Showing 81001 words to 84000 words out of 170905 words

Chapter 28 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

656

"Baby dawo ki xauna nan ki gaya min abubuwan da Farida ta koya maki yau" mikewa tayi ta dawo kusa da shi ta xauna kasa, Junaid ya kalli agogon wrist dinsa sannan ya ci gaba da danna wayarsa, El-ameen yace "Gaya min mana" dago kai tayi ta kallesa cikin sanyayyan muryarta tace "tace min girki ne abinda muka yi" dariya yayi yace "Da gaske, to me ku ka girka?" Ta kalli farida tace "Ya ma?" Dariya farida tayi tace "A'a tuna dai" shiru tayi kamar me naxarin sunan girkin, da sauri farida tace "Ohkk okk fried rice ne da coconut drink muka yi baby" tayi hakan ne don yanxun nan sai ta iya rike kai ta fara ihu hakan kuma zai ja Dr Sumayya ta bata mata rai, shi kansa El-ameen ya san in dai tayi stressing brain dinta wajen son tuno abu nan da nan kan xai fara mata ciwo, kuma yana daukan lokaci bai daina ba. Jasmine ta kallesa tace "Fried rice and coconut drink Mumy tace mu yi" yayi murmushi yace "Good kuma kin iya yanxu?" Girgixa masa kai tayi alamar A'a, zai yi magana junaid ya mike yace "Toh ni xan koma" El-ameen yace "ohK bani makullin motata" hade rai yayi yace "Xan yi amfani da shi ne" El-ameen ya mike ya warce makullin ya koma ya xauna, juyawa junaid yayi ya fice daga parlon. Da daddare yana kallon wani program khadija ta shigo parlon da sallama ta ajiye masa mug din hannunta, yana kallonta yace "Meye wannan?" Tace "Lipton mana" yace "Wa yace ki kawo min?" Tace "Ance kace wai in maka" yace "Ohk tnx" mikewa tayi ta fita, ya girgixa kai ya ci gaba da kallonsa, bayan kusan minti talatin yaji kamar motsi a balcony, mikewa yayi ya kashe wutan parlon ya rage na tv kadai ya dawo ya xauna, a hankali aka murda kofar parlon, ya jinginar da kansa jikin kujera idonsa na kan tv, Suhaima ce ta shigo parlon da hijab dinta har kasa, ta tsaya daga bakin kofar tana lekosa, shi dai bai juyo ba har lokacin, cikin sassarfa ta karaso cikin parlon ta na kallonsa tace "Ya Ahmad?" Bai tanka ta ba hakan yasa ta d'an yi murmushi ta xauna kusa da shi tace "Amm dama...." Mikewa yayi yana kallonta fuskar nan nasa kamar bai taba dariya ba yace "me ya shigo da ke nan?" Gabanta yayi mugun faduwa ta mike tace "Oh dama..." Juyawa tayi da sauri zata bar wajen ya fixgota, ya sauke mata wani mari me lafiya cikin tsawa yace "Nace me ya kawo ki nan" jikinta ya dau rawa tace "Wayyo kudi xa ka ban" wani marin da ya gigitata ya kuma kai mata, ya ja ta ya nufi daki da ita, kuka ta dinga yi a tsorace tana cewa "Kudi wllh na xo karba" belt ya dauka ta fasa ihu a rikice tana kiran Hajiyarsu, ya ja ta suka fito parlor ya xabga mata a jiki, wanda hakan sai da ya kusa sa ta sakin fitsari, dukanta yake kamar an aikosa, ta dinga ihu iya karfinta tana kiran Hajiya da Umma, Dama suna labe balcony, Hajiya ta saki murmushi haka ma Umma a tare suka ce "Alhmdllh" duk suka sauko compound din, sosai suke jin ihun Suhaima, Hajiya ta saki salati da karfi tana kwala ma suhaimar kira tana cewa "ina kike, me ya same ki" Umma ma ta dinga kwalo mata kira duk suka cika tsakar gidan da hayani, su