Showing 66001 words to 69000 words out of 170905 words

Chapter 23 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

651

Muhibba ta tabe baki tayi hanyar daki, Umma ta jabe kan kujera ta dafe kai tace "Allah ya tsine ma tsiya!" Tsaki Hajiya tayi ta fice daga part din kamar xata tashi sama. Ray din rana ne ya farkar da Junaid da safe, ya mike xaune da sauri yana kallon agogo yaga bakwai da kusan rabi, xaro ido yayi lokaci daya abinda ya faru jiya da daddare ya dawo masa gabansa ya fadi, kalle kallen dakin ya shiga yi yana tunanin what just came over him jiya, rike kansa dake sara masa yayi, ya mike tsaye da kyar ya shiga toilet, wanke baki yayi, yayi wanka snn ya dauro alwala ya fito, ya jima xaune kan pray mat bayan ya idar da sllh daga bisanni ya mike ya isa bakin kofa ya tattara pieces din bowl din jiya da Humainah ta fasa bakin kofar ya gyara wajen ya goge ya fitar da mug din Lipton din ma. Parlor ya fito ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido. Ganin har Karfe tara ya kusa ya sa ya mike a sanyaye ya fita ya nufi part din Mumy, kasa shiga parlon Mumy yayi don bai san da wani ido xai kalli Humainah ba, da kyar ya tura kofar daga karshe ya shiga, bbu kowa parlon sai kamshi me dadi dake tashi, ya karasa ciki jiki ba kwari ya xauna, Mumy ce ta fito daga daki tana kallonsa tace "Sai yanxu ka tashi?" Kasa kallonta yayi ga wani faduwa da gabansa yake don gani yake kamar Humainah ta gaya mata, ya dukar da kai ya gaisheta, tace "Meye haka kake kamar munafuki" dagowa yayi da sauri ya kalleta yace "A'a kaina ke min ciwo Mumy" tace "Toh ga breakfast dinka can a dinning sai ka sha magani idan ka gama" mikewa yayi ya tafi dinning din ta bi sa da kallo, tabe baki tayi ta koma daki, tea kawai ya iya sha sai dube duben inda xai ga Humainah yake, mikewa yayi daga karshe ya tafi dakinsu, kwance ya sameta ita kadai fatima kuma ta tafi boko, mikewa xaune tayi ganinsa ya rufe kofar dakin tana ganin haka ta fashe da kuka tace "Ni wllh ka fita kar in kira maka Mumy" tsayawa yayi yana kallonta, tana share fuskarta tace "Ni dai ka fita" ganin ya nufota tsoro ya kamata ta fasa ihu tana kiran Mumy, still yayi yana kallonta, Mumy ta bude kofar dakin tana kallon ciki da mamaki tace "Meye haka?" Ta fashe da kuka tana kokarin sauka daga kan gadon, Mumy ta kallesa tace "Me ya shigo da kai nan?" Rasa abun cewa yayi ya fara kame kame, can yace "Ni ban san..." Wani tsawa Mumy tayi masa tace "Get out!" Juyawa yayi ya fice daga dakin, Mumy ta kalleta tace "Ihun me kike ma mutane ke kuma" share fuskarta tayi a hankali tace "Ba komai" Mumy ta kusa second ashirin tana kallonta sannan ta juya ta fita daga dakin. Junaid kam part dinsa ya koma ya dau makullin motarsa ya fito ya tafi parking space ya dau motarsa ya fice daga gidan, hotel din jiya ya nufa yana gama parking ya fito ya hango El-ameen ya fito, kallo daya El-ameen yayi masa ya nufi gun motarsa dake ajiye har ya