Showing 69001 words to 72000 words out of 170905 words

Chapter 24 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

663

Hafsat ta amsa da murmushi, ta juya tana kallon Jasmine ita ma ta gaida ta, kallonta kawai Jasmine ke yi kmr idonta xa su yi magana, Junaid yace "Leave ki je kiyi abinda na sa ki" juyawa tayi ya bar parlon tana mamakin abinda yasa taki amsa gaisuwarta, Junaid ya kalli Hafsat da sauri yace "Tana fitowa sai ki gaisheta duk me xata ce kiyi ta bata amsa kawai" Hafsat ta gyada masa kai, ba a dau lokaci ba Mumy ta fito parlon, kwata kwata bata dauka da gaske Junaid yake ba, murmushi dauke fuskarta ta karaso tana kallonsu ta xauna tace "Sannun ku da xuwa" Hafsat tace "Yauwa Mama ina yini" tace "Lafiya lau, ya hanya" Hafsat tayi kasa da kai tace "Alhmdllh," ganin hankalin Mumy na kan Hafsat Junaid yyi saurin cewa "Tana gaishe ki Mumy" ya fadi hakan yana nuna Jasmine, Mumy ta kalli Jasmine don ita dai bata ji tace komai ba, ta dai yi murmushi tace "Lafiya lau, sannun ku da xuwa" Hafsat tayi saurin cewa "Yauwa Mama" Mumy ta kira fatima ta fito tace "Dauko masu ruwa fatima" kitchen ta shiga ta fito da tray ta nufi fridge ta bude ta fiddo ruwa da drink ta dawo parlon, kusa da Jasmine ta ajiye tray din ta kuma komawa kitchen ta dawo da snacks, Jasmine ta kalli Junaid da gabansa ke ta faduwa ta fara kokarin sauka kasa ai da sauri ya riketa yanda bbu wanda xai lura, ya jawo remote yayi powering tv, tvn na kawowa ta koma ta xauna tana kallo, sallaman su Umma da Hajiya yasa xuciyarsa kusan shigewa cikinsa, suka karaso parlon su Suhaima na biye da su a baya ko warce da murmushinta a fuska, Hajiya tace "Ashe bakuwar har ta iso ko a sanar da mu, sannun ku da xuwa," Mumy tace "Ae kuwa, da wai idan sun tashi tafiya xa su shiga su gaida ku" Umma tace "Allah sarki" Hafsat tace "Ina yinin ku" suka amsa mata a tare, Mumy dai sai kallon mamaki take ma jasmine dake ta kallo kamar her life depend on it ganin bata gaida su ba, Junaid ya lura da hakan hankalinsa ya tashi ba kadan ba, su kansu su Umma kallonta suke, Hajiya tace "Toh wai wacece surkuwar ta mu a ciki" Junaid na shirin cewa Hafsat ce, Hafsat ta riga sa ta hanyar nuna masu jasmine, ya xaro ido don shkkn tasa ta samesa, Umma tace "Ikon Allah, sannu Amaryar mu" nan ma dai ko dagowa Jasmine bata yi ba idonta na kan TV, Hajiya tace "Toh fah, anya amaryar nan na jin mu kuwa" Hafsat tayi saurin cewa "ba ma ta jin dadi ne muka fito..." Umma tace "Ikon Allah, ana burin auren lafiyayya shi kuma ra'ayinsa kenan bawan Allah, Allah sarki naga ma kamar ciwo gareta a kafa don bbu takalma ku ka shigo" lumshe ido Junaid yayi a hankali ya bude, shi kam ya shiga uku da matan ubansa, Mumy dai bata tanka su ba ta kalli fatima tace "Xubo masu abinci fatima" Guri Hajiya ta nema ta xauna tana cewa "Tun da baki gare mu bari mu xauna" Junaid ya watsa mata wani kallo ta gefen ido, Umma ma ta xauna tana cewa "Toh baxa a kai ta gun Hajja ba tun