Showing 51001 words to 54000 words out of 170905 words

Chapter 18 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

625

da ita a matsayin warce xai aura idan lokacin da Alhaji ya dibar masa yayi" Hajiya ta xaro ido tace "Ae ko da mun banu mun lalace, meye abun yi Bilki?" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "ba mu ga ta xama ba,"
Humainah ta kalli motar da Junaid ya shiga tace "Motar waye wannan?" Kallonta yayi ya bude ido yace "Naki" ta hararesa ta xaga ta shiga, yana warming motar ya kira El-ameen, bugu biyu ya d'aga, Yace "kana ina ne Dr?" El-ameen yace "ina gida" Junaid yace "Ohk plss ka fito mu hadu kasan layin ku" El-ameen yace "Why?" Junaid yace "kai dai ka fito, it's urgent, kuma ka taho da motarka" daga haka ya katse wayar, ya ja motar suka bar gidan, Humainah tace "Amma ya Ahmad gidan Anty Aysha aka ce ka kai ni fa xaka wani ce ku hadu a kasan layi, to yawo xaka yi da ni a mota" ba tare da ya kalleta ba yace "Ni tricycle ma zan je in saka ki yanxu ya kai ki" ta xaro ido tace "Ehh!" Yace "Yess!" yana isa layin su El-ameen ya hango motarsa ya isa gun motar yayi parking ya fito, xuge glass El-ameen yayi yana kallonsa a bit surprise yace "Whose car is dat?" Junaid yace "A good samaritan's, jiya da ka yasar da ni a titi ka wuce...." El-ameen yayi tsaki yace "Kayi mugun bata min rai jiyan nan, don me yarinya xata shirga karya wai ta mance Atm card a gida ka yi amfani da kudina ka biya uban kayan da ta siya" Junaid yace "Ba dai na mayar maka da kayan ka ba, keep dat matter aside kar kayi provoking dina" El-ameen ya tabe baki yace "Ni Mama jummai ma na ba kudin da xata tafi daxu, and dat's ur responsibility not mine" Junaid yace "Whatever, gidan Aisha xaka taimaka ka kai budurwar nan taka, ni ina son maida motan mutane ne kar ayi tunanin guduwa nayi da shi" El-ameen ya leka motar suka hada ido da Humainah, da sauri ya dauke kai ya bude ido yana kallon Junaid, Junaid yayi 'yar dariya yace "Ehh ita din ce" daga haka ya juya yana kallon Humainah da ta hade rai cikin mota ya duka yana kallonta da kyau yace " Oya fito saurayin ki ya kai ki ni....." Kuka ta sakar masa tana yarfe hannu tace "Wayyo ni, wallahi kai aka ce ka kaini bbu inda xan bin sa" ya bude ido yace "Ke ba motata bace wannan, xan maida ma me shi ne" ta marairaice masa cikin sigar shagwaba tace "Plss mana ya Ahmad don Allah ka kaini" murmushi kawai yake yana kallonta, can ya mike ya juya gun motar El-ameen da ya wani hade ya daga kafada yace "Kaji wai tsoronka take ashe, don haka plss frnd just excort me in maida motar sai mu tafi gidan Ayshan da naka motar" El-ameen yayi masa wani kallo yace "I don't have dat time, dama kiran da ka min kenan?" Junaid yayi murmushi yace "Toh shikenan, idan mun je can xa mu samu tricycle" daga haka ya xaga ya koma driver seat ya tada motar ya bar layin, tsaki El-ameen yayi ya bi motar da harara can ya tada nasa motar ya bi bayansa, Junaid na ganin haka yayi murmushi don dama yasan sai ya biyo sa. Cikin mintunan da basu wuce sha biyar ba ya iso layinsu Hafsat, yayi parking inda tayi jiya, ya fara kalle kalle don bai karbi numberta ba, Humainah tace "Ya Ahmad ina ne nan" yace "gidan su budurwata" kallonsa kawai take ya bude motar ya fita ya xaga ya bude mata ta fito, dai dai nan El-ameen ma ya fito ya rungume hannu ya hade rai yana kallonsa, murmushi Junaid yayi ya daga kafada ya nufi gate din gidan, yana danna bell maigadi ya leko, Junaid yace "Amm ina yini, Hafsat nake nema a gidan nan," Mai gadin yace "Toh bari a mata magana" komawa Junaid yayi kusa da El-ameen ya tsaya yace "Da ma ka saki ranka kar Humainah tace ta fasa" shi dai El-ameen bai tanka sa ba, Humainah kam ko kallonsu bata yi ba, bude gate din gidan aka yi ta fito sanye da jan atamfa sai farin Hijab, xaro ido El-ameen yayi yana kallonta sai kuma ya kalli Junaid, murmushi tayi ganin Junaid sai dai lokaci daya murmushin ya bace ganin El-ameen gefensa da tayi, ta karaso kusa da su ta gaida su, Junaid ne kadai ya amsa don shi El-ameen juyawa ma yayi ya shige motarsa, banda kallonta babu abinda Humainah take, Junaid ya shafa kansa yace "Ga motar ki, tnx a plenty, am grateful" ta kirkiri murmushi kawai tana gyada masa kai, ya mika mata makullin motar ta karba, ya kalli Humainah yace "ga kanwata can ku gaisa" karasawa tayi gun Humainah tana kallonta murmushi dauke fuskarta tace "Sannu, ina yini?" Humainah ta dauke kai babu yabo bbu fallasa tace "Lafiya" juyawa tayi ta bar wajen duk jikinta yayi sanyi, ta kalli Junaid tace "Toh nagode" yace "Ni ne da godiya" kallon Humainah yayi yace "Taho mu wuce" kamar xata tashi sama ta karaso ta bude bayan motar El-ameen ta shige, Junaid ya ciro wayarsa ya mika ma Hafsat yace "Sa man digit dinki mu dinga xumunci" karba tayi ta sa numberta ta mika masa suka hada ido da El-ameen dake kallonsu, da sauri ta dauke kanta, shi ko ya tabe baki, Junaid ya mata godiya ya xaga ya bude front seat ya xauna, El-ameen ya figi motar suka bar layin. Sai da suka hau main road El-ameen yace "Da nasan inda xaka kenan wllh ban xuwa, yaushe ka xama haka Captain, yaushe ka fara ware ma mace lokacin ka har da wani karban numberta, Tabdi" har suka iso gidan Aysha ana kiraye kirayen Magrib Junaid bai ce ma El-ameen komai ba, ya juya yana kallon Humainah yace "Toh gashi mun kawo, ki gaida ta" daukar jakarta tayi ta bude motar ta fice ta nufi gate, Junaid ya bi ta da kallo sai kuma ya bude motar ya bi bayanta, tsaki El-ameen ya ja ya danna masa horn, har gate Junaid ya shiga ya fixgota ta hade rai tace "Meye kuma" ya wara ido xai yi magana, ta fashe da kuka, kallonta ya tsaya yi, can ya d'ago kanta yace "What happen?" Ta fixge hannunta taki cewa komai, yace "Baki son xama gun Ayshan ne kuma?" Ta girgixa masa kai tana goge hawayen dake kuma sakko mata tace "To wace wannan yarinya" kallonta kawai yake sai kuma yayi murmushi ya ciro wayarsa daya a aljihu ya mika mata yace "Anjima xan kira ki in gaya maki wacece" juyawa tayi zata bar wajen ba tare da ta karba wayar ba, ya kuma dawo da ita ta fashe da kuka, murmushi yayi ya kama hannunta ya saka wayar, ya juya ya fita daga gate din don El-ameen ya danna horn ya kusa sau biyar, yana shiga motar El-ameen ya figi motar yana cewa "Wai meyasa kake min abinda ka ga dama ne Capt, ka wani shanya ni a mota kana biye ma karamar yarinya 'yar cikin ka, ga baiwar Allah