Showing 60001 words to 63000 words out of 170905 words
Chapter 21 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
din. Can misalin Karfe uku ihunta ya farkar da shi ya mike da sauri ya nufi dakin dai dai lokacin da nurse din ma ta fito da gudu, shiga dakin yayi ya ganta tsaye sai ihu take, ya karasa da sauri ya rike hannunta yace "Jewel!" Tsit tayi tana kallonsa, ya sauke ajiyar xuciya ya xaunar da ita gefen gado, ya juya xai fita ta mike ta bi sa da sauri, nurse din na tsaye bakin kofar fita office har lokacin yace "Taho ki rakata restroom nace babu abinda xata maki" da kyar ta karaso ta shigo dakin, shi ya kaita toilet din, ya juya yana kallon Nurse din ta karaso a hankali ita ma ta shiga toilet din ya juya ya fita. Da asuba yana kwance idonsa lumshe bayan ya dawo daga mosque yaji mutum kusa da shi, bude ido yayi da sauri ya mike xaune yana kallonta, murmushi ya sakar mata yace "Good morning jewel" dagota yayi ya xaunar da ita gefensa, remote ya dauka ya kunna mata tv, wani kallo ta dinga yi ma TVn kamar idonta xai fito, dariya ta basa ya mike ya shiga daki yaga nurse din rakube kasan gado tana bacci, yace "Nurse Sharifa" mikewa tayi da sauri tana murxa ido duk da ganinta kasan a tsorace take, yayi murmushi yace "Kin yi sllh?" Tace "Yes sir" yace "Good" toothbrush da paste dinsa ya dauko ya mika mata yace "Xaki wanke mata baki" ta karba tana kallonsa, ya fito ya dagota taki tashi idonta kyar kan TV ko kiftawan kirki bata yi, dariya ta basa sosai ya kuma dagota ta fasa masa ihu har lokacin bata dauke idonta kan kallon ba, ya dau remote ya kashe tvn, sai a sannan ta juya ta kallesa, yayi murmushi ya dagata ta mike ya shiga daki da ita, kin yarda nurse din ta wanke mata baki tayi, hakan yasa ya wanke mata da kansa, ganin hadiye komai take yasa bai mata amfani da ruwan toilet din ba, ya fita ya dauko table water ya bude ya bata ta sha ya kama hannunta suka fita, ya kalli nurse din yace "Tea xaki je ki hado min plss" ba musu ta fita sai ga ta ta dawo da cup din tea ya karba yace "Thank you, kafin ki tafi ki dawo" tace "Ohk sir" sannan ta fita, jasmine ya shiga ba tean, ta sha kadan taki shan sauran da alama tea bai dameta ba, mikewa yayi ya tafi ya wanke bakinsa toilet, juyawan da xai yi ya ganta tsaye bayansa, murmushi yayi ya kama hannunta suka fito office, ya xaunar da ita sannan ya shanye sauran tea'n, TV ya kunna mata don yana son fita ya gaida Abbansa, ai ko ta nutsu sosai tana kallon mutanen dake yawo a tvn, ya mike a hankali yanda baxata lura ba ya fita ya haura last floor xuwa office din Abbansa, wani aikin Abban nasa yasa sa, ransa bai so ba amma bai yi musu ba ya shiga yi, yana cikin yi aka yi interrupting power, ya xaro ido sanin kila yanxu xata fara ihu, da sauri ya dinga signing files din, cikin minti sha biyar ya gama ya fice, ya sauka xuwa office dinsa, yana budewa yaga wayam daki ya nufa ya tura nan ma wayam, ya xaro ido ya shiga toilet nan ma bbu ita, wani mugun tashi hankalinsa yayi ya fito da sauri ya dinga dube dube ya sauko har downstairs yana kallon nurses din yace "wata patient bata sauko ba yanxu" bai jira cewarsu ba ya fita haraban asibitin da sauri, ya dinga dube dube bai ganta ba, gun masu gadi ya nufa da sauri ya tambayesu suka ce basu ga kowa ba, komawa reception yayi ya dinga yi ma nurses din masifa basu ga wata ta sauko ba yanxun nan, nan suka shiga dube dube su ma cikin ward,haka aka yi ta nemanta cikin asibitin har da likitoci da cleaners, wasu na tunanin anya kuwa Dr El-ameen dai dai