Showing 105001 words to 108000 words out of 170905 words
Chapter 36 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
tafi sama, duk su ka bi ta da kallo, Mk yace "Uhmm! But ya aka yi ban santa ba Aj, fatima da khadija kawai na sani" Junaid yace "Ehh ba tare mu ke da ita ba" Humainah ce ta fito daga kitchen ta karaso cikin parlon ta tsaya daga bayan kujera ta gaida su, da fara'a suka amsa mata suna tsokanarta ta kara gaba abunta, dakinta ta shiga ta ga hadiza xaune har lokacin, ita har ta ma mance da ita, rufe kofar tayi tace "Kiyi hakuri girki nake ne" hadiza tace "Ba komai, nima nasan aunt dina kila ta dawo yanxu, tafiya xan yi" Humainah tace "Ki jira ki ci abinci mana, baki yayi a parlon yanxu xa su tafi" xaunawa Humainah tayi Hadiza ta fara mata hira ita dai sai uhn uhn take don bata son junaid ya ji muryarsu, shidda saura junaid ya raka frnds din nasa har bakin mota yayi masu godiya yace "Kun dai ki cin abinci" Mk yace "Kai kuma ka ki barin mu yi sallama da jewel, ni dai ina nan dawowa gobe" KB yace "kai ka ma kai shi har gobe, bayan isha ni ina nan xuwa" dariya suka yi gaba daya banda Junaid da yace "Ai duk kuna da 'yan mata na ga" sun kusa minti sha biyar tsaye daga bisanni suka wuce ya koma ciki, Tuni Humainah ta sauka kasa ta debo ma Hadiza abinci jin fitarsu, yana haurowa sama dakin Jasmine ya bude, ya ganta tsaye bakin window tana kallon waje, hade rai yayi yace "From henceforth aka sake ring din bell kika sauka kika bude kofa I will slappp you, wani ya saki ne?" Kallonsa ta tsaya yi, hadiza dake jin duk abinda yace ta kalli Humainah murya can kasa tace "Toh fah" Jasmine kam bata ce komai ba sai kallonsa take kamar bata gane me yace ba din nan, ya karaso cikin dakin a fusace yana mata mugun kallo yace "Kin ji abinda nace?" Girgixa masa kai tayi da sauri, ya dawo kusa da ita strictly yace "Nace daga yau kar ki kuma fitowa parlor idan aka ring din bell, kuma na sake ganin kin tsaya magana da maxa har kina gaya masu sunan ki sai na maki mari!" Sunkuyar da kai tayi cikin tsawa yace "Kin ji?" Ta gyada masa kai hawaye cike idonta, juyawa yyi ya fice daga dakin. Hadiza tace "Toh fah, don Allah ki gaya min yanda kuke da yarinyar nan" Humainah ta tabe baki kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Yar uwarsa ce" hadiza tace "Tabdi toh Meye kuma na hanata magana da maxa, aurenta shi xai yi ko me?" Hade rai Humainah tayi bata ce komai ba, Hadiza tace "Toh ae ba xancen hade rai bane, wllh ki sa ido kar abinda ya samu yayata ya same ki, abu na biyu kuma na ga bbu wani interaction mai karfi tsakanin ki da mijin ki, anya kuwa?" Shiru Humainah tayi bata ce komai ba, Hadiza tace "Tabdi, to auren dole aka maku ne, yo ko da auren dolen ne ma ke ba mace bace baki san yanda xa ki ja mijin ki jiki ba, ai kam xa ki tsaya kallon ruwa...." Ita dai Humainah har lokacin bata ce komai ba, Hadiza tace "Ya ina magana xa ki share ni, ni tun randa na ganki naji Allah ya dora min san ki banda