Showing 3001 words to 6000 words out of 170905 words
Chapter 2 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
tace "Zance! Lallai ba ayi abun arxiki ba kenan" dariya yyi lkci daya ya hade rai yace "Allah mum mun yi magana me ma'ana, infact ni ne ma nayi don shi shiru yyi wai kunya" Mumy tayi dariya tace "Au, kace ka kora masa budurwar knn in har kai kayi magana, tab!" Dariya shi ma yyi ya mata side hug yace "Kai Mumyna ni din ne ban iya magana ba" murmushi tayi tace "Kaje gun Abba yana neman ka" ya saketa yace "Ohk Mum" kofar da xae sada sa da part din dad dinsa ya nufa, xaune ya samesa babban falonsa yana kallon news lkci daya yana shan fruit salad din dake kan d'an table gabansa, Hajiya Fatee na xaune gefensa, sae step sisters dinsa su uku gaba daya suna palon, xaunawa yyi kasan lallausan rug din yana kallon Abbansa yace "Barka da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa daga ina kake naga baka duty ae" yace "Naje gidansu El-Ameen ne Abba," kallon Hajiya Fatee yyi yace "Ina yini Hajiya?" Tayi murmushin da bai kai ciki ba tace "Lfya lau, ya aikin" yace "Alhmdllh" Muhibbah ce ta shigo falon da sallama rike da bowl din kankana da akayi slicin, ta duka ta ajiye gefen Abba, xama tayi tana kallon junaid da ya maida hankalinsa kan Tv tace "Ina yini yaya" amsawa yyi ba tare da ya kalleta ba, Hajiya Fatee sae kallonsa ta gefen ido take, mikewa Junaid yyi yace "Sae da safe Abba" Abba yace "Yauwa ka ba Muhibbah dubu ashirin xa tayi amfani da su a makaranta gobe wae," yace "toh Abba" daga nn yyi ma Hajiya Fatee sae da safe, kanninsa ma suka yi masa sai da safe ya fice daga falon rai a bace, mikewa Muhibba tayi ta bi bayansa, bae tarda mumy a palo ba, hka yasa ya nufi bedroom dinta ya sameta har ta kwanta, xauna wa yyi daga gefenta yace "Kin kwanta mum?" Tace "Har ka fito?" Yace "Eh mum" peck din goshinta yyi yace "Gudnyt mum, xan tafi in kwanta" tace "Toh Allah tashe mu lfya, make sure kayi alwala kayi addu'a kafin ka kwanta" yace "In'sha Allah mum" mikewa yyi ya kashe mata wutan dakin ya rufe mata kofa ya fita, dakin da kanninsa suke ya bude, Aisha ce ke waya ita ko Fatima tayi bacci, ya rufe kofar ya fito parlor, xaune ya tarda Muhibbah tana jiransa, yyi mamakin rashin ganin Hijab a jikinta don da hijab ta shigo palon Abba, kauda kai yyi ya fita daga parlon ta mike ta bi bayansa, yana isa part dinsa ya bude ya shiga ya juya yana kallonta ganin tana kokrin shigowa yace "Ki jira ni a nn malama" rufe kofar yyi, ta hade rae ssae tana kallon kofar, tsaki tayi ta bude ta shiga, ganin bae palon ta nufi bedroom dinsa, ya dauko kudin zae fito suka kusa cin karo, wani tsawa ya daka mata yace "Are yhu insane xa ki biyo ni daki" kallonsa ta tsaya yi, yyi tsaki ya bangajeta ya fice a fusace, bin bayansa tayi ba tare da ta ji haushi ko kadan ba, a palo ya jefar da kudin ya nufi kofa ya bude yace "Leave yanxu!" D'an tsaki tayi ta duka ta dauki kudin ta fice, ya kulle kofarsa ya sa key don wani mugun haushinta yake ji a gidan. K'asa bacci yyi daren ranan, duk juyin da xae yi sae mahaukaciyar nn ta fado masa, hankalinsa ne ya tashi don shi dae bae mata komae ba illah taimakon yaron da yyi, mikewa yayi daga karshe ya nufi bayi ya dauro alwala ya fito ya shimfida pray mat ya shiga nafila, sae kusan Karfe uku da rabi bacci ya daukesa. Da asuba ruwan sama ya sakko kamar da bakin kwarya, kmr jiya yau ma bae fita mosque sllhn asubahin ba sbda ruwa, ruwan dumi ssae ya hada yyi wanka don ko kadan bae son sanyi shi, ya shirya cikin uniform dinsa ya dauki