Showing 75001 words to 78000 words out of 170905 words
Chapter 26 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
tace "Toh sir" El-ameen ya kalli Jasmine yace "Tashi ki bita kiyi duk abinda tayi kin ji" mikewa tayi tana kallonsa ya gyada mata kai yace "Yes follow her" tace "I should follow her?" Murmushi yayi ganin yanda take catch up da sauri yace "Yes follow her" kamar me tausayin kasa haka ta dinga bin nurse din a baya har suka shiga toilet din, nurse din ta rufe kofar tana kallonta tace "Do you want to urinate?" Kallonta kawai Jasmine take kamar me naxarin word din, a hankali tace "Urinate?" Matar ta gyada mata kai, girgixa mata kai tayi, matar ta dau kettle daya ta mika mata ita ma ta dau daya tace "Kiyi duk yanda ki ka ga nayi" a hankali Jasmine ta durkusa tana kallon nurse din runtse ido tayi jin xafi a kneel dinta, nurse din dai sai kallonta take har ta bude idon, sannan ta yi bismilla ta fara alwalan tana kallonta, jasmine ta wanke hannunta ita ma kamar yanda ta ga nurse din ke yi, haka tayi ta kwaiwayon ta har suka kare alwalan nurse din ta fito tana biye da ita a baya, har lokacin junaid na xaune kan darduma, El-ameen ma na xaune yana jiran fitowar su, mikewa yayi yana kallon junaid yace "Pray mat malam" junaid ya tabe baki ya mike ya koma kan gado, El-ameen ya shimfida ya kuma dauko wani ya shimfida a baya, ya dau hijab ya mika mata yace "Ki saka" karba tayi tana kare ma Hijab din kallo, ya mata alama da tasa, kokarin sakawa ta shiga yi ta kasa don bata san ma yanda xata saka din ba, ya karaso yana murmushi ya karba ya saka mata, Junaid ya kauda kai hade da tabe baki, El-ameen ya nuna mata inda xata tsaya kan darduman yace "Kiyi duk yanda kika ga nayi" shiru tayi tana kallonsa, yace "Kin ji?" A hankali ta gyada masa kai, ya koma darduman gaba ya tada sllh, haka ta dinga binsa sllhn tana yin duk yanda taga yayi da kyar sbda kneel dinta, har suka idar ya juya yana kallonta, jini ya gani Hijab dinta ya dawo kusa da ita da sauri yace "Ohh!" Hannu yasa xai daga hijab din ta koma baya sauri tana masa wani kallo, komawa baya yayi cikin sanyin murya yace "Yi hakuri," mikewa yayi ya fita, ta juya tana kallon Junaid da ke kallonsu, dauke kanta tayi tana nan xaune har El-ameen ya dawo da nurse, nurse din ta duka kusa da jasmine tace "Sannu" daga hijab din tayi tana kallon kneel din, kayan aiki El-ameen ya miko mata nan ta fara gyara mata wajen, rufe idonta tayi da ganinta kasan daurewa kawai take, El-ameen ya durkusa kusa da ita yana mata sannu, har nurse din ta gama, a hankali ta bude idonta da ya kada, yace "Sannu" ta kallesa sannan ta sunkuyar da kanta, mikewa nurse din tayi ta fita da kayan aikin, tashi yyi ya dauke darduman da yake kai ita ma ta mike ta dauke dayan, Junaid ya dauke kai tun kan su kallo inda yake, ledan da El-ameen ya shigo da ya nufa ya bude ya fiddo da sabbin toothbrushes da toothpaste, ya ajiye ma junaid daya ya bude daya ya matsa toothpaste ya mika mata yace "Tafi ki wanke