Showing 138001 words to 141000 words out of 170905 words

Chapter 47 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

630

sai kuma ta gyada masa kai tace "Ehh!" Yace "Dat's good" junaid dai na biye da su a baya, wata hanya daban ta dauka suka haura bene sannan ta bude wata babban kofa ta juya tana kallonsu, suna hada ido da El-ameen ta sauke idonta kasa ta ci gaba da tafiya, tsarin gun kamar na Kilishi da suka baro, babu kowa babban parlon sai jakadiya da wata me goge goge, Ta nuna masu kujera, jakadiya ta bi ta da kirari kafin tayi masu sannu da xuwa, El-ameen ne kadai ya amsa mata yana murmushi, Bedroom din Umma Zahrah ta nufa ba a dau lokaci ba sai ga ta sun fito da Umman, murmushi ne shimfide fuskarta har ta karaso parlon tana kallonsu gaba daya tace "Sannun ku da xuwa...." Sakkowa El-ameen yayi har kasa Junaid ya bi sa da ido kafin shima yayi kasa da kansa ya sauka, suka gaisheta gaba daya, tana murmushi har lokacin ta amsa, tuni jakadiya ta cike gabansu da kayan marmari da shaye shaye, Umma tace "To waye Ahmad waye takwaran mai martaba" El-ameen yayi murmushi yace "Ni ne El-ameen...." Ta kalli junaid cikin sanyin murya tace "Kai ne Ahmad kenan" kai ya gyada mata ba tare da ya dago ba, a sanyaye tace "Allah ya albarkaci rayuwar ku, yasa ku gama da iyayen ku da duniya lafiya....." El-ameen yayi saurin cewa "Ameen Umma mun gode" Umma ta kalli Zahrah tace "Kin kai su gun Kilishi?" Ta gyada kai tace "Can muka fara xuwa" Umma tace "To Maa sha Allah" ba su wani dade part din Umma ba ta dalilin bakin da tayi, Zahrah ta nufi fada gun Abbanta da su, sai dai wannan karan sauri kawai take bata bari sun jera da El-ameen din ba, bai takurata ba ya jira junaid, junaid na isa gunsa yace "ya kuma ku ka raba tafiyar?" Murmushi yyi yace "Yea hakan yafi don ni ba runguma bane iyakar abinda zan mata idan na kasa jure shariyarta gare ni" Wani kallo Junaid ke yi masa kafin yace komai El-ameen yayi dariya yayi gaba ya bar sa nan, suna shiga fada ta juya ta bar su tare da Abbanta. Da rana Umma ta takurata ta kai masu lunch tace ai masu aiki xa su kai masu, Mikewa tayi d'aga karshe dai ta fita nemo Ummi ta rakata. Sae da suka fara xuwa kitchen don tabbatar da cewar an kai abincin taga an kai, fura ta tarar ana damawa kitchen din, ta dau babban jug ta diba snn ta dau tray ta daura kai da cups ta fita tare da Ummi, suna isa part din Abdul Ummi ce ta fara shiga da sallama kafin ita, Junaid ne kwance parlon yana danna waya, yayi masu kallo daya ya dauke kai, Ummi ta xauna tana kallonsa ta gaishesa ya amsa ba tare da ya kalleta ba, Ajiye trayn hannunta Zahrah tayi ta nufi bedroom ba tare da ta kallesa ba, El-ameen ta gani da Abdul suna kallo ga cake gabansu, El-ameen ya buda ido murya can kasa yace "princess!" Tace "Uhm, kun yi lunch?" Hararata Abdul yayi yace "Basu yi ba" 'yar dariya tayi ta kalli El-ameen dake kallonta, can ta karasa ciki ta xauna kusa da Abdul ta kai bakinta kusa da kunnensa kamar me rada tace "Why is he alone?" Abdul ya kalleta yace "Ahmad?" Satan kallon El-ameen tayi sai kuma