babban kadigan na uniform me kalan Navy blue ya sa snn ya fito falo rike da rain coat dinsa, sae da ya tabbatar wayoyinsa na aljihun wandon uniform din jikinsa snn ya fito balcony ya saka rain coat din da hulansa ya nufi bangaren Mumy, a balcony ya cire rain coat din ya bude kofa ya shiga, tana kitchen da mai aikinta sai fatima suna hada breakfast, ya shiga kitchen din ya gaisheta ta amsa da cewa "Ka tashi lfya, ya ruwa?" Yace "Alhmdllh mumy" Fatima ta kallesa tace "Gud morning ya Ahmad" yace "Morning" ya fita kitchen din, tea kawae ya sha da kwae shi ma sae da mum ta takura sa wae ya makara xuwa aiki, har balcony ta rakosa tace "Baxa ka shiga gaida 'yan gidan da Abba ba kenan" ya dan tsuke fuska yace "Am late mum," tace "Toh Allah ya tsare" rain coat dinsa ya sa yace "Ameen" snn ya nufi parkin space, kusan a tare suka jero da Suhaima dake rike da lema tayi shirin makaranta, ko kallonta bae yi ba ya bude motarsa ya shige ta nufi tata motar tana kallonsa, jan motar yyi ya danna horn aka bude masa gate ya fice. A hnkli ya ke driving din har ya iso inda mahaukaciyar jiya take, samun kansa yyi da parking gefen titi yana kalle kallen inda xae ganta idonsa ya sauka kanta, xaune take cikin ruwan ta hade kai da gwiwa, duk ta jike da alama tun da ruwan ya sauko bata bar wajen ba, Junaid ya jinginar da kansa jikin kujera yana ci gaba da kallonta, duk jikinsa yyi sanyi, da kyar ya iya jan motarsa ya bar wajen ganin yana bata lkci, shi mutum ne me tausayi da raunin xuciya kamar mace, har ya isa office bae da sukuni, colleagues dinsa duk suka lura da shi suka kuma tambayesa ko Lfya yace bai jin ddi ne, Karfe biyar saura ya bar gun aikin, driving kawae yake cikin rashin kuxari, bae bi hanyar da xae ga mahaukaciyar ba ya canxa hanya, ko parking din arxiki bae yi ba ya bude motar ya nufi part din mumyn sa, kwanciya yyi kan dogon kujera ya rufe idonsa gam, Mumy ce ta fito daga kitchen ganinsa a kwance tace "Lfya Ahmad" jin bae ce komae ba yasa ta karasa kusa da shi tace "Ahmad!" Bude idonsa da ya kada yyi ya mike xaune ya dafe kansa, taba jikinsa ta shiga yi da damuwa tace "baka da Lfya ne?" Lumshe ido yyi ya kwanta jikinta ta rungume sa tace "Talk to me mana son, me ya faru?" A hnkli yace "Kai ne ke man ciwo Mumy" tace "Ci abinci mu tafi asibiti" da sauri yace "No mum, xan sha magani" hade rai tayi tace "Wani maganin xa ka sha, sau nawa kke sha bae maka aiki ba, so kake ka dauko min magana gun Abba koh" shiru yyi ta mike ta nufi dinning ta dawo rike da kulan abinci da plate da spoon, fried rice din ta dibar masa ta ajiye snn ta koma kitchen ta hado masa tea, bae son mum din tasa ta daga hankalinta shi yasa ya daure ya dinga cin abincin don kwata kwata bae da appetite. Mikewa yyi da ya gama Mumy tace "Ka tafi ka canxa kawae mu tafi clinic" yace "Toh" snn ya fita xuwa bangarensa, wanka yyi ya canxa uniform din jikinsa xuwa kananun kaya, ya d'an kwanta yana tunanin karyar da xae ma Mumy ta hakura da xuwan su asibiti, dubara ce ta fado masa ya mike da sauri ya dauki wayarsa ta fita, xaune ya sameta palo ta shirya tana jiransa, murmushi yyi yace "Mumy ynxu El-Ameen ya kira ni, I told him m nt ok, shine yace I shud cum over ya duba ni" hararansa Mumy tayi tace "Yhu should come over dai kuyi hira, my frnd mu wuce clinic" marairaice mata yyi ya mata side hug yace "Haba mum, ga ni da amini likita kice mu je clinic, kinga baxae ji ddi idan ban je ba plss"
✍🏻
*Haske Writers Association*💡
⚓ *Captain Ahmad Junaid* ⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
3.....
