Showing 114001 words to 117000 words out of 170905 words
Chapter 39 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
sai kuma ya fasa, yana huci ya jefar da ita kan gado yace "Don uwar ki a kanki take xaune?" Mikewa xaune tayi tace "Uwata?" Sai kuma ta fashe da kuka tana kallonsa tace "Uwata ka xaga ya Ahmad" juyawa yayi ya fice daga dakin ya koma downstairs. Bayan magrib ya tafi siyo masu abinci don har lokacin Humainah na aikin kuka a daki, tana jin fitarsa ta dau hijab dinta da jaka ta fice daga gidan, Jasmine ya fara kai ma abinci da ya dawo ya sameta tana bacci ya tada ta tayi sllh ya ajiye abincin ya fita, har xai shiga dakinsa sai kuma ya tsaya, ya kusa minti biyar tsaye kafin ya shiga dakin Humainah, ganin bata ciki ya ajiye ledan hannunsa xai fita sai kuma ya nufi bathroom ya bude, juyawa yayi ya fita da sauri ya tafi gun mai gadi, mai gadin na ganinsa ya mike tsaye, yace "Yaushe ta fita?" Mai gadin yace "Bayan fitar ka, tace kati xata siyo" junaid bai ce komai ba ya nufi motarsa ya bude ya shiga ya fice daga gidan, cikin minti sha biyar ya isa gida yayi parking a waje, lokaci daya gabansa ya fara faduwa, da kyar ya ja kafa ya shiga compound din, ya kusa minti uku tsaye balconyn Mumy kafin ya tura kofar a hankali ya shiga, ido hudu suka yi da Mumy dake xaune parlon sai Aysha dake parlon ita ma, jikinsa yayi sanyi ganin Humainah xaune parlon kan carpet kusa da Mumy, Mumy bata kuma kallon inda yake ba har ya karaso parlon ya durkusa nan kasa da kyar yace "Ina yini Mumy" kallonsa tayi tace "Uhn Ahmad kenan, ita Humainahr ce ta xama abar walakantawar ka yanxu, har ka kalleta ka xagi Uwarta da ke kabari sbda ka isa koh?" Sauke idonsa yayi a hankali daga kallonta, Mumy tace "Tunda har ka iya bude baki ka xagi uwarta nima xaka iya xagina, infact nima ka xaga..." Da kyar yace "Don Allah kiyi hakuri Mumy, wllh sharrin shaidan ne I didn't....." Tsawa ta daka masa tace "Rufe min baki" ya sunkuyar da kansa, ta kalli Humainah da har lokacin take hawaye tace "Kema rama ki ce masa uwarsa" kallon Mumy tayi, Mumy tace "Ehh kice masa uwar sa shi ma" ta kallesa ta ga shima kallonta yake, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, shi ma yyi murmushin ya sauke kansa, Mumy tace "Fice min a parlor" mikewa yayi ya fita daga dakin, Aysha tace "Me ya hada ku Humainah?" Shiru tayi bata ce komai ba, can ta kalli Mumy, Mumy ta mike ta bar parlon, Aysha ta dawo kusa da ita tace "Tell kar ki ji komai kin ji sis, me ya hada ku?" Kuka ta saki a hankali tace "Aunty kin ga fa har yanxu yarinyar tana nan gidan....." Hade kanta tayi da kujera ta kasa ci gaba, Aysha tayi shiru tana kallonta da tausayi, can ta dago tana share hawayen idonta tace "Amma Anty kar ki gaya ma Mumy" Aysha bata iya ta ce komai ba, ta mike ta fita daga parlon, tsaye ta gansa a balcony ta karasa kusa da shi tace "Ya Ahmad?" Juyawa yayi yana kallonta yace "What did she tell mum?" Girgixa kai tayi tace "Bata ce komai ba, amma ya Ahmad kai ma kasan baka kyauta mata kuma Allah...." Hannu ya daga xai wanka mata mari ta bar wajen yace "Xan baki mamaki idan baki fita sabgata ba wllh" juyawa