Showing 24001 words to 27000 words out of 170905 words
Chapter 9 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
mana, sosai ma, yanxun ma wani frnd dina ne ke da wata patient with mental disorder, so am putting her under medication ne yanxu, after some month idan naga ba a dace ba, I will advise him to take her to a psychiatry for psychiatrist to take over, kila a dace a can din" El-Ameen na magana ne yana kallon Junaid fuskarsa dauke da murmushin rainin hankali, junaid dae ko kallonsa bae yi ba sai danna wayarsa yake, Faisal yace "Allah sarki, xa ma a dace idan Allah ya yarda, sae dai idan ba Neurologist El-Ameen din da na sani bane," dariya El-Ameen yayi yace "Noo, Dr El-Ameen dai, yanxu dai plss xuwa gobe ka lallaba sa ko na clinic ne ya aro min, coz nasan frnd din nawa will not afford it idan nace yaje can kasashen turai ya siya, its more than expensive" ya kare maganar yana ma Junaid wani irin kallo yana murmushi, Murmushi junaid yayi ba tare da ya kallesa ba, faisal yace "Alryt xan kirasa anjima, amma a ina xaka sa ta under medication din, clinic din ku?" El-ameen ya xaro ido yace "Sai in ce ma Abba a ina na samota?" Da mamaki Faisal yace "Kamar ya, 'yan uwanta fa?" El-Ameen yayi dariya yace "Ohh ai d'an uwanta a dai yanxu daya ne kacal a duniyar nan" kallonsa kawai Faisal ke yi da confusion shi ko sai dariya yake, Junaid ya tabe baki ya mike ya nufi bathroom ya dauro alwala ya fito don lkcn sllh yayi, bae jira su ba ya fice daga dakin don xuwa masallaci, Faisal ya bi sa da kallo yayi dariya yace "Kai halin Junaid sae shi, toh meye ma'anar hakan da yake yi, namiji dan uwansa ma sai ya ma miskilanci ina ga mace" El-Ameen yayi dariya yace "Let him, I think yana d'an da brain disorder'n shi ma, of recent na lura da hakan, kaga sae in hada shi da patient din tawa in sa su under medication" dariya sosai faisal yayi, El-Ameen yace "Amma fa rufa min asiri kar ka gaya masa sae ya Iya daukar gaba da ni daga yanxu har bayan watanni" bayi ya nufa yana dariya, faisal na taya sa. A tare duk suka fito daga mosque din bayan an idar da sllh, Junaid ya nufi motarsa ba tare da ya kallesu ba yace "Am going home" Faisal yace "Haba so early dama ba hira ka xo mu yi ba" Junaid ya kallesa yace "Ga Dr nan sae kuyi hiran, am going home kafin Mumy ta fara kirana" faisal ya rungume hannu yana dariya yace "Ehh gskya ne kuma wannan, madarar ka na can a feeder kar ya huce koh" murmushi junaid yayi yace "Yea! Sure." Daga haka ya nufi motarsa, El-Ameen yayi dariya yace "Allah ka nuna mana ranan da Junaid xae girma kamar mu" makullin motarsa ya mika ma Faisal yace "kaga shigar min da motata ciki, tare xa mu tafi, ltr xan dawo inji yanda ku ka yi da Dr isah" faisal yace "Ohk sai ka dawo" motar Junaid El-Ameen ya nufa da sauri ya bude ya shiga, Junaid dake kokarin tada motar ya kallesa yace "Ya aka yi?" El-Ameen ya hararesa yace "Mu je ka siya min potatoe dina mana, ko ka xaci na manta ne" murmushi junaid yayi ya tada motar ya ja suka bar wajen. Wani eatery ya tsaya ya fito ya shiga ciki, El-Ameen ya bi sa da kallo, ba a dau lkci ba ya fito rike da take away din fried Irish har hudu, ya bude bangaren da El-Ameen ya ke ya dungure masa ledojin a kan kafarsa snn ya rufe motarsa ya xaga ya shiga, dariya El-Ameen yayi yace "Toh me kenan, ni ae wannan ya min kadan" Junaid bae tanka sa ba ya tada motarsa suka bar wajen. Sae da suka hau kan titi ba tare da ya kallesa ba yace "Ina ka nufa don ni am going home" El-Ameen yace "drop me at home," junaid ya kama hanyar gidan nasu yana isa yayi parking ya juya yana kallon sa, bude motar El-Ameen yayi yace "Gobe xa ayi diagnose dinta!" Junaid ya gyada kai yace "Allah ya kai mu" El-Ameen ya fita daga motar yace "Ka gaida Mumy" kai junaid ya kuma gyada masa sannan ya ja motar ya bar kofar gidan.
