Showing 48001 words to 51000 words out of 170905 words
Chapter 17 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
fito da plate dauke da potatoe da ketchup a gefe ta ajiye gabanta, El-ameen yace "Shikenan mama xa ki iya tafiya kar dare ya maki a hanya" Mama tace "Toh," ta maida dubanta ga khadija tace "Da kin ga ta nufi sama toh kilan bayi take son shiga, ko kuma tana son xuwa ta xuba ruwa jikinta, tana son tea sosai don Allah a dinga mata, sai wannan abun da na soya mata da kunu" Khadija tace "Toh" El-ameen ya ciro dubu talatin ya mika mata yace "Ga kudin mota mama sauran sai kiyi ma mai jego siyayya" dukawa tayi ta karba tana ta sa masa albarka, ta karasa ta shafa kanta tace "Sai na dawo diyata, Allah ubangiji ya yaye maki" kamar taji me tace ta mike da sauri, mama tayi murmushi ta dau jakarta bayan ta gyara kayan da ta xubar mata, tayi wa El-ameen sallama ta nufi kofa, ai da sauri ta bi bayanta El-ameen ya mike yyi dariya yace "ta fa gane tafiya xa Kiyi" shigewa jikin mama tayi, mama tayi dariya tace "Ikon Allah, baxan dade ba 'ya ta jibi xan dawo kin ji" El-ameen ya karasa ya janye ta daga jikin mama ta fasa wani kara xata kwace kanta yayi mata tsawa, tsit tayi tana kallonsa, mama ta juya ta fita cike da tausayinta, yana rike da ita suka koma parlon ya xaunar da ita gefensa hawaye ya gani idonta, khadija ta xamo kasa ganin hakan a hankali tace "She's crying" kallonta yayi yace "Tafi kitchen ki debo min ruwa" mikewa tayi ta nufi kitchen din, tana shiga ya dafata ya lumshe ido a hankali yace "Am sorry jewel, mama xata dawo soon kin ji" dogon hancinsa ya ji ta ja kamar yanda yake mata ya bude ido da sauri, sai kuma yayi murmushi ya lakaci nata hancin a hankali yace "Pretty~Jewel"
✍🏻
*Haske Writers Association*
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
23......
A hankali ya dago kanta yana kallonta, ya ciro handkerchief aljihunsa ya share mata idonta murya can kasa yace "Am sorry jewel" yana jin fitowar khadija daga kitchen yayi saurin dauke hannunsa a shoulder dinta ya koma baya, ta karaso parlon ta mika masa cup din ruwan, ya amsa ya ajiye sannan ya saukar da ita kasa shi ma ya sauko, dankalin da mama ta ajiye parlon ya jawo ya dauka ya hada da tomatoe ketchup ya kai bakinta, ta sa hannu ta karba ya sake mata, ta lashe tomatoe din, khadija tayi murmushi ta dawo kasa d'an nesa da su ta xauna tana kallonta, haka ta dinga shan tomatoe din kanta a kasa, ya tsura mata ido yana kallo, ta d'ago manyan idonta ta sauke kan nasa, dauke nasa yayi ya mike ya koma kan kujera yace "tafi kitchen ki hado mata tea khadija" khadija ta kama hanyar kitchen yana ganin haka ya kuma saukowa ya dawo ya xauna gabanta ya dau potatoe ya kai mata baki xata kauda kai ya rike kan ya hade rai ya tura mata dankalin yace "Eat!" taunawa ta shiga yi tana kallonsa tana yamutse fuska, ya kalli kofar kitchen sannan ya kalli ragowar ketchup din dake gefen bakinta, ya matso a hankali ya sa yatsa ya kwashe ketchup din ya lumshe idonsa ya kai baki, dai dai nan aka bude kofar