Showing 126001 words to 129000 words out of 170905 words
Chapter 43 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
ido yayi yana kallonta, sosai ta basa dariya sai dai ya dake bai yi ba, kallon jikinta tayi tace "But..." Sai kuma tayi shiru, yace "But what?" A hankali tace "Ba kayan nan ne jikina ba" murmushi yayi yace "Yea, nurses ne suka canxa maki, you have being here for three dayz," kan ta ce komai ya mike da sauri ya dauko hijab dinta dake daki ya mika mata, karba tayi ya shimfida mata darduma tace "Idan na gama xa mu wuce koh?" Kai ya gyada mata, ta hau darduman ta tada sllh, kallonta kawai yake har ta idar, ta jima xaune kan darduman kafin ta mike ta dauke tana kallonsa tace "Na gama" mikewa yayi ya mika mata makullin motarsa yace "Go out, look for parking space and wait for me there" karba tayi ta fita, bayan kusan minti biyar ya bi bayanta, tsaye ya ganta a gun ya karasa ya karba makullin sannan ya nufi gun motarsa tana biye da shi, front seat ta bude ta shiga bayan ya tada motar, cikin minti sha biyar suka isa gidan junaid, kallonta yayi xai yi magana tace "Call him fast plss" buda ido yayi yace "No, we are going in" hade rai tayi tace "No ni baxan shiga ba," kallonta ya tsaya yi yace "Why?" Tace "I just can't, pls ni dai ka taimaka ka ban kudin transport in fita in nemi park idan naje gida in'sha Allah I am sending you back ur money, give me ur account number" xaro ido tayi tace "Ohh My phone??" Lokaci daya ya ji ransa ya baci, ya tsura mata ido yana kallo, how can she be this rude, who is she da xata dinga fadin kudi haka, cire glass din idonsa yayi yace "Amma hakan bai dace da ke ba Zahrah...." Wani kallo ta watsa masa tace "I just want to be home" bude motar yayi ya fice ya bar ta, bin sa tayi da kallo can ta bude motar ta fita ta bi bayansa, a hankali ya murda kofar parlon ya shiga, kwance ya ga junaid kan doguwar kujera idonsa lumshe, ya juya ya kalleta ya ga ita ma leko sa take, karasawa yayi parlon ta bi bayansa, dukawa yayi kusa da shi yana kallonsa, lokaci daya ya bude idonsa da ya kada yana kallonsa, El-ameen yace "Sleeping?" Bai jira cewarsa ba ya dafa kansa ya ji xafi, mikewa xaune junaid yayi ya rike kansa cikin sanyin murya yace "I regret everything frnd, you told me this from the very beginning, I..." El-ameen yace "Don't say that man, One never knows where his or her reward lies...." Girgixa kai junaid yayi xuciyarsa na bugawa yace "Allah am regretting" Zahrah da ke tsaye daga bakin kofa ta karaso cikin parlon kamar me tausayin kasa, kallonta El-ameen yayi don yasan junaid bai san tare suke ba, durkusawa tayi d'an nesa da su tana kallon Junaid, cikin sanyayyan muryarta tace "I..i am sorry!" Dago kai yayi da sauri yana kallonta, ta sunkuyar dai kai tace "Kayi hakuri, but you started it 1st" wani kallo ya jefa mata, ta turo baki ta mike tana kallon El-ameen tace "Is that all?" Murmushi El-ameen yayi yace "toh bai ji abinda kika ce ba" Kallon junaid tayi tace "I said am sorry" da kamar baxai ce komai ba, sai kuma ya mike yace "Sorry for ur self" daga haka ya nufi stairs, xaro ido tayi ta bi sa da kallo har ya haura sama, ta kalli El-ameen tace "You see! He's just rude" murmushi El-ameen yayi yace "And you too!" Tabe baki tayi tace "Dan Allah ka kai ni park xan gane hanya" kamar xata yi kuka ta kare maganar, El-ameen yace "Ohk, xauna ina xuwa" sama ya tafi, ta dinga bin parlon da kallo, babban hotonsa dake manne parlon yana sanye da