Showing 84001 words to 87000 words out of 170905 words

Chapter 29 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

646

da motar yayi parking ya juya yana kallon El-ameen, El-ameen yace "Toh gobe dai Dr Sumayya xata yi tafiya ban kuma san inda xan kai patient dinka ba" junaid ya bude motar ya fita shima ya fito suka shiga cikin gidan. Parlor El-ameen ya xauna junaid ya haura sama ya sameta xaune ta kunna kayan kallon parlon, yace "Ki fito ku gaisa da abokina" Ta hade rai tace "Baxan fita ba ni indai wannan El-ameen din nan ne" juyawa yayi ya bar dakin ya koma parlo, El-ameen yace "Xuwa kayi kace ta sauko?" Junaid bai ce komai ba ya xauna, El-ameen yace "In dai nine ta rike gaisuwar ta, kaga ni kasan yanda xa ayi kafin gobe, yanxu clinic xan tafi" Junaid yace "Dama baka yi niyar xuwa yau ba kenan koh?" El-ameen yace "Da wata daban ce matar ba wannan fitsararrar ba" dariya junaid yayi ya mike ya rakasa har waje gun motarsa, Junaid yace "But ka gaya min yanda ya kamata inyi approaching dinta har ta amince" El-ameen yayi murmushi yace "Babu abinda ka iya a rayuwa sai sa uniform da yi ma Mumy biyayya kamar yaya, all the same xan kira ka later dai" daga haka ya shiga motarsa ya tada ya bar layin. Da daddare shinkafa da miyar da Mumy ta aiko masu ya diba ya ci, ya jima xaune parlor yana tunanin yanda xai shawo kan Humainah ta amince da xuwan jasmine gidan ganin har lokacin El-ameen bai kirasa ba, Karfe goma kiran El-Ameen ya shigo wayarsa ya daga, sun dade suna waya har kusan karfe sha daya daga karshe suka yi sallama Junaid ya ajiye wayar, murmushi kawai yake ba wai don yasan dalilin murmushin shi kansa ba, mikewa yyi ya haura sama ya shiga dakin sa, wanka yayi ya fito ya saka pyjamas dinsa ya xauna gefen gado har sha biyu yayi sannan ya mike ya fita daga dakin ya nufi nata, a hankali ya tura kofar ya shiga ya rufe, kwance ya sameta waje daya tana bacci tv a kunne ga remote kusa da ita alamar kallo take bacci ya dauketa, kashe wutan dakin yayi ya karaso ya xauna gefenta yana kallonta doguwar rigar bacci ne jikinta sai net da ta xura gashinta ciki, haka kawai ya ji gabansa na faduwa, a hankali ya kira sunanta, da sauri ta bude ido don ba wani nisa baccin nata yayi ba, ta mike xaune tana kallonsa, pillow ta jawo ta daura jikinta tace "Me ya faru?" Ya d'an bude ido yace "Magana xa muyi" kalle kallen inda hijab dinta yake ta shiga yi, can ta turo baki tace "Ina jin ka" mikewa yayi xai dawo kusa da ita, da sauri tace "A'ah a'ah ka tsaya a nan mana ai ina jinka" sunkuyar da kai yayi yana murmushi ya xauna, murya can kasa yace "Saboda me kika ce baki son warce xata taya ki xama?" Hade rai tayi tace "haka nan" a hankali yace "kinga Idan na fita aiki tun sassafe fa sai yamma nake dawowa, baxa ki iya xama ke kadai a babban gidan nan ba sbda in some cases sai ki ga akwai aljanai a babban gida haka" xaro ido tayi ta matso kusa da shi a hankali tace "Aljanai kuma Ya A.jay?" Yace "Of course tunda sabon gida ne ba a taba rayuwa ciki ba" kamar xata yi kuka tace "Toh ai Abbana yace min xa ka sa ni school soon, kaga sai ka sama min from 7 to 6 kaga kenan tare xamu dinga dawowa gidan" ya d'an hade rai yace "Nan da sati biyu fa xan je Lagos inyi aiki a can to ke kadai xa ki xauna?" Tace "A'ah to ba sai in je gun su Mumy kafin ka dawo ba" dauke kai yayi can ya juyo yace "Toh Idan tare xamu lagos din fa, kenan Idan na tafi aiki ke kadai xaki yi ta xama can din ma" kamar xata yi kuka tace "Toh mai aiki xaka sama min kenan?" Ya girgixa mata kai yace "A'a ba mai aiki bace amma xata dinga taya ki aikin" hade rai tayi tace "Wai wacece ita ya Ahmad?" Kamo hannunta yayi a hankali yace "Idan ta xo xa ki ganta, nd you will like her, bata da matsala" fixge hannunta tayi tana komawa baya tace "Aljanan su cinye ni wllh kuma ni kar ka sake cewa wata xata taya ni xama xan gaya ka da su Mumy da....." jawota yayi jikinsa ba shiri tayi tsit ta fara turasa tace "Meye haka ya A.jay" a hankali ya daura bakinsa kan wuyarta, lokaci daya ranan da ta gansa da Muhibba a daki ya fado mata, ta fasa ihu a tsorace tana kokarin kwace kanta tace "Don Allah ya Ahmad ka yi hakuri ka kyaleni bana so" murya can kasa yace "Meye ba kya so?" Da kyar muryarta na rawa tace "Toh to naji wacece xata taya ni xaman?" Dago kanta yayi yana kallonta, tsoro fal ya ga cikin idonta, yayi murmushi yace "Kin dai amince ta xo sai ki ganta" kai ta shiga gyada masa da sauri, a hankali ya saketa yace "Gobe da safe xa a kawo maki ita" komawa baya take tana gyada masa kai, yayi murmushi ya mike ya kashe kayan kallon dakin, kamar xata yi kuka ta isa gun bedside lamp da sauri ta kunna tace "Wayyo me yasa ka kashe" xagawa yayi daya side din ta bi sa da kallo yayi kwanciyarsa tare da juya mata baya, ajiyar xuciya ta sauke a hankali ita ma ta kwanta, juyowa yayi ta mike xaune da sauri kamar xata yi kuka, yace "Ki kashe wutan nan da kika kunna" girgixa masa kai tayi tace "Plss ya Ahmad bana son duhu" mikewa xaune yayi tana ganin haka ta kashe wutan da sauri tace "Oya yi hakuri kwanta na kashe" dariya ta basa ya koma yayi kwanciyarsa, bayan kusan minti ashirin yaji ta birgino a hankali gefensa ta kwanta. Da asuba ya tasheta yin sllh ya fita daga dakin xuwa nasa, yau ma kamar jiya daga gida aka kawo masu breakfast, tea kawai junaid ya sha yayi kwanciyarsa a parlor yana jiran xuwan El-ameen don ya kirasa yace suna hanya, Karfe goma saura El-ameen ya shigo compound din da motarsa, mikewa junaid yayi ya nufi kofa ya bude, El-ameen ne ya fara fitowa ya xaga ya bude mata side din da take ta fito, sanye take da atamfa da hijab dinta fari har kasa, kallonta junaid yake ko kiftawa bai yi, El-ameen ya rufe motar ya bude baya ya fiddo jakar kayanta yana kallonta yace "Mu je baby" kallon gidan take ba tare da ta yi motsi daga inda take ba, yayi murmushi ya shiga gaba ya fara tafiya, bin bayansa tayi kamar me tausayin kasa, ya juya yaga tana biye da shi ya ci gaba da tafiyarsa, kallonsu junaid yake har suka iso balcony ya lumshe ido ya bude ya basu hanya, El-ameen ya juya yana kallon Jasmine ya ga ta ki karasowa, yace "Come on mana" a hankali ta shiga tahowa Junaid ya bi ta da kallo har suka shiga parlon, juyawa yayi ya bi bayansu, El-ameen ya nuna mata kujera ta xauna bayan ya ajiye kayanta da ke hannunsa shi ma ya xauna yace "Baby ba ki gaishesa ba" ya fadi hakan yana