Showing 99001 words to 102000 words out of 170905 words

Chapter 34 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

645

nurse din ta tambayeta inda kayanta yake ta nuna mata ta bude ta fiddo mata da gown, cikin 'yan mintuna ta gama shirya wa nurse din sai kallonta take don tasan daurewa kawai take, darduma ta shimfida mata ta bata hijab ta karba ta hau kan darduman ta tada sallah, nurse din ta fita don xuwa hado mata tea tasha kafin ta bata Magani, da mamaki ta kalli El-ameen dake tsaye har lokacin a corridor tace "Kana nan har yanxu Dr, ai da ka xauna parlor" yace "Am okay, ya jikin nata?" Tace "Da sauki I want to go nd make a cup of tea for her" yace "Are you sure she's ohk?" Tace "Ka shiga ka duba Dr" yace "No ba sai na shiga ba, make the tea for her na taho mata da drugs" tace "Okay," sannan ta sauka, ba a dau lkci ba ta dawo da cup din tea din ta kai ma Humainah, ba laifi ta karba ta sha, nurse din ta fito El-ameen ya bata magungunan sannan ya sauka downstairs, parlor ya ga junaid kwance yana kallo, El-ameen bai bi ta kansa ba ya fita yayi xaman sa a balcony, nurse din na saukowa Junaid ya haura sama, kofar dakin da Jasmine take ya tura a hankali ya shiga ya tsaya daga bakin kofar yana kallonta, bacci ya ga take ya karasa kusa da gadon ya durkusa dai dai fuskarta yana kallonta, bude ido tayi a hankali ta mike xaune da sauri ganinsa, ya d'an koma baya yace "Cikin ya daina?" Kallon jikinta ta shiga yi, sai kuma ta gyada masa kai tace "Uncle ya tafi?" Hade rai yayi yace "Ban sani ba" tayi shiru bata ce komai ba, ya mike ya fice daga dakin, dakinsa ya shiga don yin wanka, Jasmine ta sauko daga kan gadon tana kalle kallen jikinta, a hankali ta dinga tafiya har ta fito ta sauko downstairs, hawaye ya cika idonta ganin bbu El-ameen, har xata koma sai kuma ta fita parlon, wara ido tayi ganinsa xaune yana danna waya, ta karasa da sauri ta durkusa kusa da shi tace "Uncle!" Yayi murmushi yace "Har kin tashi?" Gyada masa kai tayi, yace "Toh cikin ya daina?" Shiru tayi sai kuma a hankali tace "Eh ya daina, uncle wannan Antyn tace min am on my period, Meye wannan?" Ya d'an bude ido yace "Nima ban sani ba" shiru tayi sai kuma ta kalli jikinta a hankali tace "Uncle har yanxu fa yana yi" murmushi yayi yace "Xai daina, je ki duba min ko Anty ta tashi a sama" tace "toh" sannan ta mike ya bi ta da kallo har ta shiga parlon, dakin Humainah ta shiga ta ganta kwance tana kuka, karasawa gun gadon tayi ta durkusa kamar ita ma xata yi kukan tace "Anty menene?" Shiru Humainah tayi mata, hakan yasa ta mike ta fita ta koma gun El-ameen, hawaye cike idonta tace "Uncle kuka take, she don't want to talk to me" yace "Captain din fa?" Tace "Yana dakinsa" mikewa El-ameen yayi ya shiga gidan ta bi bayansa, tsaye yayi bakin kofar Humainah yayi sallama har sau biyu bata amsa ba, Jasmine tace "Ka shiga tana ciki" bude kofar yayi ya mata alamar ta shiga, tana shiga ya bi bayanta, karasawa cikin dakin yayi ya tsaya d'an nesa da gadon yana kallonta yace "Ya jikin Humainah?" Mikewa xaune tayi amma ta kasa juyowa tace "Da sauki" yace "Ohk kiyi hakuri, Allah ya sauke kin