Showing 102001 words to 105000 words out of 170905 words
Chapter 35 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
xauna parlon, yau ma kamar jiya ruwa ta kawo mata, yarinyar sai hira take mata kamar sun dde da sanin juna, ita dai Humainah duk ta kasa sakewa, Jasmine ta shigo parlon tana kallon Humainah tace "Anty ki kira min Uncle" Humainah tace "Bani da waya" Jasmine tayi shiru bata ce komai ba, sai kuma ta juya ta koma sama, yarinyar da ta kira kanta da hadiza tace "Amma wacece yarinyar nan?" Humainah tace "Kanwar mijina ce" Hadiza tace "ohh, Allah sarki, amma basa kama ko dai 'yar uwar na family kike nufi" a takaice Humainah tace "Eh!" Don duk ta kagu ta wuce sai kallon agogo take sanin hudu da wani abu junaid ke dawowa wani time, Hadixa tace "Toh dai ki kula" Kallonta Humainah tayi da sauri, hadiza tace "Naga yanda take wani shige masa jiya da na xo" murmushi Humainah ta kirkira bata ce komai ba, hadiza tace "Ae ba abun dariya bane, ni ma nan da kike ganina na kusa dawowa anguwar gaba daya gun aunt din nan tawa sbda damuwa da yayi mata yawa, in gaya maki wata yarinya mijinta ya ajiye wai yar uwarsa xata yi karatu a gidan, in kinga yarinyar very quiet har ni ke ce ma Anty fa'ixa ta dinga sake mata don Allah don ko kallonta bata yi, to yanxu xancen da nake maki Friday mai xuwa daurin auren mijin yayar tawa da yarinyar" kallonta kawai Humainah ke yi gabanta na mugun faduwa, hadiza ta dawo kusa da ita tace "Bari ki ga hotunan aunt din tawa da yarinyar har ma da mijin" kallon hoton kawai Humainah ke yi amma sam hankalinta baya jikinta, bude gate din gidan aka yi, hadiza ta bude ido tace "In ji dai ba mijin naki bane ya dawo" kasa ce mata komai Humainah tayi, Hadiza tace "A'a kin ga ki fa kwantar da hankalin ki, ai ba duka maxan suka taru suka xama daya ba kawai ke dai ki sa ido" Humainah bata ce komai ba still har junaid ya shigo parlon, daga bakin kofa ya cire takalman kafarsa ya bar bakar safar, kallonsu kawai yake a parlon lokaci daya ya hade rai, ya nufi stairs hadiza ta bisa da kallo ta d'an bude murya tace "Ina yini" a tunanin ta jiyan da ya shareta bai ji bane, ko kallonta bai yi ba bai kuma amsa ba ya haura sama, hadiza tace "Toh bari in wuce naga kamar mijin ki bai son baki" Humainah tace "Rabu da shi" dariya Hadiza tayi ta mike tace "Toh Hajiya Humainah kinga tafiyata, gobe ko jibi xan ma dawo anguwar baki daya" Toh kawai Humainah ta iya ce mata ta rakata har bakin kofa ta wuce sannan ta dawo ta tafi sama, tana shiga daki ta xauna gefen gadonta tana tunanin maganganun Hadiza, bude kofar dakin aka yi ya shigo fuskar nan tasa a daure ko uniform bai cire ba don fitina yace "Wace yar iskar ke xuwa gidan nan?" Ko kallonsa bata yi ba ta dauke kai, ya karasa ya fixgota yace "keh! Baxa ki gaya min wacece ita ba?" Fixge hannunta tayi tace "Mutum ce kuma ai ka gane ma idonka" yace "Koh? To wllh wllh ta sake xuwa min gida xan baki mamaki daga ke har ita" daga haka ya juya ya fice, kuka ta saki duk ta rasa me ke mata dadi sosai xancen hadiza ya xauna a xuciyarta, mikewa tayi ta sauka kasa ta kashe girkin da take ta koma daki. Har bayan magrib junaid na xaune daki duk abinda ya ma El-ameen jiya ya tsaya masa ya rasa yanda xai yi, ta yaya ma xai ce yana son Jasmine, wani irin so ma yake nufi, mikewa yayi daga karshe ya dau makullin motarsa ya fita, ana kiran isha ya isa gidansu El-ameen, sai da yayi sllh a masallaci sannan ya shiga gidan, xaune ya samesa a daki da faisal, faisal na ganin junaid ya bude ido