kansa yake ganin yanda ya wani rikice nurse Sharifa ma duk hankalinta ya tashi barin da tasan ba mai hankali bace patient din, har Abba sai da ya sauko jin wai ana neman patient daga bakin wani likita, kallon d'an nasa kawai yake yana son sanin wace patient ce wannan wanda shi kadai yasan da ita a asibitin, Salatin da Dr Ibrahim wanda office dinsa ke kallon na El-ameen yayi ya ja hankalin nurses da wasu likitocin, da hanxari duk aka karasa wajen aka gansa tsaye bakin office din yana kallon ciki da mamaki, El-ameen ya karasa shima yana kallon office din, tsaye take a office din duk tayi kaca kaca da uban files din dake kan table dinsa, ta bude show glass duk ta watsar da magunguna da allurorin dake ciki, El-ameen ya d'an saci kallon Abbansa da ya rungume hannu yana kallon ikon Allah, daga likitocin har nurses din kallonta suke su kalli El-ameen, hakan ya bata tsoro sosai ganin yanda aka taru bakin kofar ana kallonta, ta fasa wani shegen ihu da karfi tana kallon El-ameen, sunkuyar da kansa yayi, ta dinga ihu can ta tafi bayan glass da gudu ta labe har lokacin ihu take, da kyar ya dago kai yana kallon Abbansa yace "Abba... Brain disorder gareta, I..I... She's under medication ne Abba, jiya da xan xo na taho da ita..." Wani mugun kallo Abba ke masa yace "Asibitina yayi kama da na mahaukata?" Sosa kai yayi xai yi magana Abba ya masa wani uban tsawa yace "Uwar ka xaka gaya min, wasu mahaukatan iyayen ne suka baka 'yar su ka sata under medication har kake yawo da ita?" Ya lumshe ido ya bude a hankali yace "No, A gida nake mata treatment din Abba, dama...dama akwai injection da nake mata da daddare ne to kuma ka kirani clinic shi yasa na taho da ita... Yanxu ma xan maida ta gidansu..." Abba yace "Amma arnaye ne iyayenta koh?" Shiru yayi bai ce komai ba, Strictly Abba yace "Ka maida masu 'yar su ka basu shawaran su kai ta asibiti, na kuma hanaka aikin nan daga yau, in ma kana son concentrating a field dinka na neurology ne yanxu you can go and apply for work a psychiatry ba ka dinga yawo da mahaukata ba har kana kawo min su asibiti suna min barna" daga haka Abba ya juya ya bar wajen, nurses din ma duk suka juya, jiki a sanyaye El-ameen ya karasa cikin office din ya kamo hannunta suka fita, sai wani shisshigewa jikinsa take a tsorace, likitocin dake gun suka bi sa da kallo, hijab dinta ya sa mata suka fita xuwa gun motarsa yasa ta shiga ya tada mota yyi warming ya bar haraban hospital din. Hotel ya nufa da ita don dat was the only option a lokacin, yana parking a haraban hotel din kiran Junaid ya shigo wayarsa, yayi mamakin ganin kiran don yasan bai xuwa can gidan da safe bare ace yaje ne ya gani a rufe, ya kalli agogo yaga bakwai da wani abu, daga kiran yayi daga daya bangaren Junaid yace "I saw ur text jiya, kuma I hail you da ka nuna kai babba ne" El-ameen yace "what's he talking about" Junaid yace "Really! There's no need of pretending, kana ina yanxu" El-ameen ya kalli inda yake sannan ya gaya masa, Junaid yace "Me kake a hotel" El-ameen yayi shiru sannan yace "Why are you even asking?" Junaid yace "Magana xa muyi, shud I come over..." El-ameen yace "aikin fa?" Junaid yace "Na dau hutun sati daya..." El-ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "Good! Taho ka same ni yanxu" daga haka ya katse wayar, junaid ya sauke ajiyar xuciya ya dafe kansa don maganar da faisal yayi masa jiya ya tsaya masa, so yake yaji mai El-ameen xai ce game da shawaran faisal, in har shima ya basa go ahead xai jaraba ya ga ko me yiwuwa ne.