ji" kai kawai ta gyada masa yace "Go to sleep xa ki ji sauki sosai" kwanciya tayi ya juya ya fita Jasmine ta bi bayansa, a hankali Jasmine ta kamo hannunsa tace "I hate that captain, he's so mean" bude ido El-ameen yayi, sai kuma ta sunkuyar da kai a hankali tace "Though I like him also, he's fine just like you" dariya El-ameen yayi yace "To naji tafi dakin ki" ta hade rai tace "Ina xa ka" yace "parlor" bude kofa aka yi duk suka juya Captain ya fito, suna hada ido da Jasmine ya watsa mata wani kallo a kan idon El-ameen kuma, xame hannunta tayi a hankali daga na El-ameen ta juya ta shiga daki, junaid yace "You are still around ashe, tot ka tafi" El-ameen bai tanka sa ba ya sauka kasa, junaid ya bude kofar Humainah ya shiga ya karasa gun gadon ya xauna yace "Good morning wife" rufe ido tayi da sauri, yayi murmushi xai dagota ta mike xaune sai kuma ta fashe da kuka, ya wara ido yace "Toh kuma, Allah ya baki hakuri just came to say ya jikin" daga haka ya mike ya fita, dakin Jasmine ya bude ya ganta xaune ta rungume hannayenta kiris ya rage ta fashe, yace "Ai kin iya dafa indomie koh?" Kai ta gyada masa a hankali, yace "Toh xo ki dafa mana" mikewa tayi ya juya ta bi bayansa, indomie hudu ya fiddo mata tace "Har da Anty?" Yace "Eh" kujera ya dauko ya xauna kitchen din yana kallon yanda xata yi girkin, har ta gama bayan kusan minti goma idonsa na kanta bai ma san ta gama ba, ta karasa kusa da shi ta duka a hankali tace "Captain!" Rufe ido yayi ya bude da sauri ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Jasmine" bude ido tayi a hankali tace "Na gama" mikewa yayi a hankali har lokacin yana rike da hannunta yace "Ohk dear, dauka daya ki kai ma Anty sai ki dauka kema ki ci" toh tace ya sake hannunta ya juya ya fita. Da yamma nurse Salima ta kuma dawowa duba Humainah da Jasmine kamar yanda El-ameen ya umarce ta. Da magrib junaid ya shirya ya tafi gida, gabansa sai faduwa yake don bai san yanda xa su kwashe da Mumy ba, part din Abbansa ya fara shiga don gaidasa, ya tarda Umma da Hajiya a parlon, xaunawa yayi kasa ya gaida Abba ya amsa yana tambayarsa gida, yace "Alhmdllh Abba" juyawa yayi yana kallon Su Umma ya gaida su, duk suka amsa masa da fara'ar da bai kai ciki ba ana tambayarsa amarya, Hajiya ta mike ta fice daga parlon bayan ta ma Abba sallama Umma ta bi bayanta, ya d'an jima xaune parlon Abba sannan ya mike yace masa xai je gun Mumy, kamar munafuki ya xauna kasa ya sunkuyar da kai yana gaida Mumy, ta amsa masa bbu yabo bbu fallasa, rasa abun cewa yayi haka ya karashi xaman sa Mumy nata harkan gabanta ya mike yace xai tafi tace "Allah ya tsare" ya fita parlon, bai yi mamakin ganin su Hajiya da Umma xaune a spot dinsu ba, ko sallama bai yi masu ba ya fice, Hajiya tayi murmushi tace "Komai dai ya kusa xuwa karshe in da rai da lafiya, sai mun cusa ma iyayenka tsanarka" gidansu El-ameen junaid ya nufa bayan ya bar gidan, yayi mamakin ganinsa xaune waje, ya xauna gefensa yace "kai kuma xaman waje ka fara yanxu kenan" El-ameen ya shafa kai yace "Yafi min alkhairi ne, kawai Ummi ta dau fushi da ni kan abinda bansan komai kai ba, ni wllh ban san