can ko abinci nasan bata ci ba...." Junaid yace "Budurwar ka fa na rako" El-ameen ya tabe baki yace "No, ni ban ce ina sonta ba kawai nace tana da kyau ne, kuma ni ba budurwa ta bace, warce nake so ma ta fi ta komai" dariya Junaid yayi yace "Xa ma ka fadi gaskiya ne, a ina ka samo warce kake son kai da kake tsoron mata" El-ameen yace "Am serious, ni bana son mace me tsiwa da jaraba, warce nake so is very gentle...." Junaid yayi dariya yace "Ita ma bata son mai tsoron mace" El-ameen yayi tsaki yace "Can gidan fa nake son in je don nasan baxata ci abinci ba sai naje shine ka wani bata min lokaci" Junaid ya tabe baki yace "Irin kamar ka damu da ita din nan koh" El-ameen yace "Of course na damu, nama fi ka, kai da baka da aiki sai na bada kudi, ni kuma lokacina gaba daya na bata, a yanxu haka I know her likes nd dislikes, duk motsin da xata yi nasan me yake nufi, I've studied her more than you can imagine, kai you are only showing dat you are a millionaire kana nuna kai kadai ma xaka iya kashe ko nawa ne ba sai ka nemi assistant ba, ni kuma...." Junaid ya ja tsaki yace "Aikin banxa kenan, don without that money you are talking about all this you are listing won't come to action, kai da kake kyashin kashe mata naira biyar din ka, my frnd ka daina listing kan ka a wa enda suka taimake ta ma a rayuwa, you are only decieving ur self, coz I hired you and am paying you for the job, yau nace bana bukatan service dinka you are gonna quit!" Parking El-ameen yayi yana kallonsa yace "Haka kace Ahmad?"

✍🏻
*Haske Writers Association*
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

25....

Junaid yayi dariya yace "Of course haka nace ko nayi karya, ka fadi sisin da ka taba kashe mata in biya ka, kai yanxu har ka nuna mun ka fi ni damuwa da ita, wanda da na biye ka tun farko da baxa mu daukota ba ma, wani irin discourage dina ne baka yi ba, wani irin dariya ne baka min ba kan yarinyar nan..." El-ameen bai ce komai ba ya ci gaba da tukin sa, banda dariya babu abinda Junaid yake, ganin El-ameen hanyar gidansu ya nufa Junaid yace "Ohh ka fasa xuwa ka bata abincin ne?" Shi dai El-ameen bai tanka sa ba har ya isa bakin gate din gidansu, ya juya yana kallonsa yace "Idan kaga na kuma bi ta kan patient dinka, ka gaya min wanda ya fi wannan," daga haka ya fice daga motar ya shige gida. Junaid yayi murmushi yana shafa kansa yace "Uhum wai fushi yayi?" D'aga kafada yayi ya koma driver seat ya ja motar ya bar layin, gida shi ma ya nufa abun sa. Washegari Junaid na gun aiki ya dinga kiran El-ameen ya ki d'agawa, shi dariya ma abun ke basa, don bai ga abun fushi ba daga fadin gaskiya, Karfe biyar ya baro gun aiki, ya canxa uniform din jikinsa xuwa mofti ya tafi can gidan nasa, a hankali ya tura kofar parlon, nurse din dake kula da ita na tattare biscuits din da yayi littering din tsakar parlon, ita kuma tana kwance nan kasa tana bacci, Junaid ya karaso ya amsa gaisuwar da nurse din ke masa yace "Dr El-ameen ya xo yau kuwa?" Ta girgixa kai tace "Bai xo ba, na kirasa ma he's not responding" Junaid yayi murmushi ya xauna yace "Ohk, amma ta ci abinci?" Nan ma ta girgixa masa kai tace "tun jiya ma taki cin komai, kaga