Showing 9001 words to 12000 words out of 170905 words
Chapter 4 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
bbu kowa palon ya nufi dakin El-Ameen, bathroom ya shiga ya hada ruwa me dumi sosae yyi wanka, ko da ya fito El-Ameen na xaune yana shan tea, ya fiddo rigan sanyi babba a closet bayan ya goge jikinsa ya sa, wayarsa ya dauka yana dubawa ko bae jike ba snn ya ajiye gaban mirror ya dawo yyi kwanciyarsa ya ja bargo ba tare da ya kalli El-Ameen ba, El-Ameen yace "Baxa ka sha tea'n ba?" Share sa Junaid yyi, El-Ameen yyi murmushi sanin baxae kulasa ba yace "Toh fa gwara ka tashi ka sha magani kar ka k'asa tashi gobe, ana kuma tambayata ba'asi xan tona wllh" Dariya El-Ameen ya dinga yi jin Junaid bae tanka sa ba still, ya mike ya dauko paracetamol ya dawo da Goran ruwa ya xauna gefensa yace "Look frnd, tashi ka sha drug kafin ka kwanta kar ka tashi da mura gobe, yhu knw I may be annoying a times" yana murmushi ya kare maganar, mikewa Junaid yyi ya karbi maganin da ruwa ya kora ya koma ya kwanta don shi kansa yasan without dat baxae tashi lfya ba gobe. Washegari da asuba kafin ayi sllh Junaid yace xae tafi bayan ya daura alwala yyi Raka'atainil fajr, bae yarda ya dau motar El-Ameen ba don yasan hkn na iya tona masa asiri, ko mum din El-Ameen bata san yana gidan ba, El-Ameen ya rakasa bakin titi ya tsayar masa da a dai daita don ca yyi bae iya ba. Ana kokarin tada sllh ya iso anguwarsu na Government reserve area, masallaci kawae ya shiga, ana idarwa ya dde xaune yana Azkar har ya ga fitan Abbansa snn ya mike ya bi bayansa, part dinsa ya nufa ya gaishesa ya amsa masa snn yace "Kana mura ne Ahmad?" Junaid ya girgixa kai yace "Ya ma yi sauki Abba, ina shan magani" Abba yace "Gud! Babu damuwa ko?" Junaid ya shafa kai yace "Ehh Abba!" Abba yace "To Allah maka albarka" Junaid yace "Ameen Abba," Abba yace "Gobe xan fita xuwa Germany, tafiyar ya xo min da gaggawa ne, as usual am handing the family over to yhu son" Junaid yace "Toh Allah kai mu Abba, journey mercy dad, in'sha Allah" Abba ya shafa kansa yace "Ameen dear son" mikewa Junaid yyi yace "It's almost daybreak Abba, bari in je in shirya xuwa aiki" Abba yace "Its ohk, stay blessed" fita yyi ya nufi bangarensa, cikin mintunan da basu fice ashirin ba ya shirya cikin uniform dinsa na dark navy blue trouser da light blue shirt, kadigan yasa navy blue bayan ya feshe jikinsa da turare ya rike hularsa a hannu, waow yyi kyau har ya gaji lips din nan nasa kamar ya shafa jan baki, ya bude manyan idanuwansa sanin bae shafa komae ba ya daga kafada ya fita xuwa side din mum dinsa, fatima dake shara a balcony ta gaida shi, ya amsa ya shiga parlon, Mumy na jera masa breakfast dinsa a dinning ya sameta, ya nufi dinning din ya mata side hug ya kwanta jikinta a hankali yace "Sabahul khair Ummu na" Mumy tayi murmushi tace "How are yhu, baka rufe windows bne jiya naji kmr mura na neman kama ka" shagwabe mata yyi yace "Na rufe mana Mumy," ta hararesa tace "Toh ka bar Ac a kunne ko" ya girgixa kai yace "Not at all mum, kinsan ynxu lkcn ruwa ne