bakin ki" karasowa tayi ta karba tana kallonsa, murmushi yayi sanin bata gane ba kenan, yace "Follow me" da sauri tace "Follow her" dariya ta basa yace "No, follow me dai" daga haka ya shiga toilet ta bi bayansa, yana kallonta yayi mata alama da hannu da ta wanke baki da brush din, saka brush din tayi a baki ta tsaya, yace "Toh wanke bakin" tsotsan toothpaste din tayi ta cire brush din tana yamutse fuska, yace "No ba haka ba" ya mika mata hannu alamar ta basa ta mika masa ya kai brush din baki, nan ya shiga gwada mata yanda xata yi sannan ya mika mata, yanda taga yayi haka tayi yana kallonta har ta gama sannan ya nuna mata gun xuban ruwa yace "Wash ur mouth," karasawa tayi tana kallon wajen, yayi murmushi ya karaso ya bude mata ruwan ya tara da hannunsa ya kai bakinsa ya kuskure ya xubar sannan ya kalleta yace "Haka xa ki yi" tara hannunta tayi ita ma, ya tsura ma fararen hannun nata ido har ta kai ruwan baki ta kuskure kamar yanda ta ga yayi" murmushi ya mata yace "Good gal" juyawa yayi yace "Mu tafi" ta bi bayansa suka fito, bai yi mamakin rashin ganin junaid dakin ba, yana lafiya ma ya aka kare bare yanxu, kujera ya nuna mata ta xauna yace "Am coming" sannan ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita. Ba a dau lokaci ba ya dawo da bowl me dauke da apples, ya jawo table karami ya ajiye kusa da ita sannan ya daura bowl din kai yana kallonta yace "Eat" kallon bowl din kawai take, can ta sa hannu ta dau apple daya a hankali ta kai bakinta, bude kofa aka yi duk suka juya, gabansa ya fadi ganin Abbansa, Abba ya karaso dakin yana kallon gadon junaid yace "Where is my patient" El-ameen yayi saurin cewa "Ya d'an fita ne yanxu Abba" Abba yace "Ya fita da sassafen nan ya je ina?" El-ameen da gabansa ke faduwa yace "Ina jin ya fita ne, no cewa yayi xae fita ya sha iska" wani kallo Abba ke masa sannan ya kalli Jasmine dake kallonsa yace "Bana son in sake shigowa in ga yarinyar nan a nan Ahmad" kallon Abban nasa yayi a sanyaye yace "Toh Abba" Abba yace "Mutumin banxa kawai, kuma maxa kaje ka dubo min patient dina yanxu" daga haka ya juya ya fita, El-ameen ya juya yana kallon Jasmine, murmushin karfin hali ya sakar mata yace "Eat your apple" sunkuyar da kanta kawai tayi, ya juya a sanyaye ya fita daga dakin. Babu inda bai duba ba a asibitin amma bai ga junaid ba, abun yayi mugun basa mamaki kar dai gida ya wuce, dawowa sama yayi bai kuma yi gigin xuwa gaya ma Abba bai gansa ba don yasan baxai ji da dadi ba, office dinsa ya fara tafiya ya dau makullin motarsa sannan ya tafi ward din da jasmine take ya ganta har lokacin rike da apple din bata ci ba, ya karasa kusa da ita yace "Eat mana jasmine" bata kallesa ba ya kama hannunta xai dago ga ta fixge hannun tana masa wani kallon da ya fadar masa da gaba ya d'an koma baya a hankali yace "kiyi hakuri" ya gane bata son a taba ta kenan, mikewa tayi tsaye, ya fara tafiya yace "Mu je" har ya isa bakin kofa ya juyo yaga bata biyosa ba, yafito ta yayi sai gashi ta