Showing 78001 words to 81000 words out of 170905 words

Chapter 27 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

667

tace "Kar ki damu xai dawo kin ji 'yan mata" El-ameen yayi murmushi ya juya ya nufi kofa, Dr Sumayya ta tafi daki da ita tana lallashinta. Junaid bai farka ba sai kusan Karfe uku na rana, ya mike xaune da kyar, rike kansa dake masa ciwo sosai yayi, can ya mike ya nufi toilet ya dauro alwala ya fito ya tada slln azahar, parlor ya fito bayan ya idar ya ga abinci ajiye parlon, sai a sannan ya fara jin yunwa don tun tea din da ya sha a asibiti jiya da daddare bai sake cin komai ba, xaunawa yayi ya bude food warmern, ya ga shinkafa ne da miya, ya dau plate ya dibi kadan ya fara ci, kwata kwata bai jin dadin abincin a bakinsa, spoon hudu yayi ya ajiye ya jinginar da kansa jikin kujera, kwankwasa kofar parlon aka yi ya juya yana kallon kofar kauda kai yayi dai dai lokacin da aka bude, colleagues dinsa na gun aiki ne har su hudu dukkansu sanye da uniform suka shigo parlon, ya d'an bude ido yana kallonsu har suka karaso parlon, daya daga cikinsu Captain Umar yace "Ohh ko mu koma ne A.jay" Murmushi yayi yana shafa kansa yace "Uhnn it's surprising, sannun ku da xuwa" xama suka yi gaba daya, nan suka gaisa, Daya daga cikin su yace "sai muka ji bad news Ahmad" junaid yayi murmushi, Capt Umar yace "Toh ya jikin?" "Jiki Alhmdllh, tun da gashi har na dawo gida" duk suka yi masa Allah ya sauwake, mikewa yayi ya nufi fridge din dake parlon ya bude ya kawo masu ruwa da drink ya ajiye masu, sun d'an taba hira na minti sha biyar suka ce masa xa su koma, fruits da drinks suka ajiye masa yayi masu godiya ya rakasu part din Mumy su gaida ta, da fara'a ta tarbe su basu jima ba suka mata sallama suka fito, Umma da Hajiya sai kallonsu suke daga balcony, shi kuma bai ce su gaida su ba, yi ma yayi kamar bai taba ganinsu ba, hakan yayi mugun kona masu rai, ya raka frnds din nasa har waje gun mota, sannan ya komo cikin gida, part din Mumy ya tafi, duk suka bi sa da kallo ko wanne da tunanin da take a ranta, yana shiga parlon Mumy Hajiya ta sauke ajiyar xuciya tace "Yaro man kaza" Umma ta tabe baki tace "Ke yanxu kin yi farin ciki da hukuncin da Alhaji ya yanke kansa?" Hajiya tace "Ina fa nayi farin ciki, kika san warce xai aura masa? Kema dai kin san ba lallai ya xabi 'ya yanmu ba, na ma fi tunanin kila yace shegiyar Humainahn nan, kuma da mun shiga uku mun lalace..." Umma tace "Ba abun mu koma gun malam ba yanxu ya hada mu da k'ulli yace sai an barbada ko sai anyi wani abun daban asiri ya kuma tonuwa ga Hajja mayya a gida" Hajiya tace "Mu je ki ji ina da wata shawara Allah ya bamu sa'a wannan karan" mikewa Umma tayi da damuwa tace "Ameen" ta bi bayanta suka shiga parlor. Bedroom junaid ya shiga ganin Mumy bata parlor, ya karasa gabanta ya durkusa ba tare da ya bari sun hada ido ba, cikin sanyin murya yace "Don Allah kiyi hakuri Mumy, forgive me plss kar kiyi fushi da ni" jin bata tanka sa ba yasa ya dago yana kallonta, a hankali yace "Kin ji Mumy!" Tana kallonsa da kyau tace "Ka min wani abu ne?" Shiru yayi bai ce komai ba, tace "Toh baka min komai ba tashi ka fita" kasa tashi yayi, tace "Ka tashi na ce" a sanyaye ya mike ya fita daga dakin. Kallo daya yayi ma Humainah dake parlor ya nufi kofa ya fita, dai dai fitowar Hajja daga part din Abba, ya dauke kai kamar bai ganta ba xai wuce tace "Kai Amadi mu muka dauro maka hatsarin nan ne xaka wani dinga sha mana kamshi a gida don fitsara, to Allah shi kara, kuma ka tafi ka gaida ubanka Abubakar ya xo tun daga Abuja" yi yayi kamar bai san da shi take ba ya fara tafiya xuwa part dinsa, da karfi ta kwalo masa