Showing 57001 words to 60000 words out of 170905 words
Chapter 20 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
jummai tace "A'a daxu dai na bata kunu ta sha ba laifi, sai dai jikinta da dumi" Junaid bai kuma cewa komai ba, faisal yace "Toh ta sha madarar jiya?" Mama ta girgixa kai tace "A'a" Junaid dai sai kallonta yake, faisal ya mike ya isa gabansu ya duka a hankali ya daura hannunsa kan forehead dinta, tayi wani kara da ya sa shi mikewa da sauri ya koma baya, mama jummai tayi dariya tace "Toh bata sanka ba" faisal yace "Uhun na ga alama" murmushi Junaid yayi ya mike ya nufi kofa, mama tace "Kai dai Ahmad ka iya tafiya ba sallama" juyawa yayi yace "A'a ban tafi ba mama ina waje " mama tace "Toh yaushe Aminu xai dawo, ka ga maganinta ya tsaya yanxu" yace "Xai dawo, amma ba yanxu ba shi yasa ma yanxu nake shirin kai ta asibiti a ci gaba da dubata a can kafin ya dawo" daga haka ya nufi kofa ba tare da ya jira cewarta ba, ta bi sa da ido lkci daya jikinta yayi sanyi jin abinda yace, faisal ya juya ya bi bayansa, hawaye ne ya cika idon mama jummai ta dago jasmine tana kallonta tace "Yanxu raba mu xa ayi?" Junaid na fita balcony ya xauna, faisal ya xauna gefensa yace "Nayi kadan in ji damuwar ka ko Junaid" Junaid ya kallesa yayi murmushi yana girgixa masa kai, bayan kusan minti biyu cikin sanyin murya ya soma gaya ma faisal matsalar da yake ciki, faisal yayi shiru yana kallonsa cike da tausayinsa, can yace "Toh kai yanxu baka da budurwar da ta maka ne" Junaid ya girgixa masa kai yace "I don't have!" faisal ya sauke ajiyar xuciya yana kallonsa, bayan kusan minti daya murya can kasa yace "You know what Capt?" Junaid ya kallesa bai ce komai ba, faisal yace "ka auri yarinyar nan kawae...." Junaid yace "Wacce yarinya?" A hankali faisal yace "Baiwar Allahn nan da kake kokarin ganin an sama ma lafiya, I assure you ba karamin lada xaka samu ba, sannan yarinyar bata yi kama da 'yar kananun mutane ba, ina da yakinin 'yar babban gida ce, you won't regret it frnd....." Kallonsa kawai Junaid yake da mugun mamaki, faisal ya girgixa kai yace "Its for ur good, for her good Capt, yanxu misali kayi aure dole baxa ta ke samun attention gun ka ba as before and ba ko wace mace bace xata yarda da taimakon ta da kake, kaga wannan shine anyi ba ayi ba don gidan jiya yarinyar xata koma, but idan ka daure ka aureta kaga ka rufe bakin parent dinka, ita kuma sai ka ji dadin kula da ita sosai tunda you now have ur freedom har Allah ya bata lafiya, then sai ka sauwake mata idan baka da ra'ayin xama da ita ta tafi ta nemi 'yan uwanta, in ka mata haka ka mata komai na rayuwa, kai kadai ne gatan yarinyar nan Junaid, ka ajiye batun mahaukaciya ce ka aureta, I assure you dat you won't regret helping her...." Katse sa Junaid yyi yace "What the hell are you saying faisal, a haukacen xan gabatar da ita gun su Abba? Sai ince ina danginta da 'yan uwanta suke, kuma