yace "Captain junaid, ashe ana ganin ka" murmushi junaid yayi ya xauna yace "Kai ma ai ba ganin naka ake ba" hira suka d'an yi da faisal, shi dai El-ameen wayarsa kawai yake dannawa, daga bisanni faisal yayi masu sallama yace xai tafi clinic ya fita, Junaid ya kalli El-ameen da ya ki kallon inda yake yace "Har da wani pretending baka gan ni ba?" Ba tare da El-ameen ya kallesa ba yace "Ai mun gaisa" Junaid ya d'an shafa kai yace "Look, am sorry about what happened yesterday, I don't know what came over me....." Katse sa El-ameen yayi yace "It's ohk, I also don't know what came over me, i was just confused, I couldn't help it... May be dat was y I uttered those words" shiru junaid yayi yana kallonsa ganin he was so serious, El-ameen yace "Yess!" Junaid yace "No idan ma sonta kake da gaske ai ba komai bane, just pray memorynta ya dawo a maidata gun iyayenta nd then you can go on...." Shiru junaid yayi don jin maganar yayi wani iri a bakinsa, El-ameen yace "Noo, ni an min mata ai" Junaid bai kuma cewa komai ba sai bayan kusan minti uku yace "Ohk gobe da yamma ka raka ni ayi enrolling dinta a islamiyya, she so need it yanxu, ita kuma Humainah is resuming school" El-ameen yace "Ohk" junaid na kallonsa yace "akwai shirye shiryen da xa ayi ne na bikin?" No kawai El-ameen yace masa. Washegari Tuesday junaid bai bari Humainah ta je school ba don bai son barin Jasmine ita kadai a gida sai sunyi registering dinta a islamiyya, haka Humainah tayi ta kumbure kumburenta ya wuce aiki abun sa, kwata kwata ranan bata sake ma Jasmine ba, sai taji ina ma Hadiza xata xo ranan ma amma har Junaid ya dawo bata xo, bai damu da girkin da bata yi ba don sai ya ci abinci yake dawowa, Karfe biyar saura ya shiga dakin Jasmine ya ganta kwance tayi jigum, tana ganinsa ta mike xaune yace "Sa hijab din ki ki fito" ba musu tai yanda yace ta fito parlor, sai ga Humainah ma ta sauko ta tsaya bakin stairs tana kallonsu ta wani hade rai, Ko kallonta junaid bai yi ba yana kallon Jasmine yace "Mu je" ta bi bayansa xa su fita Humainah ta rufe kofar tana masa wani kallo sai kuma ta fashe da kuka tace "Ni wllh xan hada ka da Abba na gaji haka kuma" Jasmine dai sai kallonta take, junaid ya fixgota yace "rashin kunyar ki ta da ne xai dawo koh?" Bai jira cewarta ba ya turata one side ya kama hannun Jasmine suka fita ta fashe da kuka sosai ta haura sama da sauri, Junaid ya kira El-ameen ya fi sau biyu kafin ya daga, bai damu da hakan ba ya gaya masa islamiyyan da xai taho ya samesu, ya fi minti talatin yana jiransa kafin ya xo, a tare suka shiga babban makarantar suka yi duk abinda ya dace junaid ya bada kudi, aji hudu aka sa ta bayan yayi bayanin ailment dinta, shi dai El-ameen kallonsu kawai yake, suna fitowa makarantar xa su shiga mota junaid ya hango Hafsat sanye da uniform din makarantar da hijab, tuni El-ameen ya shige mota Jasmine ma ta bude bayan motar ta shiga tana kallonsa, Hafsat bata lura da Junaid ba xata wuce yace "Hafsat!" Juyowa tayi da sauri tana kallonsa, murmushi yayi yace "kwana biyu" dawowa tayi ita ma tayi murmushin tace "Alhmdllh" yace "Nan kike knn" kai ta gyada masa, ganin duk tayi wani iri yana kallonta yace "Baki da lafiya amma koh?" Murmushi ta kirkira tace "Am getting married ne" ya d'an bude ido yace "Ohh really, when?" kamar baxa ta ce komai sai kuma tace "Friday" Junaid yace "Toh Allah ya sanya alkhairi, but shine bbu gayyata" bata ce komai ba, ganin kamar bata son maganan yasa yayi mata sallama tayi wucewarta ya shiga mota.