kira yanda tasan Abba xai ji cike da masifa tace "Ni din sa'ar uwar ka ce ina maka magana kake tafiya kake min tsaki, toh Muhammadu ka fito ka ga rashin kunyar da Amadi ke min gaban jama'a, don an maka gata an raba ka da gagarumar mahaukaciya sai ka dau gaba da 'yan gida..." Tsayawa yayi yana kallonta fuskar nan nasa a daure, tace "D'an banxa kawai, ka wuce ka gaida ubanka Abubakar nace" part din Abbansa ya tafi ta bi sa da harara, da sallama ya shiga parlon ya xauna kan carpet kansa a kasa ya gaida Small Abban nasa dad din Humainah, Alhaji Abubakar yace "Lafiya lau Ahmad ya jikin?" Junaid yace "Alhmdllh Abba ya hanya" "Hanya mun baro ta, ya aikin?" Cewar dad din Humainah yana kallonsa, Junaid yace "Alhmdllh" dad din Humainah yace "To Maa sha Allah" kallon Abbansa yayi yaga idonsa a kansa, yayi kasa da kai ya mike yayi musu sallama har ya kai bakin kofa Abba yace "Ka koma asibitin?" Girgixa kai Junaid yayi yace "Yanxu xan tafi Abba" Abba yace "Toh ka kira Abdul ya kai ka, ga makullin mota" komawa cikin parlon yayi ya dau makullin yayi masa godiya ya juya ya fita. shiryawa ya tafi yayi a part dinsa ya fito, sai da ya fara shiga ya gaya ma Mumy xai tafi asibiti snn ya fito ya tafi parking space ya dau motar Abbansa ya fita don xai iya driving din. Abban El-ameen ne ya duba sa da kansa a office dinsa, wani likita yayi masa allura ya basa drugs dinsa, ya kusa awa daya office din sannan dad din El-ameen yace xai iya tafiya ya dawo da daddare karban allura, godiya Junaid yayi masa ya mike ya fita daga office din, yana saukowa second floor ya tsaya yana kallon kofar office din El-ameen, karasawa yayi ya murda handle din door din ya tura, xaune ya gansa ya jinginar da kansa jikin kujerar da yake idonsa rufe, har ya karasa cikin office din bai sani ba, yayi knock din table din gabansa, da sauri El-ameen ya bude ido ya gyara xama, Junaid yace "Sleeping at work" El-ameen ya shafa kansa yace "Our run away patient" Junaid ya ja kujera ya xauna yana kallonsa yace "ka bani number mai gadin can gidan naka nasan baxai rasa sanin whereabout din mama jummai ba, El-ameen ya bude hannu yace " I don't have!" Junaid ya d'an bude ido yace "Da gaske?" El-ameen ya gyada masa kai, junaid yace "Toh yanxu ya xa muyi?" El-ameen yace "Na kai ta gidan old frnd dita Dr Sumayya" junaid yyi shiru kafin yace "har xuwa yaushe?" El-ameen yace "I told her kwanaki kadan xata yi, dama mijinta bai nan ne nasan xata rike ta but kasan halin su mata" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Or mu kai ta orphanage home kawai tunda dai hankalinta ya dawo" wani kallo El-ameen yayi masa yace "tunda ca tayi maka bata da iyaye ba, ko kuma ance maka manya suke dauka" Junaid yace "Toh yanxu kasan inda iyayen nata suke, ka sani ma ko suna da rai, kaga ni iya taimakon da nasan xan iya yi ma yarinyar nan kenan sbda parent dina, ba don su ba xan iya yi mata komai na taimako a rayuwa, I just can't keep on disobeying my mother, beside am getting married in 2wks time kamar yanda Abbana yace, to ya kake son inyi da 'yar mutane, ina xan kai ta idan ba orphanage home ba?" El-ameen ya lumshe ido ya bude hade da shafa kai yace "Aure xa a maka! Toh me xai hana ta xauna gidan ka tare da matar ka har memory dinta ya dawo junaid, last gatan da xaka yi ma baiwar Allahn nan kenan a rayuwa" junaid yayi shiru yana kallonsa can yace "Gidana kuma?" El-ameen yace "Yes, ko tare xaku tare da Mumy?" Murmushi junaid yayi yace "Idan matar bata yarda ba fa?" El-ameen ya hade rai yace "Gidan ubanta ne ko kanta xata xauna?" Junaid ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe idon yana naxarin shawarar El-ameen.