kasan dai dole sai na kai ta gida gun Mumy, this is totally out of it...." faisal yace "Uhmm! Toh nemo wani solution din" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Don nayi aure baxai sa in ki ci gaba da taimakonta ba, ni nayi niyyar nema mata lafiya, babu kuma macen da ta isa don na aureta tayi controlling dina, da aurena ko ba aurena I will help her kamar yanda nayi niyya, yanxu dai xuwa gobe nake son gama arrangement din tafiya da ita" faisal ya d'aga kafada yace "Ohk Allah ya shige mana gaba, yanxu mu je in siya drugs ka kawo mata don akwai xaxxabi jikinta"
El-ameen ne kwance dakinsa bayan magrib, Ummi ta shigo dakin tana kallonsa tace "What's ur problem Ahmad, are you ohkay?" Mikewa xaune yayi a hankali yace "Slight headache ne Ummi" tace "Toh ka fito ka ci abinci ka sha magani mana ko kwanciyar ne xai sama maka relieve" daga haka ta juya ta fita tana naxarin maganan da Hajiya fati ta xo mata da shi daxu, wai sun ajiye mace can gidansa shi da Junaid, she trust her son, ta kuma san abinda xai yi da wanda baxai yi ba, ganin condition dinsa tun da ya dawo daga gun aiki yasa bata yi masa magana ba, ta kuma yanke shawarar ba ma sai ta masa ba kawai sawa xata yi aje a gano mata kuma idan har hakan ne ta tanadi abinda xata yi masa don she's a no nonsense ita, bayan minti kusan goma da fitan Ummi dakin Faisal ya xo, yayi mamakin ganin El-ameen din kwance yana bacci, ya tada sa yace "Lafiyarka kuwa El kai da baka bacci da wuri" El-ameen ya kuma lumshe ido yace "ina jin xaxxabi ne ke son kama ni, am not feeling OK" faisal yace "Toh ka sha magani?" Girgixa masa kai El-ameen yayi, faisal yace "Saboda me? patient dinku ma na can ita ma xaxxabin take, na dai siya mata drugs Junaid ya kai mata..." Mikewa xaune El-ameen yayi da sauri yace "Xaxxabi kuma, tun yaushe? Wani drugs din ka siya mata?"
✍🏻
*Haske Writers Association*💡
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
28.....
Faisal yace "Normal drugs na xaxxabi mana" El-ameen yace "Ohk, Allah ya bata lafiya" faisal yace "Ameen, idan Allah ya kai mu gobe xa a tafi da ita kudu" El-ameen ya d'aga kafada bai ce komai ba, faisal yace "Kayi wanka ka ci abinci sai ka sha magani xaka fi jin dadin jikin ka," ba musu El-ameen ya mike ya shiga bathroom, faisal na ganin haka ya jawo wayarsa da sauri ya nemo number Junaid, cikin hanxari ya shiga rubuta masa text kamar haka "Ban yi tunanin akwai abinda ya isa ya shiga tsakaninmu da kai har ya hada mu haka ba, all the same Allah ya huci zuciyarmu, ba wai don ka hakura kuma na maka text din nan ba sai don in nuna maka ni babba ne...." Daga haka faisal ya tura text din sai da ya tabbatar ya tafi sannan ya maxa yayi deleting ya mayar da wayar ya ajiye, ko minti goma faisal bai kara a gidan ba yayi gaba. Junaid na xaune parlon Mumy yana cin abinci text din ya shigo wayarsa, yayi mamakin ganin sunan El-ameen, ya bude text din ya karanta