Showing 165001 words to 168000 words out of 170905 words
Chapter 56 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
tsakiyar kansa, bai san lkcin da ya saketa ba ya fice daga dakin ya shiga nasa ya dau makullin motarsa ya fito ya koma dakin har lkcn tana tsaye, hijab dinta ya dauka ya kama hannunta ya nufi kofa ta shiga kokarin fixge hannun tace "Let me, just go away from my life...." ganin xata bata masa lokaci ya dauketa ya fice daga dakin bai dire ta ba sai cikin mota, ya kulle ya xaga ya shiga ya tada motar ya bar gidan, bai damu da haukan da ta dinga masa bayan motar ba ya dinga driving dinsa, tafiyar kusan minti talatin suka yi taga yayi parking, bude motar yayi ya fito ya xaga ya bude side din da take ya fito da ita, taku daya biyu ya cikata yana mata wani kallo, kalle kallen wajen ta dinga yi ganin duk bola ne, ya dawo gabanta ya tsaya yace "Kin ga nan?" Kallonsa kawai take bata ce komai ba, yace "Toh a nan na dauke ki bbu kyan gani da hannuna, kuma a lokacin da kowa ke kyamatar ki baki da wani sauran gata a duniya kina tsaka da hauka, wanda da a lkcn royal family dinki sun ganki a hakan ba lallai su taba ki ba sai dai su sa a dauko masu ke, kuma har duniya ta nade bbu wanda xae taba maki abinda na maki... Har ni xa ki ce ina shiga rayuwar ki, har na xaki wani dinga daga ma kai ke ga ki royal blood" Kallonsa kawae take hawaye cike idonta, can ta fashe da kuka sosai ta durkushe wajen, jikinsa yayi sanyi yana kallonta, bai san lkcn da ya durkusa gabanta ba shi ma ya dago kanta yace "Look I never mean to hurt you Zahrah just that...." Ganin yanda take kallonsa hawaye na sauko mata kawai ya mike ya daga ta suka koma mota, har suka isa gida bbu wanda yace komai cikinsu, yana parking ta bude mota ta fita tayi cikin gida ya fito ya bi bayanta, tuni ta shige daki ta sa key ta dinga rusa kuka, jin kofar a rufe yasa ya koma bedroom dinsa ya dau spare key ya fito ya bude dakin, ji yayi duk ya tsani kansa ganin yanda take kuka, ya karasa kusa da ita a sanyaye ya durkusa ya dago kanta yana kallonta, rungumeta yayi a hankali yace "Am sorry Jasmine.... I shouldn't have done that, forgive me pls" ita dai bata ce komai ba sai kuka, bai sake cewa komai ba, amma sun kusa minti talatin a haka jin ta daina kukan ya dago kanta yaga idonta lumshe, janyeta yyi jikinsa ya kwantar da ita ya mike ya fita daga dakin don lkcn magrib yayi. Ko da ya dawo masallaci dakin Humainah ya shiga ya ganta xaune kan darduma juyawa yayi ya koma dakinsa ya dau wayarsa mis cals din Abdul ya gani ya dauka ya kirasa ya basa hakuri snn yace bari ya kai mata, xaune ya tarda ita kan darduma ya karasa gabanta ya durkusa ya mika mata wayar, karba tayi tana kallon screen din can ta kai kunne a hankali tace "Brotherna!" Murmushi tayi ta gaishesa sai kuma ta koma harshen fullanci, kallonta kawai Junaid yake har dai suka gama wayar ta mika masa, karba yayi yana murmushi yace "thought xa ki ce masa cikin ruwa na jefa maki wayar, sai kuma naji kin ce yana gu na!" Kallonsa tayi da sauri sai kuma ta sunkuyar da kai, ya wara ido yace "You thought bana ji koh?" Bata ce komai ba yace "Don't worry I will get you a new phone princess" mikewa yyi ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, tun daga lkcn Zahrah ta d'an sauya in dai yyi mata magana ko yayane xata amsa masa, ta kuma fara gaishesa, sai dai miskilanci nan na nan, a haka har tayi sati uku gidan har lokacin kuma tare da Humainah suke kwanciya, shi dariya ma take basa, sau dayawa Humainah kan barta ita kadai dakin ta tafi dakinsa amma hakan bai sa ta daina shigowa da daddare ta kwanta ba, kwata kwata Zahrah bata nuna masu wai tana kishi, duk da irin abubuwan da yake ma Humainah a gabanta don ma Humainahn bata yarda wani lokacin don nauyinta take ji ganin shirunta yyi yawa kuma ko sau daya baxa ka ga alamar tayi fushi ba, amma fa ba haka abun yake gun Zahrah ba a can kasan ranta, so tari sai ta shiga daki xata fara kuka tayi mai isarta ta fito kuma kamar ba komai, mamakinta Junaid yake ganin yanda ko sau daya bata taba nuna ta damu da komai ba, ya rasa yanda xae yi kuma ta saki jiki da shi, bai son El-ameen yyi masa dariya shi yasa bai gaya masa komai ba, Yau da ya kasan ce Sunday duk suna parlor da daddare shi yana kwance yana kallo, lkci lkci ya ke kallon Zahrah dake xaune tare da Humainah suna cin abinci sai dai ita ba wani ci take ba jujjuyawa kawae take tana kallon ita ma, da ganinta kasan duk jikinta a sanyaye yake don actress din film din mahaukaciya ce, Humainah ma kallon take tana cin abinci, kawai gani suka yi ta sake spoon din ta mike ta wuce sama, Humainah ta kallesa, ya mike ya bi bayanta, xaune ya ganta daki tana ganinsa ta fashe da kuka, sosai ta basa dariya ya xauna gefenta ya kamo hannunta yace "What's wrong princess?" Kanta ta daura kan shoulder dinsa tana ci gaba da kuka, bakinsa ya kai kunnenta murya can kasa yace "Film din nan ne ya sa ki kuka?" A hankali ta gyada masa kai, yayi murmushi ya dago kanta yana kallon kwayar idonta, sauke nata idon tayi don baxata iya ci gaba da kallonsa ba, can kasan breathe dinsa yace "My princess, My Jasmine!" Ta kallesa kamar baxata ce komai ba sai kuma a hankali tace "My prince, My Hero"
*Haske writers association*๐กโ *Captain Ahmad Junaid*โ
_By Khaleesat Haiydar_โ๐ป
92____95
Kallonta kawai junaid yake kamar bai yrda da abinda tace ba, can yyi murmushi ya daura forehead dinsa kan nata a hankali murya can kasa yace "Sure?" Rufe idonta tayi bata ce komai ba, ya lumshe idonsa yace "I love you princess!" Boye fuskarta tayi jikinsa tana murmushi, ya kai bakinsa kunnenta yace "Ohk, am only ur hero but not ur love koh?" Murya can kasa tace "uhmm Whatever!" Misalin sha daya yana kwance yana danna waya yaji ta bude kofar dakinta, mikewa yayi ya karasa gun kofa da sauri ya bude, tana kokarin bude dakin Humainah ta juya tana kallonsa, hannu ya mata alama da ta xo, ta tsaya tana kallonsa, can ta make kafada ta girgixa masa kai, bata fuska yayi, tayi murmushi ta karasa gun kofar ta tsaya ta rungume hannayenta bata ce komai ba tana jiran jin me xai ce, fixgota yayi cikin dakin ya rufe kofar ta xaro ido tace "What's this?" Yace "Nan xa ki kwana yau!" Ta hade rai tace "And Why?" Yace "Just" hannunta ya kama suka karasa kan gadon ya xaunar da ita, a hankali tace "Ita fa?" Ya d'an bude ido yace "Ko in je in daukota?" Gyada masa kai tayi yayi murmushi ya ja