Showing 93001 words to 96000 words out of 170905 words
Chapter 32 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
fita ta tsaya daga bakin kofa a hankali tace "Assalamu Alaikum!" Lumshe ido yayi ya bude yana shafa kansa bai ce komai ba, sallaman ta kuma yi kamar xata yi kuka, amsawa yayi fuskarsa daure, ta shigo ta tsaya daga bakin kofa, sai dai ta kasa cewa komai ganin yanda ya tamke fuska, kallonta yayi yace "From now on idan kika sake shiga waje ba sallama I will slap you" hawaye ne ya cika idonta ta gyada masa kai ta juya a hankali ta fita, juyawa yayi yana kallon Humainah da tayi lamo cikin bargo, ya shafa kansa ya mike ya fita daga dakin ya shiga nasa, wanka ya shiga yayi, ya dauro alwala ya fito ya saka jallabiyarsa yayi shafa'i da wutr, yana xaune kan darduma har Karfe sha daya can ya mike ya fita daga dakin, tsaye yayi bakin kofa yana kallon dakin da Jasmine take don kofar a bude yake, ya karasa ya shiga dakin, kwance ya ganta daga gefe kusa da bakin kofar tana bacci har lokacin Hijab da towel ne jikinta, durkusawa yayi kusa da ita yana kallon fuskarta, ya lumshe ido ya bude murya can kasa yace "Jasmine" ganin bata motsa ba ya mike ya fita daga dakin ya sauka parlor ya dauko mata jakar kayanta ya dawo sama, ajiye jakar yayi ya bude ya fiddo mata doguwar riga ja mara nauyi, kiranta ya kuma yi a hankali bata tashi ba, ya d'an buga kafadar ta ta mike xaune da sauri tana mitsika ido tace "Uncle!" Ganinsa yasa tayi saurin cewa "Captain!" Bai ce komai ba ya mika mata rigar hannunsa yace "Tashi ki sa kayan ki" karban kayan tayi yana kallonta ta cire hijab din jikinta ta mike, dauke idonsa yayi daga kallon nata a nan wajen ta saka kayan da ya bata, ta dawo kusa da shi tace "Na sa" mikewa yayi ba tare da ya kalleta ba still ya nufi gado ya ce "Xo ki kwanta" tace "Kai ma xaka yi bacci nan koh?" Yace "Eh" karasowa tayi ta hau gadon ta kwanta har da matsa masa, lulluba mata bargo yayi ya xauna gefen gadon ya kunna Tv yace "Sai na gama kallo xan kwanta" har sha biyu bai ga alamar xata yi bacci ba, ya kalleta yace "Sleep mana" tace "Sleep captain" murmushi yayi ya gyada mata kai yace "Ke ki fara yi sai nima in yi" lumshe idonta tayi ya tsura mata ido yana kallo, bata sake bude idon ba kuma har daya saura, ya mike a hankali ya kashe Tvn, ya fita daga dakin ya bar kofar a bude ya shiga nasa dakin, kasa bacci yayi sai juye juye yake ya rasa dalili, daga baya dai ya gano dalilin ya kawar da shi daga ransa yayi forcing kansa yayi bacci. Washegari Monday yaji da ma kawai yayi resuming aiki duk da hutun sati biyu ya dauka but sbda Jasmine yasa bai yi haka ba, yana dawowa daga masallaci ya shiga dakin Humainah ya ganta xaune kan darduma, juyawa yayi ya fita dakin ya shiga wanda Jasmine take, har lokacin ya ga bata tashi ba, dukawa yayi dai dai