da tana nan..." Gaban Junaid yayi wani mugun faduwa jin sunan warce ta kira, Mumy tace "Xa su je" Hajiya tace "Ya kamata kam, ai da mun san da xuwansu da ko 'yar girki ne mun yi" kallonsu kawai Hafsat take ko ba a gaya mata ba tasan matan ubansa ne, Fatima ta fito daga kitchen rike da warmer din abinci da plates da spoon, Junaid ya kalli Mumy a hankali yace "Baxa su ci ba Mumy" Hajiya tace "Suka gaya maka? Ke xo ki ajiye masu" Ko kallonta bai yi ba, fatima dai ta dire abincin gabansu, a hankali Mumy tace "Xuba mana" Bude kofa aka yi Humainah da Khadija suka shigo Hajja na biye da su a baya tana cewa "Don jaraba mutum ya kwaso uban tafiya a rasa abinda xa a hada sa da sai wani tsinannen taliya can, tsiya dai a gidan Muhammadu ta kare..." Khadija na ganin Jasmine tayi still bakin kofa da mamaki, Humainah kam kallo daya ta masu ta nufi daki, Hajja ta karasa shigowa parlon tana bin kowa da kallo tace "Xaman me ake haka, me ya faru" Hajiya tayi murmushi tace "Kishiyar ki Ahmad ya kawo mana mu gaisa" Hajja ta washe hakora tace "Ikon Allah, tana ina" lumshe ido Junaid yayi ya jinginar da kansa jikin kujera don yasa tasa ta kare kawai, Umma tayi murmushi ta nuna mata jasmine tace "Ga ta can kamar bebiye ba uhm ba uhm uhm," Hajja ta karaso baki har kunne tace "Ke don baki da kunya har gida xaki xo kwacen miji, to ahir dinki ni da Amadi mutu karaba" shi dai Junaid har lokacin yaki bude ido, ji yake kamar yayi tsuntsu ya bar parlon, Hafsat ma duk ta rasa abun yi a lokacin, fatima ta bude kulan me dauke da hadadden spaghetti ta shiga xubawa, Hajja ta dunguri Jasmine tace "Ya hure maki kunnen kar ki gaisheni kenan koh, to ba karamin aiki na bane in kora ku ke da shi wllh" juyowa Jasmine tayi da sauri tana kallonta, wani kara da ya tsorata occupants din parlon ta saki da karfi, Hajja na tuntube tayi kofa da gudu tana salati a tsorace, fatima ma dake gabanta tuni ta rufa ma Hajja baya, Hajiya da Umma da su Suhaima duk aka mike a tsorace, Mumy ma ta mike tana kallon Junaid, juyowa Jasmine tayi ganin ta kora Hajja, idonta ya sauka kan spaghettin da fatima ta fara xubawa a plate, wani karan ta kuma saki a rikice ta daga kafarta tana matsawa kusa da Junaid kamar xata shige jikinsa tana kallon taliyar, ae sai ga Umma da Hajiya ma bakin kofa da gudu 'ya yansu na biye da su a baya, Mumy kanta barin wajen tayi, Khadija ta karaso da sauri ta dauke taliyar tunawa da tayi haka ta ma indomie ranan, Hajiya ta saki salati tana tafa hannu tace "Al-qur'an mahaukaciya ce" Hajja ta dafe kirji tace "Mahaukaciya kuma" Mikewa Junaid yayi ya dagota, da gudu Hajja tayi waje su Hajiya suka rufa mata baya da gudu su ma, Mumy tace "Ahmad" tsayawa yayi ya juyo a hankali yana kallonta, sake hannun Jasmine yayi ya karasa kusa da ita cikin sanyin murya yace "Na'am" jin bata amsa ba ya dago kai yana kallonta ganin yanayin fuskarta yasa jikinsa yayi sanyi sosai, strictly tace "Wacece yarinyar nan" kasa ce wa komai yayi