content din, murmushi kawai yayi ya ajiye wayar, can ya mike ya dawo parlor ya d'an saci kallon Humainah dake kwance tana danna wayar fatima, karbe wayar yayi yace "Ke baki iya gaisuwa ba ne" mikewa tayi xata wuce daki ya fixgota, ta kusa fadowa kansa, turasa tayi kmr xata yi kuka tace "Ni ka kyaleni," ya matso kusa da ita yace "Anki" ta bata fuska xata yi kuka, yayi murmushi yace "Abinda kika fi iyawa kenan ai" saketa yayi ya fita daga parlon ta bi sa da harara. Karfe takwas saura na dare El-ameen ya fito rike da makullin motarsa xai tafi clinic a bisa umarnin dad dinsa, bin sa da kallo Ummi tayi har ya fita, yana shiga motarsa driver din Abbansa ya karaso kusa da motar, xuge glass yayi yana kallonsa yace "Ya aka yi Umar?" Drivern ya d'an sosa kai yace "Yallabai dama, ji nayi Hajiya xata aika wasu xuwa can gidan ka, ina jin akwai fa binciken da take, xuwa anjima xa su je, nine ma xan kai su wai...." El-ameen ya firfito da ido yace "Gidana kuma, me tace maku xa ku je ku yi?" Umar yace "Wllh ban san me tace masu xa su je yi can ba, ni umarni kawai ta bani in kai su" El-ameen da hankalinsa ya gama tashi yace "Ohk ohk nagode kwarai Umar..." Umar din yace "Amma yallabai ka rufan asiri, naga kai din mutum ne mai kirki shi yasa nace bari in ankarar da kai, in ma da matsala ne sai ka gyara" El-ameen yace "nagode kwarai umar, kar ka ji komai" daga haka ya ja motar ya bar gidan, sai da ya fara tsayawa a atm machine ya cire kudi sannan ya nufi gidansa direct. Yana isa gidan yayi parking waje ya fita ya shiga ciki, murda kofar parlon yayi a hankali ya tura ya shiga, bbu kowa parlon sai Jasmine da plate din potatoe gabanta ta kifar kasa, mikewa tayi jin an bude kofa ta kalli kofar da sauri, ya tsaya ya rungume hannuwansa yana kallonta, a hankali ta shiga tahowa tana kallonsa itama har ta iso gabansa ta tsaya, murmushi ya sakar mata murya can kasa yace "Jewel!" Ita dai kallonsa kawai take, ya matso kusa da ita a hankali ya ja hancinta yace "Did you miss me" taba nasa hancin tayi a hankali ita ma, ya wara manyan idonsa yana 'yar dariya sai ga mama jummai ta sauko daga stairs rike da jakunkuna biyu, ai tana ganin El-ameen tayi still, ya kalleta ya kalli jakar da mamaki, lkci daya murmushin dake dauke fuskarsa ya bace yace "Ina kuma xaki da jaka mama?" Ae sai ta fashe da kuka tace "Yo naji Ahmad na cewa gobe xai kai ta asibiti ta xauna a can, a gida ma ana yi bata warke ba sai wani asibiti can, ku bar ni in je a mata na gargajiya mana tun da ba a dace da na baturen ba, don Allah ni a bar ni da ita xan kula da ita har Allah ya bata lafiyan. Idan ya so sai in baku addreshin kauyena, ku yarda da ni baxan cuce ta ba..." El-ameen kallonta kawai yake da mugun mamaki, yanxu da Allah bai kawo sa ba tafiya da ita kawai xata yi, karasowa parlon yayi yace "Ehh wannan kuma gaskiya ne mama kin kawo shawara me kyau, Amma bari muyi shawara da Junaid din koh" tana