ta dauke kai da sauri, Abdul yace "He said he's more comfortable there" da sauri tace "Alryt, ohk" sai kuma ta kalli El-ameen tace "Ga fura na kawo maku fa" ba tare da ya kalleta ba yace "Toh mun gode" mikewa tayi ta fita daga bedroom din, xaune ta samu Ummi har lokacin idonta na kan Junaid, "ki tashi mu je" ta fadi haka bayan ta dauke kai daga kallonta, shi dai idonsa na kan waya, Ummi ta mike tace "Ohk furan xa a xuba masu ne?" Da sauri Zahrah tace "Noo!" Sai kuma ta nufi tray din da ta dire daga gefensa ta durkusa ta dau cups din ta xuba furan ciki ta ajiye tana kallonsa fuskarta daure, kara wayarsa yayi a kunne ya mike xaune ya sakko da fararen kafafuwansa kasa kamar wanda aka tilasta yayi magana yace "kina ji na?" Kasa daina kallonsa Zahrah tayi, ya shafa kansa yace "Have you eaten?" Shiru ya d'an yi kafin yace "Ki dai daure ki ci, I will call back later" daga haka ya katse kiran ya ajiye wayar lokaci daya ya sauke idonsa kan Zahrah dake kallonsa har lokacin, da sauri ta dauke Kai ta mike ta nufi kofa ta fice, har dare bata kuma komawa part din Abdul ba, duk ta rasa me ke mata dadi mugun haushin Junaid kawai take ji, har shi xae nuna mata ji da kai? mikewa tayi daga karshe ta fice ta nufi bangaren Abdul, El-ameen da Junaid ne parlon wannan karan, kmr daxu kwance Junaid yake waya na kare a kunnensa, Bata ko kalli inda yake ba ta karasa gun El-ameen dake kallon wani movie ta xauna kusa da shi tayi fari da ido tace "Are you okay? Bbu damuwa koh" Yana kallonta yace "Yea, am just missing home" murmushi tayi tace "Nan ma fa gida ne" yace "Yeah haka ne" ta mike tace "Ina son ka rakani mu je garden" yace "Really?" Ta gyada masa kai tace "Yeah, I want you to keep me company" mikewa yayi yace "Alryt mu je," duk da wayar da ke kare kunnen junaid gaba daya ya mance waya yake, ba kallon direction dinsu yake ba amma gaba daya hankalinsa na kansu, kofa ta nufa El-ameen ya kalli junaid da yayi saurin dafa wayar kunnensa yace "Will be ryt back" ko kallonsa Junaid bai yi ba har ya fita, ya mike xaune, ji yayi xuciyarsa na tafarfasa kawai, ya kusa minti ashirin xaune har Abdul ya shigo, ko da ya tambayesa El-ameen cewa yayi bai sani ba, yana shiga bedroom ya mike ya fice daga part din gaba daya, ji yayi da ma safiya ce ko rana da babu abinda xai hanasa komawa katsina duk da sarki ne ya tsaida su amma da tuni sun tafi da yamma, can wani waje da bbu hayaniya kuma babu wani haske ya samu ya xauna, har sha biyun dare bai da niyar tashi ya shiga ciki, gaba daya El-ameen yayi tunanin wucewa junaid yayi don yasan halinsa barin ma Atm card dinsa na jikinsa, Abdul da mamaki ya cikasa yace "Why is he acting that way?" El-ameen yace "That's he's hobby" Abdul bai san lokacin da ya fashe da dariya ba, El-ameen yace "Yeah, an only son, mumy's pet" Zahrah dake tsaye ta tabe baki ta juya ta fita daga parlon sai dai duk jikinta yayi sanyi, kasa komawa part dinta tayi hakan yasa ta bi hanyar da tasan baxa a ganta ba ta fita waje, tafiya kawai take ba don tasan ina ma xata ba kuma meye ta fito yi, bata yi wani