Showing 39001 words to 42000 words out of 170905 words
Chapter 14 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
rai yayi ba, sha biyu da rabi ya kuma mikewa jin yana jin bacci sosai ya bude closet ya dau bargon da ya gani ya koma daya side din gadon ya shimfida a kasa ya kwanta dai dai yanda xai dinga ganinta, nan da nan bacci ya daukesa.
Bude ido yayi jin an bude kofa don ko k'adan bashi da nauyin bacci, El-Ameen ne ya shigo dakin yana ganinsa ya dauke kai, kallo daya El-Ameen yayi masa yana murmushi bai ma san idonsa biyu ba ya karasa gun da take kwance a kasa, durkusawa yayi gabanta ya dagota, ta bude ido da sauri, lumshe ido yayi jin xafin jikinta a hankali yace "Sorry, Jewel" xata koma ta kwanta yaki saketa, ya mike ya dauketa ya nufi kan gado da ita ya kwantar, kokarin sauka ta shiga yi da kyar, ya hade rai yace "No" bata kuma yunkurin saukan ba, ya gyara mata kwanciya ya mike ya shiga bayi, duk wannan abun Junaid na kallonsu, ya dawo dakin rike da bowl din ruwan sanyi ya bude closet ya ciro towel karami da babba ya saka karamin cikin ruwan bowl din ya dawo kan gadon ya ajiye bowl din kan bedside drawer, ya dagota yana kallonta don idonta biyu, ya dawo da bowl din ruwan gefensa ya matse ruwan towel din a hankali yana goge mata forehead dinta da shi, kara ta saki xata sauka ya hade rai yace "Wait!" Bata kuma yunkurin saukan ba, haka ya ci gaba da goge jikinta da yayi xafi sosai da towel din yana mata sorry, mikewa Junaid yayi, El-Ameen ya juya da sauri ya kallesa sannan yayi saurin rufeta da bargo yace "Ohh you weren't sleeping dama" Junaid bai tanka sa ba ya dauke bargon da ya shimfida kasa ya mayar cikin closet, El-Ameen ya tabe baki yace "Ni ban ma yi tunanin xan dawo in same ka ba Mumy's boy, theatre muka shiga da Abba and we came out few minutes ago, saboda nasan condition din patient dinka shi yasa na fito cikin daren nan, I ought to...." jin anyi banging kofa El-Ameen ya kalli kofar da sauri don dama yana magana ne yana matse towel a ruwa, murmushi yayi ganin ficewa yayi, ya ci gaba da abinda yake, har sai da yayi make sure temperature dinta ya dawo dai dai, still yayi ganin hawaye idonta, ya sunkuya a hankali ya goge mata fuskar yace "Am sorry Jewel, am only helping" sauka yayi daga kan gadon yaje ya xubar da ruwan ya shanya towel din a bayi ya fito, bacci ya sameta tana yi a yanda ya barta, ya gyara mata kwanciya sannan ya hada allura yayi mata da kyar don a tsorace ta farka ta fara kokuwa da shi, sai da yaga ta koma bacci sannan ya fita dakin ya shiga master bedroom duk a tunaninsa xae tarda junaid nan, sae yaga otherwise, tabe baki yayi sanin yana parlor knn, ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya canxa kaya yayi kwanciyarsa dakin, sai dai before dawn yaje dubata ya fi sau goma duk da a shigowarsa na uku ya tarda mama jummai a dakin, Karfe biyar da minti arba'in ya sauko parlor