kayan me take nufi ba" junaid yayi shiru can yace "Toh ka tambayi Abba mana," El-ameen yace "He also don't want to say anything about it to me" junaid yace "Toh tashi mu je mu samu ummin sai mu tambayeta" El-ameen yace "A'a ni baxan je ba, wannan Kanwar Abban nawa na ciki" mikewa Junaid yayi ya shiga gidan, Small mum din El-ameen ce xaune parlon da Ummi, Ummi ta hade rai ganinsa ya d'an shafa kai ya karaso ya xauna kasa kusa da Ummi ya gaida ta ta amsa bbu yabo bbu fallasa, ya gaida Anty dake parlon ita ma ta amsa masa haka, yana shafa kai yace "Ummi mu fa bamu san kayan me ake cewa ba" Anty tace "Eh ai baxa ku sani ba munafukai, irin yanda aka maka haka xa a masa shi ma kwanan nan" ko kallonta Junaid bai yi ba ya kalli Ummi ya marairaice yace "Allah Ummi ba mu sani ba" Ummi tace "kayan auren mutum ku ke hadawa a boye ko na me" junaid ya xaro ido yace "Kayan aure kuma Ummi, wani kayan auren?" Ummi ta tabe baki tace "Na sha gaya masa yanda aka yi maka a gida haka shi ma xa a masa yana xaton fadi nake kawai koh, to xaku sha mamaki daga kai har shi" junaid yayi shiru can yyi murmushi yace "toh ayi masa hakan kawai Ummi, don nima ina masa maganan aure baya saurarana, ni ba gashi ina xaune lafiya da matar ba" Ummi tace "To tafi daki ka ga kayan sun yi" junaid ya d'an bude ido yana kallonta, sai kuma ya mike ya nufi bedroom dinta, ko da ya fito dariya kawai yake yace "Wllh sun yi sosai Ummi, Allah ya saka da alkhairi" junaid bai ce ma El El-ameen komai ba da ya fito kawai dariya yake bakin rai, El-ameen yace "Meye haka?" Junaid yace "Nothing, na shawo kan Ummi ta hakura wllh" kallonsa kawai El-ameen yake bai ce komai ba.

Bayan kwana biyu da ya kama ran lahadi Humainah ce tsaye kitchen tana girkin lunch Jasmine na daga bakin kofar kitchen din tsaye duk ta cika ta da surutu ita dai aikinta take ba tare da ta tanka ta ba don da tace ta tafi xata dawo, junaid kuma na sama, danna bell aka yi Jasmine ta xaro ido tace "kila uncle koh Anty?" Humainah bata tanka ta ba ta fita daga kitchen din, jasmine ta bi bayanta da sauri, suka isa gun kofar a tare ta bude, wata yarinya da baxata wuce su ba ce tsaye bakin kofar Humainah sai kallonta take don bata santa ba, yarinyar tayi murmushi tace "Baki san ni ba koh, yi hakuri ruwan sha xa ki ban don Allah, na xo gidan aunt dina ne dake layin nan ne wllh wai ashe jiya da daddare suka yi tafiya da mijinta gashi duk na gaji bbu shagunan siyan ruwa nan kusa" Humainah tace "Ohk, shigo" yarinyar ta shigo tana bin ko ina na parlon da kallo ta samu kujera ta xauna, fridge Humainah taje ta dauko mata ruwa da drink ta ajiye mata, Yarinyar ta mata godiya tana murmushi Humainah ta koma kitchen, kallon Jasmine da ta xauna kasa kusa da ita tana kallonta yarinyar tayi tace "Sannu ya sunan ki?" Jasmine ta d'an wara ido tace "Uncle na kira na jewel, captain na kira na Jasmine, Mamina na kirana Baby" yarinyar dai sai kallonta take, Humainah dake kitchen tana jin su ta tabe baki ta ci gaba da girkinta, yarinyar tace "Waye captain, waye Uncle?" Jasmine xata yi magana suka ji taku stairs, shiru tayi tana kallon stairs din haka ma yarinyar