Showing 42001 words to 45000 words out of 170905 words

Chapter 15 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

670

in dai ba Mumy ce da girki ba to ba lallai ya ga Abba ba sae ko a masallaci, kasa samun natsuwa yayi gun aiki har sae da ya dau excuse din minti ashirin ya fita ya kama hanyar gidan El-Ameen, su biyu kadae ne parlon ita da mama dake mata kalaba daga tsaye don taki xama, sae xagaye parlon suke ana kitson a haka, tana ganinsa suka hada ido ta kurma wani uban ihu da yayi mugun tsorata mama don kan kace me har ta kai bakin kofa, shi kam tsayawa kallonta yayi, har lokacin ihun take da karfi tana shisshigewa jikin bango ko ina na jikinta na rawa, lumshe ido yayi a hankali ya bude ya kalli uniform din jikinsa White navy shirt ne jikinsa da dark trousers navy blue, ya kalleta ya ga yanda ta runtse ido tana k'uwa, bude kofar parlon aka yi El-Ameen ya shigo da ledoji a hannunsa, sake ledojin yayi da sauri ya karasa gunta, ya riketa, bude ido tayi a gigice ta kara fasa wani ihun tana ganin El-Ameen ta rungumesa, ya rufe bakinta lkci daya tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya a hankali, kallon Junaid yayi ya hade rai yace "Look captain, I've warned you not to come to this house on uniform again, look how you are scaring the life out of her, a haka xata samu lafiya? Plss ka daina xuwa nan da uniform" Juyawa Junaid yayi ya fice daga parlon, Mama dake bakin kofa har lkcn tace "Auuu wae khakin take tsoro? Allah sarki Baiwar Allah" dago kanta El-Ameen yayi yana kallonta ita ma haka, kama hannunta yayi yana rike da ita suka haura sama. Junaid na komawa gun aiki ya ci gaba da harkokinsa sai dai da ka gansa kasan there is something eating him inside, karfe biyar saura ya isa gida, ya jima xaune motarsa yana danne danne a waya, ganin motar da ke kokarin parking gefensa ya kashe motar ya fito ya rufe yayi part dinsa. Yana kwance parlor'nsa dab da magrib yana kallon wani program though absentminded yaji Humainah na kwalo masa kira daga waje, mikewa xaune yayi jin irin yanda take kiransa da karfi, ya mike da sauri ya nufi kofa ya bude, tsaye ya ganta d'an nesa da balconyn rike da kugu tana tafe hannu tace "Taho taho ka ga yaya" yana fitowa sai kuma tayi bangaren Mumy da sauri tana kwalo mata kira ita ma, wanda hakan ya ja attention din 'yan gidan da ido da kunnensu na kan duk wani motsi na gidan kamar masu gadi, Umma ta riga Mumy da fatima fitowa sannan Hajiya, su khadija Rabi'a, sadiya, Muhibba duk suka fiffito, shi kam Junaid abinda ya daure masa kai bai wuce na ganin Suhaima tsaye bakin kofarsa tana xaxxaro ido sai kokarin boye abu a hannunta take, Humainah ta dawo da sauri Mumy na biye da ita a baya haka ma sauran, Hajiya kam ko ina na jikinta rawa yake ji take kamar ta saki gudawa tsabar rudu shikenan asirinsu ya tonu, garin yaya Suhaima taje bakin kofar ba tare da ta sa ido taga bbu kowa a tsakar gidan ba, ita kanta umma sai da hanjin cikinta ya kada sai dai duk basu nuna a fuska ba, don Hajiya sai ma wani hade ran karfin hali tayi, A takaice Humainah ta rike kugu tace "Abu naga tana shirin barbada wa bakin kofar ya Ahmad, duk bata san ina can bakin pampo naje daurayo