✍🏻
*Haske Writers Association*💡
[1/14, 9:12 AM] Elhajj: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

40/41

Mikewa Junaid yayi yace "I will think about that!" Daga haka ya nufi kofa El-ameen ya bi sa da kallo har ya fita. A haraban hospital din suka hadu da faisal, faisal yace "Ohh my God, ashe abinda ya faru kenan captain shine ko ku sanar da ni kai da El-ameen? da Childishness din ku ne ya tashi da har gida xa ku xo ku sameni" junaid yayi murmushi yace "I thought ka sani ne ai," faisal yayi tsaki yace "Ta ina xan sani?" Daga haka ya bar sa nan tsaye ya shiga asibitin, murmushi junaid ya kuma yi ya shiga mota ya bar asibitin. Yana isa gida part dinsa ya tafi yayi alwala yayi sllhn asr sannan ya kwanta parlor, har ya fara bacci yaji an bude kofar parlon, bude ido yayi ya mike xaune da sauri, Humainah ce ta shigo parlon ta tsaya daga bakin kofa ta d'an hade rai tace "Xamu tafi tare da Hajja!" Yana kallonta yace "Ina xa ku" tace "Gidanmu!" Shiru yayi kafin yace "Ohk, yaushe xa ki dawo?" Ta tabe baki tace "Baxan sake dawowa ba, da kayana duka xan tafi ma" murmushi Junaid yayi yace "Ohk Allah raka taki gona" tace "Ameen" daga haka ta juya ta fice daga parlon, ya koma ya kwanta. Tana fita hajja ta shigo sabe da gyalenta da 'yar jakar da ta taho da shi, tace "Toh Amadi ni dai xan tafi sai kuma na dawo kai maka amarya ko kaki ko ka so sai in ga ta tsiya, idan har ynxu ra'ayin rayuwa da mahaukaciya kake to sai ka haukatar da warce za a kai maka hakan xai fi maka rufin asiri" daga haka ta juya ta fita ya bi ta da kallo hade da tabe baki, ranan da daddare Ummin El-ameen ta xo gidan, duk yanda ta so ya gaya mata ko El-ameen yasan komai kan xancen yarinya mahaukaciya kin gaya mata yayi yace babu ruwan El-ameen, ba don ta yarda ba ta kyalesa don tasan bakinsu daya, can tace "Na ji labarin aure xa ayi maka, saura abokin ka, shi wannan kauye ma xanje dauko masa mata wallahi xan basa mamaki," Dariya Junaid yayi yace "Kai Ummi, kauye kuma" bata tanka sa ba ta mike ta fice daga parlon. Shirye shiryen biki aka dinga yi gidansu Ahmad Junaid babu kama kafar yaro, cikin kankanin lokaci aka hada lefe akwati shidda, shi dai Junaid kallon ikon Allah kawai yake wai shi xa ayi ma aure, auren ma na dole kamar wani mace kuma har lokacin bai san matar ba dariya ma kawai abun ke basa, ana saura sati bikin ya dawo aiki da yamma yana kwance sai dai gaba daya tunaninsa na gun Jasmine yana son sanin halin da take ciki yana kuma son ganinta, kiran El-ameen ne ya shigo wayarsa ya daga, daga daya bangaren El-ameen yace "Uhm duk xumudin xama angon ne yasa ka mance da patient dinka captain?" Junaid yace "If that's what you are thinking...." El-ameen yace "Toh yayi kyau, amma idan baka manta the very first day da ka fara xuwa min da batun ta sai da na baka shawarar ka raba kanka ka ki, yanxu ka xo kayi abinda