Showing 168001 words to 170905 words out of 170905 words
Chapter 57 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
ya sakar mata ya dafa kanta, a hankali yace "Let me pray for you princess" rufe ido tayi bata ce komai ba har ya gama sannan ta bude ido tana kallonsa, langwabar da kai tayi tace "Is that all" ya gyada mata kai, ta mike ya bi ta da kallo, kofa ta bude ta juyo tana kallonsa tace "Gud nyt, I want to go to bed!" Wara ido yayi yana kallonta can yayi murmushi yace "Oh korata ma kike ko?" Girgixa masa kai tayi tace "A'a bacci xan yi ne" yace "toh ni a nan nake son in kwana" shiru ta d'an yi tana kallonsa can tace "Ohk," ta rufe kofar ta dawo tayi kwanciyarta ta ja bargo tace "Gud nyt" kai kawai ya gyada mata, kusa minti goma xaune snn ya mike ya kashe wutan dakin ya dawo ya kwanta ya birgina kusa da ita, Juyowa tayi da sauri murya can kasa yace "Baki yi bacci ba" "Uhm" kawae tace xata kuma juyawa ya jawota jikinsa. Washegari da asuba ko da ya fito daga bayi bai tarda Zahrah a dakin ba, tsaye yyi dakin don yasan baxata je dakin Humainah ba, bude kofar yyi ya fita ya bude dakin dake kusa da nata, nan ya ganta kwance ya karasa ya durkusa kusa da ita a hankali yace "Zahrah!" Idonta rufe yake, ya mike ya xauna kusa da ita ya dago ta yace "Nasan kina jina, open ur eyes pls" ganin baxata bude idon ba ya rungumeta cikin sanyin murya yace "Am sorry Jasmine" dumin hawayen ta ya ji a bayansa, ya dago kanta ta rufe idon da sauri.
3 month later.
Zahrah na daki kwance bayan junaid ya fita aiki, tana chatting da 'yar uwarta ummi taji kamar Humainah na kiranta, mikewa tayi ta ajiye wayar ta fita ta shiga dakinta, durkushe ta ganta dakin ta karasa da sauri ta durkusa kusa da ita tace "Me ya faru?" Humainah ta dago da kyar tace "Am not okay" mikewa Zahrah tayi da sauri ta fita xuwa parlor, Mama jummai dake goge goge ta kalleta ganin yanda ta sauko a rikice tace "Me ya faru Zahra'u?" Zahrah da ke shirin kuka tace "Wai tace min bata da lafiya ban san me ya sameta," mikewa mama jummai tayi ta haura sama da sauri ta bude kofar Humainah ta shiga, dagota tayi tana mata sannu ta kalli Zahrah tace "Maza je ki yi ma driver magana mu tafi asibiti" da sauri Zahrah ta kuma fita don yi ma driver magana, ita kuma mama jummai ta fito da Humainah da banda daurewa bbu abinda take, kafin su isa asibiti sai ka rantse Zahrah ke nakuda, duk ta cika masu kunne da koke koke ganin yanda Humainah ke wahala, ana shiga da Humainah dama ta kira junaid, yana dagawa ta fashe masa da kuka tana cewa "captain kaga kila haihuwa xata yi ka xo pls, she's in pain" Mama jummai ta karbe wayar tace "Rabu da ita soja kar ta daga maka hankali, ka taho muna asibiti" daga haka ta katse wayar don ko ba a gaya mata ba tasan Zahrah ta gama ruda shi, karban wayar Zahrah ta kuma yi tace "xan kira Mumy" Mama jummai ta karbe tace "A'a ki bari sai ya xo kin ji, in shaa Allahu xata sauka lafiya ki daina kukan nan" ba a dau lkci ba sai gashi ya taho asibitin, da sauri ta je ta rungumesa ta kuma fashe wa da kuka tace "My prince ni daga yau kar ka sake ce min xan haifan maka yara bana so" kallonsu kawai ake a reception din wasu na dariya kasa kasa, ya kamo hannunta yace "Ohk princess na daina" ko minti uku bai yi hospital din ba Humainah ta haifo santalelliyar 'yar ta, sai dai kuma bata san ma wa enda ke kanta ba, nan hankalin Junaid ya tashi, mama jummai ce tayi karfin halin karban yarinyar bayan an fito da ita, Zahrah kam tun da abinda likitan ya gaya ma junaid ya samu shiga kunnenta ita ma ta dinga rusa kuka ita fa sai ta shiga wajenta, har sai da nurses suka fita da ita daga reception din ma gaba daya, wata nurse da gulma ke ci ta isa gun mama jummai da tayi jigum tace "Allah sarki yar uwarta ce wancan da aka fitar ko?" Mama jummai ta girgixa kai a sanyaye