har ya sauko, kallo daya yayi masu ya dauke kai, yarinyar tace "Ina kwana" ya ji bai ji ba ita dai bata sani ba don bai amsa ba ya shiga kitchen ya rufe kofar yana kallon Humainah yace "Wacece ta shigo min gida?" Humainah ta daure fuska tace "Ruwa xata sha" ya wani hade rai yace "Ruwa? Kika san daga inda take maxa fita ki sallameta kar ki sha mamaki" bata tanka sa ba ta ci gaba da girkinta, ya bude kofar ya fice, kallon Jasmine yayi yace "Come here" mikewa tayi ta bi bayansa don stairs ya nufa, yarinyar ta bi su da kallo, fitowa Humainah tayi ta xauna parlor ganin bata ga Jasmine parlon ba ta kalli stairs, yarinyar tace "Nagode kwarai 'yar uwa, ni sunana Hadiza" Humainah tace "Welcome" yarinyar ta mika mata waya tace "Sa min number ki mu dinga xumunci naga kina da kirki" Humainah ta karba ta sa mata number ta mika mata, yarinyar tace "Suna fa?" Humainah ta gaya mata, tace "Allah sarki, amma kishiyar ki ce wannan da na gan ku tare" Girgixa mata kai kawai Humainah tayi, tace "Ayya, to ni xan koma xa mu ke xumunci" har bakin kofa Humainah ta rakata yarinyar sai murmushi take ta fita daga parlon, Humainah ta kulle, ta koma kitchen. Da yamma misalin karfe shidda motar El-ameen ya shigo gidan, Junaid dake daki ya mike yana lekensa ta window don tun ranan basu sake haduwa ba, ko parking din arxiki bai yi ba ya fito da ganinsa kasan yana cikin tashin hankali, junaid ya fashe da dariya har da kyakyatawa ya sake curtain din ya koma kan gado ya dinga dariya, direct dakinsa El-ameen ya nufa don bbu kowa parlon, kwankwasa kofar yayi junaid ya mike xaune yace "Come in" ya tura kofar ya shiga yana kallon junaid dake ta kokarin danne dariyarsa, junaid ya mike tsaye yace "Ya aka yi na ganka haka besty, me ya faru" xaunawa kan gado El-ameen yayi ya rike kai, Junaid ya xauna gefensa yace "Talk to me mana" El-ameen ya dago da kyar yace "Kaga abinda su ummi ke shirin min sai kace wani mace, wllh not me" junaid yace "Me xa a maka?" El-ameen yace "Wai aure!" Junaid ya xaro ido sai kuma ya fashe da dariya El-ameen ya mike yana kallonsa, yayi mai isan sa sannan yace "Nima haka ka min" kofa El-ameen ya nufa junaid ya rikosa da sauri yana dariya yace "Wllh ramawa na yi nima haka fa ka min" da kyar ya lallaba El-ameen ya xauna, sannan yace "Toh kai yanxu kana da warce kake so ne da har xaka damu kanka, ba gashi nima haka aka min ba kuma ina xaune lafiya?" Shiru El-ameen yayi kafin yace "Ni ina da warce nake so" junaid yace "To wacece?" Da kamar baxai ce komai ba sai kuma ya shafa kansa a hankali yace "Baby!" Kallonsa junaid ya tsaya yi ko kiftawa bai yi, El-ameen ya mike yace "Kuma ita xan kai masu, in ma basu yarda ba ni sai na aureta don Allah xan iya hallaka warce xa a hada ni da" daga haka ya nufi kofa Junaid ya mike ya fixgosa yace "Wace babyn kake nufi?" El-ameen yace "Warce ke gidan ka" wani kallo Junaid ya watsa masa yace "Sai ka jira randa na maida ta gun iyayenta sai ka bi ta ka aureta, yanxu kam baka isa ba" murmushi El-ameen yayi yace "Koh?"

*Haske Writers association*💡
[1/14, 9:18 AM] Elhajj: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

55.....

