Showing 156001 words to 159000 words out of 170905 words

Chapter 53 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

672

kowa ba, El-ameen na fitowa ya shiga toilet din shima, wani kaya irin ta sarauta lafiyayye El-ameen ya ajiye masa gefen gado bayan ya fito yace "Wai kayan da xaka sa kenan suka ce" Junaid da har lokacin bai iya hada ido da abokin nasa ya shiga jujjuya kayan, can ya mike ya tabe baki yace "No, bai yi min ba" dariya sosai El-ameen yayi su Aliyu na tayasa wanda hakan yayi mugun kona ran Junaid, Aliyu yace "Ae ko ka ki malam dole haka xaka sa, coz that's the rule tunda gidan sarauta kayi auren" sai a snn Junaid ya kalli El-ameen ya hade rai sosai yace "Nooo, bbu wanda xae dinga kafa min rule, snn bbu wanda ya isa yyi forcing dina...." Aliyu ya fashe da dariya yace "Duk karya ce wnn" El-ameen da ya kasa daina dariya yace "See you. Ka dinga bin rules kenan har sai an kai maka matar ka can gidan ka" Junaid bai tanka sa ba xai dau kayansa ya sa El-ameen ya kwace kayan yace "Kasan Allah kar fa ka dinga mana taurin kai nan" faisal yace "Look Capt you just have to obey before complaining as a good militant, idan ka bar nan naga bbu wanda xai bi ka yace ga yanda xaka yi koh?" Daukan kayan Junaid yayi ya fita parlor don sa wa, Aliyu ya fashe da dariya yace "Wato abun sai da lallaba," ko da Junaid ya dawo dakin duk kallonsa suka tsaya yi don sak yarima ya dawo, yayi kyau ba kadan ba, Aliyu yace "Uhm yarima junaid, ka hadu" junaid bai tanka sa ba, misalin karfe tara da wani abu aka doka sallama can parlor El-ameen ya fita, wata yar dattijuwa ce tsaye ta duka har kasa ta gaishesa tace "Ance in yi ma ango iso har gun Gimbiya Zahrah" El-ameen ya juya ya koma daki yace "Toh an xo daukar ka Capt, if you like go nd misbehave mu dai muna nan" sae da junaid ya ga dama sannan ya mike ya fita, dattijuwar na gaba yana biye da ita a baya, haka kawai yaji gabansa ke faduwa, tafiya me nisa suka yi har suka iso wani babban kofa ta bude kofar suka shiga wani parlor me girman gaske xama yayi parlon ita kuma ta karasa ta bude wani kofa ta shiga ciki, ba a dau lokaci ba ta fito ta risina tace "xaka iya shiga ranka shi dade" mikewa yayi ya nufi dakin har lokacin gabansa bai bar faduwa ba, yana shiga dakin wani sanyayyen kamshi ya doki hancinsa bai san lokacin da ya rufe kofar ba ya juyo ya sauke idonsa kanta.

*Haske Writers association*๐Ÿ’ก
[3/19, 9:36 PM] El-hajj๐Ÿ’ฅ: โš“ *Captain Ahmad Junaid*โš“