uniform hannunsa rike da hula ta tsura ma ido, can ta karasa gun hoton tana kallo kamar me naxari, Tsaye El-ameen ya same junaid a daki yace "Look junaid Kaga dai ta baka hakuri, plss ka sa lokacin da xa ka kaita gida I will escort you" girgixa kai yayi yace "Ni babu inda xan je" hade rai El-ameen yayi yace "Stop this Malam, it's ur responsibility naga...." Xaunawa junaid yayi yace "Leave me plss Ahmad, am going no where, ka bar ni in fara tunanin yanda xan gyara duk abinda na bata a kan yarinyar nan, you can take her home frnd duk daya ne" tausayinsa El-ameen ya ji, bai kuma cewa komai ba ya juya ya fita, tsaye ya ganta bakin kofa ta wani hade rai, El-ameen bai kalleta ba ya fita ta bi bayansa, suna tafiya tace "baxai kai ni gidan ba koh?" El-ameen yace "Yess" tsaki tayi tace "Da na sani baxan xo basa hakurin bama" El-ameen bai tanka ta ba ya shiga mota ita ma ta shiga, sai da suka kama hanya sannan tace "Toh ina xa mu yanxu" bai kulata ba har ya iso gidansa, parking yayi ya fita ita ma ta fito a fusace tace "What's this please" da kamar baxai ce komai ba sai kuma ya kalleta yace "sai na shirya xan tafi dake ai koh? I have to fuel my car and put things in order, so dole sai na xo gida" tace "Ohk" cikin gidan ya nufa ta bi sa, Hafsat na kitchen jin shigowarsu parlor ta fito, Sannu da xuwa tayi masa ya amsa ya tafi sama, ta karasa kusa da Zahrah tana murmushi tace "Welcome Jewel" kallonta kawai Zahrah take irin kallon mamakin nan da yayi kama da na rainin hankali, still Hafsat tayi tana kallonta, El-ameen ya sauko yace "Hey, Meet my wife Hafsat!" Murmushi Zahrah tayi tace "Ohh sorry, it's nyc meeting you sis Hafsat!" Kasa cewa komai Hafsat tayi El-ameen yayi murmushi yace mata xa muyi waya anjima, daga haka ya fita Zahrah tace ma Hafsat sai anjima ta fita ita ma. Sai da suka dau hanya tace "Why was she staring at me that way?" Da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Coz you look new to her, and perhaps rude" xaro ido tayi tace "Did she know me before?" Gyada mata kai yayi yace "Yeah" tabe baki tayi ta maida kanta jikin kujera tace "I've never come across a being like her all my life" murmushi yayi ya kalli agogon hannunsa yaga daya da wani abu, yace "Kika ce bauchi koh?" Kai ta gyada masa yace "Where in bauchi?" Ta kada kai tace "Idan mun je xan gane hanya" bai kuma cewa komai ba ya dau wayarsa yayi dialing number Dad dinsa yana dagawa yace masa xai d'an je Kano wani aiki ya dawo, suna gama waya ya kira Ummi ma ya gaya mata haka, ajiye wayar yayi ya maida hankalinsa kan driving din da yake, ba su yi nisa da fara tafiya ba tace "Am Hungry!" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ke da baki cin abinci idan ba na gidan ku ba" tace "Ohh yes, soft drink kawai nake so yanxu" murmushi yayi yace "Toh shi daga gidan ku aka yo shi kenan" bata kuma ce masa komai ba, yayi parking ya fita wani shopping mall ya siyo mata drink da snack, karba tayi tace "Thank you" karfe hudu saura suka shigo Kano, ya kalleta yace "Where is this?" Bude hannu tayi alamar bata sani ba, yace "Kano!" Ana kiraye kirayen isha suka shigo bauchi, yace "kin san ina ne nan?" Gyada masa kai tayi yace "Toh mun yi sauri ko ba mu yi ba?" Hannu ta buda masa alamar bata sani ba, yace "Uhm to wani anguwa ku ke?" Tace "Kawai ka dinga tafiya xan dinga nuna maka" yace "Ohk"
*Haske Writers association*💡
[3/19, 9:36 PM] El-hajj💥: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
73.....