Wani kallo Mumy tayi masa tace "Kaga ka kiyaye ni Ahmad, baxa ka gun El-Ameen din ba asibiti xa mu" shiru yyi yana kallonta sanin baxae taba convincing dinta ba, a hankali yace "Toh kiyi hkuri mumyna mu tafi asibitin" jakarta ta dauka tace "Sake ni mu tafi" saketa yyi dai dai lkcn da wayarsa ya fara ring, fiddowa yyi a aljihu yana kallon me kiran nasa ya ga El-Ameen ne, ya juya ya kalli Mumy ya ga kallon wayar take, d'agawa yyi ya kai kunne daga daya bangaren El-Ameen yace "ya ne captain, kana gida yau?" Junaid ya d'an saci kallon Mumy ya ga kallonsa take, yace "Noo! Don't worry frnd Mumy tace mu tafi clinic kawae ba sai na xo ba" El-Ameen yace "What are yhu talking about guy?" Junaid yace "No ba komae wllh, kawae dae tace mu tafi asibiti ne" tsaki El-Ameen yyi yace "HeyJunaid are you ohk, wat are yhu sayin?" Junaid yace "Ohk Tnx for ur care frnd!" D'aga hka ya katse wayar ya kashe gaba daya ya mayar aljihunsa yana sinne kai, Mumy tace "Don me xaka ce Mumy tace, maimakon kace Abban ka ne yace kaje clinic" Junaid yyi shiru yana kallonta, komawa tayi ta xauna ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shknn, ka tafi can ya duba ka, amma yana prescribing maka magunguna ka dawo Ahmad, I repeat my self ka dawo" farin ciki ya lullubesa sae dae yyi kkrin boye hakan yace "Toh Mumy I promise" har bakin motarsa ta rakasa tace "Drive carefully" yace "Sure mum" tana tsaye har ya bar gidan snn ta juya xata koma bangarenta, xaune ta ga Hajiya Fatee da Hajiya Bilkee a balconyn Hajiya fateen suna kallonsu, Mumy ta karasa tayi masu sannu da xama, Hajiya Bilki kadae ta amsa da yauwa a dakile, juyawa Mumy tayi xata bar wajen Hajiya Fatee tace "Ynxu an ma hana d'an gwal din xuwa gaida mu tsabar mulki" juyawa Mumy tayi tana kallonsu tace "Ayya Bashi da lfya ne, ynxun ma gun likita xa shi" bbu wanda ya tanka ta cikinsu, ta nufi bangarenta ba tare da ta sa ma kanta damuwarsu ba. Junaid na isa ya tarda El-Ameen na clinic, bae so hkn ba amma bbu ynda ya iya hka ya nufi Babban asibitin Dad din El-Ameen din, don shima kwararren likita ne da yyi fice a Nigeria, da yake Nurses din sun san tsakanin Junaid da El-Ameen, bbu wanda ya dakatar da shi xuwa office din El-Ameen din, murda kofar yyi ya shiga babban office din, El-Ameen dake xaune yana dube duben files sanye da farin glass a idonsa ya dago yana kallon Junaid, ajiye pen din hannunsa yyi ya rike ha6a yace "Kan ka daya kuwa captain?" Dariya junaid yyi ya xauna kan table din office din yace "Kai da ban yi hka ba da Mumy bata bari na xo ba yanxu ai" El-Ameen ya girgixa kai yace "Mummy's boy, na ga randa xaka girma ka samu freedom din kanka" murmushi yyi yana shafa kansa yace "Uhm am 30 ynxu kace ban girma ba, ae kila har in mutu baxan samu wannan freedom din gun momma na ba" El-Ameen yyi dariya yace "Idan kayi aure xa ka samu" murmushi Junaid yyi yace "Aure kuma" kallonsa El-Ameen yyi ya cire glass din idonsa yace "Amma ba ka jin ddi koh, you look weary?" Junaid ya lumshe ido ya bude da damuwa yace "Kinda frnd! Am just disturb, bani da kwanciyar hankali kwana biyun nn, M just nt my self..." Rike kai yyi ya kasa ci gaba, El-Ameen ya dafa sa yace "What's wrong frnd, tell me ur problem, 'Yan gidan ku ko?" Junaid ya d'aga kai yana kallonsa cike da damuwa yace "No! Wnn mahaukaciyar ban san ko laifi nayi da na kwace yaron nan a hannunta ba, duk na kwanta ita nake tunawa nake gani, k'asa bacci nake yanxu duk bani da sukuni" El-Ameen ya ja tsaki ya mayar da glass din idonsa ya jawo files din gabansa yana ci gaba da dubawa yace "Thought it to be something better ma, wai mahaukaciya" wani tsakin ya kuma ja, Junaid ya runtse ido ya watsar da files din yace "Haba Dr in ce maka bana iya bacci kace min yhu thought it was somethin better," El-Ameen ya rike chin dinsa yana masa wani irin kallo da mamaki yace "Wae halan kana da dangantaka da mad woman din nn ne junaid" a fusace Junaid yace "Wa ya sani" wani dogon tsaki El-Ameen ya kuma ja yace "Kaga ka rabu da ni, I have meaningful things doing ynxu, aikin gaba na ma ya ishe ni stop bothering me plss da wata mahaukaciya can." Kallonsa junaid ya tsaya yi na kusan minti biyu kafin ya sauka daga kan table din da yake ya dauki wayarsa da makullin mota ya juya ya nufi kofa, bin sa da kallo El-Ameen yyi kafin ya birkita lallausan gashin kansa a xuciyarsa yace "What's wrong with Junaid da xae damu kansa ya damu wani da wata gagarumar mahaukaciya can" mikewa yyi da sauri tun kan ya fita ya kulle kofar office din yace "Look Captain, to ynxu me kake son ayi da rashin baccin naka, ko kuma dai kawai mu je ka ba mahaukaciyar hakuri?" Junaid ya kallesa yace "bude min kofa" El-Ameen na 'yar dariya yace "Of course No baxan bude maka ba sae ka gaya min dalilin ka na xuwa gu na, which help do yhu want me to render yhu, mu je ka nemi gafararta mad woman din ne" tuni idon Junaid ya sauya kala, still behaving gently yace "Bude min kofa nace" El-Ameen yace "Noo!" Wani kara yyi ya cakumo sa yana huci yace "Bude min kofa Ahmad!" Murmushi El-Ameen yyi yace "Naki! ka xama Zaki a nn in ga" turasa da karfi Junaid yyi ya koma kan dogon kujera ya xauna ya rike kai, El-Ameen yyi dariya ya koma kan office chair dinsa ya xauna, sae bayan kusan minti goma Junaid ya dago kansa, ya kalli El-Ameen dake ta aikinsa, El-Ameen yace "Har iskokan sun sake ka kenan" Junaid bae ce komae ba ya kauda kai, mikewa El-Ameen yyi ya dawo gefensa ya xauna yace "Now tell me, ya kake son ayi?" Junaid ya sauke ajiyar xuciya cikin sanyi ya fara magana, "Frnd! May be tana son in taimake ta ne, shi yasa take bi na, she want me to help her" El-Ameen ya kwalalo manyan idanuwansa yace "Kayi me?" Shiru Junaid yyi yana kallonsa, El-Ameen ya girgixa kai yace "Yhu must