Showing 129001 words to 132000 words out of 170905 words
Chapter 44 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel
me" shiru yayi yana kallonta, sai ya ji tausayinta, a hankali yace "Bbu abinda ke jikin ki, they are just surprise ne...." Girgixa kai tayi cikin kuka tace "Noo, what are they surprise at, do I look new? Tell me plss, dukkansu guduna suke yi" lumshe ido yayi yace "Kila basu yi xaton ganin ki yanxu bane" buda ido tayi tace "Why is that?" Takun da suka ji yasa su juyawa gaba daya, Mai martaba ne tafe da dogaransa a baya, mikewa tayi da sauri ta nufesa da sauri tace "Abba!" Kallonta kawae yake, ta fashe da kuka ta tafi da gudu ta rungumesa cikin kuka tace "Abba ni ce pa Fatima" daura fuskarsa yayi a kanta cikin sanyin murya yace "Fatima!" Rungumesa tayi sosai, hawaye na sakko mata tace "Abba kila su Umma basu gane ni bane koh?" Kasa ce mata komai yayi, El-ameen dai sai kallonsa yake yaji tausayinsa ba kadan ba, dago kai sarkin yayi yana kallonsa, mikewa yayi ya karasa inda suke ya sunkuyar da kai yace "Barka dai mai martaba, ga Zahrah na maido gida, Allah ya kiyaye gaba" kallonsa kawai sarkin yake, El-ameen yace "Na bar ku lafiya" juyawa Zahrah tayi tana kallonsa, Sarki ya taka ya isa har gabansa, hannunsa ya kama ya nufi fada da shi, tsaye duk occupant din masauratan suke ko wanne a tsorace, Mai martaba da har lokacin bai sake El-ameen ba ya nufi babban parlonsa da shi, Zahrah dai na biye da shi a baya kamar xata shige jikinsa ganin wani kallo da ake mata duk inda suka wuce, xaunawa sarki yayi ya nuna ma El-ameen kujera ya xauna, ya kusa minti biyar bai ce komai ba, Zahrah dake xaune kusa da Abban ta sai jiran jin me xai ce take, hawaye ne ya sakko idonta tunawa da tayi da irin kallon da ake mata, ta daura kanta kan kafar Abban nata muryarta na rawa tace "Abba na canxa ne wai, me yasa ake guduna?" Da kyar me martaba ya saita kansa, yana rike da hannunta yace "Baki canja ba mamata" kallon El-ameen yayi yace "Bawan Allah, a ina ka ga Fatima?" Shiru El-ameen yayi kamar baxae ce komai ba, sarki dai sai kallonsa yake, sunkuyar da kai yayi yace "Bani na ganta ba ranka ya dade...." Sarki yace "Waye shi?" Dago kai yayi yace "Aminina ne, shi ne silar komai" Sarki yace "Kana da masaniyar inda ya ganta, kuma yana ina?" El-ameen yace "Ehh nasan inda ya ganta, yana katsina yanxu haka,!" Sarki yace "Ina ya ganta" kallonta El-ameen yayi yaga yanda ta kafa masa ido tana jiran jin me xai ce, lumshe ido yayi ya bude ya kalli Sarkin yace "Tana da matsala ne a lokacin" sarkin yace "Wani irin matsala?" El-ameen yace "Ehh toh, A lokacin ta samu matsalar kwakwalwa" mikewa tayi tana kallon El-ameen, sarkin ma kallonsa yake ko kiftawa bai yi, da kyar yace "Matsalar kwakwalwa?" El-ameen ya gyada kai yace "ehh, Ban mancewa dawowarsa Egypt kenan ya taso xae xo guna da yamma ya ganta gefen titi a halin Hauka....." Labarin yanda Junaid ya ganta, da irin tausayinta da yaji El-ameen ya shiga ba sarkin, bai boye masa komai ba har lokacin da junaid din ya nemi shi ma ya taimaka ya nuna shi bbu ruwansa, da yanda dai ya amince daga karshe, kuma bbu abinda ya rage tun daga hidimar da Junaid yayi da ita na Magani abinci sutura, nemo me kula da ita da yayi, har da irin matsalar da ya shiga gun iyayensa ta dalilin ta, da challenges din rayuwa da ya dinga fuskanta, duk da haka kuma bai taba gujenta ba, bai kuma fasa yi mata duk abubuwan da ya dace ba, har gidansu da ya kaita da niyar aurenta lokacin da iyayensa suka takurasa yayi aure, da dai yanda abubuwa suka gudana a lokacin, hatsarin da suka yi da ya maido mata da hankali sai dai kuma tayi loosing memory, da aurensa da Humainah da sakinta da yayi kan Zahrahn, kai bbu abinda ya boye ma sarkin har xuwansu bauchi sai dai bai fadi tijaran da Zaharar tayi masa ba, rike kai sarkin yayi don tuni idonsa ya canxa launi, Zahrah kam hawaye ne kawai ke saukowa idonta jikinta yayi mugun sanyi, tuni ta kasa ci gaba da tsayuwa ta durkushe wajen ta fashe da kuka sosai, da kyar sarkin ya iya dago kansa daga karshe, ya goge idonsa da Handkerchief din hannunsa cike da karfin hali yace "Shekara daya da watanni biyar kenan rabon mu da fatima, tun da suka yi hatsari a hanyar Kano, and....." Kasa ci gaba yayi ya mike yace "Gobe da safe xa mu tafi katsinan" daga haka ya dau hanyar da xai sada sa da Bedroom dinsa, kallon El-ameen kawae take, can ta mike a hankali ta isa gabansa ta durkusa wasu sabbin hawayen na sauko mata cikin sanyin murya tace "Will he ever forgive me?" Kallonta El-ameen yake, yayi murmushi bai ce komai ba, ta fashe da kuka sosai tace "Don Allah ka gaya min xae iya yafe min....." Saukowa El-ameen yayi yace "He will in'sha Allah" tana share hawayen da ya ki tsaya mata tace "toh Meye sunansa?" Yana kallon kwayar idonta yace *Captain Ahmad Junaid* a hankali tace "Ahmad Junaid" gyada mata kai yayi yana murmushi ta sauke idonta kasa.