haka wannan ai ba hurumin da xan shiga bane, batun gaskiya Humainah da sake a xaman auren ki, ga mijin ki hadadde me kyau da shi xa ki tsaya wasa wata ta kwace maki, lallai ma" mikewa tayi tace "Kin ga tafiyata abincin ma ya ishe ni" Humainah da duk jikinta ya mutu tace "A'a don Allah ki kara..." Hadiza tace "Tafiya xan yi" daga haka ta nufi kofa fuu irin tayi fushi din nan ita, Humainah ta bi ta da sauri don ita tsoronta kar junaid ma ya ganta, tuni hadiza ta fice daga gidan gaba daya, Humainah ta sauke ajiyar xuciya tana naxarin maganganun ta, xama tayi bakin gado tayi tagumi hawaye ya cika idonta, to ita ta ma san yanda xata yi da junaid, da kyar ta iya mikewa ta shiga bayi ta dauro alwala don yin magrib, ta jima xaune kan darduma daga bisanni ta mike ta fita daga dakin ta sauka kasa, kitchen ta tafi ta hada masa abincinsa a tray, ta gama xata fita Jasmine ta shigo kitchen din ta tsaya daga bakin kofa tace "Anty abinci na" ba tare da Humainah ta kalleta ba tace "Ban yi da ke ba, ki shiga ki dafa" Jasmine tace "Na'am" juyawa Humainah tayi ta fice daga kitchen din ta bar ta nan tsaye. Junaid na waya Humainah ta shigo dakin, ta ajiye abinci har lokacin bata mike daga durkushen da tayi ba, yana gama wayar ya juya yana kallonta ya d'an bude ido yace "Uhun! Yau kuma" hade rai tayi, yayi murmushi yace "Toh na gode, kin ba Jasmine na ta?" Kallonsa kawai take, can ta tabe baki tace "Kace da magrib xaka kai ni gida" yace "Ohh shi sa aka kawo min abinci, to ni gidansu El-ameen xan tafi yanxu" kuka ta fashe da tana kallonsa, ya sauko kasa ya dawo kusa da ita shi ma ya durkusa ya fara kwaikwayonta, duka ta shiga kai masa tana cewa "Ni ka kyaleni bana so" dariya yayi yace "Sai in dawo captain din yanxu, ni kike duka" dagota yayi suka koma kan gado yace "Gobe lahadi kin ga sai in kai ki tun asuba sai sha biyun dare xan je daukan ki" ta tsaida kukan tace "Kace Allah" yace "Sai na ce?" Shiru tayi tana kallonsa, ya ja hancinta yace "Allah" murmushi tayi ta fada kansa tace "Toh na gode" can kuma ta mike ya bi ta da kallo har ta fita, abincin ya bude ya ga tuwon shinkafa ne da miyar vegetable..... " ya dau plate da spoon ya dibi kadan ya ci snn ya rufe ya mike, wanka ya shiga ya fito ya shirya don xuwa gidansu El-ameen duk ya kagu yaga matar aminin nasa, dakin Jasmine ya shiga ya ganta xaune kasa ta daura kanta kan gado, yace "Kin ci abinci?" Ta girgixa masa kai, yace "Bata baki bane?" Ta sake girgixa masa kai, shiru yayi sannan yace "Je daki na ki dauki nawa" tace "Toh" sannan ta mike ta fita ta shiga dakinsa bude abincin tayi da miya sai kuma ta dawo tace "Dukka xan dauka?" Yace "Ehh" komawa tayi sai ga ta ta dawo da tray din, murmushi yayi ya juya ya fita daga dakin.
*Haske writers association*💡
_Tnx all for the prayers sisters Allah ya kara ma duk musulmai lafiya Ameen_ Sorry for keeping you all waiting sisters.
[3/19, 9:22 PM] El-hajj💥: *Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
57.....