A bangaren Junaid kuwa suna barin gidan yayi kwanciyarsa, duk ya rasa me ke masa dadi, har magrib yana daki ga wani xaxxabi da yake ji, sllh yayi ya dau makullin motarsa ya fita, gida ya nufa duk jikinsa a sanyaye, he regret ever meeting her, he regret helping her, he regret all that have happened, parking yayi kofar gidan ya kasa fitowa, ya hade kansa da steering, ya kusa minti sha biyar kafin ya fito jiki ba kwari ya shiga compound din, tafiya yake kamar bai son yi don bai ma san me xai fara ce ma Mumynsa ba, bai san ta inda xai fara ba, why did all this happen to him? Shi kuma irin tasa kaddarar kenan, shafa kansa yayi ranan da ya fara ganin Zahrah ya fado masa, murmushin takaici yayi, yayi saurin kauda tunanin, ido hudu yayi da Hadiza da ke tsaye sakale da jakarta alamar tafiya xata yi ga nikab a hannunta, Umma da Hajiya ma na tsaye balcony din, suna hangosa Umma tayi mata alamar da ta shiga parlor, da sauri ta shiga ta kullo kofa, girgixa Kai yayi nufi balcony din, Umma da Hajiya aka kafa masa ido da mamaki don a tunanin su gaishesu xai xo yi, ko kallonsu bai yi ba ya bude kofar ya shige parlon, Hajiya ta xaro ido tace "Ikon Allah Meye haka Ahmad?" Hadiza dake tsaye parlon ta xaro ido ganinsa, bai yi wata wata ba ya fincikota ya kai mata naushi a baki, wani kara tayi Umma da Hajiya da tuni suka shigo parlon suka shiga salati suna tambayar yana da hankali kuwa, ko sauraransu bai yi ba ya fixgota ya fito da ita tsakar gidan, dukanta ya shiga yi yana ball da ita kamar an aikosa, ta dinga ihu tana cewa a taimaketa, tuni 'yan matan gidan suka fiffito, Mumy ma ta fito, su Hajjo da aka diro daxu ma aka fito, Hajiya da ko ina na jikinta rawa yake ta dinga jan Junaid murya can kasa tana cewa "In ma laifi tayi maka kayi hakuri Ahmad.... Ka rufa mata asiri" ko saurarenta bai yi ba bugunta kawai yake kamar an aikosa, a fusace Hajja ta karaso ta fixgoxa ta sauke masa mari tace "Don uwar ka Amina dama shirin tafiya gidan ka nake yanxu, ban taba tunanin cewar da mahaukaci Muhammadu xai hada jikata ba, ita Humainahr ka sakar min, tsabar haukan naka ya girmama har gida kake xuwa jibgan mutane yanxu" kokarin gudu Hadiza take ya wani fixgota ya kuma sauke mata mari, Abba ne ya shigo compound din daga masallaci, ya tsaya da mamaki yana kallon tsakar gidan, Junaid da ban da tafasa babu abinda xuciyarsa yake ya fara waige waigen inda xai ga Humainah, ganin bata compound din ya ja Hadiza har part din Mumy duk aka bi sa da ido ya shiga har parlor da ita, salati Umma ta dinga yi tana cewa anya Ahmad lafiyarsa kuwa, ku ceci 'yar mutane don Allah, fitowar Humainah kenan daga daki ya jefar mata da Hadiza nan gabanta yana kallonta sannan ya juya ya fice daga parlon, kallon mamaki Humainah ke mata, tuni duk aka shigo parlon, Abba kam dama part dinsa kawai ya nufa, Hadiza da ko ina na jikinta rawa yake ta mike da sauri xata fita, Humainah ta rikota tace "Me ya kawo ki nan?" Juyawa tayi tana waigen inda xata ga su Umma, Hajjo tace "Ina kika santa?" Hawaye ne ya cika idonta tace "Ita ta ja min komai, ni ban santa ba...." Hajjo tace "yo ni daxu tare muka shigo gidan nan da ita, ita ce ma ta shigo min da kayana daga adai daita kuma tace min Ita 'yar wan Bilki ce, me ta maki?" Kuka sosai Humainah ta