parlon, ya koma baya da sauri yana goge bakinsa, Junaid ya shigo parlon, kallo daya yayi masu ya sunkuya ya shiga cire takalmi da safar kafarsa, El-ameen ya mike ya koma kujera yana shafa kai, karasowa cikin parlon Junaid yayi, yana sanye da trouser din uniform dinsa sai farin polo, El-ameen na kallonsa yace "Gud you came, so ya xaka yi da ita da nyt?" Xaunawa Junaid yayi bai ce komai ba, ta dauki plate din gabanta ta mike ta dawo kusa da shi ta daura kan kafarsa, murmushi ya d'an yi ya rike plate din yace "No! Thank you" El-ameen ya dauke kai hade da tabe baki, khadija ta fito rike da cup din tea ta ajiye tana kallon Junaid tace "Welcm bro" yace "Thank you, how about you telling Hajiya you will be spending the nyt at ur frnd's place?" Shiru tayi sannan ta langwabar da kai ta xauna tace "Kasan Abba yana nan" shafa kansa yayi bai ce komai ba ya dauke plate din da ta daura masa a kafa ya ajiye kasa, El-ameen ya d'aga kafada ya mike ya haura sama, kallon khadija Junaid yayi, tayi murmushi tace "Wai yaya ka ban labarin inda Ku ka ganta mana, dama kun santa ne?" Junaid yace "I donno for El-ameen" tablets dinta El-ameen ya dauko a sama ya dawo parlon, sai da ya fara shiga kitchen yayi diluting dinsu sannan ya fito, ba musu ta bude baki ya juye mata tana yatsina fuska, Khadija tayi murmushi ta daura kanta jikin Junaid a hankali tace "I like her Ya A.jay" murmushi yayi bai ce komai ba, El-ameen yace "I will be going back to clinic yanxu, nan da thirty mins xata yi bacci, duk inda ta kwanta ki kyaleta kawai" a hankali khadija tace "Ni fa ina jin tsoro, tafiya duk xa ku yi ku bar mu" El-ameen ya harareta yace "An ce maki bata komai da'alla" Junaid ya tashi shima yace "Baxata maki komai ba sister, am also leaving" shiru tayi bata ce komai ba, El-ameen yayi hanyar kofar, Junaid ya bi bayansa, da sauri ta mike ta nufe su khadija ta bi ta da kallo gabanta na faduwa, gun Junaid ta nufa, El-ameen ya juya yana kallonsu, shima Junaid kallonta ya tsaya yi, tsaki El-ameen yayi ya xaro mata ido yace "C'mon koma kar in baki knock" kara ta saki kamar ta ji abinda yace, El-ameen ya fice daga parlon, Junaid yayi murmushi ya kama hannunta suka koma parlon ya xaunar da ita yana kallonta yace "Look Jasmine xa mu dawo anjima kin ji, khadija will be staying with you har mu dawo" Khadija tace "Waow yaya sunanta Jasmine?" Da sauri ya kalleta don ya manta gaba daya tana gun, yace "Ohh! Did I call her dat" khadija tayi dariya tace "Ehh mana" ya mike yace "No I didn't" ihu ta fasa ta mike da sauri ganin ya tashi, Khadija ta langwabar da kai tace "Yaya ba ka baro gun aiki ba, stay with her plss, bata son ka tafi" yace "Am hungry, gida nake son tafiya in ci abinci" khadija tace "Ae Akwae food stuffs a nan ba sai in girka maka ba" shiru yayi sannan yace "Alryt ki min indomie kawai" tace "Toh" ta mike ta shiga kitchen, xaunawa yayi ya xaunar da ita gefensa yayi murmushi ya ja dogon hancinta yace "I will stay with you Jasmine" suna nan xaune har khadija ta dawo parlon rike da tray me dauke da indomie