kuma tun da na dawo ciki nake fita aiki shi yasa kmr muran ke son kama ni" tace "Toh I will get yhu an umbrella don ban ga amfanin Raincoat din da kake sa wa ba" yace "A'a ni nafi son raincoat dina, umbrella sae kace mace mumy" tace "Toh idan na baka kar kayi amfani da shi" langwabar da kai yyi ya xauna yana kallon ynda take hada masa tea, plate din potatoe'n da ta xuba masa ya jawo ya shiga ci yace "Aisha ta koma ne Mumy?" Mumy tace "Tun jiya" daga haka ta bar dining din ta shiga daki, a hnkli junaid ya ajiye fork din hannunsa tunawa da mahaukaciyar da suka dauko jiya da yyi, har Mumy ta fito bai kuma cin komai ba, ta kalli agogo ta kallesa tace "Kana kallon agogo dai koh" yyi yake ya ci gaba da cin potatoe'n, tutturawa kawae ya dinga yi don neman appetite yyi ya rasa, ya mike yana goge bakinsa da tissue yace "Allah amfana momy, thnks a lot" tace "Welcm, but make sure ka shiga ka gaida mutan gidan yau" d'an hade rae yyi amma da yake baya mata musu cewa yyi "Toh mumy" ta rakasa har balcony, yyi side din stepmums din nasa, bangaren Hajiya Fatee ya fara shiga tana xaune da Muhibba a palo da Rabi'a dake gugan Hijab, ya xauna kan kujera hannunsa rike da hularsa me kaman face cap me dauke da symbol din captainship a jiki, yyi k'asa da kai yace "Ina kwana Hajiya" a dakile tace "Lfya lau d'an gwal" hade rae yyi yana jujjuya hular hannunsa, Rabi'a tace "ina kwana ya Ahmad?" Yace "Lfya lau ya sch?" Tace "Alhmdllh" Muhibbah dake ta kallonsa ko kiftawa bata yi ganin ko kallon inda take bae yi ba cikin wani siririn murya tace "Ina kwana ya A.jay" ba tare da ya kalleta ba yace "Lfya lau" sae kuma ya mike ya nufi kofa yace "Na tafi aiki Hajiya," bata tanka sa ba har ya fita, Muhibba ta kalli Hajiya tace "Hajiya kinga ko amsa gaisuwata bai son yi ma" Hajiya Fatee tayi wani murmushi mai wuyar fassara ba tare da tace komae ba, Rabi'a tayi 'yar dariya tana guganta tace "Aiki" harara uwar ta wurga mata, ko sanin tana yi bata yi ba, part din Hajiya Bilki Junaid ya nufa, bbu kowa palon ya nemi gu ya xauna yana kallon agogon wrist dinsa, daga kitchen khadija ta fito ta d'an wara ido tace "Lah ya Ahmad ashe kana nan, Gud morning" yayi murmushi yace "Morning lil sis, ya sch?" Ta karaso kusa da shi ta shagwabe murya tace "Lfya lau, plss yaya ka d'an min transfer din 5k frnd dita na birthday gobe xan siya mata perfume" yace "Kije ki samu Abba mana ae bai tafi ba" ta d'an bata rai tace "Shekaranjiya fa ya canxa min phone" yace "Ohk ltr" Hajiya bilki ce ta shigo palon, kallo daya tayi masa ta dauke kai, tana kallon Khadija tace "Ke don uwar ki me ya hada ki da Suhaima kike mata fitsara?" Khadija ta hade rai ta juya ta koma kitchen, junaid yyi k'asa da kai yace "ina kwana Umma" ba tare da ta kallesa ba tace "lfya lau" Suhaimah ce ta shigo palon da alamar muryarsa taji, tace "Ina kwana ya Ahmad" mikewa yyi yace "Lfya lau" daga hka yace "Na tafi aiki Umma" bae jira cewarta ba ya fice, ta bi sa da harara, Suhaimah ta samu waje ta xauna ta xabga tagumi tana kallon Umman. Junaid na xuwa gun aiki ya dauki permission