*Haske Writers association*💡
[3/19, 9:22 PM] El-hajj💥: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
56.....
Kallo daya junaid yayi masu ya tada motar ya ja suka bar wajen, yana jin Jasmine tace "Uncle why didn't you want to talk to me?" Ba tare da El-ameen ya kalleta ba yace "Am meditating!" Ta wara ido tace "Ohh What's that?" Da Hannu ya mata alamar da tayi shiru, tayi shiru tana kallonsa, ganin junaid gidansa ya nufa El-ameen yace "Hey drop me, gida xan tafi" junaid bai ce komai ba yayi parking ya bude motar ya fita ya daga ma Jasmine hannu ta hade rai tana kallonsa, murmushi yayi ya rufe motar junaid ya ja motar ya kama hanyar gida. Yana gama parking ta bude motar ta fice ta nufi parlor, daki ta shige ta sa key ta fashe da kuka. Washegari karfe bakwai da minti goma duk suka bar gidan, farin riga ne jikinsa sai wandon uniform don bai son ya ji Jasmine tace bata son kayan, ita dai Humainah ko kallonsa bata yi ba ta wani hade rai gaban mota, jasmine ya fara ajiyewa islamiyya, sannan ya tafi da Humainah makarantar da tace take so na su fatima, yana gama parking ya dau shirt din uniform dinsa ya sa sannan ya bude motar ya fita ta bi bayansa, nan take ya biya komai ya fice ya nufi office abun sa. Da yamma yana barin gun aiki Jasmine ya fara xuwa dauka don hudu suke tashi, da fara'arta ta karaso gun motar, kamar daxu da safe bbu uniform jikinsa sai wandon, ta wara masa ido tace "Captain nayi frnds guda uku, kuma suna koya min karatu I like them" kai kawai ya gyada mata ta bude motar xata shiga yace "Koma baya" ba musu ta rufe ta koma baya, ya ja motar ya kama hanyar gida, bai yi mamakin ganin Humainah ta dawo ba, Jasmine ta durkusa kusa da ita a parlor don xaune take tana cin abinci, ai ko ta wani hade rai, Jasmine tace "Anty nayi frnds uku" banxa da ita Humainah tayi, Junaid na kallon Jasmine yace "Tashi ki tafi sama" mikewa tayi, ta yi yanda yace mata. Shirye shiryen biki ake tayi gidansu El-ameen, har ya fi junaid shiga damuwa amma ko a jikin umminsa da Abba, ana saura kwana biyu daurin auren Junaid ya je gidan don har lokacin bai kirasa ba, kallon arxiki El-ameen bai masa ba, shi ko bai damu ba ya dinga danna waya abun sa, ana kiran magrib ya bar gidan. Ran saturday misalin karfe sha daya junaid na tsaye bedroom dinsa sanye da farar shadda yana kokarin saka wristwatch, Humainah ta shigo dakin, sanye take da riga da skirt Holland da ya mata kyau ba kadan ba, ta madubi yake kallonta har ta karaso cikin dakin tace "Ina son xuwa gida yau ya Ahmad" juyawa yayi ya kalleta ya dauke kai ya gama sa agogon sannan yace "Gun Daurin aure xan tafi yanxu, sai ki jira next time" tace "Amma nasan hanya na ga" yace "toh ko kin je wa xa ki samu a gidan bayan duk biki xa su" tace "Ehh nima sai in bisu ae" shareta yayi don bai son barin Jasmine kadai a gidan ne, tace "Ka ji?" Ya hade rai yace "ki jira ran lahadi in kai ki don't disturb me plss" kallonsa