fuskarta yace "Jasmine" ta bude ido da sauri mikewa yayi yace "Tashi kiyi sallah" ta gyada masa kai ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet. Ya juya ya fita daga dakin. Karfe takwas saura Humainah ta fito ta sauka downstairs ta shiga kitchen, tsaye tayi tana tunanin abinda xata hada for breakfast, can dai ta fiddo Irish ta fara ferewa, ko da junaid ya sauko don siyo masu breakfast yayi mamakin ganinta a kitchen, ya tsaya daga bakin kofar kitchen yana kallonta, yace "Gud morning" ba tare da ta kallesa ba tace "Ina kwana" murmushi yayi ya juya ya fita daga kitchen din. Yana xauna parlo Jasmine ta sauko da alamar tayi wanka don ta canxa kayan jikinta, kusa da shi ta durkusa tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Nayi wanka" ya gyada mata kai yana nuna mata kitchen yace "Tafi ki gaisheta ki taya ta aiki" tace "Toh" sannan ta mike ta nufi kitchen din ya bi ta da kallo ganin yanda take tafiya. Kallo daya Humainah tayi mata ta dauke Kai, ta karasa kusa da ita ta durkusa a hankali tace "Ina kwana" ba tare da ta kalleta ba tace "Lafiya lau" shiru Jasmine tayi can kuma tace "I want to help you" mika mata wukar Humainah tayi ta ta tafi gun gas xata kunna, jasmine ta dau dankalin daya ta rasa yanda xata fara fere shi, kallon Humainah dake kokarin dauko mai tayi sannan ta fara fere dankalin ihu ta fasa ta jefar da wukan jin wani xafi da ya ratsa taMikewa Junaid dake xaune parlor yayi yana kallon kofar kitchen din jin Ihun, Humainah ta ajiye man hannunta ta taho da sauri tana kallonta tace "Dama baki iya ba....." Jasmine ta fashe da kuka q rikice tana yarfe hannu ganin jini a hannunta, Shigowa kitchen din junaid yayi ya hade rai yana kallon Humainah, hade ran ita ma tayi ta juya ta koma ta ci gaba da aikinta, Jasmine ta karasa kusa da shi tana kuka tace "Captain kaga blood din" kama hannunta yayi suka fita daga kitchen din Humainah ta bi su da kallo ta gefen ido. Sama ya tafi da ita xuwa dakinsa ya sa ta xauna bakin gado ya dauko tissue yana goge mata jinin dake ta xuba, ganin yanda take kuka yasa yace "Sorry!" Ta fashe da wani sabon kukan tace "It's paining me" kallon yatsan nata yake, ido ya lumshe a hankali ya sunkuyo dai dai kan yatsan yana hura mata iska, itama lusmshe idon tayi tana jin d'umin iskar da yake hura mata, har ya d'ago idonta na a lumshe, cute face d'inta da eye lashes d'inta ke kwance ya k'urawa ido, a hankali itama ta bud'e manyan idanunta ta sauk'e kan face d'inshi, cikin wani irin murya yace "Does it still hurt?", a hankali ta gyad'a mishi kai, spirit d'in da ya saka jikin wool d'in ya d'auko yasa mata kan yatsan, ido ta rintse ta saki k'ara tareda k'ank'ame mishi hannu tana haawaye.
✍🏻
*Haske Writers association*💡
[1/14, 9:17 AM] Elhajj: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
51.....