yana isa gida ya dde xaune cikin motarsa a parking lot yana danna waya, fatima ce ta leko jin bae kashe motar ba har lkcn, yana ganinta ya kashe motar ya fito ya rufe, kallo daya yayi ma Umma da fitowarta daga side din Abba knn ya dauke kai yayi side din Mumy, Umma ta bi sa da kallo ta gefen ido tayi kwafa ta nufi bangarenta. Kwanciya Junaid yayi bayan ya gaida Mumy, Mumy ta xauna tana kallonsa tace "Ga lunch dinka a dinning" yace "Toh Mumy," Humainah ce ta fito daga kitchen ta shigo palon tace "Na gama Mumy" Mumy tace "Sannu Humainah, dauko ma yayanki abincinsa a dinning" ta juya ta tafi dinning din ta dauko warmer biyu, daya me dauke da jollof rice daya kuma farfesun naman rago, ta dauki plate da spoon ta dawo palon ta dire gaban Junaid dake kwance har lkcn idonsa lumshe, ta mike ta koma ta dauko drink da ruwa sae cup ta dawo ta ajiye, Mumy tace "Toh tashi ka ci abincin mana" mikewa xaune yayi yana kallon Humainah dake durkushe wajen har lkcn ya hade rai, ita ma haka, harara ya galla mata yace "ke wa yace ki shiga dakina ki dauki turare" ta tabe baki tace "Toh meye? kuma naga turaren kala kala ne shi yasa" Mumy tayi dariya tace "Atoh!" Ya wani hade rai sosai yace "God help yhu ki sake shiga daki na ki ga" mikewa tayi tace "Mumy xan je gun Hajja" Mumy tace "Toh kiyi mata sannu da xama" daga haka ta galla masa harara ta fice daga palon, sakkowa Junaid yayi ya xauna kan carpet yace "Yarinyar nan ta raina ni fa Mumy" Mumy tayi dariya tace "Ko dai kana ciki ne Captain" kallon Mumy yayi da sauri sai kuma ya marairaice mata yace "Ina ciki kuma Mumy, A'a ni matata na nan xuwa in'sha Allah, beside bana sha'awar auren xumunci ni" Mumy tayi dariya tace "Toh ka dinga sake mata don tunanin da Hajja da 'yan gidan ma xa su yi kenan, idan suka ga kuna haka da ita, kasan yanxu samarin nowadays idan suna son mace sae suyi ta wani basarwa, kaga suna yawan fadace fadace da ita barin ma idan yar uwar sa ce, wae su nan kar ta gane suna sonta ta raina su, wasu har da duka wae kuma duk cikin so ne fa" dariya sosai Junaid yayi yace "Ae kauyanci knn Mumy" Mumy tayi murmushi tace "Atoh, sae ka ga daga karshe idan suka ga yarinyar na neman kubuce masu su haukace su fito fili suce su fa sai ita" dariya junaid yake yace "Kai Mumy, wannan ae sae film ba dai reality ba" Mumy tayi murmushi tace "Toh shknn, it seems you've neva come across dat before" yace "Uhnn toh Allah kyauta, but it kinda funny mum" abincin gabansa ya bude ya dibi shinkafar dai dai wanda xae ci da plantains da nama sannan ya rufe, yayi bismillah ya fara cin abinci, yana gamawa Mumy ta kira mai aikinta ta fito ta kwashi plates din da warmer ta kai kitchen, kiran sllhn Asr yasa shi mikewa ya shiga bayin dake Palon ya dauro alwala ya fito, fatima da fitowarta palon kenan ita ma da shirin islamiyya tace "Ya A.jay xaka yi dropping dina in jira" yace "No" kofa ya nufa ya fita daga palon. Yana dawowa daga masallaci part din Hajja ya