bude xai shiga Junaid ya bi sa da sauri yace "Hey..." Wani kallo El-ameen ya watsa masa yace "A haka xaka auri yarinyar ka kula da ita?" Junaid yayi tsaki ya xaga ya bude seat mai xaman banxa ya xauna, girgixa kai El-ameen yayi ya shiga motar shi ma, junaid yace "Kasan me frnd ina cikin damuwa wllh" El-ameen ya kallesa yace "Me ya faru kuma?" Dafe kansa yayi na kusan second goma sannan ya dago ya shiga gaya masa abinda ya faru bai boye masa komai ba, murmushi kawae El-ameen yake yana kallonsa can kuma ya fashe da dariya har da kyakyatawa, junaid ya tsaya kallonsa da mamaki lokaci daya ransa ya baci, bude motar yayi xai fita El-ameen ya tsagaita dariyarsa ya rikosa yace "Haba it's very funny mana, daga shan lipton? Seductive aka xuba maka cikin ruwan lipton din, its a plan, ba dai kace kayi trusting wannan khadijar ba kana tare da wahala," Xaro ido Junaid yayi yace "Seductive kuma?" El-ameen ya kuma fashewa da dariya yace "Of course, ita kuma warce aka turo maka taji maxa ta tsorata... Ohhh my God! Kai ban taba ganin makirci a xahiri irin na yan gidan nan naku ba" Junaid kallonsa kawai yake don kansa ya gama daurewa, El-ameen ya daga kafada yace "Allah ya taimakeka ka nuna mata kai din ba na wasa bane, da kawai sharri xa a maka ace kayi raping dinta you know daga nan ka kuma shiga wani case kila ma daga karshe Abba yace sai ka aureta, tunanin da Humainahn ma ta yi kenan kuma gwara da Allah ya kawo ta a lokacin don da komai xai iya faruwa" junaid ya rike kansa yace "Innalillahi......" El-ameen ya tabe baki yace "Allah ya kyauta! Ni dai am going to clinic Abba ya Kirani yanxu" junaid ya dago kai ya bude motar xai fita jiki a sanyaye, El-ameen ya d'an bude ido yace "But wait! ina xa ka yanxu? Uhn.... kar kuma pills din bai gama sakin ka ba kaje ka afka ma....." Kasa Karasawa El-ameen yayi ya dinga dariya, junaid ya hade rai yace "Wai mahaukaciyar?" Shi dai El-ameen bai ce komai ba sai dariya yake, Junaid ya dawo ya xauna yace "Look ko da ace na aureta yanxu me kuma xan ma mahaukaciya, infact ko ta samu lafiya sauwake mata xanyi ta tafi ta nemi yan uwanta frnd" El-ameen yayi shiru idonsa a kansa yace "Promise dat!" Shiru Junaid yayi shima yana kallonsa can yace "Promise what?" El-ameen yace "That tana samun lafiya xaka sauwake mata kuma baxa ka taba 'yar mutane ba" junaid bai ce komai ba can ya tabe baki yace "Do i need to, ba dai ni nayi niyyar yin hakan ba, ohk I promise" A hankali El-ameen yace "Kuma alkawari dai kaya ne" junaid ya masa wani kallo yace "Na fi ka sanin wannan" El-ameen yace "Good, yau Thursday sai ka fara shirye shiryen kai ta gidan ku on Sunday, I promise xan yi iya kan kokarina in ga everything goes smoothly" Junaid yace "But ni ban san wanda xai mata shiri me kyau ba irin na xamani" El-ameen yace "Ba sai kayi hiring a xo har hotel a mata ba" junaid yace "Ohk" bude motar junaid yayi ya fita ya nufi cikin hotel din El-ameen ya bi sa da kallo.