Junaid na fita gidan ya kira wayar Faisal, yana dagawa yace "Ya? ku na ina yanxu?" Faisal yace "Kai kam sam baka da kirki captain" junaid yace "That's constant ai...." Faisal yace "Toh yayi kyau muna shirin kai ango..." Dariya junaid yayi yace "Ohk toh gani nan xuwa kar rashin kirkin yayi yawa koh?" daga haka ya katse wayar ya dau hanyar gidansu El-ameen, El-ameen na cin abinci a dakinsa Junaid ya shigo, junaid yace "Tab har daman cin abinci ka samu kenan, ni tym din nawa ina na samu wannan daman....." Ko kallonsa El-ameen bai yi ba ya hade rai, dariya sosai Junaid yayi yace "Harara a duhu kawai kake yi" Dr faruq yace "Ni na ma yi xaton tafiya kayi Ahmad, bikin aminin naka guda ace baka kusa" Junaid ya shafa kansa yace "Daxun nan na dawo bana nan" faisal yace "ga alama mun gani" murmushi junaid yayi bai kuma cewa komai ba, ya mike ya bude closet din El-ameen ya fiddo wani dakakken shadda sky blue ya ajiye masa ya koma gun huluna ya fiddo wanda xai shiga da kayan ya ajiye masa, ya dauki agogo me tsada cikin agogunansa ya daura kan kayan yana murmushi yace "Ka tashi ka shirya time na wucewa" wani kallo El-ameen yayi masa ya ci gaba da cin abincinsa, can ya ajiye abincin ya mike yana kallonsu faisal yace "Ku tashi mu je" daga haka ya nufi kofa Junaid ya fixgosa yace "Ka ma isa, da wannan kayan da kke yawo tun safe xa mu kai ka" dariya faruqh yayi yace "Gaskiya ne wnn kuma, go nd change frnd" duk yanda suka yi da El-ameen kin canxa kayan yayi, sai da wani abokinsa Dr Lawal ya sa baki, sosai kayan suka yi masa kyau don bai taba sa su ba ma, junaid sai dariya yake har su faruqh suka dinga mamaki wai ashe dai yana interacting haka da mutane shidai baice musu komai ba, Karfe takwas da rabi suka bar gidan bayan El-ameen ya sallami parent dinsa, karfe tara da kusan rabi suka isa gidan nasa, junaid ya kashe mota don shi ke driving din ya juya yana kallon El-ameen murmushi dauke fuskarsa yace "Toh gashi mun kawo ka frnd, mu iyakar mu kenan, Allah ya bada xaman lafiya.." Kallonsa kawai El-ameen ke yi, faisal yayi dariya yace "Ya ka yi shiru ango" faruqh yace "Manta da su, har ciki xa mu raka ka Dr" daga haka ya bude motar ya fita Lawal ma ya fita yana dariya yace "Fadi kawai suke, but har ciki za mu raka ka, ai dole mu bada amanarka" bude motar El-ameen ma yayi ya fita ya nufi gate din, Junaid ya dinga dariya har ya shiga da su faruqh, ya juya ya kalli faisal yace "Ba don halinsa ba mu shiga faisal" faisal yace "A'a ku shiga ku fito ina nan" daga haka Junaid ya bude motar ya fita ya shiga gidan shi ma, duk xama suka yi a parlor har El-ameen aka rasa wanda xai haura sama, junaid yace "Wai tsoro ku ke ko me, to ni bari in je in sauko da ita" daga haka ya nufi sama, El-ameen ya mike ya bi bayansa, bakin kofar dakin ya ga junaid tsaye kam, abun ya ba sa dariya yana isa bakin kofar ya tura sa cikin dakin, tana xaune gefen gado fuskarta a rufe, da sauri junaid ya juya ya fito yana kallon El-ameen yace "Meye haka kuma" El-ameen ya janyesa daga bakin kofar ya shiga dakin, bin sa junaid yayi yana shafa kai, har gabanta ya isa ya tsaya, ita dai bata dago ba har lkcn kanta a rufe, fixge mayafin El-ameen yayi, junaid ya fixgosa dan kada yayi b'aramb'arama, ita ko ta rufe fuskarta da kafarta da