da fried egg a gefe sai roban ruwa da cup ta ajiye kasa tace "Gashi yaya" saukowa kasa yayi ita ma ya sauko da ita suka xauna sai kallon indomien take kamar idonta xai fito, murmushi yyi ya kalli Khadija yace "Ke baxa ki ci ba" ta girgixa masa kai tace "Na koshi" daukar fork din yayi ya debi indomie kadan ya kai mata baki bayan ya d'an huce, wani kara da yasa shi sakin fork din tayi khadija ta mike da sauri ta bar wajen, ta dinga ihu tana komawa baya tana kallon indomien duk ta ruda shi, ya riketa yana cewa "What happen jasmine, bakya so ne" ihu kawae take tana komawa baya, ya kalli khadija yace "Take it away" dauka tayi ta nufi kitchen da sauri, tsit tayi ta bi khadija da kallo, ta dawo kusa da shi ta xauna, shi kam kallon mamaki kawai yake mata, hannu ta sa ta taba long lashes dinsa, yayi murmushi ya cire hannunta yace "Indomie kike tsoro Jasmine" khadija ta fito tace "Yaya kila tsoron shi take ji, kaje kitchen ka ci" ya girgixa kai yace "no idan naje gida xan ci abincin" kallonta Junaid yayi jin ta jingina jikinsa ya ga bacci ya fara daukarta, ya mike ya kwantar da ita kan kujeran, khadija tace "Baxa ta fadi ba yaya?" Yace "Ehh, bari in tafi gida in dawo yanxu tun da tayi bacci" a hankali khadija tace "Toh amma ka dawo kafin ta tashi plss Allah tsoronta nake ji" Junaid yace "Ohk" yana fita ta dawo kusa da ita a hankali ta xauna tana kare mata kallo, doguwa ce yar siririya da ita, ta tsura ma kyakkyawan fuskarta ido da d'an karamin jan bakinta dake sheki, Khadija ta kama long fingers dinta a hankali tace "I like you sister, Allah ya baki lafiya" kallon hular kanta tayi ta dawo wajen ta d'an cire hular tana lekan kanta ta ga bakin gashinta sai sheki yake, fito da gashin ta shiga yi ta bude ido ganin tsayin gashin, ta lumshe ido tace "Waoww!" Haka tayi ta xama kusa da ita tana kallonta, komai na jikinta me kyau ne, mamaki ta dinga yi inda suka samota har suke son warkar da ita, to yan uwanta fa?? Mikewa tayi jin ana kiran la'asar taje tayi alwala tayi sallah, sannan ta d'an gyara gidan ta dawo ta xauna ta ci gaba da kallonta daga inda ta tsaya, bude kofa taji anyi ta juya da sauri, taga El-ameen ne, ya karaso parlon yace "Capt ya tafi ne" ta gyada masa kai, ya iso kusa da su yana kallonta yace "She's still sleeping koh?" Ta gyada masa kai, ajiye ledan hannunsa yayi ya tada ta ya tafi sama da ita, khadija ta hade rai ta bi sa da kallo, haka kawae taji haushin abinda yayi, ta ja tsaki ta dauke kanta hade da tabe baki ta mike ta koma kujera ta xauna, ba a dau lokaci ba ya sauko, kallonta ya tsaya yi ganin yanda ta hade rai yace "Ke in kin gaji ne tashi ki tafi gidan ku" mikewa tayi ta dau Jakarta ta fice fuu, yayi tsaki ya dau wayarsa da ke ring. Tana fita ta kira Junaid yana d'agawa yace "Ta tashi ne?" tace "Wani tashi? Bayan ya wani ce wai in tafi" Junaid yace "Wa?" Tace "Ya El-ameen mana, wai wani in tafi gida" shiru ya d'an yi kafin yace "Saboda me?" Tace "Oho masa, ya wani dauketa ya kai ta daki bayan bacci take" mikewa Junaid yayi daga zaunen da yake