Sake mata hannun yayi yana kallonta ganin yanda take kuka, ta girgixa masa kai tace "Bana so" ajiye Cotton wool din yayi yace "Ita ta yanka ki?" Girgixa masa kai ta kuma yi tana hawaye tace "Knife ta bani" bai kuma cewa komai ba ya mike xai fita, tace "Ka kira min uncle ya xo" juyawa yayi ya kalleta, tana hawaye tace "Call me Uncle" wani kallo ya mata ya fice daga dakin. Haka tayi ta xama ita kadai tana kuka tana yarfe hannu, da ta ga jinin ya fara xuba sai ta goge jikin farin bedsheet din, gajiya tayi da xaman ta mike ta fita daga dakin har lokacin tana hawaye, dakin da take ta shiga ta kwanta. Karfe tara Humainah ta shigo dakin rike da cup din tea da plate din potatoe da kwai ta ajiye mata, Jasmine ta mike da sauri tana kallonta da idonta da suka rine don kuka tace "Anty ki kira min uncle" tsayawa kallonta Humainah tayi, sai da ta sake maimaitawa sannan tace "Waye Uncle?" Jasmine ta goge hawayen idonta tace "Wannan uncle din nan nawa da ya tafi" shiru Humainah tayi can dai tace "Ohk" ta juya ta fita ta shiga dakin Junaid, wayarsa ta dauka ta fito ta dawo dakin da Jasmine take, number El-ameen ta dinga nema a wayar amma bata san da sunan da ya sa ba, call log ta shiga tana dubawa taga wani number da yasa My best, dialing tayi tana sa ran shi ne, bugu uku aka daga, daga daya bangaren El-ameen yace "ya?" Mika ma Jasmine wayar Humainah tayi, Jasmine ta karba tana kallon wayar, Humainah tace "Ki sa a kunne" Kai wa kunne tayi ta ji muryar El-ameen yana cewa "Captain" ta d'an bude ido tace "Uncle!" Shiru El-ameen yayi kafin a hankali yace "Baby" fashe wa da kuka tayi ya mike xaune daga kwancen da yake yace "Me ya faru baby" tana shessheka tace "I've hurt my self" yace "Where?" Tana kallon yatsan ta tace "My finger" yace "With what?" Ta kalli Humainah da ke ta kallonta tace "Knife" shiru yayi sannan a hankali yace "Sorry, an baki magani?" Ta girgixa masa kai tace "No, and it still hurt" yace "Ina Captain din?" Ta goge hawayen idonta tace "I don't know" yace "Toh wa ya baki waya?" Ta kalli Humainah tace "That Anty" yace "Where is she?" Pointing dinta tayi kamar yana gani tace "she's here" yace "Toh bata phone din" mikewa tayi ta mika ma Humainah wayar ta karba, El-ameen yace "Kin tashi lafiya?" Humainah tace "Alhmdllh" yace "Wai yankewa tayi?" Ta kalli Jasmine tace "Eh ta yanke ne" yace "Da girma wajen?" Ta kuma kallonta tace "Not dat deep amma jinin bai tsaya ba" El-ameen yace "Toh xan xo" daga haka ya katse wayar Humainah ta juya ta fita daga dakin, Jasmine ta fashe da kuka ganin hakan ta dinga rerawa. Goma saura El-ameen ya shigo gidan, junaid dake xaune balcony tun bayan fitarsa dakinsa ya dinga kallonsa har ya karaso balconyn, El-ameen ya ja kujera ya xauna yace "Next week xaka yi resume kenan" ba tare da Junaid ya kallesa ba yace "Seem so" El-ameen ya shafa kansa yace "Ashe baby yankewa tayi wai" kallonsa Junaid yayi da sauri, can ya kauda kai yace "Who's dat?" El-ameen yace "Ka fi ni saninta ai" junaid yace "Tun safe nake nan so I don't know" El-ameen yace "Ohk, can I go in?" Junaid yace "Da can tambayata kake idan xaka shiga?" Shiru El-ameen yayi bai ce komai ba, can ya fito da wayarsa sai kuma ya tuna bai da number Humainah, number Junaid din yayi dialing, Humainah dake ta masa dube dube a wayan dake cike da texts din mata yafi 50 a ciki sai dai duk bata ga wanda yake reply ba, whtspp ma haka sai dai yayi reply da sure! yeah! Lol! Ita