Showing 153001 words to 156000 words out of 170905 words
Chapter 52 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
gaba daya bana auren kuma, idan kuma ba haka ba xan xubar da cikin nn wllh" kallonta kawai yake da manyan idonsa, can ya tabe baki ya juya ya fita daga dakin, ta fashe da kuka sosai ta sulale nan kasa ta hade kanta da gwiwa, tafiya kawai junaid yake yana son gane ma'anar abinda Mumy ta fadi masa, Muryar Hajja ne ya dakatar da shi jin irin kiran da take masa ba kakkautawa ya juya yana kallonta da mamaki, karasowa tayi fuskar nan nata a murtuke tace "Wato ai gwara kwadayina a kan taka Ahmad, tsabar naka kwadayin ya shahara 'yar gaba daya kake son aurewa kayi ma jikata kishiya, kishiyar ma jinin sarauta, dama ga Ka da taka sarautan da ka lak'a6a ma kanka tun ba yau ba, ita kuma ta xo da ta gidansu ku taru ku sa ma jikata hawan jini ta mutu in shiga uku, to ubanka yayi kadan bare kai, ban yarda da auren nan ba kuma baxa ayi ba, su rike kujerun jirginsu can baxa a je ba...."
*Haske writers association*💡[3/19, 9:36 PM] El-hajj💥: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍
83......
Hade rai Hajja tayi tana kallon Junaid tace "Ya haka tana gaishe ka kayi mata shiru?" Bai tanka ta ba ya dauke kansa daga kallon Zahrah da yake, Hajja tace "Ae ko a haka xaka kare, wawa ne kadai ke hali irin naka" Shi dai bai kalli inda take ba bare ta sa ran amsa, mikewa Zahrah tayi jiki a sanyaye Hajja tace "Rabu da Gantalalle" daga haka ta kama hannun Zahrah suka fita, murmushi yayi ya bi kofar da ido, can ya dauke kai ya lumshe ido ya bude, mikewa yayi ya koma parlor ya xauna. Har yamma Humainah bata koma part din Junaid ba shi ma kuma bai fito ba duk da xaman part din nasa ya ishesa, Zahrah kam na bangaren Hajja dake ta jan ta jiki kamar ta maida ta ciki, su khadija sai kallon ikon Allah suke, ko ta kan Ummi bata wani bi sai Zahrah. Bayan la'asar junaid na dawowa masallaci ya shiga part din Mumy, bbu kowa parlon ya nufi bedroom din Humainah da fatima, Humainah kadai ce xaune dakin, ya karasa yana kallonta yace "Why did you leave daxu?" Sosai ta hade rai bata ce komai ba, ya rungume hannayensa yace "Baki gane ta bane?" Kamar jira take ta fashe da kuka, ya bude ido yana kallonta, tayi mai isarta tayi shiru, yace "Ina Mumy?" Kin cewa komai tayi har sai da ya kuma tambayarta, muryarta na rawa tace "Tana gun Hajja" juyawa yayi ya fita daga dakin. A hanya ya hadu da Mumy xata koma part dinta, tace "Ya jikin!" Yace "Alhmdllh Mum" tace "Ashe bakuwa aka yi" kai kawai ya gyada mata tace "Toh da kyau, El-ameen din fa" girgixa mata Kai yayi yace "Ban sani ba Mumy" daga haka ta karasa part dinta, shi kuma ya nufi bangaren Hajja, Zahrah na xaune parlor Hajja kuma ana kitchen da fatima tana gwada mata ynda xata yi ma kajin da Mumy ta Kai masu, Ummi kuma na can daki ta gaji da hayaniyar Hajja tayi kwanciyarta, Zahrah bata ko kalli inda Junaid yake ba har ya karaso ya xauna yana kallonta ta gefen ido, jikinta ne ya bata kallonta yake ta mike xata bar parlon ya fixgota har sai da ta kusa faduwa, xaro ido tayi tana kallonsa cike da masifa sai dai kuma ta kasa masifar, bude kofar parlon aka yi ya sake hannunta, El-ameen ya shigo da sallama, sai ga Hafsat ma ta shigo parlon, kallonsu kawai junaid yake haka ma Zahrah, El-ameen yayi murmushi yayi xamansa kan kujera Hafsat ma ta xauna tana kallon junaid murmushi dauke fuskarta tace "Ina yini Captain!" Murmushin ya mayar mata yace "Lafiya lau, ya kike Hafsat" tace "Alhmdllh" Zahrah