Showing 27001 words to 30000 words out of 170905 words

Chapter 10 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

620

ta bude da sauri har jikinta na rawa, ya xuba mata maganin gaba daya, sai da ya tabbatar ta shanye snn ya mike yana kallonta, banda yatsine fuska bbu abinda take, yayi murmushi ya juya ya fita daga dakin, downstairs ya sauka ya samu Mama Jummai kadae palon, yace "Junaid fa Mama?" Tace "Ya fita ae" yace "Ohk, ki taso toh ki rakata baya tayi fitsari yanxu xata yi bacci tunda na bata magani" mikewa tayi tace "Toh, ae tana da tsafta yarinyar duk me xata yi naga tana shiga bayi" yayi murmushi yace "Kin dai yrda bata komai yanxu koh" yar dariya tayi tace "Ehh na yrda, don daxu ina xaune ta sauko, duk na tsorata ba kadan ba, ae ko in gaya maka sai gani nayi ta xauna gefe na ta mimmike kafa yanda taga nayi" dariya El-Ameen yayi yace "Ae wayo gareta, idan Allah ya yrda sama mata lfya baxae wani dau lkci sosai ba, kila daga nan xuwa wata hudu ko shidda in'sha Allah" Mama jummai tace "Toh Allah ya yrda, Allah ya ba Baiwar nan tasa lfya, gashi 'yar yarinya da ita" yayi murmushi yace "Kina ga xata yi shekara nawa" Mama jummai tace "Kai baxata wuce sha shidda ba wllh, in ma ta kai kenan" yana murmushi yace "Ko kuma sha bakwai ba" Mama jummai tace "Allah sarki, amma dai ku dinga hada mata da Addu'a kunsan duniya bbu gaskiya, kar ayi ta na turawa nan kuma kila asiri ne" ya d'an yi shiru kafin yace "Anya kuwa, bana tunanin jifa ne, don da jifa ne ba lallai ta xama nutsatssiya haka ba, nd jiya naga tana ta observing wnn tumatir din cikin dankalin da na siyo kuma ta sha sosai" Mama Jummai tace "Toh Allah dai ya bata lfya amma dai ayi addu'ar ma" yace "Ameen, xa a hada mama" Sama mama Jummai ta nufa shi kuma ya xauna palon, bata mata wani gardama ba ta kai ta bayin. Ko da Mama Jummai ta sauko mikewa El-Ameen yayi ya koma sama, kwance ya sameta idonta lumshe alamar xata yi bacci, ya gyara mata kwanciya ta bude ido da sauri tana kallonsa, ya rufa ta da bargo, ya dawo dai dai fuskarta yace "Gudnyt" lumshe ido kawae tayi ya juya ya fita daga dakin ya rufo mata kofa, yayi ma Mama Jummai sae da safe ya fice daga palon, xaune ya ga Junaid a balcony, ya d'an bude ido da mamaki yace "Thought ka tafi ai" Junaid ya mike yace "Sure! Yanxu xan tafi" daga haka ya sauka balconyn yayi hanyar gate, El-Ameen ya bi sa da kallo sannan ya tabe baki ya bi bayansa, kusan a tare suka fita compound din, El-Ameen ya kalli motar da Junaid ya nufa yace "Whose car is that?" Ba tare da Junaid ya kallesa ba yace "Abdul" daga haka ya bude motar ya shiga, El-Ameen ya karasa gun motar yace "Yhu are acting strange this dayz Captain, let it not be kai ma ka fara samun brain disorder'n ne fa, aikin sai yayi min yawa" El-Ameen ya kare maganar yana murmushi, junaid ma yayi murmushi yace "Sure!" Daga haka ya ja motar ya bar sa nan tsaye, El-Ameen ya bi motar da kallo yana murmushi yace "It's Alwayz: 'Yea! Sure! D'an rainin hankali, tasa motar shi ma ya nufa ya bude ya shiga ya bar anguwar yana tunanin yanda xai yi squeezing time dinsa gobe da safe ya xo ayi diagnosing dinta.