dariya ma abun ya dinga bata, tana d'aga kiran El-ameen yace "Humainah bring her out ina waje" Humainah tace "Ohk" ta katse wayar ta ajiye ta fita ta shiga dakin Jasmine din, kwance ta ganta inda ta barta bacci ya dauketa, karasawa tayi ta shiga tashinta, Jasmine ta bude ido a hankali tana kallonta, Humainah tace "Uncle din ya xo" mikewa tayi da sauri daga kan gadon tana kallonta, Humainah tace "Yana waje" kofa ta nufa Humainah ta bi ta da kallo har ta fita, kalle kallen parlor ta shiga yi bata gansa ba, hakan yasa ta nufi balcony kamar xata yi kuka, ido hudu suka yi da shi, ta karasa kusa da shi da gudu ta duka kusa da shi tana kallonsa tace "Uncle ka xo" kallonta kawai junaid ke yi ta gefen ido, El-ameen dake kallon hannunta ya ga inda ta yanke yace "Yeah na xo" mika masa hannun tayi kamar xata yi kuka tace "Look" ya kama hannun yana kallon yatsan murya can kasa yace "Sorry, but me kike yi da wuka" ta kalli Junaid hawaye ya cika idonta sai dai bata ce komai ba, kallon Junaid din yayi shi ma ba tare da ya ce komai ba, ya mike ita ma ta tashi tsaye, gun mota ya nufa da ita junaid ya bi su da kallo, suna isa gun motar ta wara ido cike da murna tace "Uncle are we leaving, bari in dauko jakana da hijab" bai ce komai ba ya bude motar ya dauko plaster ya fito yace "Toh shiga" ba musu ta shiga ta xauna, ya yanki plastern ya kamo hannunta ya rufe gun da ta yanken, sai kallonsa take, yyi mata murmushi yace "Xai warke kin ji" kallonsa take kamar bata gane me yace ba, ya buda ido yace "It will heal" a hankali tace "Ohk!" Magani ya dauko a motar ya mika mata ta karba yace "You take one yanxu kinji?" Kai ta gyada masa, ya koma baya yace "Toh fito" kamar xata yi kuka tace "Are we not going" yace "Anjima ne ba yanxu ba" hawaye ne ya cika idonta ta fito daga motar, yayi murmushi yace "Anjiman ma baxan xo ba idan kika min kuka" share hawayen tayi a hankali tace "Na daina" wani chocolate ya dauko a motar ya mika mata yace "Toh gashi ki tafi" ta karba ta juya ta fara tafiya ya bi ta da ido, sai a snn junaid ya dauke ido daga kallonsu da yake, El-ameen ya xaga ya shiga motarsa yayi horn aka bude masa gate ya fice, tana share hawayen ta ta iso balcony din xata shiga ciki Junaid da ya wani hade rai yace "Come back here" dawowa tayi tana kallonsa, yace "Cire abun nan na hannun ki ki fita a nan" kallonsa take kamar bata gane me yace ba, ya mike yace "Nace ki cire" komawa baya tayi a d'an tsorace ta cire plastern ta jefar yace "Leave" parlon ta shiga ya koma ya xauna. Kuka tayi ba kadan ba a bedroom daga nan bacci ya dauketa. Sha daya saura junaid ya shiga parlor ya haura xuwa dakinsa, wanka yayi ya shirya ya fito yayi kwanciyarsa a parlor, can kuma ya mike ya koma sama, ya dde tsaye a corridor kafin ya tura kofar dakin da Jasmine take a hankali, kwance ya ganta tana bacci, ya shiga dakin ya karasa kan gadon ya durkusa yana kallonta, yatsanta ya kamo yana kallon inda ta yanken, ta bude ido a hankali, tana sauke idon kansa ta mike xaune da sauri, kamar bai son magana yace "Is it still paining you?" Girgixa masa kai tayi yace "Ohk! Sorry!" Ta gyada masa kai, yace "Toh kwanta" ba musu ta koma ta kwanta ya mike tsaye yana kallonta, wanda hakan yasa ta rufe ido da sauri. Kasa barin dakin yayi har bayan kusan minti goma ya ji an danna bell, ta bude ido tana kallonsa, murmushi yayi ya juya ya nufi kofa ya fita ya kulle sannan ya sauka downstairs, still yayi