fara tahowa, Suna tafe yana juyowa yaga ko tana binsa har suka fito haraban hospital din ya nufi parking space da ita, gaban mota ya bude mata ya mata alamar ta shiga, still tayi tana kallon motar kamar warce ta tuno abu, can kuma ta kallesa kamar xata yi kuka, accident dinsu na jiya ne ya fado masa lokaci daya ya gane abinda yasa taki shiga, girgixa mata kai yayi yace "babu abinda xai faru jewel, shiga" kin shiga motar tayi still, ya xaga ya bude driver seat ya shiga ya tada motar kallonsa kawai take daga waje, can ta fara kalle kallen asibitin, a hankali ta shiga daga karshe yayi murmushi ya rufo motar, yana gama warming ya ja motar suka bar haraban asibitin bayan an bude masa gate, driving kawai yake ba tare da yasan inda xai kai ta ba, duk tausayinta ya cika shi, a hankali yace "Ina xan kai ki Jewel?" Kallonsa tayi ba tare da ta ce komai ba, Kanwar Abbansa ce ta fado masa kawai ya yanke shawarar kai ta can gidan, Karfe takwas da wani abu suka isa gidan, ya bude motar ya fito ya xaga ya bude mata ita ma ta fito, yana gaba tana biye da shi a baya suka shiga gidan, bbu kowa parlon ya nuna mata kujera ta xauna, cousin sis dinsa ta fito daga kitchen da mamaki take kallonsa tace "Toh fa, yaya daga ina haka?" Yayi murmushi yace "Gida, kira min Mumy" daki ta tafi tana cewa lallai yau akwai ruwa da kankara, Hajiya salmah Kanwar dad dinsa ta fito parlon tana kallonsa tace "Kayi batan hanya ne Ahmad?" Yayi murmushi yana shafa kai yace "A'a Mumy ina kwana" ta tabe baki ta amsa tana kallon Jasmine, sunkuyar da kai jasmine tayi, El-ameen yace "Mumy na xo neman alfarma ne a gun ki pls" tana kallonsa tace "Na me fa Ahmad" yayi kasa da murya ya shiga mata bayanin Jasmine, kallonsa take baki bude har ya kai karshe tace "Ehh lallai Ahmad, wato kai ne baka jin maganar naka iyayen koh, kai ne baka san darajar su ba, to wllh maxa ka maida masa ita shi da ya jajubo ta, maganar banxa kawai, shi me wayo yaji maganar tasa uwar sai kai ne da baka san darajan naka uban ba koh....." Mikewa El-ameen yayi bai kuma sauraranta ba, Jasmine na ganin ya tashi ita ma ta tashi da sauri, ya nufi kofa ta bi bayansa, small mum din tasa ta bi sa da harara tace "D'an rainin hankali kawai, mara wayo, kuma wllh sai na kira yaya na gaya masa yasan baka dauke sa bakin komai ba." Har ya fice daga parlon bai tanka ta ba.
Junaid na fita daga asibitin dama trekking yayi har ya isa bakin titi duk da jirin da yake gani ga wani ciwo da kansa yake masa da shoulder dinsa, singlet ne da jeans jikinsa. shi matsalar sa daya Mumy bai san ta inda xai soma bata hakuri ba, ya jima tsaye bakin titi wani tricycle ya tsaya yana tambayarsa ko tafiya ne, ya shiga ya gaya masa inda ya nufa, Suna isa gida ya fito yace masa yana xuwa, gun mai gadi ya karbi dari biyar ya basa sannan ya shiga gidan, Hajja ce ta fito daga side dinta rike da wani katon kwandon kwanuka ta xuba kulolin abinci har uku da flask sai cup ta daura a kai, xaro ido tayi ganinsa ta sauke kwandon da