dai na tsaye har lokacin sai satan kallon Hafsat take, El-ameen yace "Meet Hafsat Zahrah, ae kin santa" sai a sannan ta kirkiri murmushi ta xauna tana kallon Hafsat tace "Sannu!" Hafsat ta mayar da murmushin tace "Yauwa, ya hanya!" Ba tare da ta kalleta ba Zahrah tace "Alhmdllh!" Hajja ce ta fito daga kitchen tana kallonsu El-ameen tace "Yaushe wa ennan suka shigo" Hafsat ta sauka har kasa ta gaida ta, Hajja ta washe baki tace "Sannu 'yar nan, ko sanin ki bn yi ba sai yau, ya gidan?" Hafsat tace "Alhmdllh" Hajja tace "Kema kin xo ganin bakuwa yar sarki kenan?" mikewa Junaid yayi ya fita daga parlon. Bai sake haduwa da Zahrah ba har washegari da yamma, yana son xuwa amma ya hana kansa fita, da yamman ranan kuma El-ameen ya kawo mama jummai gidan bayan wahalar da ya sha na nemanta, Zahrah na dakin Hajja, Hajja ta aiki khadija ta kirata bayan El-ameen yayi mata bayanin wacece mama jummai, tsaye Zahrah tayi bakin kofa tana kallon mama jummai dake rakube waje daya parlon, da gudu ta karaso ta rungume ta hawaye cike idonta cikin sanyin murya tace "Mama!" buda baki mama jummai tayi tana kallonta da mamaki, can ita ma ta rungumeta tace "Allah Akbar, kaddai ace min yar nan ta warke?" Hajja tace "Kaji wani mugun alkaba'i ko, yo so kike kiyi ta ganinta a haukace 'yar nan? Toh hankalinta daya da naki yanxu dai..." Mama jummai dake kallon Hajja tace "Ayya hajia, ae ni nama fi kowa son ganin warkewarta, ban kuma yi tunanin xan sake haduwa da ita a duniya ba...." Sai kuma ta fashe da kuka ta kuma rungume Zahrah tace "Allah sarki ne, Allah Akbar" Hajja ma ta fashe da kuka tace "Ae ni xan gaya maki wannan, sannan ina me maki albishir da cewa kin haye, ba ke ba wankau da talauchi har abada... Yar sarki sukutum ce nan kike gani jikin ki, yanxu haka kafar ki kafarta har masarautan su, wato da baki rike ta da kyau kin kula da ita tsakani da Allah ba da sunan ki asararriya yanxu, nasan har sai kin gaji da hawa jirgi xuwa makka...." Washegari da ya kama asabar su Zahrah na ta shirin komawa Bauchi har da Hajja da ta hada kayanta jaka guda, shi dai Abba bai ce mata komai ba amma da ganinsa kasan bbu yanda ya iya da ita ne, Mumy ce tayi karfin halin yi mata magana cewa bai kamata ba, nan ta balbaleta wai bakin cikin ita ma xata mata, ko a jikin junaid da in ma kayanta gaba daya xata dauka ta koma bauchi bbu abinda ya sha masa kai don abinda ya damesa a xuciya kadai ya ishesa, Karfe goma El-ameen ya iso gidan, part din Junaid ya nufa ya samesa parlor, tsaye yayi daga bakin kofa yace "Yah! Xaka rakamu bauchin ne yau?" Junaid ya kallesa yace "A wani dalili?" El-ameen yace "A dalilin tare xa mu da hajja" Junaid bai kuma tanka sa ba sae kwafa da yayi, El-ameen ya daga kafada ya juya ya fita, har part din Mumy hajja ta kai Zahrah su yi sallama da Humainah, dakin Mumy suka sameta Humainah ta hade rai sosai, tun bayan haduwarsu ranan da Zahrah ta xo gidan basu sake haduwa ba, Zahrah na tsaye daga bakin kofa tace "Allah ya kara lafiya" Humainah ta mayar mata da Amin ba tare da ta kalli inda take ba, Hajja tace "Kin san kowa da irin nasa laulayin, ita masifa ya daura mata... Mu je kawai" kallonta Zahrah ta kuma yi jin abinda Hajja tace sai kuma ta dauke kai ta fita. El-ameen ya jima tare da mai martaba bayan sun isa bauchi, ko da ya fito airport ya nufa don yana da aiki. Bayan sati biyu Junaid ya dawo daga aiki da yamma suka shigo gida kusan tare da El-ameen dake motarsa shi ma, El-ameen bai wani yi parking ba ya fito yana kallon