sauri, El-ameen yace "A ina kika san ni da har kika ce kina son aurena?" Mikewa tayi tsaye tace "I shud be asking you your silly ques.....!" shiru tayi tana kallonsa, can ta juya ta kalli junaid da ya xaro ido yana kallonta, shi kansa El-ameen din kallon mamaki yake mata, ta sulale kasa ta fashe da kuka tana kallonsu, Juyawa El-ameen yayi kamar xai tashi sama ya fice daga dakin, Junaid ya bi sa da kallo, can ya kalleta yace "Hafsat!" Ta daga kai tana kallonsa, rasa abinda xai ce mata yayi, can ya dau stool din dake gaban mirror ya xauna yana kallonta yace "Did you know him?" Girgixa kanta tayi hawaye na sakko mata, yace "Then how's this, I mean did it all happen?!" Share hawayenta ta shiga yi a hankali tace "Ni ban san sa ba, Abbansa ne abokin dad dina I think, kawai ni dai Abbana yace min he's getting me married, that's all I know...." Junaid yayi shiru kafin yace "But kinsan yan gidansu?" Gyada masa kai tayi tace "Eh nasan Ummi da Sumayya" yace "Shine dai baki sani ba kenan?" Kai ta gyada masa nan ma, junaid yayi murmushi yace "Ki kwantar da hankalin ki, Ahmad is my frnd, a childhood frnd, he will be of a good husband idan kin masa biyayya, just ki cire a ran ki cewar ba a son ranki aka yi auren nan ba, ki bi mijin ki, you will like him, infact love him ma dai" ita dai bata dago ba bata kuma ce komai ba, ya dade xaune yana bata magana masu kwantar da hankali, daga bisanni yace "Kin ji Hafsat?" Hawaye na bin kuncinta ta gyada masa kai alamar toh, yayi murmushi ya mike yace "Toh Allah bada xaman lafiya" daga haka ya fita, El-ameen kadai ya gani xaune parlor, El-ameen na ganinsa ya mike ya nufesa yace "Da kai aka hada baki aka min auren nan koh Ahmad" Junaid yace "Toh ya xa kayi da ni" daga haka ya nufi kofa El-ameen ya bi sa da kallo har ya fita. Ko da junaid ya koma gida dakin Jasmine ya fara shiga yaga har tayi bacci, rage Acn dakin yayi ya sa mata blanket ya dawo dai dai kanta ya durkusa yana kallon fuskarta murya can kasa yace "Good nyt dear" ya fad'a tare da lumshe idonshi yana bud'esu a hankali, mikewa yayi ya kashe wutan dakin ya fita, dakinsa ya shiga yayi wanka ya canxa xuwa pyjamas dinsa, ya jima xaune gefen gado daga karshe ya fita ya shiga dakin Humainah. Washegari da safe yana xaune parlor yana kallon wani movie Humainah kuma na kitchen tana hada breakfast Jasmine ta shigo parlon sanye da kayan islamiyya, kallonta kawai yake har ta karaso kusa da shi ta durkusa tace "ina kwana" kallon kofar kitchen yayi sannan ya kalleta yace "Sai yanxu kika tashi?" Girgixa masa Kai tayi tace "Wanka nayi" ido ya tsura mata ta mike xata tafi, a hankali yace "Jasmine" dawowa tayi ta durkusa tace "Na'am" yace "How was ur nyt?" Tace "Alhmdllh" yace "baxa ki islamiyya ba yau!" Ta kallesa da sauri tace "fashi?" Shiru yayi kafin yace "Yes for only today xa mu fita ne" tace "Toh" sannan ta mike ta nufi sama ya bi ta da ido. Karfe goma da wani abu Humainah ta gama shirinta ta shiga dakin junaid, ta hade rai ganin bacci ma yake, ta karasa gun gadon tace "Ya Ajay" a hankali ya bude ido yana kallonta ta hade rai sosai tace "Na fa gama" jawota yayi ta fada kansa yace "So early, nifa bacci nakeji?" ya fad'i yana lumshe ido, Ta turo baki tace "Dubi agogo fa" ya kalli agogon yace "Toh ai jiya da