Showing 159001 words to 162000 words out of 170905 words

Chapter 54 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

642

a tare, nan kan carpet Humainah ta ajiye masu abincin, Zahrah ta xauna ta tankwashe kafa ta dau spoon ta fara cin abincin, xaunawa Humainah tayi ita ma ta dau cokalin ba tare da ta kalleta ba ta shiga cin abincin, Zahrah ta d'an kalleta tace "How month pregnant are you?" Kallon mamaki Humainah tayi mata da kmr baxata tanka ta ba sai kuma tace "five" Zahrah ta langwabar da Kai tace "Ohk.... But me yasa mijin ki yake behaving yanda yake yi?" Humainah bata kalleta ba bare ta sa ran amsa, aka bude kofar parlorn Junaid ya shigo don dama yana waje, kallon mamaki yake masu can ya karaso parlon ya xauna yana kallon Humainah yace "Did you cook with me" kan tace komai Zahrah ta amshe tace "Of course No, not with her condition, just go get something outside to take!" Kallon Zahrah kawai yake can ya mike ya nufi stairs sai a snn yayi murmushi ya haura sama. Da daddare Zahrah na fitowa daga wanka ta xauna gaban mirror don yi shafe shafenta aka bude kofar dakin, duk da ynda gabanta ya fadi hakan bai sa ta juyo ba sai shafa lotion dinta take, tsaye yyi bakin kofar yana kallonta, ta gama shafanta ta mike ta nufi kan gado don daukar sleeping wear dinta, bin ta yyi da ido har ta dau kayan, ganin cire towel din xata yi yasa shi juyawa ya fice daga dakin ya rufo, murmushi tayi a xuciyarta tace you should have stay, tana gama shirya wa ta fito ta shiga dakin Humainah, Humainah dake kwance don ta gaji bayan dinner da ta girka ta bi ta da kallo, kwata kwata ta ki sakewa da ita, Zahrah ta xauna kan gadon ta dau remote tace "I hate staying alone... We don't do that at home" powering din Tv tayi ita dai Humainah bata ce mata komai ba. Daga karshe rufe ido ma tayi kmr ta fara bacci, xaman kusan minti talatin Zahrah tayi can tayi kwanciyarta kan gadon, bude ido Humainah tayi da sauri tana kallonta, ta gyada kai tace "Yeah, I am spending the nyt here" Humainah bata ce komai ba ta rufe idonta kuma, Zahrah ta gyara kwanciyarta ta ja duvet ta ci gaba da kallonta, bude kofar dakin aka yi Junaid ya shigo, ya buda ido yana kallon Zahrah, ko kallonsa bata yi ba idonta na kan tv, Humainah dai tayi kmr bacci take, juyawa yyi kawai ya fita daga dakin. Washegari da asuba Humainah ce ta fara tashi ta tada ta, sllh tayi ta fita ta bar ta dakin ta tafi kitchen, tana fita Junaid ya shigo, ya hade rai yana kallon Zahrah da ke kan darduma yace "Me ya shigo dake dakin matata, don ki koya mata girman Kai da unnecessary Royalism din ki koh?" Bata ko kallesa ba bare ya sa ran samun amsa, sosai hakan ya kona masa rai ya daka mata tsawa yace "Ba magana nake maki ba kika kyaleni" nn ma dai ko kallon gefen da yake bata yi ba, juyawa yyi ya fice daga dakin xuciyarsa na tafasa, sai a snn ta kalli bakin kofar ta gefen ido ta mike, ita ma ta fita ta shiga bedroom dinta tayi wanka ta shirya cikin wani lace mara nauyi da ya amsheta sosai, gyara dogon gashinta tayi ta daure a baya ta bar dankwalin a kafada ta sauka, ba wani aiki ta taya Humainah ba sai tambayoyi da ta isheta da shi kmr yar jarida, Humainah ta jera komai kan dining Zahrah ta xauna