nuna mata Junaid, kallon junaid tayi da fararen idonta a hankali tace "Ina kwana" kasa amsawa yayi ya d'an mata murmushi kawai, sosai haskenta ya kara fitowa da gani kasan ba karamin kulawa take samu gun Dr Sumayya ba, Humainah ce ta sauko parlon jin shigowar mota, kallonsu ta shiga yi da d'ad'd'aya da d'ad'd'aya daga inda take tsaye duk da ba ganin fuskokinsu take ba, El-Ameen ya hade rai, ta karaso cikin parlon idonta ya sauka kan jasmine still tayi gabanta yayi mugun faduwa tana kallonta, Junaid yace "Amm.... Kin ganta she will keep you accompany ana kiranta da Baby...." Wani kallo Humainah ke mata, can tayi dariyar rainin hankali tace "Ko kuma placenta ba!" Lokaci daya ta hade rai tace "Ita mahaukaciyar ce xata yi keep dina company??" Strictly El-ameen yace "Kar ki kuma kiranta da mahaukaciya" hararansa tayi tace "Toh ni dai baxa ta xauna gidan nan ba, kai ka yi auren ka kai ta gidan ka mana" sai kuma ta fashe da kuka ta haura sama da sauri, Junaid ya kalli El-ameen, El-ameen yayi tsaki yace "Wllh da ma bare kawai aka sama maka da wannan yar tashar! An hada ka da balaa'i kawai" junaid ya sauke ajiyar xuciya ya mike jiki ba kwari ya bi bayanta, a hankali Jasmine ta mike ta dawo kusa da El-ameen ta durkusa kusa da shi cikin sanyin murya tace "Uncle ni ka kai ni gida gun Mami" sunan da suke kiran Dr Sumayya da shi kenan, shiru El-ameen yayi yana kallonta, ta d'an taba hannunsa tace "Uncle!" Kifta ido yayi da sauri ya shafa kansa a hankali yace "Toh xan kai ki" xaunawa tayi nan kasa kusa da shi tana kallonsa murya can kasa tace "Uncle Meye meaning din mahaukaciya?" Shiru yayi nan ma yana kallonta, ta bude manyan idonta tace "Idan mun je gida in tambayi farida?" Murmushi ya mata hade da gyada mata kai.

✍🏻
*Haske Writers association*💡
[1/14, 9:15 AM] Elhajj: *Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
46.....
Kwance junaid ya sameta tana kuka a dakin, ya karasa ya xauna kusa da ita ya dago ta, turasa ta shiga yi cikin kuka take cewa "Ni ka kyaleni, ka kyaleni" a hankali yace "Listen to me plss Humainah, ba fa mahaukaciya bace" ta fashe da matsanancin kuka tace "Nace ka kyaleni ni dai" saketa yayi yana kallonta, ta koma ta kwanta tana ci gaba da kukanta, mikewa yayi ya fita daga dakin ya koma parlor, El-ameen dai kallonsa kawai yake bai ce komai ba, Junaid ya xauna ya shafa kansa yace "Shknn you can go Idan tafiya xaka yi" El-ameen yace "Toh gimbiyar taka ta yarda kar in tafi in bar yar mutane ta kasheta kana kallo" Junaid yace "In xaka tafi kayi tafiyar ka kawai" mikewa El-ameen yayi yana kallon Jasmine yace "Baby xaki tsaya nan har in dawo kin ji" kallonsa kawai take, ya durkusa kusa da ita yace "Kin ji?" Idonta ne ya cika da hawaye, a hankali El-ameen yace "Kuka kuma baby" shi dai junaid kallonsu kawai yake, El-ameen ya ciro handki ya mika mata yace "baxan dade ba xan dawo kin ji" karba tayi ya mike ya kalli Junaid sannan ya fita daga parlon. Kallonta kawai Junaid ke yi kanta a kasa tana fidgeting fingers dinta, can ya mike ya kullo kofar sannan ya dawo ya dau jakar kayanta yace "Tashi mu je" mikewa tayi a hankali tana kallonsa ya d'an mata murmushi yace "Follow me" daga haka ya