takalmana ina kallonta ba" ta fadi haka tana nuni da kusa da bangaren da Hajja ke sauka, Suhaima dake ta salati a rikice tace "Sharri xa ki min don kin gan ni a nan, na shiga uku na lalace, Hajiyanmu kina jin abinda yarinyar nan ke cewa" a fusace Humainah tace "koh ba sharri ba, ki bude tafin hannun ki munafuka, kin wani xo kina yi kamar mage baki san ina kallonki ba xaki wani ce ina maki sharri, wllh Mumy abu take shirin barbada masa bakin kofa" Hajiya ta hadiye yawu da kyar tace "Ke yanxu 'yar nan sharrin naki kan 'ya ta kuma xe sauka, duk shekarunta gidan nan bata taba barbada ma Ahmad abu ba sai da kika xo munafuka algunguma toh wllh sai Alhaji ya xo ya mana shari'a don baxan yarda da kaxafin nan ba" fuu Humainah ta haura balconyn ta fixgo hannun Suhaima dake jin kamar ta saki fitsari tana huci tace "Bude hannun to idan sharri na maki, ki bude, uwar me ya kawo ki bangaren sa da daddare ke da ko during daylight ba xuwa kike ba munafukaa, toh wllh sai kin fadi Meye wannan kike shirin barbada masa ko in gaggalla maki mari a nan don ubanki" Mumy ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "Humainah!" Humainah na girgixa kai ido rufe tace "Ni dai Mumy Allah sai ta fadi meye a hannunta ko kuma muje ta barbada shi a kofar uwarta ni baxan yarda ba"

✍🏻
*Haske Writers Association*💡
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓






_By Khaleesat Haiydar_✍





20.....

Suhaima da duk ta jike da xufa ta fara kokarin kwace hannunta daga rikon da Humainah tayi mata tana cewa "Na shiga uku ki cika ni, me na maki xaki min irin wannan sharrin?" Banda murmushi babu abinda khadija take, Hajiya dai da kyar kafafuwanta ke daukarta ga wani kullewa da cikinta yayi, Umma kuma sai wuwwurga ido take tana xufa, Sadiya ta haura balconyn a fusace tana kallon Humainah tace "Ke karamar 'yar iska cika mata hannu kar in baki mamaki yanxu....." Humainah ta juya a hankali tana mata wani matsiyacin kallo tace "Kambu! Ko kuma ni in baku mamaki ba, ai wllh sai ta fadi kullin uban meye a hannunta kuma wa ya aikota idan ba haka ba in karya hannun" Khadija tace "Toh ke Anty suhaima ki bude hannun a ga kullin mana, ko dai yaji xa ki kai masa?" Hajiya tayi kanta xata cafke ta ai da gudu ta bar wajen, cike da karfin hali Hajiya na huci tace "Ae sun yi kadan ta bude masu hannu wllh, sai dai duk...." Fitowar Abba yasa ta kasa karasawa ta fara girgije girgije ae kawae sae ta fashe da kuka tun kan ya karaso tace "Na shiga uku ni fateema me muka tare ma mutane a gidan nan ni da 'ya yana" A hankali Mumy tace "Cikata Humainah" Humainah ta girgixa kai ta cakumi rigarta tace "Noo! Ae sai ta bude hannunta mun ga ko menene wllh Mumy" shi kam Junaid tsaye kawai yayi ya kasa cewa komai duk jikinsa ba karfi, Abba na isowa ya shiga tambayar Meye haka, Humainah tace "Abba wallahi barbade take shirin yi ma Ya Ahmad Allah ya toni asirinta na kamata kuma ni sai taje bakin kofarsu ta barbada koma Meye xan kyaleta" Hajiya ta fashe da matsanancin kuka ko ina na jikinta na bari tace "Kana ji ko Alhaji, kana ji koh...." Abba kam kallonsu ya tsaya yi, can yace "Cikata Humainah" Humainah ta fashe da kuka tace "Ni wallahi baxan saketa ba