nisa da tafiyan ba tayi ido hudu da shi har lokacin yana xaune ya xuba ma taurari ido kamar me kirgan su, rasa abinda xata yi tayi a lokacin, ci gaba da tafiya xata yi ko juyawa xata yi ta koma, Dakewa tayi ta tsaya inda take, can ta karaso fuskar nan nata daure tana kallonsa tace "Don me xaka wani fito nan cikin dare ka ba mutum wahalan nemanka when I am suppose to be in bed" wani kallo ya watsa mata ta gefen ido ya ci gaba da kallon sky abun sa, fixge wayar hannunsa tayi tace "Malam magana nake maka fah?" Sai a sannan ya kuma kallonta suka yi ido hudu gabanta ne ya fadi sosai, ya mike ya warce wayarsa yace "Gadina aka baki ne?" Wani kallo tayi masa tace "Ehh sbda ta dalilina ka xo garin nan....." Shiru tayi sai kuma ta turo Baki tace "I still can't believe ma kai ka tsince ni, or are you angry don bance kayi accompanying dina bane" murmushi yayi yace "How will you believe it, tunda ba sani kika yi ba lokacin da kike xuwa in bude maki Zip, in raka ki toilet, kike xuwa bedroom dina daure da towel..... Infact har lokacin da nake taimaka maki idan kina menses....." Xaro ido tayi, tayi wani kara tace "Nooo...." Ya gyada kai yace "Yesss! Har lokacin da......" juyawa tayi da gudu ta bar gun, bai san lokacin da ya fara dariya ba har da xama. Washegari kasa fitowa Zahrah tayi, kenan idan haka ne kila har nakedness dinta ya taba gani, har da kukanta da tayi wnn tunanin, sai da Umma ta bata rai sannan ta mike ta fita xuwa gaida su da safen, hijab tasa tsabar bata jin xata iya kallon junaid, tana shiga parlon ko ta gansa shi kadai xaune yana shan tea, kin dago kanta tayi ta kuma kasa karasawa can bedroom, kallonta kawai yake yana kokarin boye murmushin fuskarsa, juyawa tayi xata fita ya mike tana ganin haka ta kwasa da gudu, wani dariya ya taho masa bai san lokacin da ya fashe da dariyar ba, Abdul da El-ameen suka fito da sauri, buda baki Abdul yayi ganin ashe yana iya dariya haka, El-ameen kam karyar da kai yayi ya rungume hannu yana jinjina abinda ya ba junaid dariya haka, da kyar ya tsaida dariyar ya daga kai yana kallonsu, Abdul yayi murmushi yace "Ohh that's more beautiful of you captain" El-ameen ya tabe baki yace "Ko xa mu iya sanin abinda ya baka dariya haka Ahmad, na tabbata mu sai mun yi fiye da wanda kayi" shafa kai junaid yayi yana murmushi yace "Bana son ku haukace da dariyar just let it" El-ameen ya daga kafada yace "Lallai kam" daga haka ya juya ya koma dakin, Abdul ya karasa ya xauna gefensa yace "Gist me more about ur self captain...." Murmushi junaid yayi yana kallonsa. Karfe sha daya junaid ya gaji da xama don Abdul da El-ameen sun fita, bbu kuma yanda basu yi da shi ya bi su ba yace A'a baxae je ba, suka yi tafiyarsu suka barsa, dama bayan azahar xasu gana da wasu yan uwan mai martaba kafin su kama hanyar kt ranan, mikewa yayi ya fita yana rike da wayarsa, tafiya sosai yayi ya ga wani waje kamar gun shakatawa ga tsuntsaye sai shawagi suke, carpet grass ne shimfide gun, shiga yayi ta wani babban kofa ya dinga tafiya yana bin ko ina na wajen da kallo, wasu kuyangu guda