ya tarda Junaid xaune kan darduma, xaunawa yayi kan kujera yana kallonsa yace "A parlor ka kwana kenan?" Junaid ba tare da ya kallesa ba yace "Yea!" El-Ameen yace "Ohk, gud morning, yanxu dai you need to transfer some money into my account xuwa later akwae drugs din da na mata prescribing, and you know wat? Suna da tsada gaskiya or I shud just text you their names, tell you where to get them, kaje da kanka ka siyo, if you need my assistance let me know" El-Ameen ya kare maganar yana d'aga kafada, Junaid ya mike ya dauke darduman da yayi sallah yace "nawa ne kudin?" El-Ameen yace "100 nd 50k will be enough" Junaid yace "Alryt" ajiye darduman yayi kan kujera ya kalli El-Ameen yace "Na tafi, I will transfer it later in the day" bai jira cewarsa ba ya nufi kofa ya fice daga parlorn, makullin motarsa ya ciro a aljihu ya fita waje inda ya ajiye motarsa ya bude ya shiga ya kama hanyar gida, driving kawae yake amma gaba daya hankalinsa ba ya tare da shi, bai san yanda xa su kwashe da Mumy ba, toh ina ma xai ce mata ya je, gidansu El-Ameen? No yasan xata iya kiran Ummi, murmushi yayi yana tunanin randa xae samu freedom, don ya fara damunsa yanxu on like before, a waje yayi parking ya fito, gabansa ne ya fadi ganin Abbansa alamar daga masallaci yake, da kyar ya ja kafa ya isa gun gate ganin Abba ya tsaya har ya risina xai gaida Abba, Abba ya dakatar da shi yace "Daga ina kake?" Yayi kasa da kai zai yi magana Abba ya juya ya shiga cikin compound, bin bayansa yayi har suka isa part din Abba, Hajiya ke ta goge goge a parlon, Abba ya xauna kujera yana kallon Junaid, a hankali ya xauna kasa ya juya yana kallon Hajiya dake kallonsa da d'an murmushi mai wuyar fassara a fuskarta yace "Ina kwana Hajiya" tace "Lfya lau Ahmad" sunkuyar da kai yayi, Abba yace "Daga ina kake Ahmad?" A hankali yace "Tare muke da El-Ameen Abba" Abba yace "Tare a ina?" Hajiya ta dawo cikin parlon tana girgixa kai tace "kwata kwata ni hankalina bai kwanta da abotansa da yaron nan wai El-Ameen ba, yaron da bai da nutsuwa ko maganan iyayensa bai ji, kusan duk dare sai ya shigo ya fita da shi, Ahmad baxae dawo gidan nan sai kusan sha biyu wani lokacin har daya, duk ina lura da yake ni ba mai nauyin bacci bace ka sani Alhaji, to amma kar mutum yayi magana ace hassada ko kuma ace don ba d'an sa bane, amma kwata kwata Ahmad ya sauya hali a gidan nan, jiya wllh wllh khadija ca tayi min mace ta gani a motarsa da magariban nan da ya fita, to ina yaje yake dawowa yanxu, kuma duk Hajiya Amina tana ganin abinda yake baxata ce komai ba saboda ta dauki son duniya ta daura ma yaro, meye amfanin haka, in ma aure yake so ba sai yayi magana ba, ae ba wae bai isa bane" tunda ta fara magana Junaid ya kafeta da ido ko kiftawa bai yi, Abba kuwa sai kallonsa yake bacin rai karara a fuskarsa.
*Haske writers Association*
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
19.....