Abba, sai ta nuna abinda ke hannunta kuma muje ta barbada shi a kofarsu, duk bata san ina can ina kallonta ba, ni wallahi baxan kyaleta ba" dariya khadija ta dinga yi can ciki ciki ganin yanda 'yar uwarta ke wurga ido kamar barauniya, da kyar Mumy ta haura balconyn ta kamo Humainah tace "Saketa Humainah" still taki sakinta ita fa sae ta bude hannunta, Junaid ya lumshe ido ya bude ya karasa kusa da su a sanyaye ya janyeta yace "Kyaleta Lil sis" fashewa tayi da wani kukan tace "Ya Ahmad abu fa tayi niyar barbadawa da ban ganta ba" ae Suhaima tun da ta samu Humainah ta saketa kan kace me har ta sauko kasa tana tuntube, ta fashe da kuka tana kallon Hajiya da Abba tace "Kudi fa na xo tambayarsa don ta ga ina leke leke shine take cewa barbade xan masa," Hajiya ta rungumeta ita ma ta fashe da kukan tace "Na sani Suhaima Allah xai saka mana kiyi shiru" Humainah ta kwace kanta daga rikon da Junaid yayi mata ta sauko tana kallonta da kyau tace "Kuma wallahi daga yau na kuma ganin kafar ki a nan wajajen sai na karya su duka biyun, munafuka kawai dama ni Hajja tace min boka da malamai kuke bi" tsawa sosai Abba ya daka mata, ta turo baki ta bangajeta tayi part din Mumy fuu tana gunguni, duk suka bita da kallo fatima ta ni bayanta, Abba ya kusa minti daya bai ce komai ba, can ya kalli su Hajiya yace duk kowa ya koma ciki, haka duk suka juya Hajiya na kuka har lkcn tana rike da hannun Suhaima Umma da baki ya mutu na biye da ita a baya, shi ma ya juya yayi part dinsa ana kiraye kirayen sllhn magrib. Mumy ta juyo a sanyaye tana kallon Junaid, shi din ma duk jikinsa yayi sanyi ba kadan ba, kasa cewa komai tayi ta sauka ta koma part din ta, ya lumshe ido ya bude ya bi bayanta. Xaune suka tarda Humainah palo sai rusa kuka take bakin rai, Mumy tace "lafiya kuma Humainah" cikin kuka tace "Mumy ba shine baku bari na mata duka ba, wllh wani kulli ne hannunta tana shirin xubawa bakin kofar na kamata" Mumy ta xauna kusa da ita tana murmushi ta jawo ta jikinta tace "Kiyi hakuri mu bar su da halinsu Allah ya fisu da shi kuma muka dogara, in'sha Allah bbu abinda xai same mu kin ji Humainah" kallon Junaid dake tsaye ya kasa xama tayi tace "Kai kuma ya Ahmad maimakon ka faffala mata mari shine ka tsaya kallonta" Xaunawa yayi yyi murmushi bai ce komai ba, lallashinta Mumy ta dinga yi har dai ta samu tayi shiru, Junaid ya mike ya shiga bathroom din dake parlon ya dauro alwala ya fito ya fita xuwa masallaci, Mumy ta kalleta tace "tashi ki je kiyi alwala" ba musu ta mike ta shiga bathroom Mumy ma ta tashi ta shiga dakinta don yin alwalan. Ana idar da Sllh Junaid ya shigo, Humainah na xaune da Mumy da fatima suna cin abinci, ya xauna yana kallonsu, kwankwasa kofa aka yi lkci daya aka bude aka shigo, Sadiya ce ta shigo ta tsaya daga bakin kofar fuskarta tamke tace "Humainah kike ko wa? Abba na kiran ki" Humainah ta galla mata harara tace "A'a Mantawa kika yi dai, Sadiya sunana" Mumy tace "Ke kina da hankali Humainah?" ta turo baki ta ajiye spoon din hannunta, Sadiya tayi kwafa tana gyada kai ta fice, mikewa Humainah tayi, Mumy tace "Ki gama cin abincin tukunna, baxa mu kuma shirya da ke ba idan kina rashin kunya" kamar xata yi kuka ta