dogon hancinta hade da daura finger dinsa daya a kan lips dinta yace "Gobe ita xata kwana nan ba ke ba!" Bata kuma ce masa komai ba, sai dai mamaki take a ranta to da can yana magana haka ashe, kan gadon ya hau ya jinginar da pillow ya kwanta ya nuna mata gefensa, kin tasowa tayi a hankali yace "Jasmine" sunkuyar da kanta tayi ta hau kan gadon ya nuna mata pillow din dake gefensa ba musu ta kwanta a hankali ya daura kanta, ya juya yana facing dinta yace "Bani labari har bacci ya dauke ni" kallon handsome face dinsa kawae take ko kiftawa bbu, hade kansa yyi da nata yace "Jasmine" ta koma baya da sauri tace "What?" Yace "Ban labari nace" tace "Bn iya ba" yace "Ohk in baki ni?" Gyada masa kai tayi, ya kashe wutan dakin ta mike xaune da sauri tace "Why is that?" Jawota yayi jikinsa yace "Shhhh! Da Hausa kike son labarin ko da fillanci, ko da larabci ko kuma turanci" murmushi tayi tana kallonsa tace "Fillanci...." Xaro ido yayi don ji kawai yake bai iya speak ba, kallon fuskarsa kawai take cikin duhun tana murmushi, kawai ji yayi tayi dariya tace "Ohk Hausa, tunda baka iya fillancin ba" dariyar yayi shi ma yace "No na iya mana, amma bari muyi da Hausan, kina ji na?" Kai ta gyada masa, ya hade hannunsa da nata murya can kasa yace "Watarana ne dai watarana ne dai, wani bawan Allah ya je course Egypt daga nan Nigeria, cikin ikon Allah ya kare course din ya dawo gida Nigeria, washegarin ranan da ya dira yayi deciding ya je gun amininsa abokinsa kuma d'an uwansa...." Kallonsa kawai Zahrah take, ya shafa fuskarta yace "are you there?" Ta gyada kasa kai, ya lumshe ido yace "Yana driving a hanya ya ga wani taro me yawa, a tunaninsa hatsari aka yi, kawai yayi deciding ya tsaya ya bada nasa taimakon... Yana fitowa ya shiga taron kin san abinda ya gani?" Boye fuskarta tayi a kirjinsa, ya dago kan yace "Are you there princess?" Ji yayi ta fashe da kuka, ya mike xaune da sauri ya dagota yace "Jasmine!" Ta kuma fashewa da wani kukan, jikinsa yyi sanyi lokaci daya, rungumeta yyi yace "Ohh I am sorry plss tunda ba ki so, sorry plss Princess na daina" lamo tayi jikinsa, a hankali yace "I didn't mean to hurt you" suna nn a haka har yaji alamun tayi bacci ya lumshe ido ya daura fuskarsa kam gashinta da ya cikasa da kamshi. Washegari da asuba kafin ya dawo daga Masallaci ta fita ta koma dakinta, yana dawowa dakin Humainah ya shiga ya tarda kwance ya karasa ya xauna kan gadon yace "Sallah fah?" Tace "Nayi" yace "Ohk Gud morning" mikewa xaune tayi tace "Ina kwana!" Yayi murmushi yace "Kin tashi lafiya" komawa tayi ta kwanta tace "Yeah" yace "to babyn fah" bata ce masa komai ba hakan yasa ya mike ya fita. Bakwai da minti goma ya sauka downstairs bayan yayi shirin fita aiki, kallo daya Zahrah da ta gama ajiye kayan breakfast kan dining tayi masa ta dauke kai, ya isa kusa da ita ya tsaya, ta gefen ido ta kallesa tace "Good morning" ya rungume hannayensa yana kallonta jin bai amsa ba ta juyo tana kallonsa ita ma, karasawa tayi gabansa ta langwabar da kai cikin sanyin murya tace "Gud morning" bai amsa ba still sai kallonta da yake, can ya kamo hannunta ta fixge tayi masa buttoning masa button din karshe na farin uniform din jikinsa ta kara