Junaid ya sauke ajiyar xuciya ya lumshe ido a hankali bai dai ce komai ba, Abba ya kalli Hajiya yace "A kira min Aminar" da sauri Junaid ya bude ido ya marairaice masa yace "Don Allah don annabi Abba ka min duk abinda xaka min, amma bbu ruwan Mumy bata ma san bana nan ba, plss..." wani tsawa Abba ya daka masa, babu shiri yayi tsit, Hajiya ta juya ta nufi kofa lebbenta dauke da wani murmushi, ba a dau lkci ba ta dawo tace "Suhaima ta tafi kiranta" Abba bai ce komai ba ta nemi waje ta xauna tana girgixa kafa tana tabe baki, ba a dau lkci ba Mumy ta shigo parlon da sallama, sai dai duk jikinta yayi sanyi ganin junaid xaune parlon tasan ba abun arxiki ya sa aka kira ta ba, kujera ta samu ta xauna tare da gaida Abba. Bbu yabo bbu fallasa ya amsa, junaid ya k'asa dago kai ya kalleta duk jikinsa yayi sanyi, Abba yace "Ke a tunanin ki so kike nuna ma yaron nan koh Amina, har ya kai matsayin da Ahmad baya kwana gida yanxu shi ba nyt duty ba kika xuba masa ido koh, toh dama an sha gaya min ban yarda ba amma yau idona ya gane min komai, don haka ni baxan bari ya dauko min abun kunya ba ina xaman xama na, just few weeks na basa ya fito da mata idan ba haka ba xai sha mamaki na wllh....." Mumy da har idonta sun cicciko ta kallesa cike da takaici tace "Alhaji kar ka manta Ahmad ba mace bane da har kake tsoron ya dauko maka abun kunya, kuma mace ake ma kulle ba namiji ba, ko yau ya ga bai son xaman gidan nan yana iya barin sa ya koma duk inda yake so don namiji yake ba mace ba kuma ya mallaki hankalin kansa, ni na haifi Ahmad na kuma fi kowa sanin halinsa ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba baxai aika ta mugun kaxamin kaxafin da ake son lika masa ba, I know my son" hawaye na bin kuncinta ta kare maganan, Hajiya ta bude baki ta saki salati tana tafe hannu, Abba ya mike fuskar nan tasa a murtuke yana kallonta yace "lallai Amina wato ni ke masa kaxafi kenan koh, to bari ki ji, wllh sati uku na basa yayi aure ya bar min gidana idan ko ba haka ba xai gane matsayina a gun sa" mikewa Mumy tayi tana kallonsa tace "Toh sai me, bai isa auren bane!" wani kallon Allah wadaran shaidanin mutum ta jefa ma Hajiya ta fice daga parlon, Hajiya ta dinga salati tana cewa "kiri kiri mutum yasan gaskiya ya danne don bai son laifin d'an sa, Allah sarki duniya" Abba ya kalli Junaid yace "Ka dai ji me nace maka, sati uku na baka wllh, get away" mikewa Junaid yayi da kyar ya fita daga parlon kansa na juya masa, part din Mumy ya shiga ganin bata parlor ya shiga bedroom dinta, xaune ya sameta gefen gado tayi tagumi, ya durkushe gabanta, ya daura kansa bisa kafarta cikin sanyin murya yace "Don Allah forgive me mum, it wasn't my intention disobeying you yesterday, I.. I am sorry mother forgive me plss" jin bata ce komai ba ya dago idanuwansa da suka kada yana kallonta, kamar xae sakar mata kuka yace "Plss Mumy kiyi hakuri!" "Ina ka tafi jiya?" Ta jefo masa tambayar tana kallonsa, rasa abinda xai ce mata yayi Cause he is not dat gud at lying, yanxun nan sae ta gano sa, ya kalli agogo, kallon agogon tayi ita ma taga bakwai saura ta d'an sauke boyayyen ajiyar xuciya tace "Tashi ka tafi" a hankali ya kamo hannunta yace "Plss Mumy kiyi hakuri nace" a nutse tace "Leave!" Ya kusa minti biyu durkushe gun sannan ya sake hannunta ya mike a hankali ya juya ya fita daga dakin ya shiga part dinsa. Cikin minti ashirin yyi wanka ya gama shirinsa, ya fito sae dai da ganinsa kasan bashi da nutsuwa, part din Mumy ya koma, ya sameta tsaye dinning tana jera masa breakfast, karasawa yayi yana rike