parlon Mumy yace "daki kuma, ke kina ina?" Khadija tace "Ehh mana, ni na riga na fito ma tafiyata xan yi" katse wayar yayi kawai ya ajiye, Mumy dake ta kallonsa tace "Wani dakin? Kuma da wa kake waya" Kallonta yayi da sauri don ya mance tana wajen yace "Ohh dama, dama na aiketa ne, shine... no wai ce min tayi yayarta ta kulle ta a daki, khadija ce" Mumy na masa wani irin kallo tace "Karya kake" ya xaro ido yace "Mumy karya kuma" ta girgixa kai tace "Ahmad am beginning to suspect you this days, behaviours dinka sun fara canxawa, i notice kana boye min wani abu, but be careful" daga haka ta shiga bedroom, Humainah dake xaune parlon ita ma tana gyada kai tace "ta tashi ne? uhnn ko waye ya tashi oho, daki kuma? Uhnn ko wani dakin yake nufi oho, ke kina ina? Uhn ko wacece haka oho, hmm we are beginning to suspect you this days Captain be careful" wani harara ya watsa mata ta mike tayi masa gwalo tace "In tayi tsami ma ji dai" da sauri ta shige dakin Mumy ita ma. Ya shafa kansa a hankali don yasan ko hauka yake baxae bari Mumy taji xancen mahaukaciyar nan ba, tabdi! mikewa yayi da sauri ya dau makullin motarsa ya fita, waje ya fita don bai shigo da motarsa compound ba ya hau motar ya nufi gidan El-ameen, cikin few mins ya isa, yana Parkin ya fito ya shiga gidan, xaune ya tarda El-ameen balcony yana waya, ya tsaya yana kallonsa har ya gama ya hade rai yace "Y did you send khadija away?" El-ameen yace "Haka tace maka, to let me get hold of her" Juyawa Junaid yayi jin an bude gate, wata mace da baxata wuce 27 ba ta shigo, ta karaso balcony ta gaida Junaid, ya gyada mata kai kawai, mikewa El-ameen yayi yace "Welcm, ki shiga daga ciki" ba musu ta shiga parlon, El-ameen yace "we are hiring her for 2 dayz kafin Mama ta dawo, sai ka biyata 10k, old nurse din clinic din mu ce" Junaid ya daga shoulder yace "Anyhow" juyawa yayi yace "sai gobe, na tafi" El-ameen yace "Wato xuwa Kayi ka ga what I was up to da nace khadija ta tafi koh?" Junaid yayi murmushi bai ce komai ba yayi gaba abunsa, El-ameen yayi kwafa ya shiga parlon. Karfe shidda da wani abu Junaid ya shigo gida, ya ga khadija tsaye nesa da balconynsu, Hajiya da Umma na xaune sai Sadiya da Suhaima, Sadiya sai cewa take "Kawai ki bar min komai a hannuna Hajiya idan na lallasa ta xata fadi inda taje wllh" Umma tace " Ni tun da ta fara mu'amala da shegiyar 'yar da aka kawo gidan nan Humainah take kowa, dabi'un ta suka canxa, ke har kin kai matsayin da xa Kiyi karyan xuwa gidan kawa ki fita tun safe sai yanxu kike shigo mana gida don Kazan ki" junaid ya karasa wajen ya gaida su yace "Hajiya tare muka fita, ta rakani ne" Umma ta watsa masa wani kallo tace "Da yake ba Aysha bace ko Fatima dole ka kareta mu bar ta ta lalace" Juyawa khadija tayi fuu ta nufi part din Mumy, Hajiya ta shiga kwala mata kira tana cewa "Kika kuskura kika shiga wajen nan mai raba ni da ke sai Allah, kuma wllh kin ji na rantse sai kin fadi daga inda kike"
✍🏻
*Haske writers Association*💡
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
24.....