tace "Kishiyarta ce" nurse din ta kwalalo ido sai kuma ta juya ta koma gun sauran nurses din ta fesa masu abinda ta ji su ma. Ba karamin karfin hali Junaid yayi ba ya kira Abba ya sanar da shi haihuwar ya kara da cewa bata da lafiya bayan ta haihu, kafin minti ashirin sai ga Mumy da su Umma da Hajiya sun iso asibitin, duk hankalin Mumy ya tashi suna asibitin har dare bbu wani improvement, Abba ma har ya xo ya koma shi ma rai ba dadi, karfe tara Mumy ta koma gida da Zahrah, sai a snn Junaid ya tuno da El-ameen don duk Zahrah ta gama rikita masa lissafi ya ma rasa da wanda xai ji, cikin few minutes El-ameen ya karaso clinic din, da yake yawancin doctors din ya san su yana neman alfarmar a bar sa ya shiga gun Humainah aka barsa ya shiga tare da wasu doctors biyu, ba a dau lokaci ba ya fito nan ya shiga kwantar ma Junaid hankali yace "Don't worry frnd she will be Alryt, tayi loosing blood ne da yawa amma xuwa gobe xa ka ga she will be okay, haihuwar ne yayi gardama" kallonsa kawae Junaid yake, El-ameen yayi masa murmushi assuringly yayi Pat din shoulder dinsa sannan ya isa gun mama jummai ya karbi babyn ba tare da ya kalli su Umma dake gun ba. Washegari kamar yanda El-ameen ya fadi cikin ikon Allah jikin nata da sauki sosai kamar ba ita ba, murna gun Zahrah kamar xata yi yaya, haka duk ta bi ta takura babyn da riko ta ki kwantar da ita, ba ita ba hajja dake ta mata gorin ita ma tayi tayi ta haifo nata dai, Da taji ance mata haka mood dinta ke canxawa, junaid sai dai yayi dariya can ciki, kwanan su biyu asibiti aka sallamesu, a ranan kuma Umman Zahrah da Ummi sai Kanwar mai martaba suka iso katsina don yin barka, kaya ba na wasa ba suka yi ma Humainah da jaririyarta, hajja ta rasa inda ta sa su don murna, kwanansu biyu suka koma bauchi, ranan suna baby ta ci sunan late mum din Humainah fatima, washegari Hajja ta tattara Humainah da yar ta suka yi gida tare da mama jummai wai sai ta gama mata wanka xata dawo, Zahrah bata ji dadi ba amma bata ce komai ba don tasan balbaleta Hajja xata yi, da daddare tana dakin Junaid tace "My prince ya xa mu dinga kiran babyn?" Junaid na danna laptop din gabansa yace "Amm baby xa mu ce koh?" Tace "Noo let call her Jasmine" kallonta yayi yace "No, I have a wife Jasmine...." Tace "yess, a wife Jasmine, a daughter Jasmine" murmushi yayi yace "Ohk, to ke yaushe xa ki haifo min naki babyn, nd I want two boys" bata rai tayi sosai ta mike xata fita ya fixgota ya rungumeta, ta fashe da kuka tace "My prince ni ka daina cewa xan haihu Allah bana so" ya buda ido Yace "Toh sbda me?" A hankali tace "Kana son in mutu koh" danne dariyarsa yayi yace "Nooo, bana son ki mutu wife toh naji kiyi ta rike babies din nawa a ciki koh?" Kai ta gyada masa ya kankameta yana dariya, tace "My prince I want to continue with my education" shiru ya d'an kafin yace "Ohk" amma da jin ohkn kasan fadi kawai yayi, har aka yi bikinsu fatima da khadija Hajja bata bari Humainah ta dawo dakinta ba, ae ko tana tafiya kai amare ya dauko matarsa suka yi gida, Zahrah dai na rungume da Jasmine da tayi wayo sosai, yarinya me kyau da ita komai na babanta ne jikinta. Satin Humainah daya da dawowa Zahrah ta dinga yi ma junaid magiyar ya kai su bauchi, ko kadan bai son bacin ran princess din tasa washegari ya daukesu gaba daya ya kai su bauchi shi ya koma gida, iyayen Zahrah basu nuna banbanci tsakanin yar su da kishiyarta ba, komai aka ma Zahrah sai an mata hatta gwalagwalen da aka ba Zahrah sai da aka ba Humainah sak irinsa, kwanansu biyar Junaid ya koma ya dauko su, da daddare yana kwance Humainah dake shirya Jasmine tace "Ya Ajay?" Kallonta yayi yace "Wife!" A hankali tace "Plss ina son kayi min wani alfarma" mikewa xaune yayi ya jawota jikinsa yace "Ina jin ki dear" sauke idonta kasa tayi tace "Ina son ka raba mana