*Haske Writers Association*💡
⚓ *Captain_Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

14.....

Junaid na isa layinsu ya kira Abdul don ya fito ya karbi motar sa, Abdul ya fito yayi instructing mai gadinsu ya bude gate, yana budewa Junaid ya shiga yayi masa parking a parking lot din gidan sannan ya fito ya mika masa makullinsa yace "Thanks Abdul, sae da safe." Masallaci ya fara shiga yayi Isha sannan ya shiga gida, sai da ya tabbatar Mumy baxata hangosa ba idan ya xo wucewa ta side dinta sannan ya wuce da sauri. Humainah ce tsaye bakin tap tana diban ruwa, ta bi sa da kallo tace "Daga ina kake ya Ahmad" ba tare da ya kalli inda take ba yace "Inda kika aike ni" dariya tayi tace "Mumy fa na ta neman ka" dawowa yayi da sauri wajenta yace "Kice Wllh, tun yaushe?" ta kyalkyale da dariya tace "Tsaya nan, tun daxu ake neman ka" ya hade rai yace "Ke wa ya gaya maki?" Ta d'an yatsine fuska tace "Tare mukayi ta neman ka ae har da Hajja, da Abba, an ma kira layin ka bae xuwa wai switch off" shiru yayi ya ma rasa tambayar da xae kuma yi mata, ta tabe baki ta kashe tap don bucket dinta ya cika, Muhibba ce ta karaso wajen, kallo daya tai ma Junaid ta dauke kai, Empty Bucket din dake wajen ta kalla tace "Ke wa yace ki taba min ruwan da na tara?" Humainah ta tabe baki tace "Oho, nima haka naga bokitin" cike da masifa Muhibba tace "Kar ki gaya min maganar banxa ba ni da ke bane a nan xaki wani ce baki sani ba" hararanta Junaid yayi ya juya xae bar wajen, Muhibba ta yi ball da ruwan da Humainah ke diba, Humainah ta xaro ido tace "lalala! Wllh sai na rama" dawowa Junaid yayi da sauri ya rike ta ganin tayi gun Muhibba, yace "Ke Babu ruwa a ciki ne?" Kamar xata yi kuka tace "Dubi fa abinda ta min ya Ahmad, Hajja ce fa ta aikeni in debo mata ruwa" yace "Ke kin taba ganin inda ake fada da mara hankali!" Humainah tace "ohh Kuma fa haka ne" yace "Gud! Ki tafi ciki ki debi ruwan ki" tace "Ko ba Hajja ta sa mai gadi ya kashe engine ruwan ba tun da rana" yace "Ehh xan je in kunna yanxu" tace "Toh" juyawa Muhibba tayi fuu ta bar wajen, Humainah ta kyalkyale da dariya, ya harareta ya juya yayi side din Mumy, da sauri tace "ni fa wasa nake maka ba a neman ka" juyawa yayi yana kallonta yace "Na fara wasa da ke ne koh?" Kwafa yayi ya nufi part dinsa. Muhibbah na shiga part dinsu ta xube jikin Hajiya dake xaune Palon da Rabi'a ta fashe da kuka tace "Hajiya kina ganin fitsaran da yarinyar nan da suka xo gidan nan da Hajja ta min, har Ahmad na Goya mata baya yana kirana mara hankali" Hajiya da bacin rai ya bayyana karara a fuskarta tace "ki ka barta baki ci ubanta kin nakada mata duka ba?" Muhibba na share hawaye tace "Toh ba yana tsaye gun ba" Sadiya tace "duk uwarsa ke xuga sa yake rashin mutunci a gidan nan wllh" mikewa Hajiya tayi kamar xata tashi sama ta fice daga palon tayi part din Junaid, yana xaune rike da remote xae yi powering Tv ta shigo, kallo daya yayi mata ya dauke kai, cikin fada tace "Ahmad ita Muhibbar kake kira mahaukaciya? Toh in har Muhibba na hauka to Amina ma haukan take, ita ce ma babban mahaukaciyar..." Mikewa yayi yana kallonta a nutse yace "Ina ganin