Showing 72001 words to 75000 words out of 170905 words

Chapter 25 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

671

dafe kanta xata durkusa, yayi saurin rikota ya dagata ya nufi sama da ita, addu'a ya dinga yi a xuciyarsa na cewar Allah yasa ba abinda yake tunani bane, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, gadon da take ya mayar da ita ta kwanta ta rufe ido, ya ja kujera ya xauna kusa da gadon yana kallonta, ta kusa minti biyar bata bude idon ba, can ta bude a hankali tana sauke ido kansa ta mike xaune da sauri tace "Ummina" gefen gadon ya xauna yace "Toh gaya min inda take in kai ki" ACn dake ward din ta tsura ma ido da ganinta kasan tunani take, wani karan ta kuma yi ta runtse ido ta dafe kanta, lumshe ido yayi shi ma ya dafe kai tausayinta na shigarta, a hankali ya dago yana kallonta cikin sanyayyan murya yace "Ki kwanta ki huta kin ji, anjima xa ki tuna inda Ummin ki take in kai ki" bude ido tayi tana kallonsa ya sakar mata murmushi ya gyada mata kai, komawa tayi ta kwanta, yace "Xa ki ci abinci" ta kallesa tace "Abinci?" Kamar me koyon word din tayi maganan, jiki a sanyaye ya mike ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, yana rufo kofar ta mike xaune tana kallon gadon da Junaid yake, saukowa tayi a hankali ta isa gun gadon ta duka tana lekan fuskarsa, ta kusa minti biyar tana kallonsa can ta kamo hannunsa a hankali murya can kasa tace "Daddy!" Mikewa tayi da sauri kamar warce ta tuno abu, runtse ido tayi ta dafe kanta hade da yin ihu, sosai kanta ke juya mata wanda hakan yasa ta fadi kan gadon, ta dau lokaci bata dago ba, can ta bude ido a hankali ta ganta kansa, xaro ido tayi ta mike da sauri tana kallon shoulder dinsa dake jini duk da bandage din dake nan alamar ta fama masa, kuka ta fashe da ta duka a hankali tana kallon shoulder din, bandage din dake kanta ta taba ta sa hannu biyu ta fixge da karfi har sai da ya fita ta matso kusa da shi ta duka ta daura bandage din kan kafadar nasa, bude kofa aka yi El-ameen ya shigo rike da plate da cup din tea, tsaye yayi bakin kofar yana kallonta ta juyo ita ma tana kallonsa ta nuna masa kafadar Junaid tace "Ciwo!" Tana fadin haka ta d'an bude ido tana kallon abinda ta kira da ciwo kamar me son gano abu, karasowa El-ameen yayi sanin she's trying hard ne ta tuna abu yace "yes ciwo ne, taho in sa maki wani bandage din you are bleeding" gadonta ya nufa, ta bi bayansa jiki a sanyaye, ya nuna mata inda xata xauna ta hau gadon ta xauna, ya ajiye plate din hannunsa ya dauko wani bandage din da plaster ya gabanta, runtse ido tayi tun kan ya taba kan, yana kallon fuskarta har ya gama sa mata bandage din, murya can kasa yace "Bude idon" a hankali ta bude tana kallonsa, ya mata murmushi ta sunkuyar da kanta, abincin ya bude ya dau spoon ya mika mata, ta karba tana kallon cokalin, yace "Eat" ganin yanda take kallon cokalin yasa ya karba ya debi abincin ya kai mata baki, ta bude bakin a hankali ya xuba mata, kallon yanda take tauna abincin yake, aka bude kofar ward din Abbansa ya shigo da wata nurse, ajiye spoon din yayi da sauri, Abba ya karaso yana kallonta yace "Maa sha Allah, Alhmdllh ashe ta farka baka sanar min ba, to ina 'yan uwan nata ita" rasa abun cewa El-ameen yayi, Abba dai sai kallonta yake ganin she looks familiar, lokaci daya ya tuna inda ya taba ganinta ya kalli El-ameen da sauri yace "Wannan ba mahaukaciyar nan bace da ka kawo min nan ranan, me ya hada ta da Ahmad?" El-ameen da xuciyarsa ke bugawa ya mike don ya ma rasa abun cewa, tsawa Abba yayi masa yace "Are you daft?" Da kyar yace "Abba ta samu lafiya ma, dama iyayenta, Abba gida...." Strictly Abba yace "Kana