Junaid ya juya shi ma ya bar wajen, Hajiya ta bi bayan khadija tana huci, a balcony ta tsaya ta tura kofar tana cewa "Kar ki bari in shigo parlon nan khadija, tun muna mu biyu ki fito ki wuce" tsayawa Junayd yayi yana kallon ikon Allah, Humainah dake xuge jakar kayanta da ta gama hadawa a parlor ta tabe baki ta mike, ta dauki remote din TV ta kure maganar gaba daya, Hajiya ta xaro ido tana kallonta, ji take kamar ta shaketa kawai ta huta, can dai tace "Ke wai ni sa'ar uwar ki ce kika raina ni haka a gidan nan, ina magana za ki kure min TV?" Humainah ta rike kugu tace "Ni ba dai uwata ba wllh" Sadiya ta karaso bakin kofar parlon tana cewa "Bata fito bane Hajiya" Hajiya ta fashe da kuka tace "Yanxu ni yarinyar nan take ma rashin kunya Sadiya, a haihuwar kaji ban yi jika da shegiyar ba" a fusace Sadiya ta shige parlon tayi kan Humainah, Junaid na ganin haka ya bi bayanta, ai tuni Humainah tayi dakin Mumy da gudu tana kwala mata kira, hakan kuma bai hana Sadiya bin ta ba tana kunduma mata xagi, wani tsawa Junaid yayi mata tun kan ta shiga dakin Mumy ya fixgota ya nuna mata kofa yace "Get out, ko a mafarki kika kuskura kika yi attempt din t'aba ta wllh sai na ba66allaki a gidan nan" kallonsa kawai take fuskar nan nata daure don tasan tana iya magana yanxu ta sha mari, Hajiya ta shigo parlon tana huci tace "Wllh Ahmad idan ka bari na saka ka gaba a gidan nan sai xaman duniyar nan gaba daya ta gagare ka, kayi hankali da ni ka bi ni a hankali, bani da kyau wllh, amma in dai ni ce mu je xuwa sai ka gwammace uwar ka bata haifo ka gidan nan ba, xaka san da ni kake" Mumy ta fito tana ma Hajiya wani kallo tace "Babu abinda kika isa ki masa wanda Allah bai masa ba, mu da Allah muka dogara, aniyar ki ta bi ki kuma" Hajiya tayi shewa tana murmushi tace "Toh mu xuba da ku," daga haka ta juya fuu ta fice, Sadiya ta bi bayanta. Junaid ya girgixa kai ya juya ya fice daga parlon, shi gaba daya xaman gidan ma ya ishe sa kawai. Mumy ta kwalo ma Humainah kira ta fito, strictly tace "ina raba ki da mutanen nan baki ji ko Humainah, ina ruwan ki da su wai da har xaki dinga shiga tsabgarsu, kinsan Allah baxa mu shirya ba idan magana za ki dinga dauko min, so kike su sa ki gaba kema koh? To maxa gama hada kayan ki yanxun nan Ahmad ya tafi da ke inda xai kai ki kafin Abba ya dawo su kuma hada ki da shi" Juyawa Humainah tayi ta koma daki kamar xata yi kuka, Khadija ta fito daga daki tace "Mumy kiyi hakuri," Mumy tace "Kinga idan kin yi laifi ki daina yo wa nan khadija, sai ki tsaya can ki basu hakuri" Khadija ta turo baki ta koma dakin su fatima. Junaid na shigowa bayan yayi wanka ya canxa kaya Mumy tace "Maxa kai ta gidan Aisha kan dare yayi Ahmad" ya kalli agogo don dama fita xai yi ya maida motar jiya, yace "Toh Mumy" Mumy ta kwalo ma Humainah kira tace "Dauko jakar ki da hijab" tana kumbure kumbure ta fito rike da 'yar jakar kayanta da Hijab, Junaid ya mike yace "Sai na dawo Mumy" Mumy tace "Allah ya kiyaye, amma motar waye ka dawo gidan nan jiya da?" Ya d'an shafa kai yace "A frnd, idan na ajiyeta xan mayar ne ma" Mumy tace "Ohk," ya fita Humainah na biye da shi a baya, Mumy tayi murmushi tace "Ba sallama Humainah" kamar xata yi kuka ta daga mata hannu ta fice, Mumy tayi dariya tace "Lallai Humainah" As usual Hajiya da Umma na balcony, duk suka bi su da hararan tsana, tsayawa yayi har Humainah ta karaso inda yake ya karbi jakar hannunta suka nufi parking lot, Umma ta kalli Hajiya tace "Ke wllh naga kamar sonta yake, dubi fa har da wani rike mata jaka, sai ya iya yiwuwa ma ya fito