girman ki a matsayin ki na matar mahaifi na, amma kika sake kika taba mahaifiyata girman nan xae xube wllh," a fusace tace "Ya dade bai xube ba girman don uwarsa, da can ganin girman mu kake munafuki, ai mu wllh sai dai mu ce Allah ya isa tsakaninmu da Amina duk ta shanye mana miji sai yanda tayi da shi, kai ma ka taso kana neman xame mana fitina da bala'i a gida to kun yi kadan daga kai har makirar uwar taka....." Wani irin kallo Junaid ke mata ya girgixa kai yace "Gaskiya jahilci cuta ne" xaro ido tayi ta dafe kirji tace "Ni kake kira jahila Ahmad?" Juyawa yayi ya koma ya xauna, ta fashe da kuka ta juya ta fice daga palon. Ko minti biyar bata yi da fita ba Khadija ta shigo tace "Ya A.jay Abba na kiran ka" ya kalleta ya dauke kai ta fita, mikewa yayi ya bi bayanta. Part din Abba ya tafi ya shiga palon da sallama, babu abinda ya daga masa hankali sai ganin Mumy da yayi a palon, ya karasa a sanyaye ya xauna kasa kusa da ita yana kallonta, ganin taki kallonsa yasa ya juya ya kalli Abba yaga yanda ya wani hade rai yana kallonsa, Hajiya na xaune palon sai sharban kuka take, Umma sai wani sauke ajiyar xuciya take tana tabe baki, ko kadan hakan bai damesa ba yafi tunanin fushin Mumy a kan ma na Abban, Abba ya mike cikin tsananin fushi yace "Ahmad maimaita abinda ka fadi ma Hajiya a palon ka daxu" ya d'an kalli Abba sannan yayi kasa da kai yayi shiru, Abba ya daka masa tsawa yace "Ba magana nake maka ba" nan ma dai bai dago ba bare yace wani abu, Hajiya aka kuma fashewa da kuka mai sauti, Abba yayi murmushin takaici yace "Wato ita Hajiyar kake kira da jahila ko Ahmad?" Junaid ya girgixa kai har lokacin bai dago ba yace "Ni ban kirata da haka ba Abba" Wani tsawa Abba ya daka masa yace "you are stupid, sharri tayi maka kenan" Junaid ya girgixa kai, a fusace Abba yace "Toh bari kaji abinda baka sani ba, in har xaka iya bude baki ka ce ma Hajiya Jahila, to bbu tantantama warcan da ta haife ka ma xaka iya kiranta da haka, ka sani matsayin uwarka dai dai yake da wa ennan da ka raina a gidan nan, kuma from henceforth a gidan nan sai ka ma uwarka fitsara ka xauna lafiya amma idan ka kuskura kace xaka masu sai ka ga the other side of me wllh, I will deal with you, maxa tashi kaje ka bata hakuri kar in baka mamaki yanxu" Junaid da yaji kamar an soka masa mashi ya daga kai da kyar yana kallon Mumy, hawaye ya gani idonta, rudewa yayi ya dawo gabanta ya durkusa yace "Noo plss mum, kar ki xubda hawayen ki saboda ni, don Allah kiyi hakuri ki yafe min" bude baki Abba yayi yana kallonsa da mamaki, Hajiya da Umma ma sai kallonsu suke cike da tsana, shi kam magiya ya dinga yi ma Mumy yana bata hakuri ba tare da ya kuma bin ta kan Abba ba, mikewa Mumy tayi ta fice daga palon, shi ma ya mike xai fita, Abba yayi masa wani mugun tsawa, juyowa yayi yana kallonsa a hankali yace "Abba xan je in dawo"