ta masa wani tsawa tace "Ba magana nake maka ba" a hankali yace "Ita nake son aure, Mumy it's a long story... Am sorry i hide everything for you, tana da brain disorder ne, so..." Mari Mumy ta sauke masa, Humainah dake tsaye bakin kofar daki tana kallon duk abinda ke faruwa ta juya a hankali ta bar wajen, lumshe idonsa yayi ya bude, Hajiya na tafe hannun ta saki shewa tace "Maganar Suhaima dai ya tabbata...." Hajja ta leko parlon tace "Amma na tausaya ma gwalma'da'dden rayuwar ka Ahmad, ka rasa shegiyar da xa ka kawo mana matsayin surka sai mahaukaciya, to Allah sai ya mana hisabi da kai, kuma maxa ku kira min ubansa duk inda yake ya dawo yaga me ya haifa ma kansa..." Hafsat da tausayin Junaid ya rufeta ta juya ta nufi kofa, da sauri Suhaima ta fincikota tace "Ke kuma algunguma munafuka har da yi ma mahaukaciyar jagora koh....." Mari me lafiya Hafsat ta sauke mata, Hajja tace "Kambu Ramaa!" Tun kan ta rama Hafsat ta kuma sauke mata wani, Muhibba da Sadiya suka yi kanta, ta fixgi wani vase dake parlon tace "Duk yar iskar da ta matso kusa da ni wlh sai na buga mata kuma babu abinda xai faru don baku son wanene ubana ba, yau Allah ya ga dama kuma sai ya daura maku haukan nan, kuma mahaukaci ai mutum ne, ba sonku Allah ya fi yi a kanta ba da ya bar ku da hankalin ku, ku ba abun farin cikin ku bane d'an ku xai yi jihadi ma, ga dai gida kamar babba amma karami ne" jefar da vase din hannunta tayi ta fice daga parlon, Hajja tace "Kaji gantalalla k'awar mahaukaciya kawai, uban waye hamagon uban naki, to mu dai xuri'armu babu mahaukaci, ke ubanki yayi jihadin ya aureta mana yar buhu kawai" tuni Hafsat ta kusa gate abunta, Hajja ta fashe da kuka tace "Ni kuu kira min Muhammadu ya xo ya ga abun da muke gani, Ahmad ya cuce mu, ya xo ya ga sa6on da Ahmad ya tafka, amma duk laifin uwarsa ce wllh kuma mu dai Allah ya isa, ina laifin ka fiddo 'yar uwar ka Humainah a matsayin warce xaka aura, ko ka xabo cikin kannin nan naka Suhaima da Muhibba, toh ni ina ya samo mahaukaciyar ma tukun" Mumy da har idonta ya kawo ruwa ta kalli Junaid da kansa ke kasa tace "Maida ta inda ka daukota kuma minti talatin kawai na baka kaje ka dawo" juyawa yayi yana rike da ita ya nufi kofa, Hajja da su Hajiya da suka ji kamar suyi shewa ana rige rigen gudu aka bar bakin kofar. Junaid na ganin dishi dishi ya nufi mota da ita, driving kawai yake amma bai ma ganin gabansa da kyau ji yake kamar a sama yake tafiyar ma, ihun da jasmine tayi da karfi yasa idonsa ya bude sosai, sai a sannan yaga irin tukin da yake da ihun da jama'a ma suke yi, kokarin kauce ma babban motar da yake kokarin karo da yayi, amma hakan bai yiwu ba don sai da suka yi karo bayan haka ya juya kan motar yayi gefen titi yayi cikin jama'a nan ma yaje ya buge da pole, sama sama ya dinga jin abinda Jasmine ke cewa, iya karfinta take cewa Umminta.... Umminta, Wayyo Umminta.... daga haka bai sake jin komai ba kuma bai sake sanin abinda ke faruwa ba.