nufi kofa Junaid ya bi ta da kallo yana girgixa kai. Da sallama Shukrah ta shiga parlorn Abba, yana xaune kujera Hajiya da Umma ma na xaune sai Suhaima da ke xaune kasa, can jikin kujera ta samu ta xauna tace "Abba gani" a nutse Abba yace "Daga yau kika sake abinda kika yi daxu sai na yi mugun saba maki, Ashe ke shashasha ce, kina daga can bakin pampo ta ya kika ga abu a hannunta" Hajiya ta goge d'an guntun hawayen idonta tace "Babu maganan taya ta gani, wllh sa ta aka yi Alhaji don wnn yar mitsitsiyar hankalinta baxae bata tayi abinda tayi mana daxu ba, to ni kam me na tsare masu xa su yi ma 'ya ta irin wannan mugun sharrin?" Kuka ta fashe da sosai, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Xancen ki gaskiya Hajiya, amma Allah ya san dai dai, kuma baya bacci" Abba ya kalli Humainah da ta wani hade rai kiris ya rage ta fashe, yace "Don uwar ki wa kike ma wannan kallon" mikewa tayi ta fashe da kuka tace "Na rantse da Allah Abba wani abu ne a hannunta tana son budewa ta barbada fa na kama ta, ni ba karya na mata ba, meyasa baka ce ta bude hannun ba tun a can..." Wani tsawa Abba ya daka mata yace "Ke!! Baki san ni ba koh?" Hajiya ta girgixa kai tace "Babu ruwan yarinyar Alhaji da ba a ce tayi hakan ba baxa ta yi ba" Abba yace "Toh maxa ki tafi ki tattaro kayanki ki koma gun Hajiya tunda munafurci kike koya can, maxa maxa yanxun nan ba sai da safe ba" Hajiya ta dan yi murmushi da iyakan sa lebbe, ficewa Humainah tayi da gudu daga parlon, tayi part din Mumy, Mumy na xuba ma Junaid abinci ta fado parlon ta xube nan kasa ta dinga rusa kuka kace yar jaririya ce, Mumy ta karasa da sauri ta dago ta tana tambayarta abinda ya faru, kuka take sosai tace "Wayyo Mumy ni gidanmu xan tafi wallahi baxan xauna a nan ba, ki bani wayar ki in kira Hajjah" Mumy tace "Kiyi hakuri, gaya min me ya faru, me Abban yace maki" cikin kuka tayi ma Mumy tsarin yanda suka yi da Abba, Mumy tayi murmushin takaici bata ce komai ba, Junaid kam lumshe ido yyi ya jinginar da kansa jikin kujera, tana ci gaba da rusa kuka tace "Ni wallahi wucewa xanyi baxan xauna ba" Mumy rasa me xata ce mata tayi, mikewa Junaid yayi ya dago ta yace "Kiyi hakuri, Abba is angry shi yasa ya maki magana haka, xaki ga ya huce xuwa gobe" tace "A'a ni ka ban wayarka in kira Hajja tafiya ta xan yi" cikin sanyin murya Mumy tace "Kar ki kirata, xai iya cewa ni na sa ki kirata" mikewa Humainah tayi ta nufi daki tana kuka. Junaid ya koma ya xauna, Mumy ta girgixa Kai ta ci gaba da xuba masa abincin da take yi. Kasa cin abincin Junaid yayi, Mumy ta lura da hakan tace "Dama ka ci abincinka ka share komai, I keep telling you Junaid never depend on ur father, duk da nasan you are not depending on him dama, kar ma ka sa rai da komai nasa, sannan kayi ta bin sa ku rabu lafiya, you can see how things are going this days nasan ba yin kansa bane, banda hada ka da shi bbu abinda ake yi, lastly be prayerful" a hankali yace "In'sha Allah Mum" tace "Ya maganan da yayi maka jiya, kasan dai yana can yana kirga kwanakin da ya baka, ko kuma ince ana can ana Kirga masa koh" shiru Junaid yayi, Mumy tace "It's better ka kwantar da hankalin ka ka fito da mata tun kan ya nuna