Karfe hudu da rabi Junaid yyi parking a parking area din gidansu, ya dade xaune cikin mota yana danne dannensa a waya har sai da Humainah ta leko daga part din Mumy, ganin haka ya kashe motar ya fito ya kulle, wuce ta yayi ya bude kofa ya shiga, ta bi bayansa tace "Me kake cikin motar ya Ahmad?" Yace "Abinda kika sa ni" dariya tayi ta bi bayansa, ya xauna Palo yana kallon Mumy a hankali yace "Sannu da gida Mumy" tace "Welcome, kai dadin xaman mota kawae kake" murmushi yayi ganin Mumy ta huce gaba daya yace "Na gaji ne Mum" Humainah ta xauna kasa kusa da shi tace "Sannu da dawowa ya Ahmad" banxa yayi mata, fatima dake palon ma tace "Sannu da dawowa yaya" yace "Yauwa" sannan ya mike yace "Bari in je in yi wanka Mumy" Mumy tace "Ba gaisheka Humainah yi ba" yace "Gulma ce fa Mumy, da tana gaishe ni ne" Mumy ta hararesa yyi murmushi kawae ya nufi kofa, Humainah ma ta bi sa da harara, Yana shiga part dinsa yayi wanka ya dawo Palo yayi kwanciyarsa, yana son xuwa gidan El-Ameen amma bai ma san inda xae ce ma Mumy xai je gashi yana ta kiransa tun a gun aiki ya ki dagawa, ashe akwai ranan da xai ga disadvantage din rashin fitarsa, don da yana fita da Mumy baxa ta dinga querying dinsa ba idan yace xae fita yanxu, mikewa xaune yayi jin an bude kofar parlour, Humainah ta shigo ta tsaya daga bakin kofa tace "Mumy tace ka xo ka ci abinci" dauke kai yayi yace "Naji" ta karaso cikin parlour'n tace "ni da ita muka yi girkin, tuwo da vegetable soup" ya hade rai yace "Who ask yhu" dariya tayi tace "Toh don ma na gaya maka" ya tabe baki ya mike ya dauki wayarsa ya nufi kofa, mikewa tayi ta bi bayansa da sauri, sai da suka fita yace "Hajja fa?" Tace "Bata nan taje gidan kawarta yau, kasan gobe xa mu koma" ya kalleta yace "Wa yace maki tare xa ku koma, bayan Abban ki yace ya ba mu ke" hade rai tayi tana kallonsa tace "Wa yace maka haka" murmushi yayi ya bude kofar parlour'n Mumy ya shiga ta bi bayansa. Kasa ta xauna tana kallon Mumy tace "Mumy wae ba da ni Hajja xata tafi ba gobe?" Mumy tace "ba tace nan xata bar ki ba" hawaye ne ya cika idonta tace "A'a ae ni ban ce xan xauna ba" Mumy tayi dariya tace "Toh bari idan ta dawo sae ki gaya mata, Meye abun kuka" dariya Junaid yayi yace "Ae sai dai tayi na jini nan xata xauna ita da fatima da khadija" ta fashe da kuka tana kallon Mumy, Mumy ta hararesa tace "kaga wuce dinning ka ci abincin ka bana son haka" mikewa yayi ya nufi dinning yace "Yi hakuri Mumy" mikewa Humainah tayi xata fita daga parlour'n Mumy tace "Ina xa ki" tana goge fuskarta tace "Xan je in jira Hajja" Mumy tayi dariya tace "Ai yanxu xata dawo, xo kiyi xaman ki a nan ki jirata" bata tsaya ba tayi ficewarta a palon. Har aka kira Magrib Junaid na kwance palon Mumy duk ya rasa yanda xae ce mata xai fita, mikewa yayi ya nufi toilet din palon yayi alwala ya fita xuwa masallaci, yana dawowa ya nufi part din Abba sanin ya shiga yanxu, Hajiya ce a parlour'n tana jera masa abincin supper a kasan lallausan rug din tsakar parlour, ya karasa ciki kansa a kasa yace "Ina yini?" Hade rai tayi tace "Ka fita don Allah abinci xai ci ynxu" tsayawa kallonta yayi, dai dai lkcn da Abba ya fito daga bedroom dinsa, Abba ya karaso cikin palon yana kallonsa, karasawa yayi inda Abba ya xauna, ya xauna daga kasa shi ma, a hankali yace "sannu da dawowa Abba" Abba yace "yauwa sannu, ya aikin?" Har lokacin bai dago ba yace "Alhmdllh!" Abba yace "Gud! Daxu baka shigo gaishe ni da