da hularsa, Mumy ta bar dinning din, sosai jikinsa yayi sanyi ya ja kujera a hankali ya xauna ya dau mug din tea'n da ta hada masa ya shiga sha ba don yana jin sha ba, tea kawae ya iya sha ya mike ya dawo parlor yana kallonta yace "Xan tafi aiki Mumy" tace "baka ci dankalin ba, wa ka bar ma? go back and eat it yanxu" ba musu ya koma ya d'an ci kadan sannan ya kurbi ruwa ya dawo yace "Na ci Mumy" tace "Allah ya tsare" a sanyaye ya nufi kofa ya fita, Humainah da fatima sun fito daga part din Abba kenan, Humainah ta nufesa ganin parking lot ya tafi ya bude motarsa, kan ta iso har ya shiga, ta bude motar ta wara ido tace "Ya Ahmad Abba yace anjima ka kai ni islamiyyar su fatima ni ma a min...." Fixgo kofar motarsa yayi ya rufe, tayi still wajen tana kallon bakin glass din motar, yana gama ba motar wuta ya ja ya bar wajen, tsaki ta ja sai kuma ta fashe da kuka ta juya suka yi ido hudu da Hajiya da suhaima dake kallon duk abinda ya faru, Suhaima ta fashe da dariya, da gudu tayi part din Mumy tana kuka kamar wata jaririya. Haka Junaid ya wuni gun aiki duk bai da sukuni, colleagues dinsa har tambayarsa suka dinga yi ko lafiyarsa yace he's just having a slight headache ne, duk ya tuna abinda Abba yace sai gabansa ya fadi ba kadan ba, wai 3wks, kuma yasan ba lallai yayi kaffara a kansa ba, tunda ya dauki kudurin taimakon baiwar Allahn nan yake fuskantar challenges iri iri ga shi bashi da rest of mind as before, and he knows he is only doing it for Allah's sake ba da wata manufa ba, damuwar da yake ciki bai hanasa yi ma El-Ameen transfer din dubu dari da hamsin din da yace na drugs dinta ba, Hudu bai karasa ba ya bar gun aiki ya dawo gida, part dinsa ya nufa ba tare da ya kalli su Umma da Hajiya dake xaune balconyn Hajiya ba yayi shigewarsa parlor yyi banging kofar, Hajiya ta tabe baki tace "Ke maganar ki gaskiya ce wllh, tsinannan uwar nan tasa bata bari yaci girkin mu, ita ke masa da kanta kullum" Umma tayi kwafa tace "Ahaf Ba baki yarda ba da, ae wannan matar ae sai dai muyi adduar ganin karshenta" Hajiya tace "Toh wai meye kuma next move din da xa mu dauka tunda gashi ance ya fito da mata nan da sati uku, ke kar fa kuma yace wannan shegiyar Humainah take kowa, kinsan fa ba kula matan yake ba, kar uwarsa tace ya fito da Humainahr kawai mu shiga uku, wannan fa shine anyi ba ayi ba" Umma ta xuba tagumi tana gwalo ido yace "Yo ni ae wannan tunanin bai fado min ba wllh, kai da mun shiga uku, ni fa Humainahn nan ba karamin tsana nayi mata ba fa don duk da dududu bata fi sati gidan nan ba naga alama bata da kunya ko kadan, kuma ko shigowa gaishe mu bata yi, sai ma taga dama take gaishe mun in ta shigo gun Alhaji, kuma ina ga kamar tsinannar Aminan nan ke xuga ta" Hajiya ta sauke ajiyar xuciya tace "Xamu san yanda xa muyi da shegiyar ita ma, kuma ma ni ban ga alamar suna soyayya ba kin san halinsa ai, kuma ni shawarata kawai mu hade kai mu san yanda xa ayi Alhaji ya hada sa da Suhaima ko Muhibba shikenan sai yanda muka yi da shi" Umma tace "Toh ai matsalar ynxu kawai kullin da aka bamu mu barbada kofarsa ne, ya xa muyi? kinsan ba xuwa can bangaren muke ba, muna xuwa yanxu xa a gano mu, kuma don tsiya wai sai da magriba, dama da rana ne bbu wanda xai lura shi kuma yana gun aiki, ita kuma sallamammiyar 'yar ki khadija ba bamu hadin kai xata yi ba" Hajiya ta d'an yi shiru sannan a hankali tace "Suhaima xata yi mana aikin, nasan halin abata tsaf xata yi ba tare da an xargi komai ba" Umma tace "Toh Alhmdllh" da haka suka ci gaba da hirarrakunsu cike da rashin tsoron Allah.