khadija ne suka fara fiffitowa sannan fatima, Hajiya tuni ta nufi part din junaid har lokacin tana kwalo ma Suhaima kira, Abba ne ya fito shi ma jin hayaniya, Ya kalli Umma yace "Meye haka?" Umma tace "Yo ina muka sani Alhaji, ihunta kawai muke ta ji mun rasa inda take" Fitowa Mumy ma tayi jin abinda Umma tace, Tuni Hajiya ta isa kofar junaid ta shiga bubbuga kofar tana kiran Suhaima, bude kofar junaid yayi bayan ya lallasata iya son ransa da belt ya cillota waje ya kulle kofarsa, birgima ta dinga yi tana cewa "Wayyo Hajiyarmu bai sha ba" Hajiya da idanuwanta suka firfito ta dagota da sauri ta toshe bakinta a jikinta tace "Ba kya ji Suhaima kin tsokanesa kenan koh?" Abba ne ya karaso yana kallonsu yace "Meke faruwa ne wai?" Da sauri Hajiya tace "A'a ita ce bata ji Alhaji fitsara tayi masa daxu, mu je kawai maganinta kenan" Abba ya kwalo ma junaid kira Hajiya da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta tace "oh Alhaji don ya hukuntata shine wani abu, bata dawowa da wuri ne daga makaranta yayi mata magana tayi masa fitsara shine ya xaneta, ai ni ya min dai dai, mu je kawai Alhaji" Mumy ce ta karaso wajen Hajiya tace "Ohh Amina ku rabu da yaron nan, don ya doketa ya hukuntata shine me... Yanxu da fatima ce ai baxa ki ce komai ba" juyawa kawai Mumy tayi ta bar wajen, Abba ya girgixa kai shima ya koma part dinsa, Sumsum Hajiya ta ja Suhaima da ke kuka tana soshe soshen suka bar wajen, Umma ta hadiye yawu da kyar ita ma tayi part dinta. Wasa wasa har biki ya rage kwana biyu, banda shirye shirye babu abinda ake a gidan kamar irin shi ya zabi matar din nan, tuni 'yan uwa da abokan arxiki aka fara xuwa daga garurruwa daban daban, sai a lokacin Junaid abun ya fara damunsa on like before da lamarin ke basa dariya, babban damuwar tasa rashin sanin wacece iyayen sa suka xaba masa, babu yanda bai yi da Mumy ta gaya masa ba ita ma tace bata sani ba, Tashin hankali gun Umma da Hajiya baya faduwa don sun rasa abun yi, komai suka yi ba nasara ciki gashi basu san wacece shegiyar da xa a aura masa ba don basu ga alamar daya daga 'ya yansu bane, da yammacin ranan Hajja ta diro gidan, magiya junaid ya dinga mata kan ta gaya masa wacece matar tasa tace ubansa yayi kadan balle shi, sosai hankalinsa ya tashi, bayan magrib Abba yasa a kira sa, yana shiga parlon ya xauna Abba yace "Babu wani shirin da za kuyi ku, ko walima ne?" Ya gigixa kai yace "A'a Abba, walimar da xa ayi a nan gida ya isa" Abba yace "Toh shkkn, hakan it's Ohk" ranan kasa bacci junaid yayi har kusan karfe dayan dare, wayarsa ya jawo daga karshe ya shiga neman number Humainah don yasan baxa ta rasa sanin matar ba, har ya gama ringing bata daga ba ya sake kiranta sai gashi ta dauka, cikin sanyin murya yace "Kina ji na Humainah" "Um" kawai tace masa kamar anyi forcing dinta, ya lumshe ido ya bude yace "Plss nasan baxa ki rasa sanin warce xa a aura min ba, ki gaya min wacece plss" taki cewa komai na kusan second talatin har sai da yace "Hello" sannan tace "Ban sani ba nima" yace "Plss" kamar xata yi kuka tace "Ban sani ba," tsaki yayi ya katse wayar ya jefar. Washegari alhamis da asuba yayi shirin fita