gida da Zahrah" shiru yayi na kusan minti uku kafin yace "Sbda me?" Hawaye ne ya cika idonta tace "Bana son ranan da xai xo mu fara xama irin na kishiyoyi da ita, bana son komi ya hada ni da ita, idan bama tare za mu ta xumuncin mu bbu abinda zai hada mu plss dear" shafa kanta yayi yace "Hakan baxae tafa faruwa ba wife, Zahrah me saukin kai ne kema kin sani, snn the both of you kuna da ilimin addini baxa kuyi kishi mara amfani a kai na ba, bana son raba kan family dina I want to see you both together" shiru tayi bata ce komai ba, yayi peck din cheek dinta yace "Yeah wife" a hankali tace "Toh school fa ya Ajay" murmushi yayi yace "Duk sai kun gama haifa min kidz dina xa ku koma sch" kallonsa tayi ya wara ido yace "Yess wife" Washegari da ya kasance sunday Humainah na gama hada breakfast don ita ce da girki snn ta koma sama, tayi mamakin rashin saukowar Zahrah which is very unusual, dakinta ta shiga tana cewa "Antyn Jasmine," don haka take kiranta, Kwance ta ganta tana bacci ta karasa ta tada ta Zahrah ta bude ido ta mike xaune tace "Momyn Jasmine" Humainah tace "Ki sakko muyi breakfast" toh kawai Zahrah tace mata ta juya ta fita, Mikewa Zahrah tayi ta shiga bayi ta wanke baki sannan ta fito, Junaid na xaune dining yana danna waya Ita kuma Humainah na serving din breakfast din, xaunawa Zahrah tayi Junaid dake kallonta ta gefen ido ya harde kafarsa da nata ta karkashin dining table din, turo baki tayi bata ce komai ba, ya matso da kujerarsa a hankali ya daura hannunsa kan cinyarta, buge masa hannu tayi ta mike ta koma wani kujerar dake nesa da nasa, murmushi Humainah dake lura da su tayi ta gama zuxxuba masu tayi xamanta ta fara cin nata, Junaid ma ya dau nasa ya fara ci, Plantain kawai Zahrah ta dauka ta Kai bakinta ta fara ci bata gama hadiyewa ba ta mike da sauri duk suka daga Kai suna kallonta, juyawa tayi ta bar dining din da gudu ta haura sama, bin ta da kallo duk suka yi, Humainah ta tallabi kuncinta tana murmushi tace "Hmmm" don kusan sati biyu kenan da ta gaya mata ita fa bata ga period dinta ba kamar xata mata kuka take gaya mata, kwantar mata da hankali kawai tayi tace ai yana yin haka wani lokacin, sai a snn ta kwantar da hankalinta ta ci gaba da harkokin gabanta, kallonta kawai junaid ke yi ganin irin kallon da take masa, can yayi murmushin shi ma ya mike ya bi bayan Zahrah, xaune ya ganta bakin kofar bathroom dinta har ta gama aman, ya durkusa da damuwa yace "Ohh sorry princess, plantain din ne baki so" bata iya tace komai ba ta mike da kyar ya riketa tace "Am feeling dizzy my prince" daukarta yayi ya kwantar da ita yayi kan gado yace "Toh bari mu je asibiti koh babyna" girgixa masa kai tayi tace "No I will be Alryt, bacci xan yi" ya jima yana kallonta har ya ga kamar ta fara bacci ya mike ya fita, yana sauka kasa Humainah ta wara masa ido tace "Congrat My Capt" xaunawa yayi kusa da ita ya jawota ya rufe bakinta da yatsa yace "Shiii don't tell her that plss" dariya tayi sosai tace "Ohk ohk"
*Haske writers association*π‘β *captain Ahmad Junaid*β
_By Khaleesat Haiydar_βπ»
End
Har dare Zahrah na kwance gashi ta ki cin komai duk jikinta yayi xafi, da yace su je asibiti sai tace no allura, shima dama tsoron kai ta yake don yasan ba karamin aiki xai yi ba idan ta gano sanadin rashin lafiyar nata, kwanaki uku ta dauka tana wahala, ganin duk ta jigata yasa kawai ya kira El-ameen sai ya lallabasa yayi mata treatment kawai ba tare da ya gaya mata me ke damunta ba, ya ji ddi da ya kasan ce mama jummai taje kauyensu da ta tona dalilin rashin lafiyan nata, dariya kawae El-ameen ke yi bayan junaid yayi masa bayani, Junaid yace "Plss frnd bana so ta sani daga min hankali xata yi wllh" El-ameen yace "Alryt I won't let her know, ni ma my Hafsat is pregnant" Junaid yace "Ohh Congrat, Allah ya raba