shiga, ya sameta xaune ta sa TV a gaba, Khadija kuma na kwance tana danna waya, xaunawa yayi yana kallon Hajja dake bin sa da kallo yace "wannan kallon fa Hajja" Hajja ta tabe baki tace "Ba sai ka tsole min idon ba" Khadija ya kalla ya hade rai yace "Ranan da xan xane ki na nan tahowa a gidan nan, baki da aiki sai danne danne kin yaye islamiyya yanxu koh" Hajja ta gyara xama tace "Ai mu sai Allah yayi mana shari'a da shegen wahalallen da ya kirkiri waya a duniyar nan ya bata mana 'ya 'ya, yanxu ace kamar Khadija daga safe har talatainin dare wancan shegen abun na hannunta tana latsawa tana murmushi, ta fa ji tsoron Allah taji tsoron gamuwarta da shi, Allah kadai yasan tsiyar da take tsulawa a shegen abun, shi kuma Muhammadu ba mai sa ido ba, ta inda bala ya fi sa kenan don har yau bai bari Humainah ta rike waya ba, wannan bala'i da me yayi kama? kana mata magana ma bata san kana yi ba ido kyar a kan waya, amma mu je xuwa ranan da Allah xai tashi kamata sai dai yar iskan wayar tayi bindiga a hannun ki wllh" kallon Hajja kawai Junaid yake kafin ya tabe baki ya kalli wayarsa dake ringing a hannunsa ya ga El-ameen ne.
✍🏻
*Haske Writers Association*💡
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍
13....
Junaid bai daga kiran ba ya juya yana kallon Khadija, Mikewa xaune tayi ta hade rai kamar xata yi kuka tace "Ni fa wllh ba chatting nake ba ya A.jay, ita Hajja bata san komai ba sai dai tayi ta magana" Junaid xai yi magana Humainah ta shigo palon fuskar nan nata a daure ta xauna gefen Hajja, Hajja tace "ke kuma fa? Ina aiken" Humainah tace "ko ba yi tayi kamar bata gan ni ba, kuma bata ce min komae ba sai aikinta take tana wake wake ta bar ni a tsaye" Junaid yace "Wa?" Ta kallesa tace "Anty sadiya mana" Hajja ta mike rai bace tace "Kambu!! Yaran nan sun raina ni wllh, don uwarta ni din sa'arta ce da xan aika tayi min abu ta share ki tana wake wake?" Kofa ta nufa kamar xata tashi sama, Junaid ya mike ya bi bayanta yace "Tsaya Hajja, me kika sata?" Tana huci ta juyo tace "Ca nayi ta min dafadukan taliya shi ke raina yanxu don Amina shinkafa tayi kamar ko da yaushe, ita bata da girki sai na shinkafa kullum" Junaid ya hade rai yace "Ita mum din tawa, Toh su wa ennan na palon naki me suke yi da baxa su maki ba" Hajja tayi tsaki tace "Xancen banxa, toh ban yi niyyan sa su ba, ko da yanda xaka yi da ni ne" tana kai wa nan ta nufi part din Hajiya da sauri, ya d'an tabe baki ya juya yana kallon Humainah yace "Sannu da hadi, ke baki iya taliyar ba sae kin je dauko magana koh?" Ta turo baki tace "Ae dai ba ni nace tayi ba, aikena aka yi" yace "Xaki yi bayani idan na kama ki ne" dauke kai tayi ya juya yayi wucewar sa, Khadija tayi dariya tace "Bari in je inyi kallo" Ana kiraye kirayen Magrib Junaid ya fito part dinsa sanye da jallabiya milk colour, dai dai nan Humainah da fatima suka fito daga part din Mumy, Humainah tace "Masallaci xaka ya Ahmad" Ya harareta yace "A'a office