aiki ya fice ya bar masu gidan, haka ya wuni bai da sukuni ranar, yana barin gun aiki Clinic ya tafi gun El-ameen, da damuwa yace "Frnd har yanxu fa ban san wacece matar nn ba" El-ameen yayi murmushi yace "gobe idan mun kai ka xaka ganta, sbda son da Abba yake maka shi yasa yake son surprising naka" Junaid yace "Plss ka daina bata min rai more, what sort of surprise is this, and what if fitinanniya ce taki yarda da xaman yarinyar a gidan?" El-ameen ya hade rai yace "Sai ka korata nasu gidan don bata xo maka da gida ba, and tana tarewa gobe ita kuma xata tare ran lahadi don ranan Dr Sumayya xa su yi tafiya, tsaf ita ma kuma xa a gyara mata nata dakin" Junaid ya dafe kai yace "Ba haka ba frnd, kasan tana iya xuwa tayi reporting ma su Abba fa" El-ameen yace "Shit, gashi har xa a maka aure gobe baka xama mature person ba, ka ki girma har yanxu junaid, look yanxu you are going to leave a free.... When I say free I mean a free life, no more Mumy Mumy Mumy, you are going to head a family of ur own don haka ko wani decision kayi a gidan ka is right ba sai wanda parent dinka suka maka ba, from tomorrow you will be on ur own" junaid yace "Uhum?" Tsaki El-ameen yayi, can yayi kwafa yace "da rabon matar nan ta rainaka idan ta lura you don't have a say of ur own!" Mikewa Junaid yayi yace "Baka san ni ba kenan" daga haka ya fice daga office din.

✍🏻
*Haske writers association*💡
[1/14, 9:15 AM] Elhajj: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

44/45

Da asuba Junaid ya dade xaune gefen gado daga bisanni ya mike, kallo daya ya ma Humaina dake bacci ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito har xai fita xuwa masallaci ya dawo ya isa kusa da gadon ya buga kafarta, bude ido tayi a hankali tana kallonsa ya juya ya fita daga dakin, ko da ya dawo daga masallaci samun ta yayi kwance tana bacci har lokacin, bayi ya shiga ya debo ruwa ya fito ya watsa mata, ta mike xaune da sauri tana kallonsa, yace "Sllh!" Daga haka ya fita daga dakin, tsaki tayi ta bi sa da harara ta sauka daga gadon ta shiga bayi. Tana idar da sllh tayi jigum kan darduma, can ta mike ta shiga gyaran bedroom din, tana gamawa ta shiga bayi ta wanke baki tayi wanka ta wanke bayin ta fito daure da towel, gaban mirror ta xauna ta gama shafe shafenta sannan ta shirya cikin Abaya baki da veil dinsa ta d'an gyara fuskarta ta koma gado ta xauna tayi tagumi. Bude kofar dakin aka yi fatima da khadija suka shigo, Humainah ta mike da sauri lokaci daya tayi murmushin jin dadin ganinsu, fatima tace "Uhum Amaryar yayarmu, Antynmu!" Hade rai tayi can ta fashe da kuka tace "Ni ba amaryarsa bace, ai Hajja tace sbda a raba sa da mahaukaciyar nan ne aka aura masa ni, amma da ya rabu da ita sai a sa ya sakeni in ci gaba da karatuna" innocently tayi maganar tana kallonsu, Khadija da fatima suka fashe da dariya barin khadija, juyawa Humainah tayi a sanyaye ta koma gefen gado ta xauna, hade kanta tayi da gwiwa tana kuka, fatima ta karasa kusa da ita da sauri tace "Toh ai ba mu ce ba haka bane ba fa Humainah" Humainah ta girgixa kai tana kuka tace "Ba wani nan nasan wayo aka min baxa a ce ya sakeni ba, yar