biscuit din nan ma na fiddo mata shima bata ci ba ta watsar, yanxun ma da kyar ta kwanta tun safe taki xama na rasa me take nema, duk ta ki yarda da ni" Junaid yace "Ohk, me yace maki ta fi so, I mean abinda take ci?" Tace "Kasan yace xai dawo jiya toh bai dawo ba bare ya gaya min, kuma duk yau ba a mata allura ba tunda bai gaya min yanda zan yi ba" Tabe baki Junaid yayi ya mike ya fice daga parlon. Gidansu El-ameen ya nufa Ummi tace ai tun safe yana clinic, ya mata sallama ya fito ya kama hanyar clinic din, Yana isa nurses din dake reception suka ce masa ai baya nan, yace "Ohk haka yace maku ku ce min idan na xo" kallonsa suka tsaya yi, ya haura sama ya tafi office dinsa, ya murda kofa yaji da gasken baya nan, tsaki yayi ya sauko ya fice daga asibitin, a mota ya dinga kiransa ya ki dagawa, shi ya rasa abun jin haushi a maganarsu ta jiya, daga fadin gaskiya, tsaki yayi ya tada motarsa ya tafi gida abun sa. Wasa wasa har 2 dayz El-ameen yaki xuwa can gidan, ya ma kashe wayoyinsa gaba daya, shi ma Junaid ya fita harkarsa bai kuma bin ta kansa ba, matsalarsa daya yanda Jasmine taki cin komai, gashi da ganinta xaka san abu na damunta, duk taki sakin jiki, though in yaje gidan da yamma ta kan je ta kwanta gefensa ko ta xauna kusa da shi, amma duk yanda xai yi da ita ta ci abinci bata ci, sai dai k'adan shi ma da kyar, in ya takurata tayi masa ihu, bini bini xaka ga ta kalli kofa ko taje can ta tsaya kamar dai tana jiran wani, on the third day Mama jummai ta dawo ya sallami nurse din, yasan yanxun xata fara cin abincin tunda ga mama jummai kila dama don bata saba da nurse din bane amma sai yaga otherwise don yi ma tayi kamar bata taba ganin mama jumman ba, ta kuma ki cin abincin still, da mama jummai ta tambaye Junaid El-Ameen ce mata yayi, yayi tafiya ne, duk abinda mama jummai tasan tana so sai da ta yi ta bata duk taki sai ketchup da take ta sha, duk baiwar Allahn ta rame. Yau Junaid na barin gun aiki ya nufi gidansu Faisal, yayi sa'an shi ma dawowan shi daga aiki kenan, Faisal yayi mamakin ganinsa barin da yaga ko canja uniform din jikinsa bai yi ba. Junaid ya xauna bayan sun gaisa yace "Ina son muyi wata magana da kai ne frnd" Faisal ya maida hankalinsa sosai yace "Am ol ears" Junaid ya shafa kai a nutse ya soma basa labarin mahaukaciyar tun daga farkon haduwarsa da ita, Faisal ya kwalalo ido yana kallonsa baki bude, har Junaid ya kai karshen labarin yana murmushi, Faisal ya sauke ajiyar xuciya yana gyada kai yace "Babban magana, but El-ameen bai kyauta ba, kuma ni ban ga abun fushi a nan ba, sabon da tayi da shi ne ya hanata sakin jiki da bata ganinsa, shiyasa take kin cin abinci!" Junaid ya tabe baki yace "Yanxu dai you are a Doctor, so nake plss ka gaya min yanda xaman psychiatry yake, is it advisable in kai ta can babu matsala?" Faisal ya kuma sauke wani ajiyar xuciyar yace "Gaskiya ina ga na gida kamar yanda El-ameen ke mata ya fi, kuma gashi har ta saba da shi samun lafiyarta ba lallai ya dau lokaci ba, yanxu dai kar ka damu xan je in same sa, nasan..." Junaid yace "No! no bana bukatan sa kuma, he shud hold on to his medication, idan taje psychiatry din suma xata saba da su" murmushi