✍🏻
*Haske Writers Association*💡
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

32....

Yau ya kasance Saturday Junaid na xaune tare da El-ameen sai Jasmine da ake ma gyaran gashi cikin hotel room din, nurse din da ke kula da ita ma na xaune dakin, kyar El-ameen ya kafeta da ido yana kallon yanda kwararriyar hairdresser din ke mata gyaran dogon gashinta, da ta yi motsi xai xaro mata ido hakan yasa ta nutsu sosai duk da taki tsaida kan gu daya sai bin ta matar take, da ganinta kasan bata so, tsoron El-ameen dake gabanta yasa bata nuna hakan ba, shi kam Junaid wayarsa kawai yake dannawa, har bayan kusan minti talatin matar ta gama mata gyaran gashin, nurse din sai murmushi take tana kallon yanda gashin ke sheki ga tsayi, ita kanta hairdresser din sai kallon jasmine take da sha'awa bata taba kawowa mahaukaciya bace an dai ce mata bata da lafiya, El-ameen ya warce wayar hannun Junaid ganin bai ma san an gama ba, Junaid ya kallesa da sauri yace "What?" El-ameen yace "Your I don't care attitude xai kai ka ga halaka fa" Junaid ya hade rai yace "Shi gyaran gashin xan tsaya kallo kamar yanda ka ke kallo ko me?" Tsaki yayi ya mike yana kallon hairdresser din ya fiddo dubu biyar aljihunsa ya mika mata yace "Thanks madam" ta karba da hannu biyu tana murmushi tace "Baxa a mata kunshi ba?" Ya juya ya kalli El-ameen, El-ameen ya kauda kansa, d'aga kafada yayi yace "A'a no need" matar tayi masu sallama ta fita daga dakin da jakar kayan aikinta. Sai a sannan Junaid ya kalli kan jasmine dake xaune har lokacin bata tashi ba sbda El-ameen, kauda kai yayi ya koma ya xauna yana kallon El-ameen yace "Look frnd ni ban san da warce xan hada ta mu tafi ba fa gobe... Am confuse" El-ameen yace "Kai baka san da warce xaka hada ta ba sai ni?" Tsaki Junaid yayi yace "Ni matsalata da kai kenan, cikin nurses din clinic din ku babu sa'arta??" El-ameen yace "Babu!" Kallonsa kawai Junaid yake, El-ameen yace "Ba na ga kwanaki ka tsaya kula wata yarinya a mall ba har da karban numberta, just call her ka nemi favour wajenta, naga wayayya ce" Junaid yayi shiru yana kallonsa lokaci daya yana son tuno sunanta, can yace "Koh?" El-ameen ya d'aga kafada, Junaid yace "But ni ban taba kiranta ba fa, sai in ce mata me?" El-ameen yace "Ka fini sanin me xaka ce" Junaid ya dau wayarsa yana son tuna sunan da ya sa mata, can sunan ya fado masa yace "Yes Hafsat I think" numberta ya duba yayi dailing, bugu uku ta d'aga ya kalli El-ameen sannan ya mata sallama, amsawa tayi daga daya bangaren, yace "Hafsat?" Tace "yea" ya d'an shafa kansa yace "Ahmad Junaid, wanda kika ara ma motar ki kwanaki" tace "Ohk kwana biyu?" Yace "Alhmdllh, kina gida ne?" Tace "No ina school," yace "Which?" Tace "Al-qalam..." Yace "Alryt xan xo in same ki later, I will cal you idan na xo" tace "Ohk.." Sallama yayi mata ya katse wayar, El-ameen ya tabe baki ya mike ya karasa kusa da jasmine ya dagota sanin saboda shi ne taki tashi, ae da sauri ta mike ya dawo da ita kusa da su, ya dauki ragowar Irish dinta ya ajiye mata gabanta. Da yamma El-ameen na office Junaid ya xo ya samesa, ya ja kujera yace "Na je na sameta, i've explain everything to her and tace babu damuwa, gobe around Eleven xa mu tafi saboda sai ta fara xuwa makaranta" El-ameen ya tabe baki yace "Ohk" Junaid yace "I prefer ta sa hijab then veil" El-ameen yace "Ohk, sai ka je kasuwa ka siyo mata sabo har kasa milk colour tunda kalan