Showing 147001 words to 150000 words out of 170905 words
Chapter 50 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
else...." Ya wara ido yace "Really? A ina kika san ni toh?" Shiru tayi kafin tace "I think... Ohk sorry it might be a dream" yana gyada Kai yace "That's woaw, a ina kika gan ni a dream din?" Kallon El-ameen dake ta kallonsu tayi tace "Wani waje, I think it's a garden... Ohh I really can't remember, yes a garden..." murmushi sosai Aliyu yayi yana gyada kai yace "It's a pleasure meeting u in dream land" bata kuma tanka sa ba ta dauke kai. Suna sauka kt El-ameen ya tare masu taxi, sun dau hanya Zahrah tace "Ina xa mu yanxu?" Kallonta yayi yace "My home, Hafsat will be glad to see you" girgixa kai tayi tace "Noo! Kai ni gun Granny din Ahmad Junaid" kallonta El-ameen ya tsaya yi, can ya lumshe ido yace "Ohk, Alryt" daga haka ya fadi ma me taxin inda xai kai su, Aliyu yace "Bari in sauka nan, kar ya rainani idan ya sake ganina gidansu" murmushi kawai El-ameen yayi yasa mai taxin yayi parking Aliyu ya sauka, El-ameen yace "Thanks frnd sai mun yi waya" d'aga ma Zahrah da Ummi hannu Aliyu yayi ya bar wajen. Suna isa kofar gidansu Junaid El-ameen ya fara fitowa sannan Ummi da Zahrah, ya ba mai taxin kudi ya kallesu yayi murmushi yace "Mu je" bin bayansa suka yi ya nufi gate. Part din Hajja ya nufa da su, khadija ce kwance parlon da Rahma mikewa xaune suka yi gaba daya suna kallonsu barin Khadija dake ta kallon Zahrah, El-ameen yace "Hajja fah?" Rahma xata yi magana sai ga Hajja ta fito cike da masifa jin muryar El-ameen, sororo ta tsaya tana kallon Zahrah, El-ameen yace "Kin yi bakuwa Hajja..." Wani shewa tayi ta karaso ta rungumeta tace "Ikon Allah, dama idan Allah ya so ka da arxiki duk nacin mahassadi sai dai ya mutu don sai kayi arxikin nan, sannu yar sarki jikar sarki, kiri kiri suka gudu suka bar ni sai gashi kin xo daukata..." El-ameen yayi murmushi ya nuna ma Ummi dake ta kallon ikon Allah kujera ta xauna, ya kalli Zahrah yace "Xan dawo da dare" daga haka ya fice daga parlon, Hajja ta rasa inda xata sa Zahrah da yar uwarta kawo wancan kawo wannan duk ta cikasu da kayan ciye ciye, Su khadija suka xama 'yan kallo, hannun Zahrah ta kama daga karshe tace "Mu je ki gaida Amina ita daya ce mata a gidan yanxu, kinsan sauran duk nasa an mayar da su gida, sbda jikokina da suka sa ma ido barin Ahmad" Ita dai Zahrah bin ta kawai take har suka shigo parlon Mumy, nan gabanta ya shiga faduwa, Fatima ce ke shara a parlon, Hajja tace "Ke ina uwar ki?" Fatima na kallon Zahrah tace "yanxu ta fita kasuwa...." Hajja tace "Toh dama wa xai aike ku ya sha takaici duk baku da amfani ai, Ahmad din na ciki har yanxu?" Girgixa kai fatima tayi tace "Yana bangaren sa" kama hannun Zahrah Hajja ta kuma yi suka fita tana cewa "Mu je ki gaida sa ba lafiya, kinsan Allah baya kyale ma ci amana da mai bakin ciki.... Toh abinda ya samu Amadi kenan" d'an murmushi Zahrah tayi duk da bata gane inda xancen Hajja ya dosa ba, bbu kowa parlon junaid haka yasa ta kuma jan ta har bedroom, ita dai gabanta ya ki daina faduwa tana biye da ita, yana xaune gefen gado idonsa na kan abinda Humainah take, sanye yake da 3qtr da singlet fari, kana ganinsa kasan har lokacin he's not