tana kkrin daukan cup tace "Yanxu sai ki je kiyi wanka kiyi kwalliya wa mijin ki..." Humainah bata ko kalleta ba ta wuce sama, tana tafiya sai ga junaid ya sauko cikin shirin Uniform, har ya karaso dining din idonsa na kanta, shayin ta kawai take sha, ya ja kujera ya xauna ya hade rai yace "A royal Home din ku ba'a koya maki gaisuwa ba ne koh" bata dago kai ba bare ta tanka sa sosai haka ya kona masa rai, sai a snn yasan ashe shariya na da ciwo, wani tsawa ya mata yace "Kee!" Dago manyan idonta tayi ta hade rai tana kallonsa can ta mike ta kwabar da cup din tean hannunta ta nufi sama kmr xata tashi sama, bin ta da kallo yyi baki bude, tunda yake shi mace bata taba yi masa haka ba, fasa breakfast din ma yyi gaba daya ya koma sama ya dau wayarsa da car key ya bar gidan. Sai wajen biyar ya dawo gida har lokacin ransa ba dadi, xaune suke parlor tana gyara Humainah gashi, ya wani hade rai yace "Duk ku bar parlon nn Immediately" ba tare da Zahrah ta kallesa ba tana ci gaba da combing gashin Humainah tace "And may we know y?" Karasawa parlon yyi cikin tsawa yace "ku bar min parlor nace" Zahrah ta yatsine fuska ta kwashi kayan gyaran gashin tace "it doesn't call for shouting! Maman baby tashi mu je" Humainah ta tabe baki ta tafi sama, Zahrah ta bi bayanta, xaunawa yyi kan kujera yana tunanin hukuncin da xai dauka kan Zahrah bai taba tunanin shariya da daukan kai na da ciwo ba sai ynxu, ranan ma tare Zahrah ta kwana da Humainah, shi dai bai ce masu komai ba, washegari ya gama shirin fita aiki ya sauko downstairs ya samesu tare suna breakfast, yana kallon Zahrah yace "Royal being, har yanxu bayin na ki basu iso bane ko dama kawai fadi aka yi" ko kallon inda yake bata yi bare ta tanka sai cin potatoe da ketchup dinta take, tsaye yyi yana kallonta, can yace "I can see you are deaf..." mikewa tayi irin ya takurata din nn a fusace ta yi hanyar stairs, bin ta yyi ya fixgota ya hadata da jikinsa kan yace komai cike da tsiwa tace "Me yasa ka fiye takura ne Mr man, get away from my life, i hate disturbance, I don't want...." Bai bari ta kai karshe ba sai jin kiss tayi, Humainah dake kallonsu dama dauke kai tayi ta ci gaba da jujjuya potatoe din gabanta, turata yayi yana mata wani kallo sai kuma ya juya ya nufi kofa da sauri, bin sa da kallo tayi a tsorace, can ta saci kallon Humainah sai kuma ta tafi sama da sauri, Junaid ya kusa minti goma xaune cikin motar kafin ya tada motar ya bar gidan. Har rana Zahrah bata fito ba, wajajen Karfe uku ganin ta fara jin yunwa ta fito daga dakin, bbu kowa parlon ta shiga kitchen ta hada tea ta fito ta dawo sama dai dai lokacin da Humainah ta fito daga dakinta, har Zahrah xata mata magana sai taga ta wani hade rai kmr bata ganta ba ta sauka kasa, Zahrah ta juya ido hade da tabe baki ta shige dakin ta. Da yamma kusan a tare Junaid ya shigo gidan da Hajja, ya wani hade rai ganinta, ita din ma ko amsa gaisuwarsa bata yi ba ta shige parlor tana kwala ma Humainah kira, Humainah dake kwance daki ta fito da sauri jin muryar Hajja, rungumeta tayi cike da jin ddin ganinta, Hajja ta turata tana kallonta daga sama har kasa tace "Ramar meye wnn Humainah, daina baki abinci yyi don yyi aure ko yaya?" Humainah tayi 