daddare ni ban yi bacci ba" kwace kanta tayi tace "Ni na hanaka" rikota yayi yace "Eh mana" murmushi kawai tayi tace "Ni dai ka tashi ka shirya ya Ajay" yace "Toh naji hada min ruwan wanka" mikewa tayi ta shiga bathroom din, ba a dau lokaci ba ta fito tace "Na hada" yace "Toh mu je ki min" ficewa tayi daga dakin da sauri, yayi dariya yace "Ashe bbu inda xan kai ki kuwa" sha biyu saura Junaid ya fito bayan ya shirya cikin kananun kaya, ya shiga dakinta ya ganta xaune gaban mirror yace "Toh mu je" ta mike cike da jin dadi ta dau hijab dinta da hand bag suka fita, sai da ya ga ta sauka downstairs sannan ya shiga dakin Jasmine ya sameta tana bacci, tada ta yayi ta mike xaune tana kallonsa yace "Kafin in dawo ki shirya kin ji" kai ta gyada masa ya juya ya fita, ana kiran azahar ya isa gida Humainah ta fice da sauri daga motar bayan yayi parking ta nufi cikin gidan, tabe baki yayi ya bude motar ya fito yayi part din Mumy shi ma, ko minti goma cikakke bai yi gidan ba don duk hankalinsa na kan Jasmine dake gida ita kadai, Mumy na lura da shi ita dai bata ce komai ba har ya bar gidan, Humainah duk ta ji kamar ta bi sa tunawa da tayi gida xai koma. Yana isa sai da yayi sllh sannan ya shiga gidan, ya kusa minti biyar a parlor kafin ya haura sama har xai shiga dakinsa sai kuma ya bude dakinta, durkushe ya ganta a dakin daure da towel alamar fitowarta daga wanka kenan, tana ganinsa tace "Captain Kaga towel din ya rike earring din, yaki ya cire" kin karasawa yayi dakin har sai da ta kuma kiransa, ya karaso ya durkusa shima ya shiga kokarin cire mata dan kunnen daga jikin tawul din, haka kawai hannunsa ke rawa ta daga ido tana kallonsa tace "Captain" bai ce komai ba ya kuma kasa cirewa, rike hannunsa tayi tace "Are you sick" bai kalleta ba bai kuma ce komai ba, hakan yasa ta cire dan kunnen gaba daya daga kunnenta, sai a snn ya daga ido yana kallonta, tace "Na cire" mikewa yayi ya fice daga dakin. Tana gama shiryawa ta sauko parlor ta gansa kwance idonsa lumshe, daga bayan kujeran ta tsaya tace "Captain na gama" bude ido yayi yana kallonta ya mike xaune, makullin motarsa ya dauka yace "Toh mu je" gaba ta shiga ya bi bayanta har suka fita parlon ya rufe. Front seat ya bude mata ta shiga sannan ya xaga ya bude maxaunin driver ya shiga ya tada motar, sai da suka dau hanya sannan tace "Captain ina xa mu?" Bai tanka ta ba hakan yasa tayi shiru bata kuma cewa komai ba, tafiyar kusan minti ashirin suka yi yayi horn bakin gate aka bude gate din ya shiga yayi parking, kallonta yayi ta sunkuyar da kai, ya bude motar ya fita yace "Come down" bude motar tayi ita ma ta fito ya shiga gaba ta bi bayansa, ring din bell yayi ba a dau lokaci ba aka bude, murmushi tayi ta basu hanya tace "Sannun ku da xuwa...." Junaid ya shiga parlon yace "Yauwa amarya, yana ciki kuwa" shiru Hafsat tayi bata ce komai ba, Jasmine ta hangosa tsaye bakin stairs ta wara ido tace "Uncle!" Da gudu ta karasa cikin parlon daga Junaid har Hafsat suka bi ta da kallo, tana isa gun stairs din ta rungume sa, murmushi El-ameen yayi ya janyeta jikinsa, Hafsat ta kalli junaid da ya dauke kai, ita ma ta sunkuyar da kai, kama hannunts El-ameen yayi suka dawo parlon tace "Uncle ban san nan captain xai kawo ni ba" junaid ya fiddo waya kamar xai