✍🏻
*Haske writers association*💡
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
30.....
Bude motar El-ameen yayi ya fito ya xaga ya fiddota yana rike da hannunta suka shiga reception din hotel din, babu wanda xai ganta yace mahaukaciya ce, xa a fi tunanin daga kauye ta fito duba da yanda take kalle kalle kamar idonta xai fito, tana kuma shisshige sa, daki yyi masu book aka basa makulli ya haura sama yana rike da hannunta, xaunar da ita yayi a dakin yana kallonta, tausayinta kawai yake a hankali yace "Allah ya baki lafiya jewel" ta dawo kusa da shi tana kallonsa, wayarsa ne ya soma ring ya dauka ganin Junaid ne ya d'aga ya gaya masa numbern room din da yake, cikin few minutes Junaid ya iso dakin ya murda kofa ya shigo, tsayawa yayi daga bakin kofa yana kallonsu da mamaki, El-ameen ya mike ya d'aga kafada yace "Ummi ta kusa gano abinda muke, so I had to take her away daga gidana" Junaid ya xaro ido yace "Da gaske?" El-ameen ya koma ya xauna yace "nafi tunanin gulma aka kai mata, nd I suspect that khadija" junaid ya girgixa kai yace "No! Khadija baxa taba exposing dinmu ba, kila dai kanwarka ce sumayya..." Kallonsa El-ameen ya tsaya yi yace "Sumayya kuma? Ae bata san komai ba" tabe baki Junaid yayi ya karaso dakin yana kallon Jasmine da ita ma idonta ke kansa, ya juya ya kalli El-ameen yace "Nan ku ka kwana kenan" El-ameen ya girgixa kai yace "Clinic, nd you know what sai da ta tona min asiri ta sa Abba ya ganta and he wasn't happy" Junaid bai ce komai ba ya xauna gefen gadon dakin, ta mike a hankali ta dawo kusa da shi ta tsaya tana kallonsa, ya d'an bude ido yana kallonta shima yace "Good morning!" El-ameen da ke kallonsu ya dauke kai yace "I heard you are taking her to Ogun state" Junaid yace "Yea but na canxa plan yanxu" El-ameen ya kallesa yace "To Which?" Junaid ya rufe ido na kusan second ashirin sannan ya bude a hankali yace "Faisal ya bani shawaran in aureta kawae, you know gidanmu an takura in fito da mata nan da few weeks, but kaga frnd ban san yarinyar nan ba, ban san daga inda ta fito ba, ban san meye sanadin haukatan ta ba, infact ban ma san ko matar aure bace, kana ganin shawaran faisal yayi, ya bani good reasons da yasa yace in aureta but am not even sure it will be possible ba lallai 'yan gidanmu su yarda ba" tunda ya fara magana El-ameen ke kallonsa ko kiftawa bai yi, Junaid ya kallesa jin bai ce komai ba yace "You are quite" El-ameen yayi saurin lumshe ido tara da yin wani murmushin da xa a iya kiransa da na karfin hali yace "Yea shawara ce mai kyau, may be xa a fi samun nutsuwa gun nema mata lafiya babu fargaba...." A hankali Junaid yace "Toh how xan kai ta gida a matsayin warce xan aura a haukace, kuma sai in ce ina iyayenta?" El-ameen yace "Ai tana da nutsuwa, shiryata kawai xa ayi ka hada ta da budurwa kamarta irin ace kawarta din nan ku je tare, bai fi kuyi xaman ten minutes ba ku fito just dat ka tabbatar