'yar dariya tace "Ni ba Ramar da nayi Hajja" Hajja ta kalli sama murya can kasa tace "Yar sarkin na sama koh?" Humainah ta gyada mata kai kawai, Hajja ta tabe baki tace "Xata ci ubanta, ko da kuwa shugaban kasa ne uban nata...." Shigowar Junaid ya sa tayi shiru ta balla masa harara, dai dai lokacin da Zahrah ta sauko jin muryar Hajja, hajja ta tsuke fuska sosai, daga inda take tsaye ta gaida ta Hajja ta saki salati tana tafe hannu tace "Yanxu 'yar nn kya gaida Uwar da ta haifi uwar ki a tsaye?" Kallonta kawae Zahrah take, Hajja tace "Toh wnn ba dab'iar arxiki bane, don da Humainah ce ko kaffara baxan yi ba baxa ta yi haka ba, ba fa masarauta kike ba yanxu!" Wani kallo junaid yake ma Hajja don ji yyi kmr ya shaketa, Zahrah ta juya ta koma sama, bin bayanta yayi Hajja tace "Munafuki, hbayaala har ta fara girki ta basa yaci ne?" Humainah dai bata ce komai ba Hajja ta ce "Toh shi ma xae ci uban nasa ne" tsaye Junaid ya ganta gaban mirror, da kmr baxae karasa ba sai kuma ya karasa kusa datace ita, juyo da ita yyi yana kallonta yace "Me yasa kika gaisheta a tsaye!" Bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, tambayar ya kuma maimaitawa nn ma dai shiru kke ji, a fusace yace "Don me xan dinga maki magana kina share ni" ga mamakinsa har lkcn bata kalli inda yake ba, ya fixgota yace "Wllh na sake maki magana kika share ni I will..." kallon mamaki yake mata ganin bama ta da niyar kallonsa, can ya juya fita. Har dare Hajja bata bar gidan ba tana dakin Humainah, Junaid ya samu Humainah dake kitchen tana xuba ma Hajja abinci yace "Zahrah ta ci abincin?" Bata kallesa ba tace "I don't know!" Ficewa yayi daga kitchen din ya koma sama ya shiga dakinta, xaune ya sameta ya karasa kusa da ita yana kallonta kana ganinta kasan tayi kuka, bai san lokacin da ya durkusa gabanta ba ya kamo hannunta yace "Zahrah!" Kallonsa tayi bata ce komai ba, ya matsa hannunta a hankali, sauke idonta tayi kasa, can underneath his breathe yace "My arrogant princess!" Bata dago ba bare tace komai ba, ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Meye amfanin miskilanci da girman kai Jasmine!"

*Haske writers association*💡

_Mata-Maza ce Khaleesat Haiydar ba namiji ba_😎⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

89.....

Zahrah ta kalli cikin idonsa tace "Who's Jasmine?" A hankali yace "You!" Dauke kai tayi ya mike ya dawo gefenta ya xauna yace "Baki bani amsar tambayata ba" shiru tayi bata ce komai ba, matse mata hannu yyi ta wurga masa wani kallo tace "Stop that" yyi d'an murmushi yace "Nasan abinda zan maki ki sauke girman kan nn naki...." Fixge hannunta tayi ta mike ta nufi toilet tace "You can't change who I am, beside you are more arrogant" daga haka ta shige toilet ta rufe, mikewa yyi ya fita daga dakin yana murmushi har lkcn, sai bayan ya fita ya dinga mamakin kansa, then what just came over him, karfe goma saura Zahrah ta shirya cikin kayan bacci ta fita daga dakinta, dakin Humainah ta tura ta shiga, suna xaune kasa ta gansu, Humainah ta daura kanta kan kafar Hajja, magana suke amma suna ganinta suka yi shiru, ko a jikinta ta karasa ta xauna gefen gado ta kalli hajja tace "Sannu da hutawa!" A dakile Hajja tace "Yauwa!" Daga