xan je" bae jira cewar ta ba ya kara gaba. Yana fito wa daga mosque bayan an idar da sllh ya tsaya da wani frnd dinsa da ke nan layin suna gaisawa, har sai da ya ga shigar Abba gida, snn yace "Abdul d'an ara min motar ka pls xan dan fita in dawo yanxu" Abdul yace "Toh mu shiga in baka key" junaid ya bisa suka shiga compound dinsu ya tsaya daga balcony har ya kawo masa makullin sannan ya nufi parking lot ya dau motar ya fita. Atm machine ya fara tsayawa ya cire kudi ya siya fruits nan wajajen sannan ya koma mota ya dau hanyar gidan El-Ameen. A waje yayi parking bayan sun gaisa da mai gadin ya shiga gidan, Mama jummai na kwance Palo kasan tiles ta shimfida xani da 'yar radionta a hannu tana saurare, ta mike xaune ganinsa tace "Sannu da xuwa Ahmad" xaunawa yayi yace "Yauwa mama ina yini?" Tace "Lfya lau, ya gidan?" Yace "Alhmdllh Mama, El-Ameen ya xo kuwa?" Tace "Ehh bae dade da fita ba, kuma yace min xai dawo" yace "Ohk, bacci take ne?" Mama jummai tace "Anya! Ina jin kamar idonta biyu" Junaid ya ajiye mata ledan fruits guda daya yace "Ga kayan marmari mama" godiya ta dinga masa ya mike ya nufi stairs ya haura sama. A hankali ya tura kofar dakin ya tsaya daga bakin kofar yana kallon cikin dakin, rakube ya ganta gefen gado ta sunkuyar da kanta, a hankali ya karaso cikin dakin yana kallonta har ya iso gabanta ya durkusa, sai a sannan ta dago kai tana kallonsa da dara daran fararen idonta, komawa baya yayi da sauri don ba kadan idanuwan nata suka bashi tsoro ba, ta wani kafe sa da ido ko kiftawa bata yi, sauke kansa yayi kasa ya bude ledan gabansa ya mike ya dawo kusa da ita ya duka a hankali ya dauki Apple daya ya mika mata, kallon Apple din take kamar me son gano abu a jiki, ya kai bakinsa ya gutsura a hankali ya fara ci yana kallonta, har sai da ya cinye sannan ya kai mata bakinta, kauda kai tayi da sauri, ya dawo gefenta ya kuma kai mata baki yace "Apple! taste ki ji" rike kanta yayi ya kai mata baki ta d'an bude bakin kadan ta gutsura, yana kallon yanda take kokarin hadiye Apple din ba tare da ta tauna ba yace "Wait, Wait!" Da sauri ya kuma gutsuran Apple din ya shiga taunawa yana kallonta ita ma haka, yanda ta ga yana yi haka ita ma ta shiga yi tana taunar Apple din a hankali, yayi murmushin sa me kyau yace "Good!" Tana hadiye wa ya kai mata baki kuma ta gutsura, karban Apple din tayi a hannunsa ta shiga ci da kanta, ya dawo gabanta ya durkusa yana kallonta, matsowa kusa da ledan ta shiga yi tana kallon ciki, ya dauki ayaba daya ya bare ya gutsura sannan ya kai mata sauran baki ta bude a hankali ya sa mata, taunawa ta shiga yi tana yatsine fuska, murmushi kawai yake yana kallonta, can ta dauki peel din bananan xata kai baki, ya karbe da sauri yace "No!" Tsuke baki tayi tana kallonsa, dariya yayi ya dauki wani Ayaban ya bude ya mika mata gaba daya, ta ajiye Apple din hannunta ta karba, cikin lkci kankani ta cinye ayabar, ya kuma bare mata wani shi ma ta cinye, haka