kana kusa da ita kar ka bar wajen, matsalar da xa a samu a nan shine baxata yi magana ba but wannan ba komai bane Kawar sai tayi mata xa ayi tunanin kunya ne da ita, kuma ai gun Mumy kadai xaka kaita komai xai xo da sauki, iyaye kuma ba matsala bane xa mu san yanda xa muyi...." shiru El-ameen yayi xuciyarsa na bugawa ya rasa dalili, Junaid yace "Uhunn will this be possible kuwa?" El-ameen ya kallesa ya dan yi murmushi yace "idan Allah ya yarda" junaid ya lumshe ido yace "Toh Allah ya sa, idan Allah ya bata lafiya sai in sauwake mata ta nemi 'yan uwanta" kallonsa El-ameen yayi da sauri sai dai bai ce komai ba, Junaid yace "Toh ita mama dake kula da ita ina ka kaita?" El-ameen yace "Na sallameta" Junaid ya kallesa da sauri yace "ohh Why?" El-ameen yace "I had to, don Ummi ta tura a duba gidan" junaid ya girgixa kai yace "Toh yanxu ya za ayi da ita a nan?" El-ameen yace "I don't know" Junaid yace "Ka kira wannan nurse din na ranan mana" ba musu El-ameen ya fiddo wayarsa bayan sun gaisa ya gaya mata dalilin da ya kirata ya kuma gaya mata inda xata samesa, kafin awa daya ta iso gun, El-ameen yace "Ga kayanta nan xaki shiryata, you will be staying with her na 2 dayz plss..." Nurse din tace "But sir ina da duty a asibiti da daddare" kallon junaid El-Ameen yayi, jin bai ce komai ba yace "Ohk xa mu san yanda xa ayi xuwa ltr" Daga haka ya mike yace ma junaid xai tafi gida, Junaid yace "But am also leaving" kudi ya ciro a aljihunsa ya mika ma nurse din yace "Gashi ki siya maku abinda xa ku ci kar ki kuma bar ta ita kadai a daki" shi dai El-ameen fita kawai yayi, junaid ya bi bayansa, tana ganin haka ta mike da sauri xata bi su a rikice amma tuni suka rufe kofar, nurse din ta kamo hannunta sanin bata komai ta ja ta suka koma dakin. Umma ce xaune tare da Hajiya a parlon hajiyar, da ganinsu kasan abun duniya ya dame su, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Allah shi kyauta, amma ita suhaima don uwarta bata tabbatar da abu ba xata xo ta fadi yanxu da ta xo gidan nan ya xa muyi, ga shi matar nan ba mutunci ne da ita ba, mu dai Allah bai yiwo mu masu sa'a ba kila" Hajiya tace "Ae ni naji dadi da abun ya tsaya iya waya balki, sai kin ji maganganun da ta gayan wllh, wai in cire ido kan d'anta, maganganu dai bbu dadin ji, sai dai ban to fa ba don mu muka ja ma kanmu, uhum Allah shi kyauta dai, duk Suhaima ce ta ja mana" Umma tace "Xai kuma iya yiwuwa fa kawai rufa ma d'an nata da junaid din asiri tayi, wannan tattaccen d'an nata, kinsan kuma fa bakinsu daya da Amina" Hajiya tace "Ni wllh duk abun ya ishe ni, duk inda muka billo ba nasara wannan wace irin fitina ce, gashi ni gabana kullum cikin faduwa yake kar yace tsinannar Humainan nan yake so, kai ni na tabbata ma ita uwar xata ce ya fito da, kinga fa 'yan kwanaki suka rage wllh duk hankalina a tashe yake" Umma tayi tagumi tace "ga dukkan alama uwar nan tasa ba a xaune take ba ita