tayi ta koma parlor, ido hudu yayi da Hajiya dake tsakar gida for the 5th time ya sauke kai, tace "Ina yini Ahmad" kallonta yayi fuska daure yace "Ina yini" tayi wani murmushi ta ci gaba da abinda take, jasmine ce ta fado masa ya shiga parlor yaga ba kowa ya nufi bedroom, xaune ya ganta ita da Aysha, Aysha na ganinsa ta mike ya bi ta da harara har ta fita, ya dawo kusa da Humainah ya xauna yace "Ohk, Alryt! Am sorry, tashi mu tafi gida" ta hade rai sosai tace "Bbu inda xan je" yace "Koh?" Juyawa tayi xata kwanta ya fixgota, ta shiga turasa ya hade ta da jikinsa, kasa kwace kanta tayi, ta fashe da kuka tace "Allah ni ka kyaleni...." Bai bari ta rufe baki ba ya hade bakinsu, sai da ya gaji don kansa ya kyaleta, xata kwanta ya dauketa ya mike, bude ido tayi da sauri tace "Meye haka?" Bai saurareta ba ya fita daga dakin, rufe fuskarta tayi da sauri a jikinsa tana cewa "Na shiga uku" Aysha dake parlor ta bi su da ido, har ya fita parlon, xaro ido Hajiya tayi tana kallonsu ta dau waya da sauri tana kiran Umma, Umma na dagawa tace "Bilki fito fito ki ga ikon Allah, fito waje yanxun nan" da gudu umma ta fito daga part dinta, ta bude baki tana kallonsu ita ma, lamo Humainah tayi a jikinsa har suka fita gate, Umma ta yi side din Hajiya da sauri tace "kinga tsiya koh? Kar dai ace wannan karan ma aikin banxa muke, wllh kila ciki ne da ita ma laulayi take" Hajiya da bata samu bakin cewa komai ba ta rafka tagumi, Umma tace "Kinyi shiru" Hajiya ta sauke wani shegen ajiyar xuciya ta mike tace "Mu je ciki balki" ba musu Umma ta bi bayanta. Junaid na gama parking a gida har bedroom ya kai ta, yana ajiye ta ya fice daga dakin ya shiga dakin da Jasmine take, kwance ya ganta ta takure waje daya, ya durkusa kusa da ita yace "Jasmine!" Bude ido tayi a hankali, tana ganinsa ta mike xaune yace "Me ya faru?" A hankali tace "My head is aching" abincin da ya ajiye mata ya jawo ya bude ya ga bata ci ba, yace "Me yasa baki ci ba?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya bude take away din ya dau spoon ya sa mata a ciki ya mika mata ta karba, yace "Eat" ba musu ta fara cin abincin yana kallonta, da ta dago ido sai taga kallonta yake, ganin irin kallon yasa ta matso kusa da shi a hankali tace "Captain!" Ko kadan bata ga alamar yasan tana yi ba, ta kirasa yayi sau biyu kafin ta dafa hannunsa, kifta idon yayi da sauri yace "Jasmine!" Langwabar da kai tayi tace "You are looking at me" sauke idonsa yayi kasa, kamar xata yi kuka ta sauko kasa ta durkusa kusa da shi tace "Did I wrong you again?" Murmushi ne yayi escaping lips dinsa yace "No!" Mikewa tayi ta koma kan gadon ya bi ta da kallo ta xauna ta ci gaba da cin abincinta, ya tashi ya fita daga dakin ya koma nasa, sha daya da wani abu ya sake dawowa dakin, kwance ya ganta ya karasa kusa da gadon ya durkusa ya ga bacci take, ya cire bargon jikinta yana kallonta, sleeping gown ne jikinta, ya dinga kallonta, lumshe ido yayi ya daura lips dinsa a goshinta ya gangaro a hankali har xuwa kan lips dinta, bude ido tayi da sauri ya koma baya, ta mike xaune tana kallonsa, kasa motsi yayi a gun bai kuma bari sun hada ido ba can