sosai El-ameen yayi ta turo baki, tace "I just have to make him forgive me before leaving that's all!" El-ameen ya d'age gira yace "Go in ki samesa...." Shiru tayi sai kuma a hankali tace "In je?" Gyada mata kai yayi ta juya ta koma part din Mumy, tafiyarta kawai yake kallo har ta isa kofa ta murda a hankali ta tura ta shiga, durkushe ta gansa a parlon kusa Humainah dake kwance kan doguwar kujera idonta lumshe, tsaye tayi bakin kofar ta kasa karasowa, kallo daya yayi mata ya dauke kai, Dakewa tayi ta karaso parlon cikin rashin kuxari, dai dai lokacin da Humainah ta mike xaune da sauri, ya mike ya xauna gefenta yana kallonta ganin yanda ta rame, hannunta ya rike kamar bai son magana don bakinsa kadai yayi motsi yace "What wife!" Ta dafe kanta bata ce komai ba, can ta d'ago da kyar tace "Amai nake ji" mikewa yayi ya daga ta suka bar parlon, ita ko lura da Zahrah da tayi still tana kallon ikon Allah bata yi ba har ya shiga da ita daki, Zahrah taji ta ma kasa tsayuwar, tunda take bata taba jin abinda ta ji a lokacin a xuciyarta ba, kawai ji tayi hawaye ya cika idonta, ta juya da sauri har tana neman faduwa ta fice daga parlon. Bata ko kalli El-ameen dake tsaye har lokacin ba ta tafi can karkashin bishiya tayi xamanta gun ta fashe da kuka, juyawa El-ameen yayi ya koma parlon Abba, drinks ne da ruwa gabansu mai martaba kuma ga dukkan alamu hajja ce ta debo masu, yana shiga tace "yauwa tafi ka kira Amadin su yi sallama da Sarkin wai xa su koma" fita ya kuma yi ya tafi part din Mumy, khadija da fatima ne parlon don dama suna ganin shigowar junaid suka shiga daki, amsa gaisuwar fatima yayi yace "Ina Junaid din?" Khadija tace "Yana daki" yace "Tafi ki ce masa Abba na kiransa" mikewa tayi shi kuma ya juya ya fita, ba a dau lokaci ba Junaid ya fito ya karasa gun El-ameen, El-ameen yace "Hope ka saurareta dai yanxu?" Girgixa kai yayi yace "Bani da lokacin ta, bana kuma bukatan godiyar da xata min ko hakurin da xa ta ban, don Allah nayi mata ba don ita ba wllh" Murmushi El-ameen yayi yace "Gaskiya ne" Junaid ya shiga parlon Abba, nan dai suka yi sallama da mai martaba dake sauraren xuwansa da El-ameen nan da kwana biyu, Zahrah na ganin fitowar Abbanta ta mike ta nufi gate da sauri, Ummi ta bi bayanta ganin mood dinta, Abdul ma bin ta yayi da kallo, har bakin mota Hajja da su Abba suka raka mai martaba, sai surutu take masa kamar irin ta san sa da can, junaid dai na biye da su a baya, lokaci lokaci mai martaba kan juyo ya kallesa, ita ko Zahrah can wani mota ta tafi ta tsaya a baya Ummi sai tambayarta take meyasa mood dinta ya canxa amma ta ki cewa komai, a hankali junaid ya dinga bin wajen da kallo ganin bai ganta ba, har cikin motar dake gabansu sai da ya kalla bbu ita, El-ameen dai na tsaye rungume da hannayensa yana kallonsa, tsaf ya gane me yake nema, kawai yayi murmushi, Mai martaba kansa sauraren Hajja kawai yake amma rashin ganinta ya sa ya fara waige waige shi ma, can dai yace "Ina Zahrahn ta xo ta shiga mota" Ummi ce tace "Toh kinji Abba na neman ki ma, ki taho mu je" ba musu Zahrah ta fito daga bayan motar sai dai duk jikinta a sanyaye, satan kallonta Junaid ya dinga yi har ta iso gun motar da suka taho da, Hajja ta jawota ta rungume tace "Kice ma Uwar ki ina nan xuwa, xata yi babbar bakuwa don tare xamu taho da su Amadi, Allah ya maki albarka ni dama tun farkon ganin ki kika kwanta min don akwai ni da tausayi" kai kawai Zahrah ta gyada mata ta bude bayan mota ta shiga Ummi ma ta shiga, junaid bai fasa mata kallon sata ba, ita ko bata ko kalli su waye a tsaye gun ba, tana shiga motar ta rufe ido, bata kuma bude ba sai da taji tashin motar da fatan kai wa gida lafiya da su Hajja keyi masu, ta kalli tagar motar suka yi ido hudu da junaid, dauke kai tayi da sauri, can kuma ta kalli El-ameen dake kallonta shi ma, d'an murmushi ta kirkira ta daga masa hannu a hankali, shi ma ya mayar mata da murmushin, driver ya ja motar suka dau hanyar fita daga layin. Tuni su Abba suka shiga gida, Hajja dai har lokacin bata fasa daga ma motocin da har sun bar layin hannu ba baki a wangale, El-ameen yace "Toh ae sai ki sauke hannun haka" juyowa tayi da sauri tace "Kaga ikon Allah ko Aminu, ashe dama tsinannun matan Muhammadu ne ke tare mana hanyar arxiki a gidan nan, yo gashi suna barin gidan sai ga sarki sukutum ya kwaso kafafuwa ya xo ganin jikana...." El-ameen yayi dariya yace "Toh jikan naki dai ba mutumin kirki bane don walakanci ya ma yarinyar daga ta bi sa tayi masa godiya kin dai san hali..." Tsuke fuska tayi ta kalli Junaid dake tsaye da sauri tace "Wato don ubanka ni xaka ma bakin ciki koh? Toh Allah ya isa idan aka hanani kujerun makka nah, kai baka yi murnar ta dalilin ka sarki ya shigo gidan ubanka ba, kasan alkhairin da yake shirin yi ma xuri'ar mu.... Ka xata sarauta abar wasa ce... Toh gobe gobe ka shirya mu je ka bata hakuri, kasan alkhairin da ubanta ke shirin maka...." Junaid da takaici ya ishe sa yace "Bana bukatar komansu don ni sbda Allah nayi, mahaifina na da rufin asiri dai dai gwargwado, nima ina da nawa rufin asirin don haka babu abinsu da xae rude ni, ke dai ki je a kai ki makkan....." Bude baki Hajja tayi tana kallonsa cike da masifa can ta gyada kai tace "Shegiya nake idan ban je na ce ma Ubanka mari ka sharara mata ba" daga haka ta shige gate fuu, El-ameen ya fashe da dariya, junaid ya hade rai sosai yace "Ka bar min irin wannan abun Ahmad bana so" El-ameen ya tabe baki yace "Haka kawai mutum ya daura ma kansa wani hali da baxai fishesa ba a rayuwa, to riban me ka ci don ka walakantata Ahmad, ka dai san tafi karfin ka...." A fusace Junaid yace "Ni dai na fi karfinta don bata ma gabana, don Allah nayi abinda nayi" dariya El-ameen yayi yace "Shi yasa naga ka dage sai satan kallonta kake...." Daga haka ya daga kafa ya shiga gidan ya bar sa nan tsaye.