uku ya gani suna tahowa ya bi su da kallo kafin yace "Ana shigowa nan kuwa" a tare suka gyada masa kai, daya daga cikinsu tace "Sai dai Gimbiya na nan ita ma!" Yace "Wace gimbiyar?" Tace "Gimbiya Zahrah" bai ce komai ba yayi gaba abunsa, xaune take ita kadai tana kallon cartoon da laptop din dake ajiye gabanta ta xauna kan kafafuwanta, gefenta kuma bowl ne me dauke da kayan itatuwa, juyawa tayi jin taku bayanta, suna hada ido ta mike da sauri har tana ball da bowl din fruits din gabanta, ta kuma juyawa da shirin gudu tayi karo da laptop dake ajiye, tsallakesa tayi ta bi wani hanyar da gudu, bin ta yayi da kallo kafin ya tabe baki ya xauna ya daga laptop din, ya dau apple daya ya shiga ci ya canxa cartoon din xuwa something meaningful yana kallo yana murmushi. Da yamma misalin hudu da wani abu junaid da El-ameen ne xaune a fadar me martaba dake dauke da mutane da dama tun daga waziri, advisern sarki har xuwa kasa, sannan ga 'yan uwansa da abokan arxiki, kanninsa mata da maza, Abdul na xaune daga gefen Abbansa, Ummi na xaune daga daya bangaren sa, Umma da Kilishi ma duk suna fadan xaune, Zahrah ce karshen shigowa ta nufi gun Ummanta ta xauna gefenta, kallon Junaid kawai sarki yake, can kuma sai ya kalli El-ameen, bayan kusan minti biyu na silence sarki yayi gyaran murya yace "Ahmad!" Dago kai junaid yayi yana kallonsa, Sarki yace "Nasan ba lallai in iya biyan ka abinda ka min ba amma ka fadi duk abinda kake so nan duniya in dai bai saba ma shari'a ba nayi maka alkawarin yi ma shi idan Allah ya yarda," shiru junaid yayi, can ya dago ya kalli Zahrah da idonta ke kansa suna hada ido ta dauke kai, kallon El-ameen yayi yaga wani gu daban yake kallo, can ya girgixa Kai yace "Bana bukatan komai mai martaba, I helped her for Allah's own sake" kallonsa kawai Sarki ke yi, can ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh shknn, Allah ya albarkaci rayuwar ka Ahmad" cikin sanyin murya junaid yace Ameen, sarki yayi murmushi ya juya yana kallon El-ameen yace "Kai fa takwara na?" Kallon junaid El-ameen yayi suka hada ido junaid ya sauke kansa kasa, Zahrah ma idonta na kan El-ameen gabanta na faduwa, haka kawai junaid ma ya ji gabansa na faduwa, bayan kusan second ashirin El-ameen yace "Ina son ka min alfarmar bani aurenta, na kuma yi maka alkawarin xan rike ta da amana...." Wani mugun bugu xuciyar junaid yayi, Zahrah kam kallon El-ameen take ko kiftawa babu, Mai martaba da ya kafa ma El-ameen ido shi ma yayi murmushi yace "Na baka! Xan kuma biya maka sadaki" kallon mamaki duk occupant din palace din ke ma sarki sanin baya magana biyu, El-ameen da ya rasa wani irin godiya xai ma mai martaba ya mike ya isa gabansa ya durkusa yana kallonsa, shafa kansa mai martaba yayi yace "You are blessed in'sha Allah son" El-ameen ya kama hannunsa ya lumshe ido ya kai lips dinsa, mikewa Zahrah tayi hawaye cike idonta ta kalli junaid da yaki dago kai har lokacin tayi ficewarta daga fadan.
*Haske Writers association*

[3/19, 9:36 PM] El-hajj💥: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

80......