matsar kwalla tace "Toh" xaunawa yayi yana kallon Jasmine dake ta binsa kamar xata shige jikinsa, yayi murmushi ya xaunar da ita ya jawo ragowar potatoe din da ta xubar ya dau daya ya kai mata baki, ta bude bakin ya saka mata, kallon Mama jummai dake kallonsu tana 'yar murmushi yyi yace "Mama xaki d'an siyo mata fruits a bakin titi don Allah," tace "Toh" ya fiddo kudi ya mika mata yace "Na dubu xa ki ce a baki" karban kudin tayi ta fita sabe da gyalenta, jasmine ta bi ta da kallo, mikewa yayi ya isa kofa yana lekan ko ta tafi sannan ya juyo ya kusa cin karo da Jasmine da har ta biyosa, murmushi yayi ya isa gun jakunkunan da mama jummai ta sauko da, ya bude yaga wanda ke dauke da kayan Jasmine din, duddubawa yayi ya fiddo da hijab ya sa mata, sannan ya dauki jakunkunan biyu ya rike hannunta suka fita daga gidan ya kulle da key, yana rike da hannunta ya nufi gun mai gadi, yace "Kana ji na Usman, xa mu dan yi tafiya ne amma baxa mu dade ba" ya fiddo kudi aljihunsa ya mika masa yace "Ga kudin ka na wannan watan, yanxu xaka tafi xan kulle gidan ne, sai ka tsaya bakin gate har mama ta dawo ka bata Jakarta da kudin nan ita ma, da xaran mun dawo xan neme ka" Mai gadin da ko kadan bai ji dadi ba yace "Toh shikenan yallabai, Allah ya kiyaye hanya, ya dawo da ku lafiya" El-ameen yace "Ameen, d'an je ka canja min wutan gidan xuwa na gen" ba musu maigadin yaje yayi yanda yace masa gidan ya dawo ba wuta gaba daya, ya dawo shima ya hada nasa kayan, suka fito gaba daya, El-ameen ya kulle gidan yace "Don Allah ka jira har tsohuwar ta dawo ka bata hakkinta da kayanta," mai gadin yace "In'sha Allah yallabai" daga haka El-ameen ya nufi motarsa da ita da sauri yana rike da nata jakar kayan, ya bude front seat yasa ta shiga, ya ajiye jakar kayanta a bayan motar ya rufe, ya xaga ya shiga motar ya tada ya bar wajen, kafin ya isa titi ya ga Mama jummai na ta xabga uban sauri rike da ledan fruits, ta basa tausayi sosai, yasan tsakaninta da Allah take son yarinyar amma cutar dake damunta na asibiti ne ba na gargajiya ba, kuma tun da ta fara tunanin guduwa da ita wataran ko ba yanxu ba sai ta gudu da ita din, may be some other time xa su kuma nemanta, kallon jasmine yayi yaga yanda ta kafa ma glass din motar ido ko kiftawa bata yi tana kallon motoci dake tafiya kan titin kamar me son gano abu, yayi murmushi ya kamo hannunta yace "Jewel" kallonsa tayi da sauri, ya sakar mata murmushi, ta maida dubanta kan titi, sosai yake tausayinta don a yanxu dai bata da gata a duniya sai nasu, murmushi yayi tunawa da yayi axumi uku ya hau kansa fa. Tafiya kawai yake ba tare da yasan takamaiman inda xai kai ta ba ma, duk he's just confuse, yasan ko ya kira Junaid yanxu ma ba fitowa xai yi ba yana can Mumy ta gama basa abinci ta lullubesa yayi bacci, tsaki yayi yana girgixa kai.
✍🏻
*Haske Writers Association*💡
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
29....