fara ta durkushe gun tace "Ita ce silar komai, ita ke xuwa gidana kullum...." Salati Hajja ta saki tace "Ita ta sa ya sake ki kenan?" Humainah ta gyada kai hawaye na sauko mata, Hajja ta cakumo Hadiza tace "Ni dama nasan ba yin kan jikana bane wannan, nasan baxai aikata haka a banxa ba, to ko ki fadi wanda ke tura ki gidan ta ko in xuba maki fetur yanxu in babbakaki" juyawa Umma tayi ta fice daga parlon Hajiya ta bi bayanta da sauri, Hajja ta kwada mata mari tace "Baxa kiyi magana ba" Mumy da duk jikinta yayi sanyi ta karaso tace "Ki yi hakuri Hajja ki sake ta...." Wani kallo Hajja ta watsa mata tace "Ke ja can dalla" shaketa Hajja ta yi tace "Baxa kiyi magana ba?" Hadiza ta fashe da kuka tace "Ni Umma ce da Hajiya suke tura ni" salati Hajja ta saki tace "Suke tura ki kije kiyi me?" Shiru Hadiza tayi Hajja ta ja ta xuwa gun tv tana neman wayar wuta tace "Toh xa ki ga ikon Allah idan ba ki bude baki kin ban labari ba" juyawa Humainah tayi hawaye na bin kuncinta ta koma daki, Hadiza da tayi mugun tsorata jikinta na rawa tana hawaye tace "Wllh tura ni suke in je in dinga xugata" Hajja ta saketa tana tafa hannu tace "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, dama su suka kashe ma jikata aure, to su ma na su na rawa yanxu, ina Muhammadu" daga haka ta fice daga parlon kamar xata tashi, jigum Mumy tayi tana kallon Hadiza dake ta waige waige kamar munafuka, can kuma ta fice da gudu daga parlon. Tafiya kawai El-ameen ke yi a hankali, haka kawai gabansa ke faduwa ganin anguwar da ta nuna masa wai nan xa su bi, tafiya me nisa suka yi tace "Here!" Juyawa yayi da sauri yana kallonta yace "Where?" Nuna masa babban entrance din tayi tana bin ko ina da kallo ganin canji da dama tace "there!" Kasa daina kallonta yayi tace "Just horn, sai ka sauke glass xan masu magana" girgixa kai yayi yace "Wai gidan sarautan nan?" Kallonsa ta tsaya yi kafin tace "Eh gidanmu ne!" Dauke kai yayi can ya juyo yace "Kina nufin ur father is a king?" Bude motar ta shiga kokarin yi tace "Yeah my father is a king" danna horn yayi kamar yanda tace har lokacin idonsa na kanta, ita ko sai kalle kalle take fuskarta dauke da mamaki ganin changes da dama, wasu dogarai ne suka fito suna kallon motar, karasowa suka yi ta sauke glass tana kallonsu, ganin bata gane ko daya daga cikinsu ba ta bude motar ta fito tace "Ku bude mana hanya" daya daga cikinsu yace "Daga ina?" Fitowa El-ameen yayi yace "Baki daga katsina" bude masu hanyar aka yi, ya koma mota ita ma haka, ya ja motar ya shiga ciki, tafiya mai tsayi suka yi kafin su kai wani gate, kallon El-ameen tayi kamar xata yi magana sai kuma ta fasa, wasu guards suka karaso gun motar, sauke glass tayi daya daga cikinsu yace "Daga ina?" kallonsa kawai take don shi ma bata san sa ba, toh yaushe aka canxa guards din bakin gate kuma, a takaice tace "Bude mana gate" El-ameen yace "Sorry, baki daga katsina, mai martaba na sane da xuwan mu" komawa yayi aka bude gate din ya ja motar xuwa babban haraban palace din, juyowa tayi da sauri ta kallesa tace "Everywhere looks strange" kashe motar yayi yace "How strange" a hankali tace "Naga changes da yawa ne"
*Haske Writers association*💡
[3/19, 9:36 PM] El-hajj💥: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
74.....