his self, Humainah kuma na durkushe gabansa tana xuba masa pepper soup din kayan ciki da Mumy tayi masa, juyawa suka yi gaba daya suna kallon bakin kofar, Hajja ta washe baki tace "Amadiii...." Kallon mamaki kawai yake ma Zahrah ko kiftawa babu gani yake kamar mafarki yake, ita kanta kallonsa take ta kasa karasowa, Hajja ta janyo ta hakan yasa ta saurin dauke kai daga kallonsa Hajja tace "Mai martaba ne ya turo ta ta gaisheni...." Humainah da tayi ma Zahrah kallo daya bata kuma dago kanta ba, xuba pepper soup din kawai take ba tare da tasan abinda take ba ga wani bugu da xuciyarta yake, Can ta mike bayan ta rufe kulan xata fita Hajja ta fixgota tace "Keee baxa ku gaisa ba, me sunata kenan fatima, ita ce wanda yayanki ya ceci rayuwarta tana ganiyar hauka, baki ganeta bne..." Humainah da xuciyarta ke bugawa har lokacin ta kalli Zahrah a karo na biyu, ita kanta Zahrah kallonta take, Hajja ta kalli Zahrah tace "Kin ga matarsa kenan, ita ma jikata ce, na ma fi sonta a kan sa wllh, xan iya komai a kanta, sunanta Humainah" kasa cewa komai Zahrah tayi, ita kanta xuciyarta bugawa yake, Da kyar dai ta bude baki tace "Sannu!" Ba karamin Dakewa Humainah tayi ba na ganin ta bata amsa tace "Yauwa!" Daga haka ta fice daga dakin, Zahrah taji duk jikinta yayi sanyi, a ranta kuwa tunani take ashe akwai warce xata fi ta kyau, kallon junaid tayi taga har lokacin idonsa na kanta, ta sunkuyar da kai da sauri, Hajja da baki ya ki rufuwa tace "Toh ki karasa ki masa sannu man, amanata ya ci Allah ya kamasa kin san gudu suka yi basu je da ni ba, daxu da asuba ina idar da sllh na daga hannu biyu nace Allah na yafe masa, kila shi yasa kika gansa a haka yanxu" murmushi Zahrah ta kirkira tana jan kafa ta karasa gaban gadon da kyar tace "Ya jikin?" Bai ce komai ba bai kuma fasa kallonta ba irin kallon da na kasa fassarawa, ji tayi kafafuwanta sun gaza daukarta, ta kasa ci gaba da kallonsa, ta durkushe wajen.
*Haske writers association*💡
Afuwa!
[3/19, 9:36 PM] El-hajj💥: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍
83......
Hade rai Hajja tayi tana kallon Junaid tace "Ya haka tana gaishe ka kayi mata shiru?" Bai tanka ta ba ya dauke kansa daga kallon Zahrah da yake, Hajja tace "Ae ko a haka xaka kare, wawa ne kadai ke hali irin naka" Shi dai bai kalli inda take ba bare ta sa ran amsa, mikewa Zahrah tayi jiki a sanyaye Hajja tace "Rabu da Gantalalle" daga haka ta kama hannun Zahrah suka fita, murmushi yayi ya bi kofar da ido, can ya dauke kai ya lumshe ido ya bude, mikewa yayi ya koma parlor ya xauna. Har yamma Humainah bata koma part din Junaid ba shi ma kuma bai fito ba duk da xaman part din nasa ya ishesa, Zahrah kam na bangaren Hajja dake ta jan ta jiki kamar ta maida ta ciki, su khadija sai kallon ikon Allah suke, ko ta kan Ummi bata wani bi sai Zahrah. Bayan la'asar junaid na dawowa masallaci ya shiga part din Mumy, bbu kowa parlon ya nufi bedroom din Humainah da fatima, Humainah kadai ce xaune dakin, ya karasa yana kallonta yace "Why did you leave daxu?" Sosai ta hade rai bata ce komai ba, ya rungume hannayensa yace "Baki gane ta bane?" Kamar jira take ta fashe da kuka, ya bude ido yana kallonta, tayi mai isarta tayi shiru, yace "Ina Mumy?" Kin cewa komai tayi har