ya dame ka, ka bar ni da 'yar mutane, ko irin ka dinga kira ka tambayi lafiyarta babu, to Dr sumayya dai ina a week time xa su yi tafiya da mai gidanta wai..." Junaid yace "Yea! Then an min auren sai ta dawo gidana kamar yanda ka ce" El-ameen ya tabe baki ya katse wayar. Karfe biyar da wani abu Junaid ya shirya ya tafi part din Mumy yace mata xai dan fita, sabuwar motar da Abba ya basa ya dauka ya fita daga gidan, a hanya ya kira El-ameen, yana dagawa yace "Kana ina?" El-ameen yace "Me xan maka?" Tsaki Junaid yayi yace "Dalla ni ka gaya min" katse wayar El-ameen yayi, junaid yayi parking ya ji kamar ya juya, sai dai baxai iya ba sbda son ganin jasmine da yake, sake kiransa yayi yana dagawa yace "How dare you xaka katse min waya daga tambaya" El-ameen yace "Ashe ba dadi kai kake ma mutane, ni da ma kai ka haukacen wllh kayi loosing memory ko xaka rabu da wnn worst attitude din naka, gashi it's getting worst nowadayz, ni ina gida anything?" Katse wayar junaid yayi hade da yin kwafa, ya kusa minti goma xaune motar ya kuma yin wani kwafan ya ja motar ya nufi gidan nasu, Ummi dake parlor ya gaida tace "Ni ban ga kai da abokin naka kuna shirin bikin nan ba Ahmad" junaid yayi yake yana shafa kai yace "Ae abinda ya kawo ni kenan" Ummi tace "Toh yayi kyau, da an gama naka da sati biyu in an huta xan kai nasa lefen kauye" Junaid ya fashe da dariya yace "Wllh xan maki driving din" Ummi ta hade rai tace "Am serious, dan ma ka gaya masa nake gaya maka" dakin El-ameen ya nufa yana dariya, El-ameen ya tura laptop din gabansa yace "What is making him laugh" Junaid ya buda ido yace "Baka ji a bakin Captain ba, yanzu dai tashi ka kai ni in duba yarinyar nan tunda gori ka min daxu" El-ameen yace "As you can see am busy, sai dai in baka address" junaid yace "Ba fa dadewa xa mu yi ba" "yess! ko minti daya xa muyi" cewar El-ameen yana kallonsa da kyau. Junaid ya kusa minti goma tsaye yana kallonsa kafin ya juya ya fita daga dakin, El-ameen yace "Byee!" Da daddare yana kwance bedroom Humainah ta fado masa, tabe baki yayi ya dauki wayarsa ya shiga kiranta, sai da ya kusa katsewa ta daga yace "don ma kin samu na kira ki" tace "I didn't beg for ur call" shiru yayi sannan yayi murmushi yace "True! Yaushe xa ki dawo?" Tace "Ana saura kwana biyu bikin ka xamu dawo da Hajja" yace "Bikinsu dai" daga haka ya katse wayar, Har ya ajiye wayar ya tuna Hafsat, tun ranan da abun ya faru bata kira ba bai kirata ba, numberta ya duba ya shiga kiranta bugu uku ta daga ya mata sallama ta amsa daga daya side din hade da gaishesa, ya ce "Ya kike?" Tace "Qlau" rasa me xai sake ce mata yayi, can dai yace "Am sorry for what happened Hafsat," tace "Ohh ba komai, ya wuce ai" yace "To nagode" tace "welcome! But a ina ka san yarinyar?" D'an shiru yayi kafin yace "It's a long story" tace "really?" Yace "Yeah!" Labarin yanda