*Haske Writers association*💡
[3/19, 9:36 PM] El-hajj💥: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By khaleesat Haiydar_✍🏻

78.....

Ranan laraba da safe misalin goma su Junaid suka yi set off din xuwa bauchi sai dai ta plane don yace baxae iya xaman mota ba, shi ma din ba karamin takurasa Abba yayi ba kafin ya amince xai je don da ca yayi shi baxae je ba don sbda Allah yayi abinda yayi, xuwa lokacin dae ba laifi Mumy na amsa gaisuwarsa sae dai ba kamar da ba hakan yasa duk ya ji ba dadi, tun ranan litinin yake gidan, ko yaje aiki nan yake dawowa da yamma, tausayin Humainah yake sosai hakan yasa ko da yaushe yana kusa da ita, part dinsa ya mayar da ita daga karshe ita dai Mumy nata ido, duk da luran da yayi su Umma basa gidan haka ma Suhaima da Muhibba ko sau daya bai taba tambayar inda suke ba, harkokin gabansa kawai yake, Hajja dake ta shiri tun daga ranan litinin din tana jiran ranan jumma'a da Abba yace za su je bauchi da su Junaid bata san har sun tafi ba safiyar laraban, suna cikin taxi da xai kai su Airport wayar El-ameen ya fara ringing, cirowa yayi yaga Aliyu ne ke kiransa, shi har ya ma mance da shi, d'an murmushi yayi ya daga kiran, daga daya bangaren Aliyu yace "Masu Jasmine/jewel/baby!" Murmushi El-ameen yayi yace "Yea, mara mutunci da abokina bai dawo sense dinsa ba sai dai ka ga sammaci wllh" dariya Aliyu yayi yace "Ae nasan ya dawo ne, bayan ka xo ka dauketa ka mayar masa ae magana ta kare" El-ameen yace "Exactly, kuma albishirin ka, ita ma ta dawo, ka dai gane me nake nufi..." Aliyu yace "Ohh really, dama na ga alama soon xata dawo.... But what brought her back!" El-ameen yace "That's a long story, yanxu ina hanyar bauchi ne" Aliyu yace "me xaka yi bauchi" El-ameen ya saci kallon junaid dake kallonsa yace "Ohk! Let's chat!" Daga haka ya katse wayar, wani uban tsaki Junaid ya ja ya dauke kansa, El-ameen yayi dariya, junaid bai kuma kallon inda yake ba har suka isa airport. sha daya suka sauka bauchi, El-ameen ya tare masu taxi duk suka shiga baya ya fadi ma me taxin inda xai kai su, Sai a sannan ya juya yana kallon junaid yace "ka cika umarnin da sarki ya baka kuwa?" Junaid ya kallesa yana jiran jin umarnin me, ganin El-ameen bai kuma cewa komai ba har bayan kusan minti biyar yace "Wani umarnin?" El-ameen yace "Ashe kana da baki"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login