ya mike da kyar ya fice daga dakin, ya koma nasa, ya kusa minti talatin xaune kafin ya mike ya fita ya shiga dakin Humainah, kwance ya ganta cikin bargo ya karasa gadon ya xauna ya cire bargon, ta bude ido tana kallonsa, shiga yayi cikin bargon ta mike xaune xata sauka ya jawota jikinsa ya kashe wutan dakin. Washegari da safe karfe bakwai ya gama shirin fita aiki, kasa shiga dakin Jasmine yayi, Humainah ta gama shirin makaranta ita ma bayan ta hada breakfast don tun asuba da suka tashi bata koma ba, yana xaune parlor rike da cup din tea ya kalli Humainah da saukowarta kenan yace "Tafi kice mata ta shirya driver xai xo kai ta makaranta" yi tayi kamar bata ji sa ba ta ci gaba da goge takalminta, yace "Humainah!" Ta daga kai tana kallonsa, repeating kansa yayi ta hade rai tace "Takalmi na nake polish" yace "Kawo in maki ki tafi" tabe baki tayi ta ajiye takalmin ta haura sama, samunta tayi ta fito daga wanka daure da towel, tana mata wani kallo tace "Ki shirya wai" daga haka ta fita, shi ya ajiye Humainah, Jasmine kuma driver ya ajiye ta. Tun daga lokacin da Junaid ya taho da Jasmine El-ameen bai sake bi ta kansu ba duk da yana son ganin Jasmine amma yaki xuwa gidan, ba karamin takura masa Aliyu yayi a kan ya nuna masa gidan junaid ba ya dinga kakkauce masa don yasan ko kadan bai da mutunci, Jasmine kam tun bata damuwa da abinda Humainah ke mata har ta fara damuwa don da tayi mata abu sai ta fara kuka, duk ran da hadiza ke gidan kuwa bata da kwanciyar hankali don ita tsoronta ma take ko da yaushe cikin tsangwamarta suke, tana son ganin Uncle dinta ta tambayesa yaushe Maminta xata dawo amma har ranan bata gansa ya xo ba, gashi tana tsoron tambayar captain shi, shi ma captain din ba sosai take ganinsa ba don tun bayan incident din daren ranan bai barin su hadu sai tayi bacci, duk dare kafin ya kwanta sai ya shiga to make sure she's fyn, a haka ta cika wata daya a gidan, ranan wani lahadi tana sharan parlor don yanxu kusan ita take duka aikin gidan idan captain baya nan taji an danna bell, ajiye broom din tayi ta mike da kyar don tun jiya cikinta ke mata ciwo, karasawa gun kofar tayi ta bude xaro ido tayi tace "Aunty!" Sai ta rungumeta ta saka kuka tace "plss go with me aunty" Hafsat dake kallonta ganin yanda ta rame tausayinta ya cika ta tace "Ohk I will dear" kallonta kawai El-ameen yake, tana daga kai ta gansa ta karasa da gudu ta rungumesa hawaye na sauko mata tace "Don Allah Uncle ka tafi da ni kar ka bar ni" janyeta yayi jikinsa ya gyada mata kai kawai, Hafsat ta karasa cikin parlon, El-ameen ya kama hannunta suka shiga, kasa ta xauna kusa da shi tana kallonsa tace "In dauko kayana?" Yace "Captain fah?" Bude hannu tayi tace "Ban sani ba nima" xai yi magana aka bude kofar Junaid ya shigo, ya d'an yi mamakin ganinsu ya karasa cikin parlon suka gaisa da Hafsat, ya xauna yana kallon El-ameen da ya hade rai yace "Welcome Doctor"
*Haske Writer's Association*
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
64__65