motar junaid da ya nufi parking space, junaid ya fito El-ameen ya karasa kusa da shi yana kallonsa ganin kamar ba shi ba, can dai yace "Abba na ciki kuwa Captain" junaid yace "Ban sani ba nima, any problem" El-ameen yace "Then let me check" bin sa da kallo junaid yayi kafin ya nufi n bangaren Mumy ya gaisheta, ya tafi nasa part din. Bakwai saura junaid ya fito don xuwa masallaci dai dai lokacin da Abba ya fito tare da El-ameen, kallon mamaki junaid ke masa don bai san yana nan har lokacin ba, tunanin abinda xai kawo sa gun Abba har ya dade haka ya dinga yi amma ya kasa gano komai, ya dai nufi gun Abba ya gaida sa daga haka suka nufi masallaci gaba daya. Ko da suka dawo daga masallaci El-ameen sallama kawai yayi ma Abba ya shiga motarsa ya bar gidan, kasa daurewa junaid yayi bayan isha ya dau makullin motarsa ya tafi can gidan El-ameen, Hafsat ce ta bude kofar ganinsa tace "Sannu da xuwa captain, you came to our home today" murmushi yayi yace "Lallai kam, yana ciki?" Tace "Ehh yana ciki bismillah" hanya ta basa ya karasa xai xauna parlor tace "Yana sama ae" yace "Yi masa magana pls" tace "Study room dinsa fa yake" mikewa yayi yace "Ohk" daga haka ya haura sama, xaune ya samesa yana duba wani littafi gaba daya hankalinsa na kai, wanda hakan yasa bai dago ba don a tunaninsa Hafsat ce ta shigo, karasawa Junaid yayi, El-ameen ya dago da sauri jin turarensa, kallon mamaki yayi masa sai dai bai ce komai ba, Junaid ya xauna yace "Me ya kawo ka gidanmu daxu?" El-ameen ya buda ido yace "Yeah, Nasan ba don Allah ka taso ka taho gidana ba," sai kuma yayi murmushi yana girgixa Kai yace "it's very unfortunate Zahrah ta bata frndship dinmu, a da sati baya karewa ba tare da ka xo inda nake sau uku ba ko sau hudu, sauran kwanaki kuma ni xan je but yanxu....." Junaid ya d'an yi murmushi yace "Ae kai ma ba xuwa kake ba" El-ameen bae tanka sa ba ya ci gaba da duba littafin gabansa, junaid yace "I asked you a question..." El-ameen yace "Nothing, naje ne ya shigar min gaba gun neman auren Zahrah, as in shine waliyyina" Junaid da ya ji wani abu ya tsaya masa a xuciya ya dake yace "Why him?" El-ameen yace "Coz dad dina yace bbu ruwansa da batun auren...." Junaid ya hadiye wani abu da kyar yace "and what did he said about it?" El-ameen ya matsar da littafin gabansa yace "Yace babu damuwa idan har hakan baxae bata ma dad dina rai ba.. Nd I told him shi ma ya turo ni gunsa" mikewa junaid yayi kansa na juyawa ya kalli agogon hannunsa yace "Ohk, all good, it's getting late xan koma" El-ameen yace "Toh baka tambaye ni yaushe ne daurin auren ba?" Junaid yaji gabansa yayi mugun faduwa ya koma ya xauna xuciyarsa na bugawa sosai yace "When?" El-ameen yace "This Friday!" Kasa cewa komai Junaid yayi, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, bude kofa aka yi Hafsat ta shigo ta dire masu babban tray mai dauke da warmers din abinci ta fita sai ga ta ta dawo da wani tray mai dauke da ruwa da drinks sai cup ta fita, El-ameen yace "Mu ci abinci frnd..." Junaid yace "No! No, am ohk" El-ameen yace "Alryt then, you wait muyi shawaran abubuwan da xa ayi na bikin it's just 4 dayz left" Kallonsa kawai Junaid yake, El-ameen ya dau table water daya ya bude ya sha kadan yace "Yeah, though sarkin yace baya bukatan komai namu, amma dai mu ma mun san abubuwan da ya kamata, so ya kaga ya kamata mu yi" mikewa junaid yayi yace "Look, ka kira Faisal or Aliyu am not good at that" daga haka ya fice daga parlon, El-ameen ya bi sa da kallo yana murmushi.