gaba. Da yamma yana parlor xaune bayan ya dawo daga aiki su kuma suna kitchen aka danna bell, mikewa yayi ya isa gun kofar ya bude, El-ameen ne tsaye daga gefensa kuma Dr Sumayya, El-ameen ya wara ido yace "ko mu koma" Junaid yayi murmushi yana kallon Dr sumayya ya bata hanya yace "Sannu da xuwa Dr, bismillah" murmushin ta mayar masa ta shiga parlon tace "Yauwa Captain ina daughter nah" yace "Uhm tana ciki bari in kirata" daga haka ya nufi kitchen, xama tayi parlor El-ameen ma ya xauna tace "Allah sarki rayuwa, kamar ba ayi ba yanxu koh?" Murmushi kawai El-ameen yayi, tace "Allah ya baku lada gaba daya.... Amma na so ace kai ka sameta ba wnn Capt mara son son jama'a ba" Junaid na shiga kitchen ya kamo hannun Zahrah dake tsaye Humainah kuma na ta aikin, yace "You know what princess, xaku gaisa da bakuwa yanxu, ta taimake ki ita ma sosai lkcn da baki da lafiya, you stayed with her for 3 month ta kuma kula dake sosai, she's Dr sumayya by name, tare suka xo da El-ameen" kallonsa kawai Zahrah take yayi murmushi yace "Yeah princess," juyawa yayi ya kalli Humainah dake ta harkan gabanta yace "Wife ki kawo masu drink pls" daga haka ya kama hannu Zahrah suka fita, kallonta kawai Zahrah take kamar yanda ita ma Dr Sumayyar ke kallonta har suka karaso parlon, Dr Sumayya ta mike tana murmushi ta bude mata hannunta, karasa Zahrah tayi ta shige jikinta, Dr Sumayya tace "Am happy you are back my baby.... Alhmdulillah, am happy for you baby" Zahrah ta rufe idonta da ya cika da hawaye Dr Sumayya ta janyeta jikinta tana kallonta cike da tausayinta. Su El-ameen na barin gidan bayan magrib Junaid ya shiga dakin Zahrah bai yi mamakin ganinta a sanyaye ba ya xauna kusa da ita ya kamo hannunta yace "Yeah you owe a lot to her, after you loosed ur memory ita ta rike ta kuma dinga nuna maki abubuwa, komawarsu abroad yasa kika dawo gidana,then baki ma son rabuwa da ita you were crying xa ki bita" kallonsa kawae Zahrah take, yayi murmushi ya lakaci hancinta yace "Yess princess..." Danna bell da aka yi downstairs ya sa ya kalli bakin kofa can yayi peck din cheek dinta ya mike yace "Am coming princess" daga haka ya fita ya sauka kasa, yana bude kofar yayi still yana kallon wa enda ke tsaye bakin kofar, Hajiya ce ta kirkiri murmushi tace "Ahmad, ina yini" bai amsa ba sai kallonta da yake, Umma dai sai wurga ido take, Hajiya tayi karfin halin bin ta gefensa ta shiga parlon sai a snn ya juya ya bar bakin kofar ya koma parlor, Umma ma ta shigo duk suka karasa parlon kamar masu tsoron taka tiles din parlon, xaman sa yyi parlor suma suka shigo suka xaxxauna, Umma tace "Sannu Ahmad ina yini ya aiki" sai a snn ya kallesu, can yyi kasa da kai yace "Sannun ku da xuwa" washe baki Hajiya tayi tace "Sannu Ahmad, ya iyali" yace "Alhmdllh" daga haka ya mike ya wuce sama, bin sa da kallo suka duk jiki yayi sanyi, dakin Humainah ya shiga ya ga tana bayi, ya fita ya koma dakin Zahrah tana nn yanda ya barta ya xauna kusa da ita ta kallesa tace "Waye?" Hannunta ya kama yace "My step mothers" d'an bude ido tayi tace "You have them?" Murmushi yayi ya daura goshinsa kan nata yana rike da hannunta yace "Yeah, and they don't like me" tace "Why?" Ya girgixa Kai yace "tafi ki kai masu ruwa" ba musu ta mike ta fita, tunanin abinda xai kawo su gidansa ya shiga yi, can ya mike ya koma dakin Humainah tana xaune gaban mirror yace "Ki tafi ki gaida su Hajiya" tana kallonsa ta madubi tace "Wace Hajiya" yace "warce kika sa ni mana" daga haka ya fita, ta kusa minti biyar tana naxari kafin ta mike ta sa hijab ta fita. Kasa karasawa parlon tayi yanda suke kallonta haka ita ma take kallonsu, Zahrah dai na xaune kasa bayan ta kawo masu ruwa har da abinci, can Humainah ta karasa ta xauna ita ma kasa tana kirkiran murmushi tace "sannun ku da xuwa" amsa ta suka yi ko Wanne na murmushin dole, bata kuma cewa komai ba can dai ta mike ta koma sama, har aka yi isha Junaid bai shigo parlon ba iyaka ya tafi masallaci ya dawo ya koma sama, can dai Umma na kallon Zahrah tace "D'an yi mana magana da shi xa mu koma ne" mikewa tayi ta tafi sama ta shiga dakinsa, yana danna laptop ta samesa ta karasa tace "Xa su wuce wai" kudi ya ciro har dubu hamsin ya mika mata yace "Ki basu" xaunawa tayi kusa da shi ta karbi kudin ta ajiye tace "Nooo, ka fito kuyi sallama" yace "Why?" A hankali tace "From there expression sun yi regretting everything" yayi murmushi ya dago fuskarta yace "And that's because basa gidanmu yanxu" tace "Kamar ya?" Mikewa yayi yace "Am coming" daga haka ya dau kudin ya fita, xaunawa yayi parlon ba tare da ya kallesu ba Umma tayi karfin halin cewa "Ahmad dama mun xo ne mu roki alfarmar ka taimake mu kayi ma Alhaji magana mu koma dakin mu, sai kuma a yafe juna abubuwan da suka faru a baya.... Sharrin shaidan ne" shi dai kansa na kasa can yace "Toh..." Ya mika masu kudin yace "Allah kiyaye hanya" Hajiya ta karba tace "A'a har da wahala haka Ahmad, to Allah yayi albarka" Ameen kawai yace ya mike ya nufi stairs yace "Bari in kirata" daga haka ya haura sama. Yau Zahrah kin fitowa tayi xuwa dakin Humainah don ma kar ya kuma kiranta dakinsa, duk ya kagu ya ji fitowarta amma shiru har Karfe sha biyu, to ko dai har ta xo ta wuce bai sani bane, mikewa yayi ya fita ya nufi dakinta, a hankali ya tura kofar ya ganta kwance, tana ganinsa tayi saurin rufe ido ya karasa ya xauna gefenta yace "Yau baki tsoron kwana ke daya kenan?" Ba tare da ta bude ido ba tace "Eh" wara ido yayi yace "Da gaske?" Xata juya masa baya ya rikota yace "Jasmine" bude ido tayi ta mike xaune ta buda masa hannu alamar what, murmushi yayi ya kamo hannunta yace "Nothing, m just missing you" tace "Ohk thank you, Gud nyt" yace "Uhm korata kike?" Gyada masa kai tayi yayi dariya yace "Ohk xan tafi, but you know what?" Kallonsa kawai take, ya lumshe ido ya bude murya can kasa yace "Ba mu taba sallah tare mun roki Allah ya albarkaci auren mu ba" tace "Ni na taba yi" ya buda ido yace "I mean togeda princess, c'mon tashi kiyi alwala muyi sallah" tace "Ina da alwala na" ya d'ago kanta yace "Gud" daga haka ya mike ya dau darduma ya shimfida masu, juyawa yyi yana kallonta yace "Taso mana" ta nuna masa hijab dinta tace "Bani" yace "Meyasa baxa ki dauka da kanki ba" tace "Nothing" murmushi yayi ya dauko ya mika mata ta sa sannan ta mike. Nafila ya ja su raka'a biyu, ya jima xaune yana addu'a bayan sun sallame snn ya juya yana kallonta, murmushi