gold ne kayan" Junaid yace "Ka raka ni mana..." El-ameen yace "as you can see am busy, idan tsoron mutanen kasuwan kake sai ka ba nurse din dake wajenta kudi taje ta siyo kai sai ka tsaya da ita kafin nurse din ta dawo" Junaid ya mike yace "Ohk" sannan ya juya ya fita, bin sa da kallo El-ameen yayi yana girgixa kai, can yayi murmushi ya ci gaba da abinda yake. Washegari lahadi junaid ya rasa me ke masa dadi, bai san yanda Mumy xata dauki jasmine a matsayin warce yake shirin aure ba idan aka gano bata da hankali, Karfe takwas da wani abu ya shigo parlon Mumy, Humainah ce ke ta goge goge a parlon, tana ganinsa tayi hanyar daki ya bi ta da kallo, tun daga incident din ranan take avoiding dinsa, dakin Mumy ya tafi ya sameta tana gyaran dakin, ya gaidata ta amsa tare da cewa "Jiya Karfe nawa ka dawo gidan nan?" Ya shafa kansa yace "Tara saura, naga kamar kin yi bacci ne shi yasa ban shigo ba" bata ce komai ba ya juya kamar munafuki ya fita, a tsatstsaye yayi breakfast ya fita xuwa gaida Abbansa, Hajiya ce parlon tana hada masa breakfast, ya xauna kasa ya gaida Abbansa sannan ya gaisheta, tayi murmushi tace "Lafiya lau Ahmad" ya kusa minti biyar xaune parlon jin Abba bai ce masa komai ba ya mike yayi masa sallama ya fita. Karfe goma saura Junaid ya shirya yayi ma Mumy sallama ya fita, Mumy dai jin sa kawai take da yace ranan xai kawo mata surkarta, yana fita gidan Hajjo ta diro da 'yar Jakarta babu notice. Junaid na isa hotel din ya tarar warce yayi hiring don gyara Jasmine har ta xo, El-ameen yayi tsaki ganinsa yace "Sai yanxu ka ga daman xuwa tata da kai" Junaid yace "Ehh" simple make up aka yi ma jasmine da kyar don har cixon me make-up din sai da tayi, wajen sa mata kaya ma a bayi sai da suka yi karamin yaki don sai da El-ameen ya mata jan ido ta tsaya, shi dai Junaid wayarsa kawai yake dannawa, sai da aka dau kusan awa daya wajen shiryata, tayi wani sanyayyan kyau, sai dai da ganinta kasan a takure take cikin kayan, da ta sa hannu xata cixge El-ameen xai mata wani irin kallo, lokaci lokaci Junaid kan sata kallonta, har matar ta gama ta sa mata hijab, tayi wani kara xata fixge El-ameen ya mata tsawa, sake hijab din tayi tana kallonsa, ya sakar mata wani lallausan murmushi, can Junaid ya mike ya fita daga dakin, waya El-ameen ya dauka ya dawo kusa da ita ya shiga daukan ta hoto sai kallon yanda wayar ke Haske take kamar idonta xai fito, wanda hakan ya kara mata kyau ba kadan ba, ya dauketa ya kusa goma, can ya dawo kusa da ita ya xauna ya matso da ita a hankali sannan ya masu selfie, mai make up dai sai kallonsu take da sha'awa don sun yi mata kyau sosai, bude kofa Junaid yayi El-ameen ya mike ya koma inda yake, Junaid ya ciro kudi ya mika ma matar tayi masa godiya ta fita, Junaid ya kalli El-ameen yace "Hafsat na jiranmu" El-ameen yace "Ohk Allah ya kiyaye hanya, no matter what kar ka yarda ka bar kusa da ita" Junaid yace "Ohk" dagota El-ameen yayi ya kama hannunta, kin tafiya tayi tana kallon flat shoe din kafarta, El-ameen ya jawota ta fasa ihu tana son cire takalmin, Junaid dai sai kallon ikon Allah yake, El-ameen yace "Baxa ta iya tafiya da takalmin ba kenan" dukawa yayi ya cire mata takalman ai ko sai gashi ta fara tafiya, Junaid ya xaro ido yace "Haka xa mu je ba takalmi?" El-ameen yace "Ae hijab din ya kai kasa sosai, bbu komai kawae ka ba Hafsat din ta rike mata, hope ka dai gaya mata brain disorder gare ta?" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Tabdi!" Daga haka ya juya ya fita, El-ameen yayi murmushi ya bi bayansa yana rike da hannunta, kallonsu kawai ake tun daga cikin hotel din har suka fito haraban hotel din, junaid na isa gun motarsa ya juya yana kallonsu, wani mugun faduwa gabansa yayi suna hada ido da ita, ya tsura masu ido su biyun, a hankali take tahowa kamar me tausayin kasa, El-ameen na rike da ita har suka iso gun motar ya bude front seat ya shigar da ita, junaid ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Jikina na bani baxa mu yi nasara ba..." El-ameen ya girgixa kai yace "No! Allah xai daura ka kansu, just pray before going in, nd ka nuna masu ba ta da lafiya ka taho da ita, kaga hakan baxae sa a takurata tayi magana ba, kuma duk me aka ajiye mata kayi saurin dauka ka bude ka bata, if not saukowa kasa xata yi ta xauna ta jawo gabanta, though in TV a kunne yake ma ba lallai ta lura da komai na parlon ba attention dinta gaba daya xata ba Tvn, idan kaga kallon xai yi yawa kawae ka kashe Tvn ma, don't force her on anything don sai ta iya maka ihu" a hankali junaid yace "Ohk!" El-ameen yayi murmushi ya gyada masa kai, juyawa junaid yayi ya bude mota ya shiga ya tada suka bar haraban hotel din, a hanya ya dau Hafsat kamar yanda suka shirya, sai kallonta Hafsat take gaban mota don ita bata ga alamar hauka tare da ita ba, junaid na kallonta ta madubi yace "Bata yi kama da mahaukaciya ba koh?" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba har suka iso gida, a parking lot ya ajiye motar, sai a sannan yaji gabansa na faduwa, ya juya yana kallon Hafsat yace "plss xaki kama hannunta..." Ta yi shiru sai kuma tace "Baxa ta min komai ba" ya gyada mata kai yace "Yea baxata maki komai ba" bude motar yayi ya fito ita ma ta fito, ya xaga xuwa daya side din ya bude ya fito da ita, kalle kalle kawai take idon nan Maa shaa Allah, Hafsat ta kasa karasowa don duk tsoro ya cika ta, Junaid yace "No plss kar ki sa a xargi abu, wllh baxata maki komai ba, xo ki riketa plss" da kyar ta karaso tana kallon Jasmine, yana d'aga kai yaga Umma da Hajiya xaune balcony as usual wani mugun bugu xuciyarsa yayi, ya dauke kai da sauri yana kiran Allah a xuciyarsa. Hafsat na mika hannu xata rike nata tayi bayan junaid da sauri, kiris ya rage xuciyarsa ya shige cikinsa don yayi xaton ihun nan nata xata yi, ganin yanda su Umma ke ta lekosu yasa kawai ya kama hannunta ya nufi part din Mumy, Hafsat ta bi bayansa da sauri.

✍🏻
*Haske Writers Association*💡
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_

33.....

Mikewa Hajiya tayi da sauri tana kallon kafar Jasmine tace "Balki tashi ki ga ikon Allah" da sauri Umma ma ta tashi ta bude baki tana kallon kafarta, a hankali Junaid ya tura kofar parlon ya shiga gabansa na faduwa, babu kowa parlon ya karasa ciki yana rike da hannunta har lokacin ya isa 3 sitter ya xaunar da ita shi ma ya xauna ya kalli Hafsat ya nuna mata gefen jasmine, ta karaso ta xauna suka sa ta tsakiya, kalle kallen parlon kawai jasmine ke yi, yana son xuwa ya sanar ma Mumy xuwansu amma yana tsoron kar ta bi sa, haka suka ta xama parlon, Hafsat dai sai kallonsa take ganin bai da niyar ta shi ya sanar da mutan gidan xuwansu, fatima ce ta fito parlon, ta d'an xaro ido ganinsa tace "Lah Ya Ahmad!" yace "Kira Mumy" kallon Hafsat tayi ta gaida ta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login