*Haske Writers association*💡
Ayi ta hakuri da ni a haka har mu kare pls.
[3/19, 9:36 PM] El-hajj💥: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
85.....
Kallon Hajja kawai junaid yake don ya kasa fahimtar inda xancenta ya dosa duk ta cikasa da hayaniyar dake baraxanar haddasa masa ciwon kai, Muryar kawunsa yaji na kiransa ya juya yana kallonsa yayi masa alama da ya xo, part din Abbansa ya nufa ta bi sa tana ci gaba da xaxxaga masa bala'i shi dai bai tanka ba, bai same su parlor ba ya karasa har bedroom, hajja tayi tsaye nn parlon tana ta ci gaba da bala'i ta inda take shiga ba ta nn take fita, xaune ya samu Abbansa da frnds dinsa biyu sai kawunsa, Kawunsa wato Abban Humainah ne yace "Ahmad!" Ya dago a hankali yana dubansa amma ya kasa cewa komai. Kawun yace "Na'am mahaifin yarinyar nan ya bukaci da ka aureta, don me da ku ka dawo baka sanar ma iyayenka komai ba sai abokin ka ne ke fadi ma Abbanka few dayz back....." Kasa cewa komai Junaid yayi sai dai kansa yayi mugun daurewa, Abbansa dai sai kallonsa yake, Alhaji umar yace "Kayi shiru Ahmad, gaskiya ne Kai mijin mace hudu ne bbu wanda xai hanaka kara aure tunda kana da halin yin hakan sai dai kawai Kayi kokarin xamo me adalci tsakaninsu, amma meye na boye ma iyayenka, da nufin ka yau sai ka taho kace a tashi aje maka daurin aure, Babanka yayi ta xuba maka ido amma shiru baka ce masa komai ba...." Alhaji Habib yayi dariya yace "Kar fa ku ga laifinsa, that's what it takes to be a 1st child, wauta ne kawai irin tasa" Kawunsa yayi murmushi yace "Gaskiya ne, to Allah ya sanya alkhairi Ahmad, ae kai din mijin mata hudu ne, Allah ya baka ikon adalci" ae sai kawai Junaid ya sunkuyar da kai ya ma rasa gane wani yanayin yake ciki, yanxu ana nufin shi xa'a aura ma Zahrah, amma ai basu yi haka da kowa ba, how is this? No ya ma san kawai basu fahimce xancen bane amma da abokin sa xa ayi auren, Muryar Abokin Abbansa yaji yana ce masa ya tashi ya je, dagowa yayi da sauri cikin sanyayyen murya yace "Kuyi hakuri Abba, ni....." Kasa ci gaba yyi don bai ma san abinda xai ce ba, cewa xai yi shi bai sani ba ko kuwa ce musu xai yi ba fa da shi xa a daura auren ba, Abban Humainah yace "Tashi kaje, Allah yayi maka albarka... Ya baka ikon adalci tsakaninsu" mikewa yayi da kyar ya fita daga dakin cike da confusion to yaga ae ba fa da shi xa ayi auren ba, how is all this???? Ko kallon Hajja da ta cika parlor da muryarta bai yi ba ya fice daga parlon, ya tafi part dinsa ya dau makullin mota ya fito ya dau motarsa sai gidan El-ameen, Hafsat dake ta mopping din Balcony ta gaishesa da fara'a tace masa yana sama a study room, yana haurawa sama ya bude kofar dakin, Xaune ya samesa idonsa lumshe ya karasa gabansa yana kallonsa, bude ido El-ameen yayi ya gyara xama ganinsa yace "Yahh, xaka iya xuwa kuwa?" Junaid yace "Ahmad I don't