Junaid kam wankansa yayi ya dauro alwala ya fito ya shirya cikin kananun kaya yayi la'asar a dakin sannan ya fito yayi part din Mumy, suna xaune da Humainah tana mata tsifa, Ya xauna yana kallon Mumy yace "Ina yini Mumy" bbu yabo bbu fallasa tace "Lfya lau" shiru yayi, Mumy ta hade rai tace "Ka kyauta Ahmad ita 'yar uwar taka ka walakanta gaban idon makiyan ka koh?" Humainah ta bata rai, sai kuma ta fashe da kuka, Mumy tace "Ji walakanci, meye haka ke kuma" mikewa tayi fuu ta koma dining tana rera kuka, Mumy tayi tsaki ta galla masa harara ta shige daki. Murmushi yyi yana shafa kansa ya mike ya nufi dinning din, kujerar dake kusa da wanda ta xauna ya ja ya xauna ta mike xata bar wajen ya rikota ya mayar da ita ya xaunar yace "Wai dama daxu magana kike min" ta fizge hannunta tace "Ohon maka" dariya yayi yace "Ni fa nayi xaton da kofar mota kike, toh tunda da ni kike yi hakuri..." Ta fashe da wani sabon kukan tace "Allah bana so" murmushi kawai yake yana kallonta yace "Toh kar ki so din, har da wani kwalliyarta tayi xaton da El-Ameen xamu dawo" ta dago da sauri tana kallonsa ta tsuke fuska tana goge hawayen idonta tace "Wani kwalliya nayi" giranta ya taba a hankali yace "Ba gashi ba har da wani shafa baki kika yi anan irin yanda kuke yi" ya kuma kallon pink lips dinta yana murmushi yace "Har da wani shafa jan baki a nan duk don ki burgesa" buge masa hannu tayi fuskarta daure tace "Tun da kai ka shafa min ba" mikewa tayi xata bar wajen ya rikota da sauri yana dariya yace "Toh na dai ce kiyi hakuri koh" ta turasa tayi gaba abunta, murmushi yayi ya tabe baki, fatima dake bakin kofar kitchen tayi gyaran murya tace "Uhum ya A.jay Humainaj kadai yake ma dariya a gidan nan" wani kallo yayi mata, ta juya da sauri ta koma kitchen tana dariya, tsaki yyi ya bude food warmern dake dining din, kadan ya xuba shinkafar ya ci ya dawo parlor don duk bai da Appetite, kofa ya nufa ya koma part dinsa ya kwanta ya lumshe ido, yana son ya gansa can gidan El-Ameen ya ga halin da Baiwar Allahn ke ciki amma yasan baxai ma fara cewa xai fita ba, haka yayi ta juye juye kan kujeran duk ya rufe ido ita yake gani, shi kam tun da ya fara ganin yarinyar nan nutsuwarsa ya ragu, toh ko dai haushin taimakon nata da yayi take ji shiyasa ya kasa samun kwanciyar hankali, bude ido yayi jin an bude kofarsa, ya juya da sauri ya ga Humainah ce, ta hade rai ta dungure masa bowl din fruit salad din hannunta a kasa, murmushi yayi yace "da kin xubar ai," ko kallonsa bata yi ba ta fice. Washegari haka ya tafi aiki da safe as usual, ba laifi Mumy ta d'an kulasa da yaje breakfast, Abba kuwa dama da yaje gaishesa ca aka yi masa yana bacci, ko ta kan Umman bai bi ba yayi ficewarsa don ya saba