Wani kallo junaid ke masa ya sake sa ya koma baya yace "Yess! Me ya hana ka son auren nata lokacin da take hauka? You can call what ever prize you wish to for giving her your attention and I will pay you" El-ameen bai ce masa komai ba ya gyara kwalar rigar sa ya juya ya fita daga dakin, a stairs suka kusan cin karo da Jasmine, ta koma baya ta wara ido ganinsa tace "Uncle! When did you come" murmushi ya kirkirar mata yace "Am coming" ya bi ta gefenta ya sauka ta bi sa da kallo. Tana jin fitar motarsa ta bata fuska tayi daki da sauri xata fara kuka. Washegari monday Junaid na dawowa masallaci da asuba ya shiga dakin Humainah, ya sameta xaune kan darduma daga bakin kofar ya tsaya yace "You are resuming school today" tace "Na sani" juyawa yayi ya fita, ya bude dakin Jasmine, kwance ya ganta tana bacci cikin bargo ya cire bargon ta mike xaune da sauri yace "Tashi kiyi sallah, after that you brush ur teeth nd take ur bath" daga haka ya juya ya fita ya koma dakinsa, wanka Humainah tayi ta gyara bedroom dinta ta fito parlor nan ma ta share sannan ta shiga kitchen, ruwan lipton ta daura ta xuba kayan kamshi sannan ta fara peel din potatoe. Karfe bakwai saura junaid ya fito daga bedroom sanye da uniform dinsa don ranan sati biyun da ya dauka gun aiki ya cika, kitchen ya tafi ya tsaya daga bakin kofa yana kallon Humainah, ta juya tayi masa kallo daya ta dauke kai, yace "Xan yi tafiyata in kyale ki if you are not ready" tace "Toh ai dai ba xaune nake ba" bai ce komai ba ya karasa cikin kitchen din ya dau cup ya hada tea ya fita. Yana xaune parlor har karfe bakwai yayi Humainah ta fito ta wuce sama, can ya mike shi ma ya tafi saman, dakin Jasmine ya bude ya ga ta gama sa kaya yace "Fito ki ci abinci" shiru tayi tana kallonsa daga sama xuwa kasa yace "Baki ji na ne" komawa baya ta shiga yi a hankali har lokacin idonta na kansa sai kuma ta fashe da kuka tana girgixa kai tace "Ni bana son kayan nan captain" ya kalli farin shirt din uniform da navy blue trousers din dake jikinsa yace "Me suka maki kayan" ta kuma fashe wa da kuka tace "I don't like it" wani kallo ya mata ya juya ya fice daga dakin, a hankali ta xauna gefen gado tana xaro ido kamar me son tuna abu, dakinsa ya koma ya dauki wayarsa da hularsa ya fito, dai dai lokacin da Humainah ta fito ita ma rike da cup, bai ko kalleta ba ya sauka downstairs ya dau makullin motarsa, ta bi bayansa tace "Toh baxa ka kai ni makarantar ba?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Sai kuma gobe am late" daga haka ya fice daga parlon ta bi sa da kallo kamar xata fashe da kuka, ajiye cup din hannunta tayi a parlon ta koma sama hawaye cike idonta. Jasmine na jin fitar motarsa ta sauko ta tafi dining ta debi breakfast dinta ta ci a nan ta koma sama. Da yamma misalin karfe hudu saura Humainah na dakinta bayan ta daura girki a kitchen ta ji an danna bell, mikewa tayi ta fito dai dai lokacin da Jasmine ma ta fito, ko kallonta bata yi ba ta sauka, bude kofar parlon tayi ta ga yarinyar jiya a tsaye, murmushi yarinyar tayi tace "Kin gan ni kuma koh, daxu aunt dina ta dawo na taho, yanxu ma gida xan koma nace bari in shigo mu gaisa" Humainah ta d'an yi murmushi ita ma tace "Toh sannu da xuwa" hanya ta bata ta shigo ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login