nufi stairs ta bi bayansa, dakin dake kusa da na Humainah ya bude ya shiga ta tsaya daga bakin kofa tana kallon dakin, juyawa yayi yana kallonta yace "Shigo mana" a hankali ta shiga dakin ya rufe kofar, kan gado ya ajiye jakarta ya bude closet yace "Ki ajiye kayan ki duka a nan kin ji?" Sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, ya nuna mata kofar bayi yace "ga toilet nan" kallon kofar tayi ta gyada masa kai, yace "Are you hungry?" Girgixa masa kai tayi da ganinta kasan a tsorace take, yayi murmushi ya kunna mata tvn dakin yace "Ki xauna kiyi kallon ki toh" ta gyada masa kai ya juya ya fita daga dakin ya rufo mata kofar, da sauri ta mike ta nufi kofar ta bude, yana tsaye bakin kofar Humainah ya juyo yana kallonta, dawowa yyi yace "Ya aka yi?" Kamar xata yi kuka tace "ina jin tsoro" shiru yayi yana kallonta ta bude kofar sosai ta koma ta xauna a dakin, Dakin Humainah ya karasa ya bude ya shiga ya sameta har lokacin tana kuka ya rungume hannayensa yana kallonta, can ya karasa kusa da gadon ya xauna yace "Ke yanxu baxa a iya cin arxiki gun ki ba, baxa ki yi taimako ba, kwana biyu fa kawai xata yi ta bar gidan" ko kallonsa bata yi ba ya dagota ya rungumeta yace "plss mana, wllh xata bar maki gidan soon, she's not staying long" turasa tayi tace "Bana so, kuma ni ka rabu da ni" hade rai yayi ya saketa ya mike yace "Toh wai gidan ki ne nan din? Ko a kanki take xaune" dago kai tayi tana kallonsa, ya watsa mata wani kallo ya juya ya fice daga dakin, wani sabon kukan ta fashe da har da shessheka. Dakin sa ya koma ya kwanta yana tunanin anya decision din da yayi na kawo jasmine gidan yayi daidai kuwa, har aka kira Azahar yana kwance, mikewa yayi daga karshe ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito, nan dakin yayi sllh yana xaune kan darduma bayan ya idar aka danna bell din gidan, mikewa yayi ya fita har lokacin dakin da jasmine take a bude yake, parlor ya sauka ya bude kofa, fatima da khadija ne bakin kofar rike da flask din abinci, gaishesa suka yi ya karba yace "Mun gode, ku gaida mutan gidan," daga haka ya kulle kofar ya dawo cikin parlor, plate ya dauko a kitchen ya dibi couscous din dake cikin flask din ya bude na miya ya diba sannan ya rufe ya dau goran ruwa da cup da spoon ya haura sama, dakin da jasmine ke ciki ya shiga, kwance ya ganta a kasa ta takure waje daya tana bacci, ya shigo dakin ya ajiye abincin hannunsa yace "Jasmine" sau uku yana kiranta ganin bata tashi ba ya durkusa gabanta ya d'an taba ta, bude ido tayi ta mike xaune da sauri ganinsa, yayi mata murmushi ta sunkuyar da kai, yace "Me yasa baki kwanta kan gadon ba" shiru tayi bata ce komai ba, ya dauko darduma ya shimfida a kasa yace "Dawo nan" mikewa tayi ta xauna kan darduman ya ajiye mata abincin da ruwa a kai yace "ga abinci ki ci" kai ta gyada masa, yace "Toh ci mana" a hankali ta dau spoon din da dibi abincin ta kai baki tana kallonsa, murmushi ya mata yana kallon yanda take tauna abincin, yace "You like it?" Kai ta gyada masa, ya mike yace "Toh maxa ki cinye kafin in dawo" daga haka ya fita daga dakin ta bi sa da kallo. Ko da ya dawo xaune ya sameta ta tura abincin gabanta tayi jigum, ya karaso