yarinya da ni xan je ss3 za ayi ma aure bayan ku ba a maku ba....." Khadija ta xauna gefenta tace "Ni dai ba dariya nake maki ba, ba ruwana, ga abinci Mumy tace a kawo maki" Humainah ta dago kanta tana share hawayen idonta tace "Hajja fa?" Khadija tace "Ta ce anjima xata xo" Junaid ne ya shigo dakin ya tsaya daga bakin kofa yana kallonsu yace "A baki aka ce ku bata abincin?" Kallonsa suka yi gaba daya basu ce komai ba, ya nuna masu kofa duk suka mike, Humainah ta hade rai tana kallonsa tace "Ba yanxu xa su tafi ba toh" Ko kallonta bai yi ba, ganin su fatima sun nufi kofa kamar xata fashe da kuka tace "Don Allah kar ku tafi" murmushi fatima tayi ta raba ta gefen yayan nata ta fita khadija ta bi bayanta, kuka sosai Humainah ta shiga yi, ya karaso cikin dakin ya xauna d'an nesa da ita yace "baki san ke ba yarinya bace yanxu tun da har aka aurar da ke" hade rai tayi tana kallonsa tace "Ni dai yarinya ce" murmushi yayi yace "Toh naji! tsoron xama ke kadai kike a dakin da kike son su xauna da ke?" Ta kallesa hade da gyada masa kai, yace "Toh xan samo maki warce xata dinga taya ki xama ai kina so?" Tana kallonsa tace "Amma babba ce?" Ya girgixa mata kai yace "No yar yarinya ce kamar ki sai ta dinga taya ki xama kuna kwana ma tare" sosai ta hade rai tace "A'a bna so, xan iya xama ni kadai" shiru yayi yana kallonta, can yace "Saboda me?" Ta mike tace "Haka nan kawai, xan iya xama ni kadai abuna" daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, lumshe ido yayi ya bude yana naxarin abinda ta ce, Mikewa yayi shima ya fita daga dakin ya koma nasa. Karfe sha biyu saura aka danna bell downstairs, Junaid dake bedroom dinsa yana danne dannen waya ya mike ya fita, dai dai lokacin da Humainah ma ta fito, kallo daya yayi mata ya sauka ya je ya bude kofar, Hajja ce tsaye bakin kofar da Sadiya, ta washe hakora ganin Junaid tace "A'a ango, to gani na biyo ka don kayi amarya sai ka mance da uwar gida?" Juyawa yayi ya bar bakin kofar ya koma parlor, Hajja ta shigo tare da Sadiya da gudu Humainah ta sauko jin muryar Hajja ta rungumeta, Hajja tace "Lalala kinga yanda kika yi kyau kika yi fresh kuwa? Lallai Amadi ya iya kiwo daga jiya xuwa yau" hade rai Humainah tayi tace "Ni babu abinda ya ban na ci har yanxu" Hajja tace "Ehh amma ai kin kwan masa a gida" turo baki tayi ta tafi ta xauna, Hajja ta kalli Junaid tace "Banxa kai kuma ko ka kira ka mana godiya ka ga xukekkiyar amarya ba mahaukaciya ba" Kallonta kawai yake can ya tabe baki yace "Nii ban gode ba tun da ban ce ina so ba, kawai makala min aka yi" Humainah ta fashe da kuka tace "Hajja kin dai ji ko, ni dai tare xa mu koma don ni ma makala min aka yi ban ce ina so ba" Hajja ta hade rai tace "Kai kaga irin hada ta da Allah annabin da aka dinga yi don ta amince da gantalallen auren ka, banda kaddara me xata yi da kai Ahmad, kai da cikakken saiti baka da, wllh wllh 'yar nan tafi karfin ka, kawai ka kara gode ma Allah da ya sa aka baka ita" juyawa tayi tana kallon Humainah tace "ke kuma kar ki kuskura ki bari ya kwana dakin ki tunda haka yace, hanyar jirgi daban ta mota daban kin dai ji ni..." Humainah ta gyada mata