Parking yayi a gefen titi yana tunanin inda xai kai ta, gidan frnds dinsa masu mata? girgixa kai yayi don yasan ba lallai basu yi thinking negatively ba, Hotel? Ya girgixa kai coz it's not decent, to ina xai kai ta? Dafe kansa yayi cike da confusion, can ya dago ya juya yana kallonta ya ga ita ma shi take kallo, yayi murmushi a hankali yace "Ina xan kai ki jewel?" Dauke kanta tayi ta jinginar jikin glass din motar tana lekan waje, ya tada motar ya kuma hawa kan titi ya dinga driving din kamar bai son yi, cikin mintunan da basu wuce ashirin ba ya iso clinic, yayi parking a wajen da aka tanadar don ajiye mota, kalle kallen haraban hospital din ya dinga yi, ganin patients ne Kawai ya fito, ai tana ganin ya fita ta fasa ihu ita ma xata fito, ya juyo da sauri yace "Wait jewel yanzu xan bude maki" xagawa yayi daya side din ya bude motar ya fito da ita, kalle kalle ta shiga yi, ya rike hannunta ya shiga asibitin da sauri, bai saurari nurses din dake gaida sa ba ya haura sama da ita ya bude office dinsa suka shiga, key ya sa ma kofar sannan ya juya yana kallonta ya sauke ajiyar xuciya yace "We've got a good solution koh" kama hannunta yayi ya nufi bedroom din dake office din ya xaunar da ita kan gado yana kallonta, kwan kwasa office dinsa ya ji ana yi ya mike da sauri ya fita, mikewa tayi ita ma da saurinta ta bi bayansa, ganin ta biyosa yasa bai bude kofar ba yace "Who's there?" Muryar nurse yaji tace "ur attention is needed at the theatre sir" a fusace yace "Toh da ban xo ba fa" shiru tayi yyi tsaki ya kama hannun Jasmine ya maida ta dakin, xaunar da ita ya kuma yi a hankali yace "Look jewel, yanxun nan xan dawo kar ki bi ni plss" ya kusa second goma yana kallonta sannan ya mike a hankali xai fita ita ma ta tashi da sauri, yace "Ohhw ina xan kai ki jewel?" Fita yayi ta bi bayansa, ya isa show glass din dake office din me dauke da magunguna da ruwan allurori ya bude ya dauki wani kwalban allura ya rufe, syringe ya dauka ya juya suka kusa cin karo, yace "Sorry!" kama hannunta yyi suka koma dakin ya sa ta xauna, cikin few minutes ya hada alluran yayi mata a lap, 'yar kara kawai tayi masa tana bata fuska, yayi kasa da murya yace "Sorry jewel!" sun kusa minti goma xaune yana yi yana kallon agogo, yaji an kuma kwankwasa kofa, ya mike da sauri ita ma ta mike sai dai da ganinta kasan duk jikinta ya mutu, rike hannunta yayi ganin yanda take layi ya fito office din yace "Yes!" Muryar Abbansa yaji yace "S'ako na bai iso gare ka bane, ka wani garkame office kana ce min yes" xaro ido yayi yace "Ohh No, kaya nake canzawa ne Abba gani nan xuwa yanxu" Abba bai kuma cewa komai ba, hakan yasa ya kama hannunta suka koma dakin, kwantar da ita yayi ta lumshe ido, ya sauke ajiyar xuciya ya mike ya bude inda kayan shiga theatre dinsa suke, ya cire na jikinsa ya saka sannan ya lullubeta ya fito daga dakin ya rufe da key. Sha biyu saura ya fito daga theatre, yana komawa office ya bude dakin yaga bacci kawai take, toilet din dake nan ya shiga yayi wanka ya fito ya saka kananun kayansa ya fito office ya xauna ya kifa kansa kan table don bacci yake ji, wata nurse ta shigo rike da cup din coffee ta ajiye masa kan table tace "Sir" dagowa yayi yace "Thanks" har ta kai kofa xata fita yace "Nurse Sharifah" juyawa tayi ta dawo tace "Sir?" Yace "Nan sama kike ko k'asa yau?" Tace "a nan nake duty" yace "good, akwai patient a dakina, i want you to stay with her throughout the nyt, mental disorder gareta, in case xata farka cikin dare ki rakata restroom" shiru tayi tana kallonsa tsoro bayyane fuskarta, murmushi yayi yace "She won't hurt you, bata komai, just in case kar ta tashi ne yasa nace ki tsaya da ita" a hankali tace "Ohk sir... Let me explain to..." Katse ta yayi yace "No! Xan je in mata bayani" daga haka ya mike ya fita. Ta lallaba ta isa kofar dakin ta tura a hankali ta leka ta ganta tana bacci cikin bargo, a haka ya dawo office din yace "Ki shiga baxa ta maki komai ba nace" gyada masa kai tayi ta shiga dakin, ya dau coffee dinsa ya sha bayan ya huce sannan ya mike yayi kwanciyarsa kan kujeran dake office