Karfe sha daya ya fito, driving yyi xuwa clinic din dad din El-Ameen, Yana rike da hularsa ya haura sama xuwa office din El-Ameen, Nurses din suka bi sa da kallo ko kiftawa bbu, yana attending to patient ya same sa, ba tare da ya kallesu ba ya shige bedroom, xama yyi yana addu'ar Allah yasa baxae dau lkci da patient din nasa ba, ko minti biyar ba'ayi ba sae ga El-Ameen ya shigo yana kallonsa yace "Ya? Duty din naka ya kuma shifting xuwa yamma ne?" Junaid yace "No of course, yarinyar da muka bari kulle a gida fa?" El-Ameen ya hade rai ya galla masa harara yace "Kaga xaka fara daga ma mutum hankali da sassafen nn koh, Toh me xa ayi mata ynxun? Ba sae xuwa yamma in mun gama aiki ba" Junaid ya girgixa kai yace "Yanxu fisabilillah da xaka fito baka yi breakfast ba Dr? Ita ba mutum bace da xa a bar ta ba ruwa ba abinci har xuwa yamma?" El-Ameen yyi masa wani kallo yace "Toh wai wa ya hana ka xuwa kai mata abincin ynxu, iyaka ka xo kace in baka makullin gida in baka, pls let me be Captain, am getting sick of you," Junaid ya lumshe ido ya rike kansa don walakancin El-Ameen ya fara isan sa, mikewa yyi ba tare da ya kallesa ba yace "Ohk! Bani keyn" El-Ameen ya d'an shafa kai yace "Alryt am sorry, haka ne kuma fa ya kamata a kai mata abinci, tun da ita ma mutum ce kamar Junaid" ficewa Junaid yyi ya bar masa dakin, El-Ameen yyi dariya ya bi bayansa, makullin gidan dake table dinsa ya dauka ganin Junaid ya bar office din shi ma ya fita, kusan a tare suka iso gun motar junaid, El-Ameen ya bude gaba ya shiga, junaid ma ya shiga ba tare da ya kallesa ba yace "Kaga hand me dat key ka fice min a mota" El-Ameen ya gyara xama yace "Toh fitar da ni mu ga" Junaid ya fi minti biyar bae tada motar ba, El-Ameen kuma yaki fita, sanin ba fitan zae yi ba kawae ya tada motar ya ja suka bar asibitin, wani eatry ya fara biyawa ya siyo abinci da ruwa sae hollandia drink, El-Ameen ya rike kai ya dinga dariya da ya ga hollandian, shi dae Junaid bae tanka sa ba, sae da suka dau hanyar gidan yace "kaga malam da ka rufa ma kanka asiri ka bude hollandian nn mu shanye kawae, dama am thirsty, banda haka a ina ta san wani hollandia in ba neman magana irin naka ba" driving kawae Junaid yake bae tanka sa ba, El-Ameen yyi dariyarsa me isarsa yana mamakin Junaid, a waje suka yi Parkin motar, El-Ameen ya bude gidan suka shiga, kallon Junaid yyi da ya tsaya yace "A'a Toh ka shiga gaba mana goga" murmushi Junaid yyi bae ce komae ba yana shafa kai don shi har ga Allah tsoro yake, El-Ameen ya dinga kyalkyala dariya har suka isa kofa Junaid na biye da shi a baya, El-Ameen na bude kofar ya koma baya da saurinsa ya fiffito da ido, Junaid na ganin hka kan kace me sae gashi a tsakiyar compound cikin 'yan sakwanni, El-Ameen ya rike kai yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya nanata hakan ya kusa sau goma, Junaid na daga tsakiyar compound sae tambayar me ya faru yake, cikin tsawa yace "Junaiddd xo ka ga abinda ka jawo min"
✍🏻
*Haske Writers Association*💡
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
6.....