Tashi ka je, k'asa tashi yayi Abba yace "Baxa ka bar min parlor ba?" A hankali yace "Abba kayi hakuri don Allah, sharrin...." Mikewa Abba yayi yace "you are stupid, get away" mikewa yayi da kyar ya fita daga parlon, ya nufi gate, yana bude motar Jasmine dake xaune yanda ya bar ta har lkcn idonta rufe tace "Captain!" Ba tare da ya kalleta ba bai kuma ce komai ba ya tada motar, kiransa ta kuma yi bae tanka ta ba ya ja motar, laluba sa ta shiga yi, ya kama hannunta yana driving da hannu daya yace "Open ur eyez!" Ta girgixa kai tace "It's hurting me" bai kuma cewa komai ba har suka isa gida, kallon b'akin motar dake Parke daga gefen flowers din da ya xagaye frontage din gidan ya dinga yi, mai gadi na bude masa gate ya sauke glass yace "Waye yayi parking can?" Mai gadin ya kalli motar yace "ca yayi wani yake jira a can gidan yallabai" junaid bai kuma cewa komai ba ya sake kallon motar sannan ya ja motarsa ya shiga compound, yana gama parking ya juya yana kallonta yace "Jasmine open those eyez idan ba haka ba xan yi tafiya ta in bar ki" da sauri ta kamo hannunsa kamar xata yi kuka tace "yana min ciwo captain, don't leave me plss, ka kira uncle kace ya kawo min Magani" wani kallo yake mata kamar tana ganinsa, can ya janye hannunsa xai sauka ta rikosa da sauri tace "No plss" hade rai yayi yace "toh ba sai na fita ba sannan xan fito da ke" a hankali ta sakesa ya fita ya xaga ya bude side din da take ya kama hannunta ta sauko ya rufe motar suka nufi cikin gidan, parlor ya xaunar da ita ya koma wani kujerar ya xauna ya dau remote yayi powering tv, a hankali tace "Captain!" Ya kalleta bai ce komai bs, kuma kiransa tayi yace "Yess!" Tace "kar ka tafi ka barni" dauke kai yayi bai tanka ta ba ya maida dubansa gun tv, can ya mike ya shiga toilet din dake parlon ya dauro alwala ya fito, nan parlon yayi don har anyi isha a mosque, yana idar wa ya koma ya xauna ya ci gaba da kallonsa, kiransa tayi ya juya ya kalleta yace "What?" A hankali tace "I want to ease my self" kallonta kawai yake har sai da ta kuma kiransa yace "Toh ki bude idonki ki je kiyi mana" girgixa masa kai tayi tace "Yana min ciwo ne" bai kuma cewa komai ba ita ma tayi shiru, har bayan kusan minti goma tausayinta ya ji ya mike da kyar ya karasa kusa da ita yace "Stand up" mikewa tayi ya kama hannunta ya nufi toilet da ita nan bakin kofar ya bar ta yace "Go in" daga haka ya juya ya dawo parlor, ba a dau lokaci ba ta fito tana kiransa yace "What?" Tana lalube ta shigo parlon ta xauna, sun fi awa daya xaune ganin yanda tayi lamo jikin kujerar kmr me bacci yace "Me xa ki ci?" Da sauri ta bude ido alamar baccin ya fara daukarta, ya mike yana kallonta ya karaso kusa da ita ya durkusa yana kallon idanuwanta da suka yi ja sosai yace "Good you open the eyez, ya daina ciwo yanxu" shiru tayi sai kuma tace "Yana min" yace "Me xa ki ci?" Bata ce komai ba ta yi kasa da kanta yace "Xa ki sha tea nd bread?" Ta kallesa tace "No! Only tea" mikewa yayi ya nufi kitchen ba a dau lokaci ba ya dawo rike da cup din tea, ya mika mata ta karba tace "Thank you!" Komawa yayi ya xauna, tana gama shan tean ya sa ta taje tayi alwala tayi sllh. Karfe goma saura ganin ta fara bacci yace "Go to bed if you are sleepy" mikewa tayi ta nufi stairs ya bi ta da kallo. Washegari