nn Zahrah ta maida dubanta kan tv, Hajja ta kalli Humainah kmr xata yi magana sai kuma tayi shiru ta kyabe baki, Humainah ta d'an kalli Zahrah tace "Abincin ki downstairs" ba tare da Zahrah ta kalleta ba tace "Am not hungry" Hajja ta galla ma Humainah harara ta hade rai, har kusan sha daya Zahrah na dakin ita dai bata ce masu ba suma haka, tun da ta shigo kuma sun ki yin hirar da suke, can dai ta kalli Hajja tace "Sai da safe" da sauri Hajja tace "Ehh Allah ba mu alkhairi" ba sai Hajja ta ga tana kkrin kwanciya kan gado ba, ta yo waje da ido tace "Mai xan gani haka?" Humainah da ta danne dariyar da ya kusa taho mata tace "Nan xata kwanta mana" Zahrah ta kalli Hajja tace "Bacci xan yi a nn" Hajja ta wage baki tana mata kallon mamaki can dai tace "Su wa kika bar ma dakin naki ne" Zahrah tace "A nn nake kwana" Hajja ta kalli Humainah tace "Wai?" Humainah ts gyada mata kai, Zahrah ko tayi kwanciyarta, can dai Hajja ta rufe baki tace "Wai tun da aka kawo ta nn take kwanan maki?" Humainah tace "Uhm" Hajja tace "Tabdi, toh me salubabben yace?" Humainah tayi yar dariya tace "Ba ruwansa" Hajja tace "Toh Allah ya sauwake maku gaba daya" tuni Zahrah ta ja bargo, Hajja da ta kasa daina mamaki tace "Wai meye haka nake gani, to ni ina xan kwanta?" Humainah tace "Ki tafi dakinsa ku kwanta" dai dai nn Junaid ya shigo dakin, yayi mamakin ganin Zahrah kwance dakin, Hajja tace "Yanda yake wawa haka ya samo mata duk wawaye, banda haka ni ko a tarihi ban taba jin kalan abinda nake gani a dakin nn ba, toh shigowa Kayi Kai ma ka kwanta a tsakiyarsu ko ko?" Mikewa Humainah tayi ta dinga dariya, Junaid dai sai kallonta yake don har ya mance rabon da ya ga tana dariya haka, dauke kai yyi yana murmushi can dai ya kalli Hajja yace "Toh yau kinga hakan a gidan Ahmad Junaid" wani kallo ta wurga masa tace "Yi man shiru, gantalalle har kullum wautan yan fari ba cika ka xai yi ba, dama Kai kace ta dinga xuwa kwana nn?" Junaid ya kalli Humainah yace "You leave the room for them nd come to my room" daga haka ya juya ya fita, a fusace Hajja tace "Ka xagi Muhammadu wllh, ke kuma uwar me yace?" Humainah tayi murmushi tace "Yace kije dakinsa ki kwanta" duka take shirin kai mata ta mike da sauri ta fita daga dakin, daga nn bata sake ganin Humainah ba tayi jiran tayi jiran har ta gaji, kwafa Hajja tayi tace "Lallai yaran nn, dakin mijinta ta tafi ashe" kallon Zahrah da tayi bacci tuni kan gado tayi, sai kuma ta fara mamaki, taga dai ko kwana hudu ba ayi da tarewarta tabe baki tayi ganin ta kasa gano komai ta mike ta dau bargo ta shimfida a kasa da pillow, can misalin biyu Zahrah ta farka mikewa xaune tayi ita kadai ce kan gadon, can ta kalli Hajja dake ta sharar bacci a kasa, sauke kafafuwanta kasa tayi ta mike ta xaga inda take ta durkusa ta shiga tada ta, bude ido Hajja tayi tana salati, Zahrah tace "Akwai sanyi kasa meyasa baki hau gado ba" Hajja tace "Kai ai sai jikina yyi ciwo, nn ya ishe ni" Zahrah tace "Toh" mikewa xaune Hajja tayi tace "Toh ae gwara da kika tada ni, xan yi tsayuwar dare dama" Zahrah tace "Ina take ita?" Hajja ta tabe baki tace "Ae kya bar ni budurwa" daga haka ta mike tana salati ta shiga bayi, mikewa Zahrah tayi ta koma tayi