sauri cikin daga murya ta ce "Alhmdllh jama'an gida Bilki, Fatee da Amina ku fito gashi ya ji sauki ya dawo.... Amadina ya dawo, yaron kirki ya dawo...." Haka ta dinga yi kamar ta samu waka, Umma ce ta fara fitowa da sauri su Muhibba na biye da ita, sai Hajiya da khadija, fatima ma ta fito, da gudu khadija ta tafi ta rungumesa cike da murna, yake su Hajiya da Umma aka shiga yi ana gode Allah ana jajantawa, Shi dai junaid bai kallesu ba ya nufi part dinsa Hajja ta bi bayansa da sauri tana cewa "Amadina ya dawo, yaron kirki ya dawo" tun kan ta iso ya sa ma kofar key ya shige bedroom, ruwan xafi ya hada yayi wanka a toilet ya fito ya shirya, sai dai singlet kadai yasa da bakin jeans sbda kafadarsa, kwanciya yayi jin xaxxabi na neman rufesa, ko minti goma bai yi da kwanciya ba aka bubbuga kofar parlon ya mike da kyar ya bude, fatima ya gani tsaye, ta gaishesa ta masa ya jiki ya amsa sannan tace Abba na kiransa. Gyada mata kai yayi ta juya ta tafi, ya koma ya xauna parlon gabansa na faduwa ya kusa minti biyar sannan ya mike jiki ba kwari ya fita daga parlon ya tafi part din Abba, da kyar ya iya shiga parlon ganin dukka mutan gidan xaune da alaman shi ake jira, bai bari sun hada ido da kowa ba, kansa a kasa yayi surveying inda xai xauna ya xauna kawai, sai a sannan ya d'an dago kai yaga kusa da Humainah ya xauna, sunkuyar da kai yayi, banda kallonsa babu abinda ake yi a parlon, Mumy kadai ne bata ma kalli inda yake ba, Abba ya soma gaisarwa, sannan Hajja dake ta kallonsa baki har kunne, sai kuma Hajiya da Umma, bayan nan ya daga kai yana kallon Mumynsa cikin sanyin murya ya gaisheta, ta amsa ba tare da ta kallesa ba, Abba yace "Meye dalilin ka na baro asibiti ba a sallame ka ba?" Sunkuyar da kansa yayi bai ce komai ba, Abba ya girgixa kai yace "Toh ka kyauta, Ahmad ban yi mamakin abinda ka aikata jiya ba, don dama ni na dade da sanin kai ma mahaukaci ne, iyayen ka ne dai basu sani ba......" Hajja ta kyalkyale da dariya har da kwanciya tace "A'a Muhammadu wllh nima ina sane kawai dai ban taba fadi bane, tunda hannun ka baya rubewa ka yanke ka yar, amma Amadi kam mahaukaci ne" sunkuyar da kai junaid yayi, Hajiya da Umma sai danne dariyarsu suke, Humainah tayi murmushi ta sunkuyar da kai ita ma, Abba ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya kyauta, amma kafin haukan naka ya xame mana bala'i na yanke shawarar yi ma aure nan da sati biyu kawai, ko kwandalar ka bana bukata xan maka komai, shi yasa ma nace xan maka aure, alkawari ne wannan na daukar ma kai na" dagowa yayi da sauri yana kallon Abba, su Hajiya duk aka kwalalo ido, Hajja tace "Atoh" kallon Mumy junaid yayi yaga idonta na kan TV, xufa ya dinga ji na keto masa, a hankali yace "Abba!" Abba ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu yace "No, ba shawarar ka nake nema ba, ba kuma xan maka abinda xai cutar da kai ba."
✍🏻
*Haske Writers association*💡
[1/14, 9:12 AM] Elhajj: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
39.....