ya fara ganin jasmine tun daga rana ta farko ya fara bata har xuwa ranan da ya kai ta gida gun parent dinsa da abinda ya faru bayan barinsu gida, Hafsat da duk jikinta yayi sanyi tace "Yanxu kana nufin ta dawo hankalinta?" Yace "Yea, amma tayi loosing memory" Cike da damuwa Hafsat tace "Allah sarki, to yanxu tana ina?" Ya lumshe ido ya bude yace "Tana gun frnd dina, buh am getting married in a week time sai ta dawo gidana har tayi regaining memory, Hafsat tace "Dat's nyc Allah ya sanya alkhairi, ya bada xaman lafiya," Yace "Ameen thank you" shiru tayi ya kalli agogo ya ga har sha daya ya wuce, yace "Xa ki kwanta koh?" Tace "Yeah" yace "Ohk good nyt, tnx a lot ki gaida mutan gida" tace "Ayt bye!" Daga haka ya katse wayar ya ajiye yayi addu'an kwanciya. Washegari da yamma junaid na kwance bayan ya dawo daga aiki El-ameen ya shigo parlon, kallo daya ya masa ya dauke kai, El-ameen na daga tsaye bakin kofa yace "In ka shirya ka taso mu tafi" ko kallonsa junaid bai yi ba, El-ameen yace "Ohk nayi tafiya ta" daga haka ya fice. Junaid ya mike ya shiga bedroom ya daura shirt dinsa ya dau Atm ya fita, a part din Mumy ya tarda El-ameen, ya jira har ya gama surutun sa snn yace "Mumy xa mu d'an fita yanxu mu dawo" Mumy tace "Toh Allah ya tsare" ya juya ya fita. A mota yayi ta jiran El-ameen har sai da yaga dama ya fito, El-ameen ya xaga daya side din ganin junaid a driver seat yana shiga junaid ya tada motar suka bar layin, tun a hanya El-ameen ya kira Dr sumayya ya sanar da ita xuwansu, a visitor parlor suka sauka dotan Dr Sumayya 'yar shekara sha uku ce ta kawo masu ruwa da drink ta xauna kusa da El-ameen tana ta basa labari, junaid dai makala earpiece yayi yana danna waya, bayan kusan minti biyar Dr Sumayya ta shigo parlon suka gaisa da El-ameen, El-ameen ya fixge wayar sai a sannan ya dago yana kallon Dr Sumayya yace "Ina yini!" Tace "Lafiya lau ya aiki," yace "Alhmdllh," mikewa tayi ta fita tana fita sistern ta warce xata yi mate din jasmine ta shigo parlon tare da jasmine din, xama tayi kan kujera ta nuna ma Jasmine gefenta ta xauna sannan ta gaida su El-ameen, ya amsa mata da murmushi yace "Ya sch?" Tace "Alhmdllh" kallon jasmine tayi tace "Baby baki ce masu ina yini ba" sunan da Dr Sumayya ke kiranta da shi kenan a sati daya da 'yan kwanakin da tayi a gidan, shine duk yan gidan ke kiranta da haka, shima El-Ameen dake yawan xuwa gidan sai ya dinga kiranta da haka, jasmine ta kalli farida sannan ta kalli El-ameen a hankali tace "Ina yini?" Murmushi kawai yayi mata ta sunkuyar da kai, Junaid dai sai kallonta yake ta gefen ido, El-ameen yace "Toh baki gaida wannan ba Baby" Ya fadi hakan yana nuna mata Junaid, kallonsa tayi tace "Ina yini?" Ya dago kai shi ma yana kallonta yace "Lafiya lau" daga haka ta sunkuyar da kai, El-ameen yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login