ya dinga yi mata har ta ki karba kuma, ta dauki Apple din da ta ajiye tana kallo, karba yayi ya kai mata baki, ta dafe hannunsa da duk nata biyu ta gutsura a hankali tana taunawa, kallon hannunta kawae yake don duk haskensa ta fi sa nesa ba kusa ba, tana rike da hannunsa haka ta dinga cin Apple din, dai dai nan El-Ameen ya shigo dakin, xaro ido yayi ya rungume hannu yace "Tabdi! Me kke yi haka captain, she will bite the hell out of yhu wllh!" A hankali Junaid ya xame hannunsa daga nata, ta daga ido tana kallonsa, ya kamo hannunta ya danka mata Apple din sannan ya mike yana kallon El-Ameen, El-Ameen ya tabe baki yace "Ina raba ka da shisshige ma mahaukaciyar nan baka ji koh? Randa xata nuna maka halinta na hauka I won't be around fah" Junaid bai tanka sa ba, El-Ameen yayi kwafa ya ajiye ledan drugs din hannunsa da fresh yoghurts ya dawo gabanta yace "Ashe kin iya cin fruits" bata kallesa ba sae cin Apple dinta da take, ya d'an yi murmushi ya nufi inda alluranta suke don hada wanda xae mata, Junaid ya juya ya nufi kofa, mikewa tayi da sauri ganin haka, sae kuma ta bi bayansa, dai dai stairs yaji kamar ana binsa, ya juya ya ganta tana tahowa, kallonta ya tsaya yi, har ta karaso gabansa ta kama hannunsa ta saka masa Apple din, sannan ta daura nata hannun kan nasa ta kai bakinta ta fara cin Apple din, murmushi kawae yake yana kallonta, El-Ameen ya fito daga dakin ya rungume hannunsa yana kallonsu yace "Uhunm! It seems she's getting use to yhu yanxu, kaga kawae sae ka tattaro ina ka ina ka ka dawo nan ka tsaya da ita sai ka cike Ladan ka" yana magana ne yana murmushi, Junaid ya xame hannunsa daga nata ya damka mata Apple din ya juya ya fara sauka stairs din, bin sa tayi da sauri, El-Ameen ya daka mata tsawa, a tsorace ta juya tana kallonsa, ya karaso inda take ya kama hannunta suka koma daki, xaunar da ita yayi gefen gado, ya bude yoghurt din da ya shigo da ya xauna gefenta ya kai mata baki, ta kauda kai da sauri, wani kallo yayi mata yace "I will slap yhu" kamar ta ji me yace bata sake yunkurin dauke kai ba, ya dafa kanta ya kai mata yoghurt din bakinta, a hankali ta dinga sha tana kallonsa, tari ta fara yi ya cire yoghurt din da sauri daga bakinta a hankali yace "Sorry," ya dafa kanta ya kuma kai mata baki, ta dauke kai da sauri tana kokarin karban roban, sake mata yayi ta kallesa sannan ta fara tuttular da shi nan kasan dakin, fixge wa yayi da sauri yace "Ance maki idan aka koshi xubar da abinci ake?" Kallonsa kawae take ko kiftawa bata yi, ya ja dogon hancinta yace "Da wani idanuwanta a wajen" jan hancin ita ma tayi yanda ta ga yayi, yayi murmushi yana kallonta, yoghurt din hannunsa ya rufe ya ajiye sannan ya mike ya nufi inda drugs dinta suke, diluting yayi mata a cup ya dawo gefenta ya xauna, matsawa ta fara yi daga kusa da shi, ya jawo ta ta fasa ihu, d'an buge mata baki yayi tayi tsit tana kallonsa, ya kai mata maganin baki taki budewa, sae da yayi mata tsawa sannan