maka matsayinsa gun ka kamar yanda yayi ikirari" ae gaba daya abincin fita ran Junaid yayi, da kyar ya dinga tutturawa, Mumy na kula da hakan duk tausayin sa ya rufeta, tasan ba yin kan Abba bane yake masa haka, amma bbu yanda ta iya sai dai ta dage da Addu'a kamar yanda ta saba. Mikewa yayi jin ana kiran isha ya shiga bathroom ya dauro alwala ya fito ya tafi masallaci, ana idar da sllh yana tsaye da Abdul suna gaisawa ya ga tsayuwar motar El-ameen, El-ameen yayi parking ya fito suka gaisa da Abdul sannan ya kalli Junaid ya shiga gida, part din Mumy ya nufa suka gaisa ta tambayesa mutan gida yace Duk suna lafiya, ya kalli hanyar bedrooms yace "Wa ke kuka kuma Mumy?" Mumy tayi murmushi tace "Humainah ce, daga Abba yayi mata fada wai fa" dariya yayi bai ce komai ba, Mumy tace "toh je ka lallasheta kila tayi shiru, ni taki saurara na" shiru yayi sai kuma ya mike kamar munafuki ya nufi bedroom din Mumy, tura kofar yayi ya shiga ya sameta xaune can karshen gado tana rera kukanta, ya kusa minti biyu tsaye kafin yasa kai ya shiga dakin, ya karasa inda take a hankali, ya duka yana kallonta, tuni ta hadiye kukan da take ta kauda kai, ya d'an bude ido yace "Am, dama Mumy ce tace in xo in baki hakuri wai kina kuka" juya masa baya tayi da sauri, ya d'an sosa kai murya can kasa yace "Kiyi hakuri" taki cewa komai, a hankali yace "Kin ji" Junaid ne ya shigo dakin yana ganinsu ya saka dariya yace "Uhnn! har dakin ka biyota Dr, ba sai ka jira in dawo in kira maka ita ba" El-ameen ya mike yace "Mumy ce tace in xo in bata hakuri Mr man" daga haka ya fice daga dakin, Junaid yace "ba wani nan da'alla kai dai fadi gaskiya" Humainah ta mike xata shiga bathroom ya fixgota yana dariya yace "Oya sorry lil sis" fixge hannunta tayi tace "Ae next time ko boka aka kawo xa a ajiye bakin kofar ka baxan ce komai ba" dariya yayi sosai yace "Nafa ce kiyi hakuri, beside Allah ya fisu I believe" goge mata fuskarta yayi yace "Yanxu sai ki je ki wanke fuskarki kiyi kwalliya kin ga saurayin ki ya xo" Turasa tayi ta shige bathroom, yayi murmushi ya fita, a parlor ya tadda El-ameen yace "Mu je" mikewa El-ameen yayi, Mumy tace "Baxa ka ci abinci ba Ahmad" El-ameen ya girgixa kai yace "Naci abinci Mumy" Mumy tace "Toh shikenan," har sun fita Mumy ta kira Junaid ya dawo, ya isa gabanta yace "Gani Mum" tana kallonsa a hankali tace "Kayi addu'a kafin ka shiga" ya sunkuyar da kansa yace "Toh Mumy" daga haka ya fita daga parlon, suka nufi part dinsa da El-ameen, yayi yanda Mumy tace masa ya bude kofar ya shiga, El-ameen ma ya shiga, El-ameen ya xauna yana kallon Junaid yace "Did you tell anyone about our patient?" Junaid yayi shiru sannan ya girgixa kai yace "Not at all" El-ameen yace "Ohk, daxu mama Jummai take ce min xata je kauyensu gun dotan ta ta haihu, amma kwana biyu kawae xata yi, toh I don't know yanda za ayi abun, who will stay with ur patient during her absent?" Junaid yayi shiru yana kallonsa, can yace "Or shud we get a new...." El-ameen yace "Noo! Kwana biyu tace xata yi beside yarinyar tafi sabawa da ita kafin ta saba da wata kuma is something else, yau satin su kusan uku tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login