sai da ya kuma tambayarta, muryarta na rawa tace "Tana gun Hajja" juyawa yayi ya fita daga dakin. A hanya ya hadu da Mumy xata koma part dinta, tace "Ya jikin!" Yace "Alhmdllh Mum" tace "Ashe bakuwa aka yi" kai kawai ya gyada mata tace "Toh da kyau, El-ameen din fa" girgixa mata Kai yayi yace "Ban sani ba Mumy" daga haka ta karasa part dinta, shi kuma ya nufi bangaren Hajja, Zahrah na xaune parlor Hajja kuma ana kitchen da fatima tana gwada mata ynda xata yi ma kajin da Mumy ta Kai masu, Ummi kuma na can daki ta gaji da hayaniyar Hajja tayi kwanciyarta, Zahrah bata ko kalli inda Junaid yake ba har ya karaso ya xauna yana kallonta ta gefen ido, jikinta ne ya bata kallonta yake ta mike xata bar parlon ya fixgota har sai da ta kusa faduwa, xaro ido tayi tana kallonsa cike da masifa sai dai kuma ta kasa masifar, bude kofar parlon aka yi ya sake hannunta, El-ameen ya shigo da sallama, sai ga Hafsat ma ta shigo parlon, kallonsu kawai junaid yake haka ma Zahrah, El-ameen yayi murmushi yayi xamansa kan kujera Hafsat ma ta xauna tana kallon junaid murmushi dauke fuskarta tace "Ina yini Captain!" Murmushin ya mayar mata yace "Lafiya lau, ya kike Hafsat" tace "Alhmdllh" Zahrah dai na tsaye har lokacin sai satan kallon Hafsat take, El-ameen yace "Meet Hafsat Zahrah, ae kin santa" sai a sannan ta kirkiri murmushi ta xauna tana kallon Hafsat tace "Sannu!" Hafsat ta mayar da murmushin tace "Yauwa, ya hanya!" Ba tare da ta kalleta ba Zahrah tace "Alhmdllh!" Hajja ce ta fito daga kitchen tana kallonsu El-ameen tace "Yaushe wa ennan suka shigo" Hafsat ta sauka har kasa ta gaida ta, Hajja ta washe baki tace "Sannu 'yar nan, ko sanin ki bn yi ba sai yau, ya gidan?" Hafsat tace "Alhmdllh" Hajja tace "Kema kin xo ganin bakuwa yar sarki kenan?" mikewa Junaid yayi ya fita daga parlon. Bai sake haduwa da Zahrah ba har washegari da yamma, yana son xuwa amma ya hana kansa fita, da yamman ranan kuma El-ameen ya kawo mama jummai gidan bayan wahalar da ya sha na nemanta, Zahrah na dakin Hajja, Hajja ta aiki khadija ta kirata bayan El-ameen yayi mata bayanin wacece mama jummai, tsaye Zahrah tayi bakin kofa tana kallon mama jummai dake rakube waje daya parlon, da gudu ta karaso ta rungume ta hawaye cike idonta cikin sanyin murya tace "Mama!" buda baki mama jummai tayi tana kallonta da mamaki, can ita ma ta rungumeta tace "Allah Akbar, kaddai ace min yar nan ta warke?" Hajja tace "Kaji wani mugun alkaba'i ko, yo so kike kiyi ta ganinta a haukace 'yar nan? Toh hankalinta daya da naki yanxu dai..." Mama jummai dake kallon Hajja tace "Ayya hajia, ae ni nama fi kowa son ganin warkewarta, ban kuma yi tunanin xan sake haduwa da ita a duniya ba...." Sai kuma ta fashe da kuka ta kuma rungume Zahrah tace "Allah sarki ne, Allah Akbar" Hajja ma ta fashe da kuka tace "Ae ni xan gaya maki wannan, sannan ina me maki albishir da cewa kin haye, ba ke ba wankau da talauchi har abada... Yar sarki sukutum ce nan kike gani jikin ki, yanxu haka kafar ki kafarta har masarautan su, wato da baki rike ta da kyau kin kula da ita tsakani da Allah ba da sunan ki asararriya yanxu, nasan har sai kin gaji da hawa jirgi xuwa makka...." Washegari da ya kama asabar su Zahrah na ta shirin komawa Bauchi har da Hajja