Bude motar tayi ta sauka, shi ma ya sauko, har ta nufi kofar shiga fada sai kuma ta juyo tana kallonsa tace "Ni xan bi ta baya, may be Abbana na tare da baki, you follow there" girgixa kai yayi yace "No i will wait out here" tabe baki tayi ta juya ta dau wata hanyar daban ya bi ta da ido har ta bace masa, ajiyar xuciya ya sauke ya koma can inda wasu bishiya ke a jere ya ja daya daga fararen kujerun dake gun ya xauna, wayarsa ya ciro ya shiga kiran layin Junaid, bugu uku ya daga, El-ameen yace "Amm muna bauchi Man" Junaid dake xaune laptop gabansa yace "Ohk, it's good" Shiru El-ameen yayi kafin yace "Guess what frnd?" ajiye laptop din yyi a gefensa yace "Not in the mood" Murmushi El-ameen yayi yace "Ohk Gudnyt" katse wayar junaid ya jefar da wayar hannunsa ya mike ya fice daga dakin. A hankali Zahrah ta tura kofar ta shiga babban parlon da nan ne masaukin manyan baki a fadan, bbu kowa parlon, ta dinga bin parlon da kallo ganin shi ma ya canxa mata, hanyar da xai sada ta da bangaren Ummanta ta nufa da sauri, lokaci daya taji gabanta na faduwa, jakadiyar Umma ce mutum ta farko da ta fara haduwa da a hanya, wara manyan idonta tayi ta karasa da sauri tace "Baaba na dawo, ina ummana, ina su Ummi.....!" Wani kara jakadiyar tayi a gigice ta saki kayan hannunta ta juya da gudu ta bar gun tana salati, still Zahrah tayi ta bi ta da kallon mamaki, kan kace me sai ga ma'aikatan fadan sun bubbullo jin ihun jakadiya, sai dai duk wanda yayi tozali da ita sai ya bar gun a guje, duk ko ina ya hargitse, ita dai tana tsaye kamar warce aka dasa a gun cike da mamaki, a hankali ta shiga bin jikinta da kallo ko wani abu ne jikin nata, bata gama recover ba sai da yayanta ya shigo parlon taga yana mata wani kallo, da sauri ta nufesa ta ga ya juya ya bar gun, sosai jikinta yayi sanyi ta ji kafafuwanta sun kasa daukarta, Umma ce ta fito da stepmum dinta, sai dai ga mugun mamakinta sai gani tayi ita duk sun yi still a position dinsu suna kallonta ko kiftawa babu, Ummi ce ta shigo ita ma suna ido hudu ta fasa wani kara a rikice ta juya da gudu ta bar gun, juyawa Zahrah tayi da sauri hawaye cike idonta ta fita da gudu, a hankali Umma ta sulale gun ta fadi kasa a sume, rikicewa jakadiyar ta da sauran ma'aikatan dake gun suka yi suka yo kanta, Zahrah na fita dama inda ta hango El-ameen ta nufa tana isa gunsa ta xube gun ta fashe da kuka sosai tace "Why is everybody running away from me, mene a jikina da suke gudu plss tell