kai tana goge hawayen idonta, Hajja ta nemi kujera ta xauna tana cewa "Banda walakanci an samu an lallaba yarinya da kyar ta amince ta rufa maka asiri ta aureka xaka dinga gaya mana magana, ko fa kwandalar ka bbu a bikin nan don tsiya.... Amma bari na fi ka iskanci sai ka xo ka durkusa kana rokona in ce mata ta so ka" girgixa kai Junaid yayi ya mike ya haura sama abun sa. Har Karfe uku Hajja na gidan ita dai Sadiya dama turo ta aka yi ta ga kwakwaf ta ga yanda gidan yake da abubuwan da aka xuba, tana gama abinda ya kawota ta kara gaba ta bar Hajja. Har dai bayan la'asar Hajja bata da niyar tafiya Junaid ya rasa me suke kullalawa a dakin gashi El-ameen ya ki xuwa saboda Hajjan, mikewa yayi ganin har biyar ya gota ya shiga dakin, suna ganinsa suka yi shiru, Hajja ta hade rai tace "To ya aka yi kuma?" Ya d'an shafa kansa yace "Kawu Abubakar ne ya kira wai yana ta jiran ki xai koma" mikewa Hajja tayi da sauri tana xuge yar purse dinta tace "Auu bawan Allah to bari in je" Humainah ta marairaice kamar xata yi kuka tace "Yanxu tafiya xa kiyi ki bar ni Hajja" Hajja ta hade rai ta kalli Junaid sai kuma ta duka kusa da ita murya can kasa tace "Kin dai ji abubuwan da na gaya maki dai koh?" Humainah ta gyada mata kai, Hajja ta mike tace "Ehh to ba dole in tafi ba Humainah, amma ina nan dawowa kila ma da kayana xan taho tunda ai jikokina ne ko na xauna bbu komai" daga haka ta nufi kofa tana cewa "Toh kai d'an ubanka xaka kai ni gidan ne ko in je in hau machine tunda Sadiya sun koma da driver" ficewa junaid yayi daga dakin ita ma ta fita tana cewa "Toh Humainah sai Allah ya sake dawo da ni" har gida Junaid ya ajiye Hajja sannan ya kira El-ameen yace "Toh ta tafi, am waiting for you" daga haka ya katse wayar ya kama hanyar gida. Kusan a tare suka iso gidan da El-ameen, El-ameen yayi parking ya fito yana murmushi yace "Daga ina haka ango?" Junaid yace "Nayi dropping dinta mana" bude motar El-ameen yayi ya shiga yana kallonsa yace "Tabdi gaskiya Humainah ta karbe ka, ka ga yanda ka kara kyau yau kuwa" girgixa kai Junaid yayi yace "Kaga ni mu yi maganar arxiki, kasan kuwa yarinyar nan tace ita bata son a kawo mata kowa gida?" El-ameen ya hade girar sama da ta kasa yace "Kamar ya? Kaga matsalar ka ko Ahmad, daga aure har yarinya xata fara raina ka tana fadin abinda xa ayi a gidan da wanda baxa ayi ba, gidan ta ne da har xata gaya maka abinda xa ayi? Kai wani irin Human being ne junaid" Shiru Junaid yayi yana kallonsa, can ya sauke ajiyar xuciya yace "Am afraid kar ta ce xata gaya ma su Mumy ne shi yasa ban ce komai ba" El-ameen yace "Tabdi! Yarinyar nan fa wllh sai kayi gaske da ita Idan ba haka ba second Mumy dinka xata xama, naga alamar fitinanniya ce, shikenan kai kuma ka xama abun tausayi baka da say a duniya sai na Mumy da wife, haba sai kace ba captain ba kawai ka cika ma kanka girman kai da miskilanci maimakon being ur own self, ita wannan har ta ma wuce ka bubbuge ta Idan tace xata kawo maka rainin hankali" girgixa kai junaid yayi hade da yin murmushi yace "Uhum lallai" horn ya danna aka bude gate ya shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login