be crazy Junaid, meye hadin ka da wata mahaukaciya can har kake tunanin taimakon ta, kai ka daura mata haukan, ko kasan me ya haukatar da ita? Wait! which help ma xaka iya rendering dinta tukun, taking her to psychiatry nd staying with her there ko yaya?" Junaid ya tabe baki yace "Ae dan Mumy da Abba baxa su yrda bne da nayi hkn wllh" El-Ameen yyi dariya sosai yace "Ehh lallai Junaid ka ja ma kanka" Junaid yyi kasa da murya yace "Listen to me plss Dr, ban da kai akwae wanda xan kai ma damuwar da na k'asa gaya ma mahaifiyata duk kusanci na da ita, why kake min hka frnd?" El-Ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "Noo ba hka ba Junaid, ynxu tell me ya kake son ayi, hw did yhu want me to help in here?" Cikin kwantar da murya junaid yace "yhu are a Neurologist as well as a qualified MD, I knw yhu can cure her by the grace of Allah idan ka sa kanka, yhu neva can tell where one's reward Lie's" wani matsiyacin kallo El-Ameen ke yi masa kafin ya mike yace "Gaskiya ka janyo ma kanka fitina ka ja mana muma da muke tare da kai Ahmad, dama ban da abun ka me ya kai ka kama mahaukaciya kai da kake tuki a mota, Ohh My God! ga irinta nn ka tabo aljana, don Wllh yhu are not on ur right senses" Mikewa Junaid yyi shi ma yace "Stop this El-Ameen, meye illar taimakon Baiwar Allah da xa mu yi? Haba idan wani yace min xaka yi hka I won't believe wllh," El-Ameen yyi shiru yana kallonsa baki bude, cike da mamakin aminin nasa, Junaid ya juya ya nufi kofa rai bace, girgixa kai El-ameen yayi yace "listen Captain" ko sauraransa Junaid bae yi ba ya fice daga office din, ya birkita kansa ya bi bayansa da sauri, a tare suka isa inda motar Junaid yake, El-Ameen yace "Haba frnd listen to me, ynxu mu koma ka min bayani sosai yanda zan gane abinda kake nufi don wllh am confuse" hararansa Junaid ya shiga yi yace "Ka dae san ba kai kadai bane abokina likita ba koh?" El-Ameen ya d'an yi murmushi yace "I know" hannunsa ya rike suka koma asibitin dae dae lkcn da wayar Junaid ya shiga ringing, fiddo wayar yyi yaga Mumy ce ke kiransa, El-Ameen yace "Mummy's boy" d'agawa Junaid yyi daga daya bangaren Mumy tace "Ka kyauta Ahmad" Junaid ya marairaice yace "Ohh Ummata, drip karami yake kara min ne fa, nd am feeling much beta ynxu har na ci abinci kuma" Murmushi Junaid yyi bayan ya gama sauraranta yace "in sha Allah mum" daga hka ya katse wayar suka nufi office din El-Ameen.
El-Ameen ya tallabi chin dinsa da hannu biyu yana kallon Junaid yace "ina jin ka, Allah sa ka dawo senses dinka yanxu, ya kake son ayi kace?" Junaid ya lumshe ido ya bude yace "Wae da cure dinta nake son kayi ko nawa ka bukata xan biya ka" El-Ameen yyi murmushi yace "Ohh i see, A can kan bola xan dinga tafiya ina samun ta kenan" Junaid ya ce "Noo of course, dauko ta xa mu yi" El-Ameen ya bude ido yace "Mu kai ta ina? Gidan ku?" Hararansa Junaid yyi