Ko k'adan Junaid bai kuma gane abubuwan da sarki ke cewa ba a wajen gashi bai yarda ya dago kai ba, mikewar da El-ameen yayi ya sa shi mikewa shi ma, kiran sunansa da ya ji anyi ya sa shi juyawa yaga sarki ne ya kirasa, sarki na kallonsa yace "Allah ya tsare hanya, ina kuma sauraron xuwar kakar ka" da kyar ya iya amsa masa yana kirkirar murmushi sannan ya juya ya fita, tun a hanya ya dake yayi patting shoulder din El-ameen yana murmushin karfin hali yace "Congrat frnd!" Kasa ce masa komai El-ameen yayi yana kallonsa, suna isa part din Abdul junaid bai ko kalli kayayyakin sawan da Abdul ya jido masu a boutique jiya ba, atm dinsa ya dauka da waya xai fita, wani abokin Abdul yace "Baxa ka canxa kaya ba Captain, Abdul din da xai kai ku airport ma bai gama shiri ba" cike da karfin hali junaid yace "Yeah, ina waje nan...." Daga haka ya nufi door, El-ameen dake tsaye ya bi sa da ido, a hanya Junaid ya hadu da Abdul, Abdul yace "A'a ina xa ka captain" junaid ya kirkiri murmushi yace "Ina jiran ku a waje" hannunsa Abdul ya kama yace "Noo baka isa ba, sai ka sake wanka ka canxa kaya" duk yanda Junaid ya so Abdul ya kyalesa kin saurarensa yayi har sai da ya mayar da shi part dinsa, dole yayi wanka ya canxa kaya, duk suka shirya, Abdul ya tafi da su xuwa gun Mum dinsa suka yi mata sallama ta hadasu da turarruka masu tsadan gaske, sannan ya kai su part din Umma, ita kadai ce xaune parlor da jakadiyarta, tana ganinsu ta saki fuska nan suka yi mata sallama ta dinga sa masu albarka, shi dai Junaid kansa na kasa, tsaraba sosai ta hada masu su biyun su kai ma Mum dinsu, El-ameen yayi mata godiya, shi ma junaid da kansa ke kasa yayi godiyar, Abdul yace "Umma ina Zahrahn fah?" Umma tace "Ina jin bacci take" mikewa yayi ya nufi bedroom din Umma, Umma ta bi sa da kallo har ya shiga, kwance ya sameta cikin bargo Ummi na xaune gefenta tayi tagumi, Abdul ya karasa da sauri yace "What's wrong with her" a hankali Ummi tace "She's just crying, me yasa Abba xai yi mata haka.... In ma haka ne ba sai ya basu kudi me yawa ba, ina jinin sarauta da auren....." Wani kallo ya watsa mata ya cire bargon yana kallon Zahrah, mikewa xaune tayi ta fashe da kuka tana kallonsa, ya xauna yace "Look ki hadiye kukan nan ki min magana, aurensa ne baki so?" Shiru tayi bata ce komai ba sai hawaye, yace "Ki min magana mana" girgixa kai tayi a hankali tace "A'a...." Yace "Baki son auren?" Tana goge fuskarta tace "Ni baxan iya cewa bana so ba, they helped me and...." Ya mike yace "Good you know that! Kina hauka ma duk sun xauna da ke da amana bare aure, yarima kamar ki kike so ko wa?" Girgixa kai tayi yace "to yanxu tashi ki wanke fuska ki taho kuyi sallama da su" mikewa tayi da kyar tayi yanda yace mata ta daura alkyabbarta ta rufe kusan rabin fuskarta ta bi sa suka fita tare da Ummi, sosai Umma taji dadin ganin ta fito don bata yi tunanin xata fito ba a yanda ta dinga kuka, har mota ta rakasu Ummi na rike da hannunta, shi dai Junaid yana gaba sai dai yayi murmushi idan aka ce wani abu, Ummi tace "Ya Abdul mu raka ka airport din plss?" Yace "Alryt mu je" front seat junaid ya bude ya shiga, El-ameen ya koma baya Ummi ta shiga sannan Zahrah, Abdul da Ummi kadai ke hira a motar, daga Zahrah, Junaid har El-ameen bbu me cewa komai, a hankali ta daga alkyabbar fuskarta suka yi ido hudu da Junaid don kallonta yake ta madubi, ta sauke idonta da sauri, suna isa airport junaid ya fita sannan El-ameen, Ummi ma ta sauka, sai da Abdul ya fita sannan Zahrah ma ta fito, karasawa El-ameen yayi kusa da Zahrah ya mika mata wani disc din hannunsa, ta daga kai tana kallonsa, sai kuma ta karba, kallo daya junaid yayi masu ya fara tafiya, Abdul ya bi bayansa haka ma Ummi, da kyar Zahrah tace "What's this?" Ya rungume hannayensa yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login