son ganin the odza side of me ko Ahmad?" Sunkuyar da kai yayi, Abba yace "Maxa fitar min da ita daga nan ka maida ta gun iyayenta, mutumin banxa kawai" juyawa Abba yayi ya bar wajen ya isa kusa da Junaid yyi gwaje gwajensa, ya jima yana kallonsa kafin ya kalli nurse din yace "We might need to diagnose his brain, ya dau lokaci bai farfado ba" daga haka ya juya ya fita nurse din ta bi bayansa, tun da El-ameen ya ji abinda Abba yace gabansa ya fadi ba kadan ba, ya karasa gadon da sauri yana kallon Junaid, kansa ya dafa na kusan minti uku sannan ya cire hannunsa a hankali cikin sanyin murya yace "Come back pls frnd, for the sake of ur patient...." Juyawa yayi yana kallonta ya ga hawaye idonta ya karasa da sauri yace "Me ya faru?" Ta fashe da kuka, shiru yayi yana kallonta don ya lura ba ko wani magana ma take ganewa ba, kamo hannunta yayi a hankali yace "Kiyi hakuri kin ji, xan kai ki gidan ku" ita dai kallonsa kawai take, tunanin inda xai kai ta yake, sanin in har Abba ya dawo ya kuma ganinta ransa xai baci, gashi bai son barin Junaid, murda kofar dakin aka yi, ya juya da sauri Mumy ta shigo tare da Humainah da fatima, jikinsa yayi sanyi ya sunkuyar da kai. Humainah ce tayi karfin halin karasawa kusa da gadon da Junaid yake ta durkusa ta fashe da kuka, fatima ta juya ta fice daga ward din, Mumy bata iya ta karaso cikin dakin ba, Humainah ta kamo hannunsa cikin rawar murya tace "plss ka tashi ya A.jay..." El-ameen ya karasa kusa da ita yace "He will be fine ki daina kuka kin ji" juyawa Mumy tayi ita ma ta fita daga dakin, Humainah ta kallesa hawaye na bin kuncinta tace "Toh me yasa har yanxu bai tashi ba" dagota yayi yace "Xai tashi nan da few minutes in'sha Allah" kallon jasmine dake ta kallonta tayi kawai ta juya ta fice daga ward din tana kuka sosai, juyawa yayi yana kallon Jasmine ya karasa kusa da ita, hawaye ne ya gangaro idonta a hankali tace "Yayanta ne?" Kallon mamaki yake mata don in tayi wani maganar kamar ba ita ba, gyada mata kai yayi yace "Ehh!" Daga haka ya xauna ya ci gaba da bata abincin, kadan ta ci ta dauke kai xai yi magana aka bude kofa mikewa yayi da sauri, gabansa ya fadi ganin Abba ne ya dawo, yace "Abba ynxu xan fita da ita wllh" wani kallo Abba yayi masa sannan ya nufi gadon da Junaid yake, wani ruwan ya sa masa ya juya yana kallon El-ameen yace "tana gama karban sauran treatment dinta gobe ka fitar min da ita a asibiti, don't let me repeat my self tomorrow" kai ya gyada da sauri yace "Yess sir" juyawa Abba yayi ya fice, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya ya xauna yayi tagumi, da dukkan alamu tayi loosing memory ko ba duka ba, kuma xai dauki months kafin ta dawo dai dai shima sai tana shan drugs ana kuma yi mata abubuwan da ya dace, in kuma Allah yasa tayi toxali da wani nata kila ya dawo gaba daya, a hankali ya daga kai yana kallonta ya ga ta jingina jikin gado idonta lumshe, mikewa yayi da sauri ya kwantar da ita ta bude ido ya sakar mata murmushi yace "Sleep jewel!" A hankali tace "Sleep" ya gyada mata kai daga haka ta lumshe idonta. Har sha biyun dare yana dakin, hankalinsa ya tashi sosai ganin Junaid bai farfado ba har lokacin, wata nurse ce ta xo tace Abba na kiransa ya mike ya fita jiki ba kwari, yana fita jasmine ta farka ta mike xaune da sauri tana kalle kalle a hankali tace "Ummina" ta kusa minti goma xauna ta ga Junaid na motsi, ido ta kafa masa, can ta sauko a hankali ta iso kusa da gadon ta duka tana kallonsa, a hankali ya bude idonsa ya shiga kalle kallen dakin idonsa ya sauka kanta, ta d'an koma baya tace "Sleep" kallonta kawai yake, ta d'an yi murmushi ta buda masa manyan idonta ta kuma cewa "Sleep"