_By Khaleesat Haiydar_โœ๐Ÿป

84.....
Washegari ba karamin farin ciki junaid yayi ba ta dalilin lagos da xasu wani aiki da wasu daga cikin colleagues dinsa, kwana biyar xa su yi a can, yana dawowa da yamma ya jima part dinsa kwance kafin ya mike ya tafi gun Mumy tana kitchen ya sameta ya jingina jikin kofa bayan ya gaisheta yace "Mumy gobe xan je lagos aiki..." Kallonsa tayi tace "lagos?" Ya gyada mata kai yace "Ehh amma ba ni kadai ba, kwana biyar xuwa sati daya xa muyi" Mumy tace "Toh Allah ya tsare, ka fadi ma Abban ku?" Girgixa kai yayi yace "Anjima xan gaya masa" Tace "Toh shikenan, gobe Hajja ma xata dawo" yace "Ohk, ni da safe xan tafi ba lallai mu hadu ba" juyawa yayi ya fita daga kitchen din, har ya nufi kofa sai kuma ya dawo ya shiga dakin su fatima. Kasa bacci yayi daren ranan, sarai yasan me ke damun xuciyarsa amma ya dinga kokarin karyata hakan, tsaki ya ja daga karshe ya mike ya shiga toilet ya dauro alwala ya fita. Da safe ya gama shirinsa tsaf, kananun kaya kawai ya diba sai uniforms dinsa, ya nufi part din Mumy yayi mata sallama, tayi masa addu'ar Allah ya kai su lafiya ya tsare su, ya mike ya shiga bedroom din da Humainah take, bai fi 7 minutes ba ya fito ya dau jakarsa ya fita daga parlon, khadija ce ta rakasa har bakin gate bayan ta karbi jakarsa don driver din Abba ne xai tafi da shi gun aiki daga can sun wuce lagos, karban jakar yayi yana kallonta kmr baxae ce komai ba sai kuma yace "Su Hajiya fa?" Shiru tayi tana kallonsa, ya bude mota yace "Alryt, sai mun yi waya lil sis bye!" D'aga masa hannu tayi har motar ya bar layin. Da yamma junaid suka sauka lagos, Apartment din abokinsa Capt kabir ya sauka a barrack dinsu, wanka kawai yayi ya sauya uniform din jikinsa ya dau makullin motar kabir bbu yanda kabir bai yi da shi ya ci abinci ba ya ki, ya fita da mota duk da bbu takamaiman inda za shi, damuwa ne kawai yayi masa yawa, bai dawo gidan ba sai bayan magrib, Kabir dake xaune parlor da wasu abokansa biyu ya bisa da kallo don hannu kawai ya daga masu ya shiga bedroom, mikewa Kabir yayi ya bi bayansa, kwance ya samesa dakin yana kallonsa yace "Are you okay junaid?" Junaid yace "Yeah, just stress sai slight headache" kahir yace "Alryt Allah ya sauke, ga abinci na siyo ka ci ka sha Magani" junaid yace "Na ci abinci, drugs kuma ba sai na sha ba, idan nayi bacci xai min sauki" kabir yace "Toh shkkn" daga haka ya juya ya fita. Washegari da ciwon kai sosai junaid ya tashi, ko Kabir bai bari ya kula da halin da yake ciki ba, ya shirya cikin uniform dinsa ya daure ya sha tea kadan, Kabir yace "Ga makullin bike, don in ka fita da mota yanxu da matsala" junaid ya karbi makullin yace "No hold up No Lagos" dariya Kabir yayi yace "Exactly!" Junaid yace "Baka duty da safe ne?" Kabir yace "Yea, sai evening" Junaid yayi murmushi yace "Jin dadi" daga haka ya nufi kofa ya fita. Gaba daya a harbor ranan junaid was just absentminded, ga ciwon kansa sai karuwa yake duk ya kagu karfe hudu yayi ya gansa a gida. Biyar saura ya isa gida ko uniform bai cire ba ya haye gado dai dai lokacin da wayarsa ya dau ruri, jawo wayar yayi da kyar yana kallon screen din da kamar ya ajiye sai kuma ya daga ya kai kunne, El-ameen yace "Ashe kana lag!" Junaid yace "Yeah...." El-ameen yace "Shine bbu notice, beside you know it's not possible bikina ace baka nan, haka ka kin wnn wlkcnin lokacin da aka aura min Hafsat....." Katse