ya durkusa gabanta yace "Baki ci ba kuma" ta girgixa masa kai a hankali tace "Na ci" yace "No! kadan kika ci" spoon din ya dauka ya dibi abincin ya kai mata baki, a hankali ta bude bakin ya xuba mata, haka ya dinga bata har abincin yayi rabi ta kauda kai tace "Na koshi" ajiye spoon din yayi yana kallonta yace "Toh tashi ki je kiyi alwala ki xo kiyi sllh" mikewa tayi ta nufi toilet yace "Baki cire hijab din ki ba" dawowa tayi ta cire Hijab din ta ajiye, ya bi ta da kallo har ta shiga toilet din sai dai bata rufe kofar ba, mikewa yyi ya fita ya koma dakin sa. Lokaci lokaci ya kan lekota, tausayinta kawai yake ba kadan ba barin yanda ya lura duk a tsorace take, ana kiran sllh magrib ya shigo dakin bai ganta ba, kiranta ya shiga yi amma shiru ya juya ya fita ya sauko downstairs, kitchen ya sameta tana wanke d'an plates din da aka bata, ya tsaya bakin kofa yana kallonta, da sauri ta juyo a tsorace, wara ido yayi yace "Uhum!" A hankali tace "washing nake yi" murmushi yayi mata yana gyada mata kai, ta juya ta ci gaba da wanke plates din, yace "Me xa ki ci for Supper?" Ta juyo tace "Supper?" Ya gyada mata kai yace "Yea dinner" ta d'an langwabar da kai a hankali tace "na koshi" wara ido yayi yace "me kika ci?" juyawa tayi ta ci gaba da wanke wankenta. Har ta gama yana tsaye bakin kofar, ta juyo tana kallonsa, murmushi yayi mata ya fita daga kitchen din ta bi bayansa suka haura sama, yace "Tafi kiyi sllh" kai ta gyada masa ta shiga dakin da take, shi ma ya shiga nasa. Ana idar da sllh ya tafi siyo masu abinci, ajiye abincin yayi a parlor bayan ya dawo ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujera, can ya mike ya shiga kitchen ya dauko plate ya dau take away daya ya juye ya sa spoon ya dau ruwa ya tafi sama, xaune ya sameta bakin kofar dakin tana ganinsa ta mike tsaye, yace "uhum!" a hankali tace "Tsoro nake ji" kallonta ya tsaya yi kafin ya shigo dakin ya ajiye mata abincin hannunsa yace "Toh xo ki ci abinci" ta karaso ta xauna inda ya ajiye mata abincin, bin sa da kallo tayi har ya fita sai dai bai rufe mata kofar ba. Har xai shiga dakinsa ya tsaya ya kalli dakin Humainah, karasawa yayi ya bude kofar, xaune ya ganta can karshen gado kanta hade da gwiwa, a hankali ya karasa kusa da ita ya xauna yace "Still crying?" Mikewa tayi xata bar wajen ya fixgota ya ce "Ina xa ki?" Ta fashe da kuka sosai, rungumeta yayi a hankali yace "Alryt am sorry, kiyi hakuri... She's going tomorrow tun da baki so" boye fuskarta tayi jikinsa tana kuka a hankali, yace "Toh ba nace kiyi hakuri gobe xata tafi ba" muryarta na rawa tace "Toh wacece ita" dago kanta yayi yana kallonta, can yace "Ohk I will tell who she is" janyeta yayi a jikinsa ya koma baya yana kallonta yace "Amma fa it's a long story" sunkuyar da kanta tayi, nan ya fara bata labarin ynda ya hadu da jasmine har xuwa wannan lokacin, kallonsa kawai take ko kiftawa bbu bata kuma ce komai ba, ya lumshe ido ya bude yace "Tana regaining memorynta Idan Allah ya yarda xa ta koma gun iyayenta, ita din abun tausayi ce, a yanxu bata da kowa sai mu da muka taimaketa" dauke kai Humainah tayi, ya matso kusa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login