*Haske writers association*💡
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

36.....

A hankali ta koma baya jin bai ce komai ba har lokacin idonsa na kanta, ta d'an bata fuska ta juya masa baya dai dai shigowar El-ameen ward din, da sauri ya karaso gun gadon yana kallonsa ganin idonsa bude, murmushi ne yayi escaping lips dinsa yace "Ohh Captain! You are back" Lokaci daya murmushin ya bace ganin yanda Junaid ke kallonsa, dukawa yayi a hankali yace "Ahmad!" Nan ma dai kallonsa kawai Junaid ke yi, El-ameen ya girgixa kai da sauri yace "No plss say something frnd, kana ji na..." D'aga sa yayi xaune yace "Ahmad talk to me" dafe kai El-ameen yyi a xuciyarsa ya dinga furta innalillahi.... Jasmine ta matso kusa da shi a hankali tana kallonsa, Dagowa yayi da kyar ya kuma kallon Junaid yace "Captain!" Dukawa tayi kamar yanda yayi ita ma cikin sanyayyan muryarta tace "Captain!" El-ameen ya juya yana kallonta, ta buda masa ido tace "Captain" juyawa yayi ya maida dubansa ga Junaid yaga kallonta yake, mikewa El-ameen yayi jiki a sanyaye ya nufi kofa, jasmine ta bi sa da kallo har ya fita sannan ta juya tana kallon Junaid tace "Captain" kallonta kawai yake, ta matso kusa da shi tana kallon shoulder dinsa a hankali tace "Ciwo!" Sai kuma tayi murmushi tace "Yana ma zafi?" Kallonta Kawai har lokacin ko kiftawa bai yi, shiru tayi kamar me naxarin abinda ta fada can ta rike kanta ta sulale nan wajen tayi k'ara tana cewa Umminta dai dai shigowar El-ameen da Abbansa sai wani Dr faruqh, Junaid ya lumshe ido ya bude, El-ameen ya karasa da sauri ya dagota yana kallonta, Abba ya girgixa kai tare da yin kwafa yace "When I say tomorrow I mean tomorrow" a sanyaye El-ameen ya maida ta kan gadon da take ya kwantar da ita har lokacin ta ki bude ido, Abba dake ta kallon Junaid ya duka gabansa a hankali yace "Ahmad?" Junaid ya dago ya kallesa sannan ya maida kansa kasa yace "Na'am" Abba ya juya ya kalli El-ameen da ya xaro ido yana kallon Junaid, da sauri ya karaso har lokacin idonsa a kansa, Abba yyi murmushi yace "Alhmdllh! Ina ke maka ciwo yanzu?" Junaid yayi shiru, a hankali Abba ya kuma cewa "Ahmad" ya dago ya kallesa yace "Ba ko ina Abba" Abba yace "Are you sure?" Ya gyada masa kai, Abba yace "Maa sha Allah, Allah ya tsare gaba bari a kawo maka tea yanzu sai ka sha drugs" daga haka Abba ya juya ya fita, Dr faruqh yayi murmushi yace "Allah ya kara kiyayewa Captain Junaid" Junaid yace "Ameen" daga haka Faruqh ya juya ya fita, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "gaskiya kana da matsala junaid, ni meye nawa xa ka share ni" Junaid bai tanka sa ba ya sauka daga kan gadon ya nufi toilet, El-ameen ya bi sa da kallon mamaki, girgixa kai yayi ya juya yana kallon jasmine ya ga har ta fara bacci, ya karasa kusa da ita ya duka murya can kasa yace "Jewel" bude ido tayi tana kallonsa, ya mata murmushi yace "Sleep" cikin sanyin murya tace "Captain!" Yayi shiru yana kallonta kafin ya girgixa mata kai a hankali yace "Doctor!" Rufe idonta tayi bata sake budewa ba ya mike ya gyara mata kwanciya ya rufa mata bargon da ke kan gadon, junaid ya fito ya nufi gadon da yake, El-ameen ya bi sa da kallo yace "patient din ka ta samu lafiya" Ba tare da junaid ya kallesa ba yace "Naga alama" El-Ameen yayi murmushi yace "Hakan kuma ya faru ne ta dalilin accident din da ku ka yi, nd this clearly shows dat hatsari ne cause din haukanta, sai dai kuma ga dukkan alamu tayi loosing memory...." Wata nurse ce ta shigo da cup din tea ta karasa kusa da Junaid ta mika masa ya karba ya fara sha, ta ajiye magungunan hannunta ta gwada masa yanda xai sha ta bude fridge ta fiddo masa ruwa ta ajiye sannan ta fita, El-ameen yace "Ina magana xaka wani min shiru?" Junaid ya kallesa yace "Ai na ji ka, and am glad ta samu lafiya dama abinda nake so kenan, yanzu abinda ya rage shine in sama mata inda xata fara rayuwa har memoryn ta ya dawo....." El-ameen yace "inda xa ka sama mata kamar ina?" Junaid ya kallesa sannan yace "Inda xata xauna ta ci gaba da rayuwa nace" El-ameen yace "Toh ai ban gane irin gun da kake fadi bane" Junaid yace "Ko mama jumman nan sai in sa a nemo min in damka mata ita ta rike har tayi recalling abubuwa ta nemi iyayenta" El-ameen yace "Haba, she still need medication har ynxu fa....." Junaid ya kallesa yace "Nayi iya taimakon da xan mata a yanzu, idan mama jumman ma ta dauketa dole xan basu kudi that will be enough for der needs....." El-ameen yace "No plss ba sai an kai ta kauye ba, ka bari ka cike ladan ka kawai" Junaid yayi masa wani irin kallo yace "Bana ketare maganar mahaifiyata, tace in maida ta inda na samo ta and dat's wat am going to do..." Shiru El-ameen yayi na wani lokaci kafin yace "Amma baka mata adalci ba" Junaid yace "Look ka bar ni in ji da abinda ke damuna yanzu El-ameen, ban san da idon da xan kalli mahaifiyata ba, ban san ta wani sigar Abbana xai dauki batun nan ba, I've tried my best na mata iyakar abinda ya kamata tunda gashi ta dawo hankalinta...." El-ameen bai kuma cewa komai ba ya lumshe ido ya bude sannan ya fita daga ward din. Junaid ya jinginar da kansa jikin bango daga xaunen da yake ya lumshe ido, har kusan Karfe biyu El-ameen bai dawo dakin ba, ya juya yana kallon gadon da take kwance, saukowa yayi daga kan gadon da yake ya karasa nata gadon yana kallonta, lumshe ido yayi cikin sanyin murya yace "Na so taimakon da xan maki ya fi haka Jasmine, I can't help, baxan iya tsallake umarnin Mumyna ba, am very glad kin dawo mai hankali, nasan you will cope da new environment din da xa ki samu kanki har tunanin ki ya dawo" ya kusa minti goma kusa da ita kafin ya mike a sanyaye ya koma gadonsa. Ciwon kai bai bar sa ya runtsa ba har Karfe hudu, yana nan kwance aka bude kofar El-ameen ya shigo, lumshe ido yayi kamar me bacci, El-ameen ya karasa kusa da shi yana kallonsa, ya daura hannunsa kan forhead dinsa ya ji da dumi sosai, kallon magungunan da ke gefensa yayi da mamaki ganin bai sha ba, ya jima tsaye kansa kafin ya juya ya koma gun jasmine, kwata kwata daren kasa bacci yayi sbda tausayinta, da ya tuna abinda Abbansa yace kan gobe bai son ganinta asibitin sai jikinsa yayi sanyi, in kuma ya tuno furucin junaid ma sai yaji tausayinta sosai, dukawa yayi yana kallon fuskarta, yaga ta bude ido da sauri, komawa baya yayi ta mike xaune tana mitstsika ido tace saw "Captain!"