da ta hada kayanta jaka guda, shi dai Abba bai ce mata komai ba amma da ganinsa kasan bbu yanda ya iya da ita ne, Mumy ce tayi karfin halin yi mata magana cewa bai kamata ba, nan ta balbaleta wai bakin cikin ita ma xata mata, ko a jikin junaid da in ma kayanta gaba daya xata dauka ta koma bauchi bbu abinda ya sha masa kai don abinda ya damesa a xuciya kadai ya ishesa, Karfe goma El-ameen ya iso gidan, part din Junaid ya nufa ya samesa parlor, tsaye yayi daga bakin kofa yace "Yah! Xaka rakamu bauchin ne yau?" Junaid ya kallesa yace "A wani dalili?" El-ameen yace "A dalilin tare xa mu da hajja" Junaid bai kuma tanka sa ba sae kwafa da yayi, El-ameen ya daga kafada ya juya ya fita, har part din Mumy hajja ta kai Zahrah su yi sallama da Humainah, dakin Mumy suka sameta Humainah ta hade rai sosai, tun bayan haduwarsu ranan da Zahrah ta xo gidan basu sake haduwa ba, Zahrah na tsaye daga bakin kofa tace "Allah ya kara lafiya" Humainah ta mayar mata da Amin ba tare da ta kalli inda take ba, Hajja tace "Kin san kowa da irin nasa laulayin, ita masifa ya daura mata... Mu je kawai" kallonta Zahrah ta kuma yi jin abinda Hajja tace sai kuma ta dauke kai ta fita. El-ameen ya jima tare da mai martaba bayan sun isa bauchi, ko da ya fito airport ya nufa don yana da aiki. Bayan sati biyu Junaid ya dawo daga aiki da yamma suka shigo gida kusan tare da El-ameen dake motarsa shi ma, El-ameen bai wani yi parking ba ya fito yana kallon motar junaid da ya nufi parking space, junaid ya fito El-ameen ya karasa kusa da shi yana kallonsa ganin kamar ba shi ba, can dai yace "Abba na ciki kuwa Captain" junaid yace "Ban sani ba nima, any problem" El-ameen yace "Then let me check" bin sa da kallo junaid yayi kafin ya nufi n bangaren Mumy ya gaisheta, ya tafi nasa part din. Bakwai saura junaid ya fito don xuwa masallaci dai dai lokacin da Abba ya fito tare da El-ameen, kallon mamaki junaid ke masa don bai san yana nan har lokacin ba, tunanin abinda xai kawo sa gun Abba har ya dade haka ya dinga yi amma ya kasa gano komai, ya dai nufi gun Abba ya gaida sa daga haka suka nufi masallaci gaba daya. Ko da suka dawo daga masallaci El-ameen sallama kawai yayi ma Abba ya shiga motarsa ya bar gidan, kasa daurewa junaid yayi bayan isha ya dau makullin motarsa ya tafi can gidan El-ameen, Hafsat ce ta bude kofar ganinsa tace "Sannu da xuwa captain, you came to our home today" murmushi yayi yace "Lallai kam, yana ciki?" Tace "Ehh yana ciki bismillah" hanya ta basa ya karasa xai xauna parlor tace "Yana sama ae" yace "Yi masa magana pls" tace "Study room dinsa fa yake" mikewa yayi yace "Ohk" daga haka ya haura sama, xaune ya samesa yana duba wani littafi gaba daya hankalinsa na kai, wanda hakan yasa bai dago ba don a tunaninsa Hafsat ce ta shigo, karasawa Junaid yayi, El-ameen ya dago da sauri jin turarensa, kallon mamaki yayi masa sai dai bai ce komai ba, Junaid ya xauna yace "Me ya kawo ka gidanmu daxu?" El-ameen ya buda ido yace "Yeah, Nasan ba don Allah ka taso ka taho gidana ba," sai kuma yayi murmushi yana girgixa Kai yace "it's very unfortunate Zahrah ta bata frndship dinmu, a da sati baya karewa ba tare da ka xo inda nake sau uku ba ko sau hudu, sauran kwanaki kuma ni xan je but