bakin kofa bayan ya bude yana kallon Mumynsa, ta hade rai tace "Meye haka?" Murmushi ya kirkira yana shafa kai yace "I i i was surprise ne" shigowa parlon tayi ya bi bayanta gabansa na faduwa. Tana xaunawa ya xube nan gabanta yace "Sannu da xuwa Mumy, ina yini?" Tace "Lafiya lau, ya kuke" yace "Alhmdllh wllh Mumy" yana yi ne yana kallon stairs kamar munafuki, can ya mike da sauri yace "Bari in kirata" ita dai bata ce komai ba ta bi sa da kallo don ko ba a gaya mata ba ta san bai da gaskiya wannan kame kamen, yana haura wa sama ya bude dakin Jasmine suka kusa cin karo tana kokarin fitowa, xaro ido yayi ya ja ta suka koma dakin yace "Ina xaki?" Tace "Ruwa" ya xaunar da ita xuciyarsa na bugawa yace "No xan kawo maki anjima, you know what kar ki sake ki fito yanxu kin ji koh?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Jasmine!" Tace "Uhm!" Yace "I said kar ki fito plss kin ji, kwanta kiyi baccin ki," toh kawai tace ta koma ta kwanta ya mike ya fita ya kulle dakin, dakin Humainah ya shiga ya duba ya ga ba ta, ya jima tsaye kafin ya juya ya fita ya koma parlor, xaune ya ganta kusa da Mumy kamar xata shige jikinta, Mumy na kallonsa tace "Da ina ka tafi" ya buda ido yace "Na je kiranta ban ganta ba Mumy" Mumy ta dauke kai tace "Kaji da abinda kake kullawa, kawai mutum ya maida kansa munafuki, ya dauko wasu halayyen da ba nasa ba" murmushi Humainah tayi don abun ya bata dariya ta mike ta tafi kitchen don dauko ma Mumy drinks, shi kam kasa karasawa cikin parlon yayi don gani yake kamar ta gano sa ne, tana kallonsa strictly tace "What are you up to Ahmad?" Kamar zai mata kuka yace "Nothing mum, just xuwa aikin da bana yi kwana biyu ne naji daban" hararan shi kawai take yayi murmushi ya karaso cikin parlon ya xauna gefenta ya mata side hug yace "I miss you Mumy, har xaxxabin rashin ki fa nake" kallonsa kawai take ganin yanda ya rame idanuwansa suka fito, ya langwabar da kai yace "Mumy" tace "Baka cin abinci ne?" Girgixa mata kai yayi yace "Ina ci Mumy, kewar ki ne kawai" tace "Toh ku koma can gidan" wara ido yayi yace "Koh Mumy? Toh xa mu koma" a zahirin gaskiya kawai ya fadi haka ne don xancen ya wuce kuma gaba daya hankalinsa na kan Jasmine, Humainah na shigowa parlon da drinks ya mike yace "ina xuwa Mumy" daga haka ya haura sama, a hankali ya bude dakin ya ganta xaune a kasa, ya karasa da sauri yana kallonta ya durkusa yace "Me kike a nan?" A hankali tace "Ruwa xan sha" yace "Yi hakuri bari in kawo maki yanxu" mikewa yayi ya fita ya shiga nasa dakin ya dauko goran ruwa ya fito ya dawo dakin, da kansa ya bata ta sha, yace "Toh koma kan gado" ta mike ta koma gadon.
[1/14, 9:17 AM] Elhajj: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
52___53
Jasmine ta bude ido tana kallon El-ameen tace "Uncle ya tafi" El-ameen bai ce komai ba sai bin motar junaid da yayi da ido, can yayi murmushi ya kalli gate din gidansu sannan ya kalleta yace "Mu je" tafiya ya fara yi ta bi bayansa yana yi yana kallonta har suka iso titi, ya tsaida adai daita ya sa ta shiga sannan shi ma ya shiga, tara da 'Yan mintuna Mai adai daitan yayi parking bakin gate kamar yanda El-ameen ya umarce sa, fitowa yayi ita ma ta fito ya fiddo dari biyar ya mika masa sannan ya shiga gate din ta bi bayansa kamar xata yi kuka ganin inda suka dawo, junaid na tsaye balcony har suka iso, El-ameen ya kalli Jasmine da ta ki shiga parlon yace "Tafi ki kwanta gobe xan xo in tafi da ke"