sa junaid yayi yace "I will be back on Friday!" El-ameen yace "Uhm, now you are talking, har na kai mana dinki...." Lumshe ido junaid yayi trying to be calm yace "Alryt, but am busy yanxu, I want to hang up...." El-ameen yace "Ohk.... Xan kira anjima in fadi maka decision din da muka yanke da su Aliyu, i.e how everything is gonna be" Gyada masa kai kawai Junaid ya iya yi ya katse kiran ya jefar da wayar nan kan gado yayi rub da ciki ya runtse ido. A kwana biyun da junaid yayi a Lagos kowa ya gansa yasan ba karamin abu bane ke damunsa, duk ya rame ga shi ko abinci bai iya ci, bbu yanda Kabir bai yi da shi ya fadi me ke damunsa ba sai dai yace zazzabi ne, ranan laraba ikon Allah kadai ya maidosa gida daga gun aiki, Kabir dake ta shirin fita aiki ya bi sa da kallo har ya shiga daki sannan ya bisa yace "Kaga kar ma ka fara kwanciya ka taso mu tafi asibiti or I call ur mum in gaya mata" junaid bai yi masa musu ba don shi daya yasan yanda yake ji a lokacin, Kabir bai bari ya cire uniform ba suka fita xuwa NNRH dake nan barrack din, bayan sun ga likita aka yi admitting dinsa nan take, malt kawai ya iya sha a cikin abubuwan da Kabir ya siyo masa bayan an sa masa ruwa, ya kalli Kabir dake tsaye yana kallonsa yace "Don't worry frnd ka tafi aiki I will be ohk, bacci ma xan yi yanxu" sai da Kabir ya ga baccin xai yi da gaske sannan ya dau makullinsa ya fita. Washegari da safe junaid na bacci Kabir ya shigo ward din, yaga sabon ruwa ne ma aka sa masa, xaunawa yayi gefensa dai dai lokacin da wayar Junaid dake kan gadon yayi haske ta dalilin kiransa da aka yi don a cylnt wayar yake, My best ya gani jikin screen, da kamar baxae daga ba sai kuma ya dauka don yasan baxai wuce abokin da ya san sa da shi ba wato El-ameen, El-ameen na jin muryar Kabir bayan sun gaisa yace "Ahmad din fa?" Kabir yace "Ba ya jin dadi tun jiya, har ma anyi admitting dinsa clinic" El-ameen yace "Subhanallah! Ya jikin nasa yanxu?" Kabir yace "Alhmdllh, he's sleeping" El-ameen yace "Toh Allah ya sauwake, but a barrack din ku ya sauka?" Kabir yace "Yeah nan ya sauka" El-ameen yace "Alryt xan kira later" daga haka ya katse wayar, sai a sannan ya ga uban missed calls din dake wayar, ajiyewa yayi ya koma kujera ya xauna. Karfe uku junaid na xaune har lokacin da ruwa a hannunsa, shi ji yayi kamar ma kara masa ciwon ake, gashi ya kasa cin komai sai ruwa da yake sha, kabir da bai jima da shigowa ba yace "Ka dai kira gun aiki ka fadi dalilin absence dinka" kai kawai junaid ya iya daga masa, Kabir yace "Toh meyasa baka son a fadi ma su Mumy?" Shiru junaid yayi masa idonsa lumshe, kabir ya dau wayar Junaid din ta dalilin kiran da ya shigo, El-ameen ne ke kira ya kalli Junaid yace "Xa ka iya daukan kiran, it's ur frnd?" Junaid ya bude ido yana kallon wayar girgixa masa kai yayi, hakan yasa shi ya daga, bayan sun gaisa El-ameen yace "Wai jikin nasa har yanxu?" Kabir yace "Yea, muna hospital dai" El-ameen yace "Alryt! Clinic din cikin barracks din?" Kabir yace "Yeah Nnrh!" El-ameen yace "Toh Ga shi kayi ma security din ku na gate magana, I am at the gate" da mamaki Kabir yace "Kana Lagos ne dama?" El-ameen yace "Nop, I just landed" daga haka ya mika wayar, Kabir yayi masu magana sannan El-ameen ya shiga barrack din. Cikin mintunan da basu wuce 7 ba El-ameen ya isa hospital din snn ya kira Kabir ya fito ya shiga da shi, rungume hannu El-ameen