Faisal yayi, Junaid ya mike yace "Plss ka binkitar min psychiatryn da ka ga is ohk... I might come back later ko kuma in kira ka. Don yanxu Mumy xata fara kirana its almost six o'clock" Faisal ya bi sa da kallo har ya fita sannan ya shafa kai yace "Lallai Junaid da El-ameen, mahaukaciya kuma???" Mikewa yayi shi ma ya dau makullin motarsa ya fita xuwa gidansu El-ameen din, Ummi ce da Sumayya xaune parlor, ya gaida Ummi, ta amsa da fara'a tana tambayarsa mutan gida yace "Duk Suna lafiya Ummi, El-ameen na nan kuwa" tace "Ehh yana daki" dakinsa ya nufa ya tura kofar ya shiga da sallama, Ummi ta kalli Sumayya tace "Ki kai masa drink, ki tambayesa ko xai ci abinci" mikewa tayi ta nufi kitchen, kwance faisal ya sami El-Ameen da laptop a gefensa sai dai wayarsa yake dannawa, El-Ameen ya mike xaune ganinsa, Faisal yana murmushi ya karaso ya xauna gefensa yace "Yane the great Dr Ahmad El-ameen" El-ameen yayi murmushi shi ma ya mike xaune yace "Daga ina haka da yamma?" Faisal na kallon fuskarsa ganin yanda manyan idanuwansa suka fito yace "You look pale, are you ohk?" El-ameen ya lashe lebbensa yace "Stress ne frnd, ya aikin?" Faisal yace "Alhmdllh, Ya captain naka...." Dai dai sanda Sumayya ke kokarin shigowa dakin da faranti me dauke da drink da ruwa jin an ambaci Junaid ta tabe baki ta tsaya jikin kofar, El-ameen yace "Yana gidansu!" Faisal yayi dariya yace "Kuna nan har yanxu kamar 'yan biyu abun ku" El-ameen yayi murmushi yace "Sure!" Faisal yace "Uhmm!" El-ameen na kallonsa yace "Ya aka yi?" Faisal yayi murmushi yana girgixa kai yace "Bana tunanin akwai abinda ya isa ya hada ka da Captain..." Sumayya ta gyara tsayuwa da kyau ta baxa kunnuwa, El-ameen yace "Ban fahimta ba" Faisal yace "Daxu ya xo ya sameni ya kuma ban labarin baiwar Allahn da ku ke kokarin ganin kun ceto rayuwarta daga....." El-ameen ya katse sa yace "No! Da yake kokarin ganin ya ceto rayuwarta dai" Faisal yayi murmushi yace "Haba Dr, bayanin da Captain yayi min is not enough ace kayi fushi haka, kuma naga kun saba haka a tsakanin ku, kar ka manta lada ba kadan ba xaka samu idan yarinyar nan ta dawo hankalinta" El-ameen yace "No ni bn yi fushi ba faisal, just dat nayi quit ne, ya nemi wani likitan ko ya kai ta psychiatry..." Faisal yace "No pls, kar kace haka Dr, ba don Junaid xaka yi ba don Allah xaka yi...." El-ameen yayi murmushi yana girgixa kai yace "You know what?" Faisal ya girgixa kai, yace "Wllh wllh ban yi kuma, I've quit, he shud take her to the psychiatry, ka dai ji rantsuwar musulmi na maka, but babu damuwa xai iya ci gaba da amfani da gidana" Sumayya dake jikin kofa har lokacin duk tayi confuse ta rasa gane kan maganar, to wace yarinya suke magana a kai, yanke shawaran kiran Suhaima tayi tasan xata bata labari, El-ameen ya mike yace "kaga am going to clinic yanxu faisal" faisal ya sauke ajiyar xuciya yace "Ban ji dadin rantsuwar da kayi ba El-ameen, don Allah xaka yi ba don Junaid ba" El-ameen ya koma ya xauna yace "Look faisal, kullum! I mean everyday, karfe bakwae na safe baya karasawa nake barin gida in tafi gun yarinyar don akwai injections din da nake mata a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login