ta tsaya yi hawaye ya cika idonta, ya dau makullin motarsa ya fita ya bar ta nan tsaye, dakin Jasmine ya shiga ya ganta xaune kan darduma da Qur'ani gabanta, sosai take catch up, amma da ganin ta kasan ta san su a da ne shi yasa, ya durkusa gabanta yana kallonta a hankali yace "Mu'allima Jasmine!" Dago manyan idonta tayi ta kallesa sai kuma tayi murmushi ta rufe fuska, murya can kasa tace "Captain kayi kyau" yace "Uhnn koh?" Ta gyada masa kai yace "Uncle din ki xai yi aure yau, can xan je" ta xaro ido tace "Toh ni baxan je ba? kuma ni bai gaya min ba" kamar xata yi kuka ta kare maganar, Langwabar da kai yayi yace "Maza kadai ke xuwa ai" shiru tayi bata ce komai ba, ya kamo hannunta yace "gobe sai na kai ki gidan ki ga amaryar" kai ta masa nodding a hankali tace "Toh" ya dago chin dinta yace "Tea'n ya ishe ki?" Tace "Uhm na koshi" yace "Ohk," sannan ya mike ya daga mata hannu ya nufi kofa, bin sa da kallo tayi har ya isa kofa, a hankali tace "Kayi kyau" juyowa yayi da sauri sai kuma yayi murmushi yace "Ae kin gaya min" sunkuyar da kai tayi ya juya ya fita, har xai sauka sai kuma ya shiga dakin Humainah, xaune ya ganta ta hade kai da gwiwa, ya karasa kan gadon ya dagota ya ga kuka take, xaunawa yayi gefenta ya jawota jikinsa yace "Toh ba nace maki ran Sunday xan kai ki ba" ta fashe da wani sabon kukan, ya rungumeta yace "Toh yi hakuri, da yamma sai in kai ki by then su ma sun koma gida" shiru tayi bata ce komai ba, yace "kin ji" dago kai tayi tana kallonsa, ya buda mata ido ya ciro wayarsa ya shiga daukarsu hotuna, mikewa yayi daga karshe yace "sai na dawo" daga haka ya fita daga dakin, direct gun daurin auren ya tafi, El-ameen yi yayi kamar bai taba saninsa ba, shi kam ko a jikinsa don dariya ma yake basa, nan dai aka daura auren a kan sadaki dubu dari biyu, ko minti biyar Junaid bai kara ba ya bar wajen ya tafi gida abun sa. Misalin karfe biyar aka danna bell, Humainah dake kitchen tana girka supper ta fito da sauri tana kallon kofar, karasawa tayi tun kan junaid ya fito ta bude kofar ta ga hadiza tsaye, sosai gabanta ya fadi, hadiza tace "Gida ni kadai nace bari in yo nan!" Humainah ta kirkiri murmushi tace "Shigo mana" shigowa hadiza tayi Humainah tace "Mu je daki" ba musu Hadiza ta bi bayanta, Humainah dake ta addu'ar kar junaid ya fito ta bude dakinta da sauri ta shiga hadiza ta bi bayanta, hadiza tace "Ko dai mijin ki na nan ne" Humainah tayi murmushi tace "Yana nan" Hadiza tace "Atoh bari in tafi, amma shi bai xuwa gun aiki ne...." Humainah tayi dariya tace "No kiyi xaman ki ai ba shigowa xae yi ba, karfe hudu xuwa biyar yake dawowa daga aiki" Hadiza ta xauna gefe tace "Mijin naki ne naga bai fiye son mutane ba" Humainah ta yi yake tace "Bari in duba girki a kitchen" daga haka ta fita daga dakin. Dakin Junaid ta nufa ta tura a hankali ta gansa xaune yana kallo a laptop, xata rufe kofar yace "Who rang the bell?" Rasa abinda xata ce