ma abinda muke shi take yi, baki ga yau tun safe ta fita ba, ita da bata xuwa ko ina" Umma tace "Toh ke sai yau kika sani, ni ai tun ba yau ba nasan ita ma a tsaye take, bar ganinta haka green snake under the green grass ce wllh, amma dai akwai wani plan din da nake ta shiryawa a raina sai dai wllh ni kaina tsoronsa nake, amma hakan kadai shine mafita ba boka ba malam cikin kwanciyar hankali, sae dai kuma plan din na bukatan hadin kan mu ne, bbu bakin ciki ko nuna banbanci bare kyashi in suhaiman inma muhibbar" Hajiya tace "Haba balki, Ae mun xama daya wllh kawai gaya min wani plan ne wannan" shigowar motar junaid suka ji ko wannen su tayi shiru tana tabe baki, Umma tayi kwafa tace "ka kusa shigowa hannu yaro" Junaid na gama parking ya shiga part din Mumy, bbu kowa parlorn jin ana soye soye kitchen ya nufi kitchen din, Humainah ce kitchen din tana suyan nama, tana ganinsa ta hade rai ta dauke kai ta ci gaba da abinda take, karasowa kitchen din yayi ya rungume hannayensa yace "Fitsara kika koyo gidan Ayshan kenan?" Daure fuska tayi sosai ta kashe gas din ta rufe naman da ta soya ta juya xata fita ya fixgota ta fado jikinsa, 'yar kara tayi ya Rungumeta yana kallonta, tuni jikinta ya dau rawa ta fara turasa tana cewa "Meye haka ya Ahmad ka sake ni..." D'ago kanta yayi ta kasa kallon fuskarsa sai kokarin kwace kanta take, yayi murmushi murya can kasa yace "Ba fitsara ba!" Ta girgixa kai da sauri ba tare da ta bari sun hada ido ba tace "don Allah kayi hakuri ban gane kai bane, baxan kara ba" Muryar fatima da ya ji yasa ya saketa da sauri, ko second uku bata kara ba ta fice daga kitchen din tana tuntube, juyawa yayi shi ma ya fita yana mamakin hakan da yayi don bai taba shigen haka ba, mumynsa kadai yake runguma a rayuwarsa. Karfe hudu da wani abu yana kwance part dinsa kiran El-ameen ya shigo wayarsa, ya d'aga daga daya bangaren El-Ameen yace "ka dai ji abinda nurse din nan tace daxu, kuma baka kira kace ga yanda xa ayi ba, kai fa matsala gare ka" junaid ya d'an yi shiru sai kuma yace "Wllh ban san yanda xan ce xa ayi ba friend, baxai yiwu ka kaita ko gidan frnds dinka masu mata ba?" El-ameen yace "Kai ma ai naga kana da frnds din masu mata, ka kai ta mana" daga haka ya katse wayar, junaid ya tabe baki ya ajiye wayarsa ya koma ya kwanta, wata old time frnd El-ameen ya kira don xuwa tayi spend din daren da Jasmine ganin time na wucewa. Khadija ce kwance parlonsu misalin takwas da rabi ta fara bacci, Muhibba dake parlon ita ma xaune ta buge kafarta tace "Baxa ki kai ma ya Ahmad ruwan lipton dinsa ba ne wai kina neman kiyi bacci" kallonta khadija tayi tana murxa ido tace "Lipton kuma, a gun Mumy yake sha ai" Muhibba tace "Amma daxu ya aiko Humainah wai ki dafa masa ki kai masa, ohh bakya parlon ashe" mikewa khadija tayi tace "Da gaske" Muhibba ta tabe baki ta ci gaba da kallo abunta tace "A'a karya" Hajiya dai abincin gabanta take ci amma