*Haske Writers Association*💡

Yau ma dai ba yawa, sorry.







[1/14, 9:12 AM] Elhajj: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

37/38

Murmushi El-ameen ya mata yace "Good morning" ita ma a hankali tace "Good morning!" Ya gyada mata kai yana murmushi har lokacin, duk abun nan da suke Junaid na kallonsu, yana ganin El-ameen xai juyo yayi saurin lumshe ido, El-ameen ya nufi kofa ta bi sa da kallo kafin ya fita tayi saurin cewa "Captain!" Juyawa yayi ya kalleta ya girgixa mata kai yana murmushi yace "No, Am doctor!" A hankali tace "Doctor?" Ya d'an bude ido yace "Yess" juyawa yayi ya fice. Saukowa tayi daga gadon ta nufi gadon Junaid ta duka tana kallon long eyelashes dinsa don har lokacin idonsa a lumshe yake, a hankali tace "Captain!" Ya bude ido da sauri yana kallonta, tayi murmushi tace "Good morning!" Mikewa xaune yayi ya mayar mata murmushin yace "Morning jasmine, how you?" A hankali tace "Am fine, and you?" Shiru tayi da sauri kamar me naxarin abinda tace, can ta runtse ido ta dafe kanta ta durkusa wajen, ya sauko da sauri yana kallonta, ta kusa minti biyar a haka shi dai bai dagota ba bai kuma san ma me xai ce mata ba, mikewa tayi a hankali tana rike da kan ta juya ta bar wajen ya bi ta da ido, xama tayi kan kujeran da ke kusa da gadonta ta kifa kanta ta inda ba ciwo, komawa yayi ya xauna har lokacin yana kallonta. El-ameen ne ya shigo dakin bayan an idar da sllhn Asuba, ya samu Junaid xaune kan darduma, ya ajiye ledan hannunsa ya ja kujera ya xauna yana kallonsa yace "Good morning captain, ya jikin?" Junaid yace "Alhmdllh" kallon magungunansa El-ameen yayi yace "Jiya baka sha drugs din ka ba ashe?" Junaid bai ce komai ba El-ameen ya tabe baki ya mike yana kallon jasmine dake xaune har lokacin kan kujera kanta kife kan gado, karasawa yayi yana kallonta ya ga bacci ma take a haka, ya dan duka yace "Hello!" Bude ido tayi da sauri tace "Hi" murmushi yayi yace "Good, tashi kiyi sllh" dago kai tayi da sauri tana kallonsa tace "Sallah?" Ya gyada mata kai, tayi shiru tana kallonsa kamar bata taba jin Kalmar ba, shi dai Junaid kallonsu kawai yake, El-ameen yace "Am coming" daga haka ya juya ya fita, ba a dau lokaci ba ya dawo tare da wata nurse rike da hijab, ya kalli nurse din yace "Ki rakata bayi, ki gwada mata yanda xata yi alwala" nurse din ta kalli jasmine sannan ta kallesa tace "Ban gane ba sir" Yace "Yes alwala xaki yi tana gani tana bin ki" nurse din ta kuma kallon jasmine dake kallonta ita ma ta ajiye hijab din hannunta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login