El-Ameen ya juya yana kallon Junaid ganin ya ki karasowa da karfi yace "baxa ka xo ka ga abinda mahaukaciyar da ka sa na kawo gidana tayi ba, ya Salam!" Junaid na jin hka ya karaso da sauri yana leka parlon, kwalalo ido yyi yana kare ma palon kallo, palon komawa yyi kamar wanda aka yi karamin yaki, don duk ta tarwatse plasman palon da frames gaba daya, lafiyayyen centre table din ma bata raga masa ba, ko ta ina kwalabe ne a falo, duk ta tuttuge labulaye da karafunansu, kujeru kam upside down ta juyasu dukka, Junaid bae san lkcn da ya fashe da dariya ba har da rike ciki, El-Ameen ya bude baki yana kallonsa idon nan nasa ya kada, fixgosa yyi yana huci yace "Yhu see wat you've caused koh Ahmad, gud! this mad woman is adding not a minute more in my house" yana fadin hka ya turasa ya shiga palon, da sauri junaid ya hadiye dariyarsa ya rikosa yace "Haba frnd, Chill plss ka mance mahaukaciya ce ita kamar yanda kake kiranta, I promise wllh duk xan siya maka abubuwan da tayi damage, that's a promise frnd!" marairaice masa Junaid yyi yace "Plss!" El-Ameen yyi kwafa yace "Yanxu naji bayani, kuma ga motata ma can a gida bbu kyan gani, kasan yanda xa kayi da shi, I need it the way it was before, nd don't forget it's my favourite car" Junaid yyi murmushi yace "Kar ka damu xa a gyara" El-Ameen yace "Gud! Kuma ynxu idan mu ka shiga naga tayi fitsari ko otherwise wllh kai xaka gyara min waje" Junaid ya d'aga kafada yace "Na yarda" Nan El-Ameen ya sa kai ya shiga falon yana bin ko ina da kallo, sae a lkcn ya kula da jinin da yayi littering din falon alamar duk ta ji ciwo, kamar ance ya kalli bayan kofar falon ya ganta durkushe wajen duk jini jikinta, suna hada ido ta mike da sauri xata yi waje ya yamutse fuska ya fixgota da karfi, kokuwa ta shiga yi da shi ya mata wani lafiyayyen rankwashi ae sae ga hawaye a idonta tana kallonsa, Junaid da yyi shiru yana kallonsu a hankali yace "Haba El-ameen rankwashi kuma?" Ko kallonsa El-Ameen bae yi ba, ya ja ta suka koma sama xuwa dakin da aka ajiyeta, bude baki yyi ganin duk ta fasa glass din windunan dakin ma, ita nan duk neman hanyar fita take, kwalo ma Junaid kira yyi da karfi, Junaid ya nufi stairs da sauri ya haura ya shiga dakin, El-Ameen na huci yace "Ohh my God! Dubi windows dina Captain" Junaid ya langwabar da kai yace "Duk xan gyara maka as soon as possible" El-Ameen yyi kwafa yace "Allah kar ya wuce kwana biyu, kuma ni ka xo ka ajiye mata abincin my frnd, I have important things doing a office" karasowa Junaid yyi ya ajiye abincin ya bude yana kallon yanda ya rike hannunta gam sai mutsu mutsu take, El-Ameen ya kai ta k'asa ya nuna ta da yatsa yace "Wllh Kika sake min barna a gidana sae na gaggalla maki mari, wawiya kawai" ita dae kanta na k'asa, tsaki yayi ya mike yana kallon Junaid yace "Mu je plss malam gashi ka kawo mata abincin hankalinka ya kwanta" Junaid yace "But ya kamata mu samo 'yar dattijuwa yanxu koh?" Wani kallo El-ameen yayi masa yace "Ya kamata dai ka samo" daga haka ya fice daga dakin, Junaid ya bi sa da kallo sannan ya kalleta, har lokacin bata d'ago ba, abincin ya matsar mata gabanta a hankali yace "Ki ci abinci kin ji, we are only helping yhu Baiwar Allah" ita dae kanta na kasa sai d'ada takurewa waje