lafiya" El-ameen na sa mata ruwa bacci me nauyi ya dauketa, haka suka ci gaba da lallabata El-ameen na xuwa bata allura yana sa mata ruwa, har bayan sati uku taga ciwo yaki tafiya nan ta fara tunanin ko dai ciki ne ma da ita don har lkcn bata ga period ba, mikewa tayi da kyar tana ganin jiri ta dauko wayarta ta yi Google din signs and symptoms na pregnancy, nan taga duk abubuwan da take ji a jikinta a lissafe gun bata san lkcn da ta wurgar da wayarta ba ta mike da gudu ta fice sai dakin Junaid ya fito daga wanka kenan ta fixgoxa ta fashe da kuka sosai tace "Na shiga uku my prince kila I am pregnant ne" xaro ido yayi irin yayi mamaki din nn yace "Pregnant kuma, wa ya gaya maki" a rikice tace "I Googled it, kuma I've missed my period for a long time, plss my prince mu je asibiti a cire na shiga uku mutuwa xan yi kila baxan iya haihuwa ba ka taimakeni plss" tana kuka sosai ta kare maganan, ya danne dariyarsa ya rungumeta ya isa kan gado da ita, ya kai bakinsa kunnenta yace "Haba my princess, Toh ba ga Humainah ba ta haifi nata bbu abinda ya sameta, kuma tare fa xa mu haifa babyn" cixo ta kai masa a kirji tace "Nooo baxan iya ba mu tafi asibiti plss" yace "Nooo bbu inda xa mu je ina son babyna, I want to see my little prince or princess, baki son ki ga royal kidz dinki wife?" dagowa tayi tana kallonsa a rude ta kuma fashe wa da kuka tace "My prince saura kadan fa Momy Jasmine ta mutu" rungumeta ya kuma yi yace "Baxa ki mutu ba sai kin haifa min royal kidz my princess, sai mu kai ma Umma kinga she will not be lonely again ga ta ga princes and princesses dinta" shiru tayi hawaye na sauko mata, yayi murmushi yana shafa gashinta yace "Yeah tare xa mu haifo su wife" cikin kuka tace "Promise?" Yar dariya yayi yana shafa cikinta yace "I promise my princess" rungumesa tayi muryarta na rawa tace "Ohk, xan haifi babyn sai mu kai ma ummata" yace "Waoww yauwa my royal wife, nd Umma will be very happy..." Kallonsa tayi yayi mata gwalo ta turo baki sannan ta tura cikin nasa ya shiga kissing dinta.
Hmmm! Alhmdulillah a nan na sauke littafina mai taken *Captain Ahmad Junaid* kura kuren da nayi a ciki Allah ya yafe min, na kuma sadaukar da littafin nan xuwa ga My Sweetest bro like no other, my abokin fada, my abokin argument, infact my everything *Ahmad M Bello* da kuma my best frnd, my abokin shawara, the handsome tall d'an Fulani, the great *Captain Ahmad Junaid murnai* Allah ya albarkaci rayuwar ka, ya kare ka daga sharrin mutum da aljan, ya baka mace ta gari ya rabaka da iyayenka lafiya ya kuma bar mu tare, ka girma in baka daughter nah, uhm bari in bar sa haka kada ya ji sa wane jirgi a sama Lol.
My sweet Mum Allah kara maki lafiya da duk musulmai baki daya, ya dawo min dake lafiya am missing you so muchh, My sweetest Big mum Ummu Aneesah am grateful for ur encouragement from the Beginning of this novel to the end, Allah raya maki Jamcy da Humy, sai dai kinsa my Novel is not that romantic oo Lolπ My greetings goes to all the occupant of Haske asso, Allah ya kara hada kawunanmu, I hail you all with respect, where are you my Ummu Shakur, fido s Dangi, phatiemarkh, Asmy b Aliyu, Hafsat Ummu ilham duk ina gaida ku and am grateful for the encouragement alwayz, and finally my fans!!! words alone can't express my feelings toward you all, sai dai kawai ince Allah bar xumunci ya bar mu tare ina sonku, ina alfahari da ku, ina ji da ku har kullum, My brother from another mother *Anas Sufyan* tnx for the tsokana and everything from d beginning of C.A.J to the end, ban mance ki ba *Sharifata* a sister from another momma tooo.
Hmm my siblings _Maryam, Fatima, Baby, ilham, Ameer, Fadil, Sudais, Haiydar and my Umar am missing you all_π
Taku har ko da yaushe *Jiddah M Bello* A.k.a *Khaleesat Haiydar/ Lag~Lady*π΅π»ββ
Na bar ku lafiya fansβπ»