*Haske Writers Association*💡
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓


_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

34.....

El-ameen ne xaune cikin special ward
ya hade kai da gadon dake kusa da shi, bude kofar ward din aka yi ya dago da kyar, dai dai lokacin da Hajja ta karaso gun gadon da gudu ta daura hannu a ka ta saki wani uban ihu tana salati su Hajiya ma suka shigo ko wanne tana salati, mikewa El-ameen yyi ya fice daga ward din, ba a dau lokaci ba nurses har hudu suka shigo suka fitar da Hajja da su Hajiya, kuka Hajja take rusawa iya karfinta tana cewa "Ku gaya min ko mutuwa yayi don Allah, wayyo mahaukaciya ta cuce mu, kila yana tukin ta shake mana shi ya saki steering, wayyoo ni Dijee" Su Hajiya dai sai matsen kwalla ake kamar gaske, El-ameen ne ya xo wucewa Hajja ta bi sa da gudu tana cewa "Tsaya Aminu gaya min me ya samu Ahmad din, don Allah gaya min ya mutu ne? Wayyo an kassara Muhammadu don shi daya gare sa" Tafiya kawai El-Ameen yake tana binsa da gudu har ya isa ward din ya shiga ya rufe kofar yasa makulli, ta fashe da matsanancin kuka tace "Allah ya isa tsakani na da kai dan iska" A hankali El-ameen ya karasa gadon da Junaid ke kwance yana kallonsa, a shoulder dinsa yaji ciwo banda nan bbu wani waje kuma sai dai har lokacin he's unconscious, juyawa yayi yana kallon Jasmine dake kwance a wani gadon har lokacin ita ma bata farfado ba, ya xauna ya hade kai da gado, shine mutum na farko da aka fara kira aka sanar ma hatsarin wanda hakan na nuni da shine mutum na karshe da suka yi waya da Junaid din, bude kofar ward din aka yi Abbansa ya shigo da wata nurse biye da shi a baya da clinic tray, mikewa yayi Abba yace "Meye amfanin saka su gaban da ka xo kayi ga injections ba a gama ba....." Baya ya koma Abba ya dafa goshin Junaid ya kuma yi masa gwaje gwaje sannan ya juya ya koma gun jasmine, a forehead dinta ta ji ciwo sai kneel dinta daya, ita ma ya mata gwaje gwajen da xai yi ya juya yana kallon El-ameen yace "Ka karbi injections din hannunta ka masu, in ka gama ka xo office ka dau wanda xaka xuba a ruwa" daga haka ya juya ya fita, nurse din ta karaso ta mika masa tray din hannunta ya karba ta juya ta fita, Junaid ya fara yi ma sannan ya karasa gun Jasmine ya mata a lap. Kasa fita daga ward din yayi ya koma ya xauna duk jikinsa ba kwari, Abbansa ne ya kuma dawowa tare da Abban Junaid, Abba ya karasa gun gadon yana kallon Junaid da ganinsa kasan kawai yana boye tashin hankalinsa ne, Allah ya basa lafiya kadai yace ya juya ya fita Abban El-ameen ya bi sa a baya, El-ameen ya koma ya xauna, har bayan azahar babu wanda ya farka cikinsu, har lokacin kuma Hajja na asibitin tana rera kuka har an gaji an kyaleta, su Hajiya duk sun koma gida, kiran la'asar ya sa El-ameen ya fita daga ward din don xuwa yin sallah, yana fito ko minti biyar ba a yi ba jasmine ta bude idonta a hankali, bin dakin ta shiga yi da kallo a hankali har idonta ya sauka kan Junaid, kokarin mikewa xaune ta yi taji kamar an tsikara mata allura a kneel ga kuma drip din da ta gani jikinta, ta koma da sauri ta kwanta tana kallon drip din hannunta, fixgewa tayi ta ajiye, ta kusa minti bakwai xaune kamar me son tuno abu wanda hakan da take yi yasa kanta yayi mata wani mugun nauyi ga tsara mata da yake kamar xai tsage, kara tayi ta rike kan da hannu biyu taji abu kamar hula a xagaye mata, da sauri ta cire hannunta, bayan kusan minti biyu taji ciwon ya rage, saukowa ta shiga yi a hankali daga kan gadon, kamar me tsoron tiles din dakin ta dinga tafiya tana dingishi har ta isa gadon da Junaid ke kwance tana lekan fuskarsa, komawa baya tayi da sauri, sai kuma ta saka kuka tana yarfe hannu lokaci daya tana kare ma dakin kallo, a hankali tace "Ummi...." Sake lekan fuskarsa tayi ta kusa minti biyu idonta a kansa kafin ta juya a hankali ta bar wajen, muryoyi taji daga waje ta nufi wani kofa da ta gani da gudu ta bude ta shige ta fashe da kuka, ji tayi an bude kofa can waje tayi saurin jingina a jikin kofar bathroom din, kallon gadonta kawai El-ameen yake da mamaki, can ya juya ya kalli Junaid, da sauri ya nufi toilet tana jin ya murda ta juyo da sauri ta tura kofar da duk hannunta biyu, sau daya ya tura kofar ya bude ta koma baya da sauri tare da juya masa baya, kallonta ya tsaya yi da mamaki, a hankali yace "Jewel" xaro ido tayi zuciyarta na bugawa har lokacin kuma bata juyo ba, karasawa yayi ya dafata yace "Jewel" k'ara tayi da karfi yyi saurin juyo da ita yace "Hey It's me jewel" tsit tayi tana kallon fuskarsa xuciyarta na bugawa, murmushi ya sakar mata ya kama hannunta yace "Am glad you are fine!" fixge hannunta tayi da sauri ta fashe da kuka tace "Ummina!" Tana fadin haka ta sake juya masa baya tana rera kuka, still yayi na kusan second ashirin sautin xaxxakan muryarta na kai kawo a kunnensa, ya kifta ido ya kusa sau biyar, can ta juyo a hankali suna hada ido ta sunkuyar da kai ta raba ta gefensa xata fita yyi hanxarin tare hanyar, da kyar ya iya bude baki yace "Wait! Wait Ina...ina Ummin naki?" Kallonsa kawai take sai kuma a hankali ta buda masa hannu alamar bata sani ba, cikin sanyin murya yace "Baki sani ba?" Ta gyada masa kai hawaye ya gangaro fararen idonta, murmushi ne yayi slipnn lips dinsa a hankali yace "Ohh! Alhmdllh!" lokaci daya murmushin ya bace tunawa da yayi sai fa ya iya xama kuma tayi loosing memory ya girgixa kai da sauri yace "No! no gaya min ya sunanki?" Kallonsa kawai take yi, ya gyada mata kai yace "Yyees tell me, ya sunanki?..." Gefensa ta kuma rabawa xata fita ya rikota, ta juyo da sauri ta warce hannunta tana masa wani irin kallon da yasa hanjin cikinsa kadawa, komawa baya yayi da sauri ta fice daga toilet din ya bi ta da kallo xuciyarsa na bugawa.