yanxu....." Junaid ya d'an yi murmushi yace "Ae kai ma ba xuwa kake ba" El-ameen bae tanka sa ba ya ci gaba da duba littafin gabansa, junaid yace "I asked you a question..." El-ameen yace "Nothing, naje ne ya shigar min gaba gun neman auren Zahrah, as in shine waliyyina" Junaid da ya ji wani abu ya tsaya masa a xuciya ya dake yace "Why him?" El-ameen yace "Coz dad dina yace bbu ruwansa da batun auren...." Junaid ya hadiye wani abu da kyar yace "and what did he said about it?" El-ameen ya matsar da littafin gabansa yace "Yace babu damuwa idan har hakan baxae bata ma dad dina rai ba.. Nd I told him shi ma ya turo ni gunsa" mikewa junaid yayi kansa na juyawa ya kalli agogon hannunsa yace "Ohk, all good, it's getting late xan koma" El-ameen yace "Toh baka tambaye ni yaushe ne daurin auren ba?" Junaid yaji gabansa yayi mugun faduwa ya koma ya xauna xuciyarsa na bugawa sosai yace "When?" El-ameen yace "This Friday!" Kasa cewa komai Junaid yayi, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, bude kofa aka yi Hafsat ta shigo ta dire masu babban tray mai dauke da warmers din abinci ta fita sai ga ta ta dawo da wani tray mai dauke da ruwa da drinks sai cup ta fita, El-ameen yace "Mu ci abinci frnd..." Junaid yace "No! No, am ohk" El-ameen yace "Alryt then, you wait muyi shawaran abubuwan da xa ayi na bikin it's just 4 dayz left" Kallonsa kawai Junaid yake, El-ameen ya dau table water daya ya bude ya sha kadan yace "Yeah, though sarkin yace baya bukatan komai namu, amma dai mu ma mun san abubuwan da ya kamata, so ya kaga ya kamata mu yi" mikewa junaid yayi yace "Look, ka kira Faisal or Aliyu am not good at that" daga haka ya fice daga parlon, El-ameen ya bi sa da kallo yana murmushi.
*Haske Writers association*💡
Ayi ta hakuri da ni a haka har mu kare pls.
[3/19, 9:36 PM] El-hajj💥: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
85.....
Kallon Hajja kawai junaid yake don ya kasa fahimtar inda xancenta ya dosa duk ta cikasa da hayaniyar dake baraxanar haddasa masa ciwon kai, Muryar kawunsa yaji na kiransa ya juya yana kallonsa yayi masa alama da ya xo, part din Abbansa ya nufa ta bi sa tana ci gaba da xaxxaga masa bala'i shi dai bai tanka ba, bai same su parlor ba ya karasa har bedroom, hajja tayi tsaye nn parlon tana ta ci gaba da bala'i ta inda take shiga ba ta nn take fita, xaune ya samu Abbansa da frnds dinsa biyu sai kawunsa, Kawunsa wato Abban Humainah ne yace "Ahmad!" Ya dago a hankali yana dubansa amma ya kasa cewa komai. Kawun yace "Na'am mahaifin yarinyar nan ya bukaci da ka aureta, don me da ku ka dawo baka sanar ma iyayenka komai ba sai abokin ka ne ke fadi ma Abbanka few dayz back....." Kasa cewa komai Junaid yayi sai dai kansa yayi mugun daurewa, Abbansa dai sai kallonsa yake, Alhaji umar yace "Kayi shiru Ahmad, gaskiya ne Kai mijin mace hudu ne bbu wanda xai hanaka kara aure tunda kana da halin yin hakan sai dai kawai Kayi kokarin xamo me adalci tsakaninsu, amma meye na boye ma iyayenka, da nufin ka yau sai ka taho kace a tashi aje maka daurin aure, Babanka yayi ta xuba maka ido amma shiru baka ce masa komai ba...." Alhaji Habib yayi dariya yace "Kar fa ku ga laifinsa, that's what it takes to be a 1st child, wauta ne kawai irin tasa" Kawunsa