safe ba" shafa kansa yayi yace "Na shigo Umma tace kana bacci" Abba yace "Ohk, amma baka karasa bedroom ba" junaid ya gyada kai kawae, Abba yace "kafi kowa sanin bana baccin safe ae" shiru Junaid yayi bai kuma cewa komai ba, kallonsu kawae Hajiya keyi ta gefen ido tana jera abincin da take rai ba dadi don bata so haka ba, Abba ya sauko kasa ya jawo babban food warmer, ya dau plate xai dibi shinkafa, Junaid ya karba yace "Bari in xuba maka Abba" sake masa spoon din Abba yayi, ya dibi shinkafar da stew a gefe da cow meats, snn ya xuba masa vegetables a kai kamar yanda ake masa, Abba ya dauki wani spoon din yace "Bismillah" sai da Abba ya fara ci sannan Junaid ya debi shinkafar a hankali ya kai bakinsa, Hajiya kamar ta hadiye xuciya ganin ko ta kanta Abba bae bi ba, taunar abincin kawae junaid yake ba don yayi masa ba, banda girkin Mumynsa babu na wanda yake ci, girki in ba nata bane ko kallonsa bai yi, shiyasa a ko da yaushe take bata tym dinta tayi masa girki, a tare suka gama cin abincin da Abbansa, bai yi Mamakin sakkowan Abba da wuri ba don in dai suka hada sa da shi, bai daukan lkci yake kuma jawo sa jiki, kwata kwata baya fushi mai tsayi da only son din nasa, hakan ba karamin daga ma su Hajiya hankali yake ba, sun dai rasa yanda xa su yi da Junaid a gidan, a tare suka tafi masallaci sllhn Isha da Abba, sae da suka dawo ya ba Abbansa hakuri a kan abinda ya faru jiya, Abba yace "Its Ohk, ka dai kiyaye halshan ka nan gaba" yace "In'sha Allah Abba" sun jima suna hira da Abba sannan yayi masa sai da safe ya mike ya fita ya shiga part din Mumy, tana xaune palo tana kallo, ya xauna gefenta ya dauki remote xae canxa tasha, Mumy ta karbe remote din tace "ya haka, bari a gama program din mana" kallon Humainah dake kwance kusa da fatima yayi yace "Har kin hakura xaki xaunan kenan?" ta daga kai tana kallonsa bata tanka sa ba ta dauke kai, Mumy tayi dariya tace "babban kawai" bude kofa aka yi hade da sallama, Junaid ya kalli agogo jin muryan El-Ameen, ya ga tara da rabi, Mumy tace "Kai dai baka jin fitan dare koh El-Ameen" junaid yayi murmushi yace "Kin manta likita ne Mumy" El-Ameen ya karaso parlon ya xauna yana murmushi ya gaida Mumy, da fara'a tace "lfya lau bokon turai ya aiki" yace "Alhmdllh Mumy" Fatima tace "Welcome bro" yace "Thank you sis" kallon Humainah dake xaune hankalinta na gun kallo yayi sannan ya kalli Junaid, Mumy tace "baki gaida yayanki ba Humainah" ba tare da ta kallesa ba tana ci gaba da kallonta tace "Ina yini" idonsa na kanta yace "Lfya lau" hira suka dinga yi da Mumy, ganin hiran ba me karewa bace Junaid ya mike ya nufi kofa yace "Ina part dina in ka gama karyan" dariya Humainah tayi a karo na farko ta kalli El-Ameen da ya hade rai yana kallon Junaid, Mumy ma tayi dariyar tace "Ae dae ya fi ka wllh tun da har yana daurewa yayi karyar" Junaid dake bakin kofa ya saka dariya yace "Surutun fa iyakansa a gida Mumy, mutumin da ko magana bai iya yi ma mace ba a waje sai kame kame," El-Ameen yace "Ehh ae kai naga ka iya d'an rainin hankali" banda dariya bbu abinda Humainah ke yi Mumy da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login