yayi yana kallon Junaid can yace "Sannu, were you sick ne dama" Junaid ya kallesa yace "Am feeling much better yanxu" El-ameen yace "To ina drugs din da suka baka?" Kabir ne ya dauka ya mika masa yayi dariya yace "Kaddai ka xo ka nuna masu kai likita ne a nan fah, Kaga kai ba uniform gare ka ba" murmushi El-ameen yayi yace "Niii! Ae ko xan yi magana sai mun fita" dariya sosai kabir yayi, El-ameen ya ja kujera ya xauna yana kare ma ward din kallo, Junaid yace "Ya hanya!" Mamaki ne ya kama El-ameen ya kallesa yace "Ohh Alhmdllh! Yaushe xa su sallameka?" Girgixa kai yayi yace bai sani ba, El-ameen bai kuma cewa komai ba, ana yin La'asar Kabir ya bar clinic din don xuwa gun aiki, Washegari Friday da safe aka sallamesu daga hospital bayan ya tabbatar masu he's very okay, ko kadan El-ameen bai gaya masa ranan ne daurin aure ba duk da yasan ya sani, karfe tara ya shirya ya tafi can gun da suka xo yin aiki don shaida masu ranan xai koma kt, goma saura ya dawo ya tadda El-ameen kadai parlor yana waya, bedroom ya shiga ya hada kayansa ya fito, El-ameen da har ya gama wayar yace "Are we good to go?" Kai kawai Junaid ya gyada masa, yace "Toh baxa kuyi sallama da kabir din ba?" Junaid yace "mun yi waya da shi ya tafi ikj ba lallai xa mu hadu ba...." El-ameen yace "Ohk" daga haka ya mike ya karba jakar Junaid suka fita, junaid ya kulle masa apartment din ya ba neighbor dinsa key din, bike suka dauka xuwa airport road, bayan sun isa suka dau cab xuwa cikin airport din, El-ameen dai na ta lura da shi don ko ba a fadi masa ba yasan daurewa kawai yake, sai da suka hau jirgi Junaid ya dake yana kallonsa yace "Thought yau ne daurin auren?" El-ameen yace "Yeah! After juma'at prayer, xa ma ka iya xuwa kuwa" junaid yace "No!" Suna isa kt Junaid ya nufi gida shi ma El-ameen ya nufi nasa gidan. Part din Mumy junaid ya shiga ganin bbu kowa parlor sai tv dake kunne ya shiga dakin Mumy, xaune ya ganta a daki ya karaso ya durkusa ya gaisheta, bbu yabo bbu fallasa ta amsa tace "Ahmad ashe kai ka haifi kanka ban sani ba?" Kallonta yayi da mamaki jin abinda tace, tace "Leave immediately" kasa daina kallonta yayi lokaci daya yana tunanin me kuma yayi, da kyar yace "Mumy wani abun ya faru ne kuma?" Wani kallo ta watsa masa tace "Ka fita nace" mikewa yayi da kyar ya fita daga dakin, bedroom din su Humainah ya shiga, kwance take tana ganinsa ta mike xaune, ya karasa gadon jiki ba kwari ta mike tsaye, xai yi magana ta dakatar da shi tace "Ya Ahmad ni dai ka sake ni gaba daya bana auren kuma, idan kuma ba haka ba xan xubar da cikin nn wllh" kallonta kawai yake da manyan idonsa, can ya tabe baki ya juya ya fita daga dakin, ta fashe da kuka sosai ta sulale nan kasa ta hade kanta da gwiwa, tafiya kawai junaid yake yana son gane ma'anar abinda Mumy ta fadi masa, Muryar Hajja ne ya dakatar da shi jin irin kiran da take masa ba kakkautawa ya juya yana kallonta da mamaki, karasowa tayi fuskar nan nata a murtuke tace "Wato ai gwara kwadayina a kan taka Ahmad, tsabar naka kwadayin ya shahara 'yar gaba daya kake son aurewa kayi ma jikata kishiya, kishiyar ma jinin sarauta, dama ga Ka da taka sarautan da ka lak'a6a ma kanka tun ba yau ba, ita kuma ta xo da ta gidansu ku taru ku sa ma jikata hawan jini ta mutu in shiga uku, to ubanka yayi kadan bare kai, ban yarda da auren nan ba kuma baxa ayi ba, su rike kujerun jirginsu can baxa a je ba...."