tayi, ta bude hannu alamar bata sani ba ta juya ta fita, kitchen ta koma don ci gaba da girkinta ta ga Jasmine tsaye tana juya miyan, wani kallo ta watsa mata tace "Wa ya sa ki?" Jasmine ta ajiye cokalin hannunta tace "Taya ki nake" Humainah tace "Fita!" Ba musu ta fita dai dai lkcn da aka danna kararrawan parlor, kallon kofar tayi ta karasa ta bude, su uku ne tsaye bakin kofar ta tsaya kallonsu, daya daga cikinsu yayi murmushi yace "Hi, Ahmad na nan?" Ta d'an bude ido tace "Waye shi?" Na gefensa yace "Junaid!" Ta kuma bude ido tace "Waye shi?" Kallonta suka tsaya yi gaba daya, ta girgixa kai tace "A'a mu bamu da Ahmad junaid a gidan nan, Captain kawai muke da" xaro ido suka yi gaba daya suka fara dariya, murmushi tayi ita ma tana kallonsu, daya yace "Toh ina captain din?" Tace "Bari in kira sa" Juyawa tayi ta gansa bakin stairs a tsaye ya hade rai yana kallonta, ta juya ta kalli kofar kitchen taga Humainah ma tsaye tana kallonta, karasowa captain yayi parlon yana kallon colleagues din nasa, Capt Umar yace "Ehh lallai kam captain kadai gare su a gidan, dubi wani kallo da yake ma mutane" murmushi junaid ya kirkira yace "Sannun ku da xuwa, ku karaso mana" Capt kb yace "the great Aj, bamu gan ka gun daurin auren aminin naka ba" junaid ya bude ido yace "ohh! Ae kam na je, kawai dai na bar gun da wuri ne" karasawa cikin parlon suka yi duk suka xauna, Tuni Humainah ta koma kitchen ta ci gaba da aikinta, Gaisawa junaid yayi da frnds din nasa, har lokacin Jasmine bata bar parlon ba duk da satan kallonta da yake yana hararanta, durkusawa tayi kusa da shi tace "Captain in kawo masu ruwa?" Kai kawai ya gyada mata ba tare da ya kalleta ba, Ta mike ta nufi kitchen, Capt Mk yace "Sistern ka ce amma wannan" kai junaid ya gyada ba tare da ya kallesa ba, Capt kb yace "Ahhh toh ni dai ina ciki, har ta fi ka kyau wllh, ina kama kafa ni dai yaya Ahmad" dariya sauran suka yi, Capt Mk ya hade rai yace "Ae don ta min ne shi yasa na tambayi ko kanwar sa ce...." Dariya Capt Umar yake yana kallonsu duka yace "Toh duk na riga ku wllh, tana bude kofar ta min, na dai yi shiru ne kawai" Sosai junaid ya daure fuska bai ce komai ba, Capt Mk yace "Toh pa, ya da hada rai Ahmad ko dai ba blood sis bace?" Wara ido junaid yyi yace "Kai haba blood one kuwa, irin ni babban yaya din nan shi yasa na daure fuska duk ku gama haukan ku....." dariya suka yi gaba daya, jasmine ta shigo parlon da goran ruwa guda uku a hannu duk ta mimmika masu, tace "Anty baxa ta bar ni in shiga kitchen in dauko cups ba" Kb yace "Gaskiya Anty bata kyauta ba, toh ya sunan ki?" Ta kalli junaid da ke kallon wani gun daban tayi dariya ta xauna tace "Ka ga Captain yana ce min Jasmine, Uncle na ce min jewel, mamina na ce min Baby" kb yace "Waow that's nyc, i will call you jewel also!" Ta kalli junaid xata yi magana ya mata wani mugun harara, mikewa tayi da sauri tace "In tafi Captain?" Yace "Ehh" juyawa tayi ta