daya take, kwala masa kira El-Ameen yyi ya fito da sauri, El-Ameen ya sa ma dakin key yace "barnan ya tsaya iya dakin" shi dae Junaid bae ce komae ba har suka fito, El-Ameen ya tafi gun tap din dake compound din gidan ya wanke hannunsa yana tsaki ya nufi gate Junaid na bin bayansa, a cikin mota El-Ameen ya ciro waya ya shiga neman nmbr, yana dialing ya sa hands free, sallama aka yi masa ya amsa yace "Jibril kana ji na," d'aga daya bangaren aka ce ehh oga, yace "Gud mai gadi nake son ka samo min nan da 'yan awanni don Allah, wanda ka sani kasan halinsa fa" D'aga daya bangaren aka ce "Toh oga, in'sha Allah xa ayi hkn" katse wayar El-Ameen yyi, Junaid ya tada motar suka bar layin, sae da ya fara ajiye El-Ameen clinic bbu wanda yace ma kowa komae, yana fice masa a mota ya ja motar ya nufi office shima, El-Ameen yyi murmushi yace "Ina xaune xa ka dawo ka same ni ne ae"
Karfe hudu da rabi Junaid ya koma gida daga gun aiki, tunaninsa daya karyar da xae ma Mumy ta bar shi ya fita, don ryt from time shi ba mae xuwa ko ina bane daga gun aiki sae gida sai in kuma yaje kallon kwallo shi ma ba ko da yaushe ba don yafi son kallon a gida, ko da yaushe yana manne da ita shi dai, yawanci ma El-Ameen ne ke xuwa gidansu shi bae fiye xuwa can ba sosae, yana xaune bangaren Mumy bayan ya gama lunch, ita kadae ke hiranta sai fatima dake ta shirin islamiyya, shi kam duk hankalinsa baya tare da shi kawae ya kafa ma tv ido ne kmr me kallo, agogo ya duba ya ga har biyar, ya fiddo waya ya kira lambar driver yace ya xo ya samesa bangaren Mumy, ba a dau lkci ba drivern ya xo, Junaid ya ciro dubu goma ya mika masa yace "Gashi wannan ka siyo fruits din dare kamar ynda kake siyowa ka kai ma kowa nasa" Drivern ya risina ya karba yace "Toh yallabai," Junaid ya ciro Atm dinsa yace "ka d'an biya Atm Machine ka ciro min dubu talatin" Drivern ya karba yace "In'sha Allah yallabai" yana fita Mumy tace "Me xaka yi da dubu talatin Junaid" Junaid yace "Su Umma xan ba ko suna bukatar abu kafin Abba ya dawo jibi" Mumy tace "Ohk Hakan yyi" yana xaune sae kallon agogo yake a kai a kai har Ishaq ya dawo da ledoji hudu dauke da fruits kala kala, ya ajiye ma Mumy nata snn ya ciro 30k ya mika ma Junaid, Junaid yace "Yauwa ka raba dubu sha biyar biyar ka kai ma Hajiya daya Umma daya" Mumy tace "A'a kai ya kamata ka kai masu" bae yi musu ba ya karbi kudin hannun Ishaq, Mumy tace "Ajiye naku fruits din ka fara kai masu nasu" Ishaq ya ajiye leda daya ya fita da biyu don kai ma Umma da Hajiya, ba a dau lkci ba ya dawo ya dauki nasu ledan na masu gadi da masu wanki da share sharen gidan ya fita don xuwa su raba bayan yyi godiya. Junaid ya kalli Mumy yace "Mumy xan je gidansu El-Ameen!" Mumy tace "Gidansu El-Ameen kuma, wae wnn sintirin xuwa gidansu El-Ameen da kke kwana biyun nn kalau kuwa Ahmad? Ko dae gun budurwa kake xuwa?" Ta kare maganan tana murmushi, Dariya yyi ya shafa kansa yace "Kai Mumy budurwa kuma, shi dae nake rakawa fa" Mumy na murmushi har lkcn tace "uhn uhn kai dae fadi gskya Ahmad" ya shagwabe mata yace "Mumy ni da gske wllh ba gun budurwa nake xuwa ba, El-Ameen nake raka wa" Mumy tace "In ma gun ta kake xuwa ae ba laifi bne Ahmad, it's high time yhu start planning of settling down with a