*Haske Writers association*💡

Ba yawa kuyi sorry, na gaji ne yau
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

35.....

Da kyar El-ameen ya iya juyawa ya fita daga bathroom din, ya ganta tsaye kusa da kofa tana kokarin budewa, tsayawa yayi yana kallonta har ta bude xata fita yayi saurin cewa "Wait wait ina xa ki" ko kallonsa bata yi ba ta fice, xaro ido yayi ya juya yana kallon Junaid kamar idonsa biyu din nan, bayanta ya bi da sauri ya tarar har ta sauka stairs tun kan ta karasa shiga reception ya sha gabanta, xuciyarsa na bugawa ya dake yace "Look, kin ga baki da lafiya ina xa ki" shiru tayi tana kallonsa, ya kasa kallon cikin idonta, cikin sanyin murya yace "Kiyi hakuri ki bari ki kara samun lafiya sai a kai ki gidan ku kin ji?" Jin bata ce komai ba ya dago da kyar yana kallon kwayar idonta, hawaye ya gani fal idon, ya dauke kansa, a hankali yaji tace "Toh ina ne nan?" Ya kuma dagowa da sauri yana kallonta yace "Asibiti," maimaita abinda ya fada tayi a sanyaye ya gyada mata kai, tace "Meye hakan?" Buda ido yayi yana kallonta lokaci daya jikinsa yayi sanyi, ya girgixa kai da sauri yace "Ki gaya min sunan ki tukun!" Shiru tayi tana kallonsa, can tace "Suna?" Ya gyada mata kai, kafa masa ido tayi kamar dai tana son tuno sunan, a xuciyarsa ya dinga furta innalillahi, k'ara tayi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login