*Haske writers association*๐Ÿ’กโš“ *Captain Ahmad Junaid*โš“

_By Khaleesat Haiydar_โœ๐Ÿป

87___88

Durkushe ya ganta a dakin tana kuka, tana ganinsa ta hadiye kukan ta hade rai sosai, hade rai shi ma yayi yace "Did you just say something?" Mikewa tayi tana masa wani kallo tace "We the royal blood don't say things twice...." Dariya sosai ta basa, sai dai ya dake bai yi ba ya Karasa gabanta yana kallonta, ko dar bata nuna ba duk da a tsorace take ganin yanda fuskarsa ke a daure, wani murmushi yyi yace "Mind you gidan Capt Ahmad ne nn ba so called royal home din ku ba" tabe baki tayi ta juya masa baya tace "I don't care where I am, I Still remain who I am..." kallonta ya shiga yi daga sama har kasa can ya gyada kai yana murmushi ya juya ya fita. Da rana El-ameen ya xo gidan, suna xaune parlor da Junaid ganin bai ga Zahrah ba sai Humainah dake kitchen, yace "Captain rowar ganin amaryar ake min" Junaid ya mike yace "Noo Not at all..." Daga haka ya haura sama ya tura kofar bedroom dinta, xaune ya sameta tana ganinsa tayi saurin goge hawayen fuskarta ta dauke kai, daga nn bakin kofa yace "ki fito ku gaisa da El-ameen.... Miss Royal being" wani kallo ta masa sai kuma ta mike ta dau hijab ta saka tayi ficewarta daga dakin ta bar sa tsaye, da murmushi fuskarta suka gaisa da El-ameen sai dai bata yrda sun hada ido ba, El-ameen na ganinta yasan kuka tayi, kallon Junaid da ya tsiri danna waya yyi sai dai bai ce komai ba, ita kuma ta mike, da har xata koma sama sai kuma ta nufi kitchen, Humainah dake hada stew ta kalleta ta dauke kai ta dalilin faduwa da gabanta yayi, Zahrah ta dake tace "Sannu da aiki" Humainah tace "Yauwa, thanks" kallon kayan lambun dake ajiye kitchen din Zahrah tayi ta karasa ta dauka ta nufi washing basin ta shiga wanke su, ita dai Humainah bata ce komai ba sai satan kallonta take, har ta gama wanke su ta dauki chopping board da wuka ta shiga yankasu, bayan kusan minti goma Zahrah tace "Ki ara min wayar ki" Humainah tace "Yana daki" har suka gama aikin bbu wanda ya sake cewa komai, ko da Zahrah ta dawo parlor bata ga El-ameen ba alamar ya wuce, sama ta nufa Junaid ya bi ta da kallo don yyi mamakin kitchen da ta shiga, can Humainah ma ta fito ta nufi sama ita ma ya bi ta da ido can ya mike ya bi bayanta, Zahrah na haura wa sama dakin da tasan na Humainah ne ta bude ta shiga, can kan gado ta ga wayar ta dauka ta xauna gefen gado, Humainah ta shigo dakin, sosai tayi mamakin ganinta xaune dakin, bata ce komai ba ta tafi gaban mirror, Bude kofar aka yi Junaid ma ya shigo, still yyi bakin kofa yana kallon Zahrah, kallo daya tayi masa ta dauke kai, ta mika ma Humainah wayar tace "bude min pattern" Humainah ta karba Junaid ya fixge wayar hannunta yana kallon Zahrah yace "Wa xa ki kira?" Ba tare da ta damu ba tace "Abbana" juyawa yayi ya fice da wayar, tabe baki tayi ta kalli Humainah ta mike ta nufi kofa, Humainah ta bi ta da kallo har ta fita ta juyo tace "Idan kin xuba abinci ki kira ni, we don't eat alone at home" daga haka ta fita, mamakinta sosai Humainah ta dinga yi, tana xuba abincin kuwa ta dawo sama ta bude kofar dakinta ta kirata, mikewa Zahrah tayi ta fito suka sauka kasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login