kwanciyarta, da asuba hajja ce ta tada ta tayi sllh, tana idarwa tana daga kan darduman ta gaida Hajja dake ta jan carbi, Hajja ta amsa tace "Kin tashi lafiya?" Zahrah ta gyada mata kai, Hajja tace "Amma kina da ciwon baki koh? Naga kmr magana na maki wahala?" Murmushi Zahrah tayi, Hajja tace "Toh ae ba abun dariya bane sai in sa a sama maki Magani...." Zahrah tace "A'a lafiyata lau!" Hajja tace "Tohhh! Kuna waya da mutan gidan ku?" Girgixa kai Zahrah tayi, Hajja tace "Sbda me" Zahrah tace "Ba waya" Hajja tace "Baki xo da waya bane dama?" Girgixa kai kawai Zahrah tayi, Hajja tace "Toh Allah ya kyauta" daga haka bata sake cewa komai ba, can Hajja tace "Dawo nn in maki tambaya" mikewa Zahrah tayi ta koma kusa da ita ta xauna, murya can kasa Hajja tace "Halan gudun mijin ki kike?" Girgixa kai Zahrah tayi ba tare da ta kalleta ba, Hajja tace "Anya? Toh wace gulmar ta kawo ki nn jiya Idan ba gudunsa kike ba?" Zahrah tayi murmushi ta girgixa mata kai, Hajja tace "Ke ki fa bude baki ki min magana" a hankali tace "Ni dama a nn nake kwana" Hajja tace "Toh har ya maki kwanakin ki bakwai ne?" Kai Zahrah ta gyada mata, Hajja tace "Karya kike" murmushi Zahrah tayi ta mike tace "Zan je kitchen" daga haka ta fita Hajja ta bi ta da kallo tace "Ikon Allah yau naga halitta" Breakfast Zahrah ta shiga kitchen tana hadawa, cikin minti arba'ain ta gama soye soyen, ta kuma dafa hadadden lipton mai kamshi ta kuma dau nama a deep freezer ta gyara tayi pepper soup da shi, bakwai da kusan rabi ta kai ma Hajja nata, Hajja dake kan darduma har lkcn tace "Ahhh, Dama kuna girki 'ya yan gidan sarauta, to wa ya koya maki girkin?" Murmushi Zahrah tayi ta ajiye mata ta hada mata tea snn ta mike tace "Zan yi wanka" daga haka ta fita ta koma dakinta, ta fito daga wanka tana gyara gashinta aka bude kofar dakin, juyawa tayi, tayi masa kallo daya ta dauke kanta, sanye yake da uniform, hannunsa rike da hularsa ya karaso cikin dakin har ya iso bayanta yace "Ashe an koya maki girki gidan ku" bata ko kallesa ba bare yasa ran samun amsa, kwace comb din hannunta yayi, ta jawo mai xata shafa ya karbe man, wani man ta kuma dauka ya kwace duk ya jefar da su kan gado, tana son tashi amma ta kasa sbda tawul kadai ta daura, gashi yana bayanta, ta madubi yake kallonta shi ma ya hade rai yanda tayi, "Pls ka daina shiga rayuwata Ahmad" bai san lkcn da murmushi yayi escaping lips dinsa ba yace "Ohh really kinsan sunana ashe" mikewa tayi kafin ta bar gun ya rikota, turasa take son yi amma ta kasa, kawai ta saki kuka, buda ido yayi yace "Kuka?" Ganin yanda take kukan sai ya tuno masa da lokacin da take da disorder, ya ji duk jikinsa yyi sanyi, ya kamo hannunta suka koma gefen gado ya xaunar da ita cikin sanyin murya yace "Ohk ohk... Am... am sorry princess, am sorry Jasmine" ganin taki daina kukan bai san lkcn da ya rungumeta ba ya lumshe ido a hankali yace "I said am sorry xan bar shiga rayuwar ki...." A hankali ta tsaida kukan nata, dogon gashinta ya kama ta fixge gashin a hannunsa, murmushi yayi murya can kasa yace "Jasmine dita ta da ba haka take ba, she alwayz wants to be with her Captain, always happy when ever

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login