get what my parent are telling!" El-ameen ya shafa kansa yana murmushi yace "Wai na auren ku da Zahrah?" Buda ido junaid yayi yace "Aurena da Zahrah kuma?" El-ameen yace "Yeah" xaunawa junaid yayi jin ya kasa ci gaba da tsayuwar yace "You are getting me confuse, wace Zahran...." Murmushi El-ameen ya kuma yi yace "To ya na iya maka frnd? Ban son wani abu ya sameka mu rasa ka a kan Zahrah, ni na nema maka aurenta, isn't it nyc..... Nasan yea you are in love with her..... Son da kake mata ya take nawa so I have no option then to let go, ita ma na ga tana son ka sosai shi yasa nayi haka from the beginning, nasan dai yanxu no more love sickness nd the rest, just that kar ku cuci Humainah....." Tuni idon Junaid ya kada ya kasa ce masa komai yana kallonsa, El-ameen ya dunkule hannunsa ya kamo na Junaid ya kai masa knuckle yana murmushi yace "Chop knuckle frnd" Ana saukowa juma'a aka daure auren Capt Ahmad Junaid da Princess Zahrah El-ameen Moddibo a kan sadaki 1m wanda mahaifinta ne ya bayar, daurin auren nan ya samu halartan dubban mutane da 'yan gidan masarautu da dama daga ko ina na states din Kasar duk ta dalilin Sarki El-ameen Moddibo, masarautan bauchi ya xamo bbu masaka tsinke tsabar jama'a, kusan duk manyan da suka xo daurin auren mamakin mijin Zahrah suka dinga yi ganin shi ba basarake ba, shi ba yarima ba, shi ba jinin sarauta ba, shi ba kowa ba just a mere military personnel with CLASS, ba karamin alfahari sarki El-ameen yake da junaid ba da ya xamo sirkinsa, Junaid ya gaisa da mutane da dama sunfi dari kowa son ganinsa yake ta dalilin yanda sirkinsa wato sarki ke koda sa gaban abokansa sarakai da manyan kasa, baka taba fadin yanayin da Junaid yake ciki a lkcn sai dai kawai kaga yayi murmushi wani lokacin wanda iyakarsa lips, gam yake rike da hannun El-ameen dake gefensa don bai son su rabu, Su Abba basu suka bar bauchi ba sai kusan magrib don ba karamin walima aka shirya ba, xuwa bayan isha masarautan bauchi yayi tsit baka taba cewa anyi komai ciki don tuni aka tsaftace ko ina, Junaid dake xaune daki na musamman da aka basu shi da El-ameen, Aliyu, faisal da wasu frnds dinsa biyu, ya rike kansa har lokacin don ya kasa gaskata da shi fa aka daura auren nan yau, El-ameen ya dawo gefensa yace "Toh programs kusan goma ne fa gabanmu Mr man!" Dagowa yayi da sauri yana kallonsa, El-ameen yayi dariya yace "Atoh, gwara ka bar rike kai this is just the beginning, Abdul yace ka shirya xaka gun Zahrah, wato xaka je ganin amaryar ka....." Da 'yar dariya El-ameen ya kare xancen daga haka ya shiga bathroom don watsa ruwa, Aliyu dake ta danna waya yace "Duk karya ce!" Faisal ya kallesa ya danne dariyarsa yace "Meye karyar?" Aliyu yace "Wannan ji da kan da miskilancin wani mana" dariya sosai Faisal da sauran frnds din Captain suka dinga yi, shi dai Junaid bai tanka