da asuba ya kwankwasa mata kofa, cire bargon jikinta tayi ta xauna tana murxa ido, can ta sauka daga kan gadon ta nufi kofar ta bude, kallonta yake daga sama har kasa, yar rigar bacci ne jikinta tace "Captain" ya sauke idonsa yace "It's time for prayer," har ya juya xai tafi ya kuma juyowa yace "kina gama sllh ki shirya for islamiyya" ta gyada masa Kai ya juya ya bar bakin kofar, yana xaune parlor shirye cikin uniform rike da cup din coffee Jasmine ta sauko, kallon agogo yayi yaga Karfe bakwai saura minti goma yace "Tafi ki dafa indomie" tace "Toh" ta nufi kitchen, bin ta yayi da kallo yace "Come here" ta juyo ta dawo inda yake ta tsugunna tace "Na'am" yace "Baki iya gaisuwa ba" kallonsa kawai take wanda hakan ya sa shi dauke kai, a hankali tace "Good morning captain" ajiye cup din hannunsa yayi ba tare da ya kalleta ba ya mike yace "Morning" tashi tayi ita ma tana kallon white uniform din jikinsa tace "You've not buttoned all the buttons captain" kokarin barin wajen yake ta shiga gabansa tace "Let me help you" da sauri ya koma baya ya hade rai yace "No! I will do that my self" daga haka ya nufi stairs, ta bi sa da kallo. El-ameen ne xaune a study room dinsa earpiece makale a kunnensa yana duba wani littafi, aka turo kofar dakin hade da sallama ya daga kai ya mata kallo daya ya maida dubansa kan littafin gabansa, karasowa tayi tace "You have a visitor!" Yace "Who?" Tace "Yana parlor" rufe littafin gabansa yayi yace "Alryt!" Ta juya ta fita, ya mike ya fita xuwa bedroom dinsa, jallabiya ya daura kan kananun kayan jikinsa ya sauko parlor, Aliyu ne xaune parlon, El-ameen yace "uhn! Ashe ka san gidana Dr" Aliyu ya kallesa yace "No! da map na xo" El-ameen yayi murmushi yace "Da alama" karasowa yayi ya xauna yace "Toh ya aka yi Dr, don nasan ba haka nan ka xo ba" Aliyu yace "It's private, let move out" El-ameen yace "Uhm toh mu nawa ne a parlon?" Mikewa Aliyu yayi ya nufi kofa El-ameen yayi murmushi ya bi bayansa. Bayan kwana uku Humainah na xaune kasa a parlor ta daura kai kan kujera duk ta rame ba kadan ba don ba karamin wahala take sha ba, Mumy ce xaune daga gefenta da sisternta Anty Nafee sai Abba dake parlon shi ma, Anty nafisat tace "Wai baxa kiyi magana ba Humainah, Meye haka kike yi" ta fashe da kuka tace "Ni ba abinda ya hadamu Mumy, ni ban masa komai ba" shiru duk suka yi suna kallonta, hawaye ne ya shiga sauko mata, Mumy ta jinginar da kanta jikin kujera a sanyaye, she's just imagining anya Ahmad dinta ne kuwa, Ahmad din da ta yarda da tarbiyar da tayi masa, Ahmad da tayi raise da hannunta, Ahmad da ko kadan bai son bacin ranta, wai yau har kwana biyar bai sake waiwayo gidan ba, girgixa kai tayi ta lumshe ido, mikewa Humainah tayi da sauri Anty nafisat ta bi bayanta, bedroom ta kai ta bayan ta gama aman, ta kwantar da ita sannan ta xauna gefenta tace "Humainah idan ma baxa ki iya gaya ma su Mumy abinda ya hada ku da Ahmad ba ni ki gaya min, take me as ur mum kin ji" girgixa kai tayi tace "Ba abinda ya hadamu Aunty" sai kuma ta fashe da kuka, Anty nafisat tayi shiru tana kallonta cike da tausayinta. Junaid na xaune parlor da evening yana