Junaid bai kuma cewa komai ba ya sunkuyar da kansa, Abba yace "Tashi kaje, idan lokaci yayi xaka san matar taka" da kyar Junaid ya mike ya nufi kofa ya fita daga parlon, part dinsa ya koma ya kwanta, lokaci daya yaji xaxxabi na neman rufesa, ya jima kwance kafin bacci ya daukesa. Driving kawai El-ameen ke yi ba tare da yasan inda xai kai ta ba, sai a lokacin ya fara daya sanin sallamar mama jummai da yanxu kawai sai ya kai su hotel, parking yayi gefen titi ya dafe kansa yana tunanin abun yi, can ya dago yana kallonta ya ga kallonsa take, murmushi ya sakar mata ta sauke idonta daga kansa, wayarsa ya ciro ya shiga neman number wata course mate dinsa kuma frnd dinsa a da, bugu uku ta daga suka gaisa, ya tambayeta oga da yara, daga daya bangaren tace "Suna nan qlau, kana duniya kuwa El-ameen, ko ma dai ce min xaka yi bikin ka ya kusa?" Dariya yayi yace "Haba dai d'an yaro da ni, aure ba yanxu ba sai na kara girma" dariyan tayi ita ma tace "Continue deceiving ur self, ga mu dai har mun kusa aurarwa," yace "Toh wa ya sani ko ni xa a ba wa ma," tace "Allah ya sauwake, me 'ya ta xata yi da sa'an ubanta" dariya yayi sosai yace "Ban dai xo da naira nace ina so bane, yanxu dai kina kt ne?" Tace "Ina nan ina xa ni," yace "Toh a gaya ma oga gani nan xuwa dai" tace "Sai kace gaske" yace "Allah kuwa, gani xuwa favour xan xo nema gun ku" tace "Toh sai ka xo, ina xuba ido" yace "Alryt tnx" daga haka ya katse wayar, juyawa yayi yana kallon Jasmine dake ta kallonsa, ya buda ido hade da mata murmushi, sunkuyar da kai tayi, ya ja motar suka bar wajen, cikin minti ashirin ya isa gidan Dr Sumayya, bakin gate yayi parking ya kirata, tana dagawa yace "Ga ni a waje" tace "Toh ka shigo mana" yace "Ohk" bude mota yayi ya fito ya xagaya ya bude mata ta fito ya rufe sannan yace "let go" a hankali tace "Ohk" wara ido yayi ya gyada mata kai yace "Good" daga haka ya fara tafiya ta bi bayansa, Dr Sumayya ce ta bude masu kofa tana murmushi tace "Sannu da xuwa Dr, ashe tare da bakuwa ku ke" yace "Exactly Mrs Sumayya" parlor suka shigo tace "Sannun ku da xuwa" xaunawa tayi suka kuma gaisawa, ya tambayeta yara tace sun tafi sch, yace "Maa sha Allah, bakuwata na kawo maki ta d'an yi kwana biyu" ta kalli Jasmine tace "Da gaske?" Yace "Serious" murmushi tayi tace "Ohh she's welcome, budurwar ka ce?" D'an wara ido yayi yace "No, no, xan ma iya cewa patient dita ce" Dr Sumayya ta kyalkyale da dariya tace "Ohhh I see" murmushi yayi yace "Ohhh serious" kallon Jasmine tayi tace "Sannu 'yan mata ina kwanan mu" El-ameen ya kalleta ya dawo gefenta yace "Tell her good morning jewel" kallon matar Jasmine tayi a hankali tace "Good morning" matar ta dan bude ido tana dariya tace "Toh fa" murmushi El-ameen yayi yace "She just recovered from posttraumatic stress disorder, and tayi loosing memory yanxu" Dr Sumayya jikinta yayi sanyi tace "Allahu Akbar, toh ina iyayenta" girgixa kai yayi yace "Its a long story Dr, bamu san iyayenta ba, Abokina Captain Junaid ne helper dinta, shi ya tsinto ta ya bada suggestion in mata treatment, gaba daya expenses din kuma shi yayi volunteer....." Dr Sumayya tace "Ahmad Junaid dai dana sani me ji da kan nan?" Dariya El-ameen yayi yace "Ohh Really? Toh shi!" Tace "Ikon Allah, ashe yana da mutunci da taimako" El-ameen yace "Sosai ma, don baku xauna da shi bane" Dr Sumayya tace "Kai amma yarinyar ta ban tausayi wllh, Allah sarki" El-ameen yace "Kwana biyu xata yi a nan, akwai d'an matsala ne kuma we are trying to fix it up, ki dinga bata pain relieving drugs sbda injury din kanta" Dr Sumayya tace "In'sha Allah" mikewa yayi yace "Ni xan koma office" tace "Toh shikenan take care!" Mikewa Jasmine ma tayi da sauri ya juya yana kallonta yace "You will stay with aunt kin ji...." Hawaye ne ya ziraro idonta, jikinsa yayi sanyi yace "No kar ki yi kuka I will be back soon" Dr Sumayya ta karaso ta kama hannunta