*Haske Writers association*💡
[3/19, 9:36 PM] El-hajj💥: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
75.....
Washegari da ya kasance litinin misalin karfe takwas na safe Zahrah ta fito daga part din mai martaba bayan ya bata umarnin da ta tafi ta gaida Ummanta da stepmum dinta kilishi, bata yarda ta kwana ko ina ba sai gun sa tunda shi kadai ne bai gujeta ba, kuma ga bakin da suka dinga tururuwan xuwa ganinta tun a daren jiyan hakan yasa tayi xamanta gun Abbanta, a nan part din nasa tayi shiryawarta ta saka kayan da jakadiyar Umma ta kawo mata da safen, bangaren Ummanta ta nufa fuskarta rufe da hular alkyabbar jikinta don bata son kallon da ake mata, xuciyarta fal tunanin Junaid ta dinga tafiya a hankali, ta rasa dalilin da ya tsaya mata a rai haka, har mafarkinsa sae da tayi daren jiya, gashi ko ganesa ta tabbatar baxa tayi a hanya ba da xa su hadu, bata damu da mutanen da ta dinga wucewa ba wasu na gaisheta wasu na mata sannu da xuwa har ta iso bangaren Umma, xaune ta sameta parlor ga baki da dama xaxxaune parlon, da ganinta kasan har lokacin bata yi recover daga shock din jiya ba, a sanyaye Zahrah ta karasa har tsakar parlon ta duka ta gaida mutanen dake ta kallonta ko wannensu ya amsa mata cike da fara'a, karasawa tayi gaban Ummanta ita ma ta gaisheta, amsa mata tayi cikin sanyin murya tana kallonta, kasa ci gaba da tsayawa gun Zahrah tayi, ganin Umma taki sakewa da ita, ta mike kawai ta fice hawaye cike idonta, bangaren Kilishi ta nufa nan ma baki ta samu fal a parlon, ba laifi kilishi ta ja ta jikinta hawaye na sakko mata tace "Sannu Zahrah, Allah ubangiji ya kara mana tsawon rai mai amfani...." Rungumeta Zahrah tayi tana kuka, nan ta dinga lallashinta tace "Gode ma Allah xatayi da bawan Allahn da ta dalilin sa ta dawo gida yanxu" jikinta ya kuma yin sanyi sosai ta ji banda taga junaid bbu abinda ke damunta yanxu, mikewa tayi tana share hawayen ta, Ummi ta gani tsaye ita ma tana hawayen, da sauri ummin ta karaso ta rungumeta tace "I missed you sweet sis...." Zahrah bata iya cewa komai ba sae hawaye, janye jikinta tayi ta fita daga parlon, a hanya ta hadu da yayanta tana ganinsa xata canxa hanya ya janyota ya rungumeta, rufe fuskarta tayi a kirjinsa, a sanyaye yace "Welcome back Lil sis, ba gudun ki muke ba, it's just....." Girgixa kai yayi lokaci daya idonsa ya kada yace "We missed you Zahrah" bata iya ta ce komai ba sai kai da ta gyada masa kawai, yace "Baki je gun bakon da ku ka xo tare ba" goge fuskarta tayi tace "yanxu xan je" saketa yayi yace "Yea ki tafi yanxu, nima daga can nake" gyada masa kai tayi ta nufi bangaren saukan baki inda El-ameen yake, Xaune ta gansa parlor yana waya, ta nemi gefe ta xauna sai kallonsa take, yana gama wayar tayi saurin dauke idonta daga kansa, ya d'an bude ido yace "Good morning princess" d'an murmushi tayi tace "Good morning" yana murmushin shi ma yace "How you!" Ba tare da ta kallesa ba tace "Am good," yace 'Happy to be home ryt?" Lumshe ido tayi ta bude ta gyada masa kai, yace "My wife said I shud send her regards" kallonsa tayi tana murmushi tace "Am grateful" yace "In the next 1hr xa mu kama hanyar katsina" da sauri tace "Amma ai da ni xa a je koh?" Yace "No I don't think so...." Bata fuska tayi tace "Nima nace xan je" dariya yayi yace "Ohk ohk!" Shiru tayi sai kuma tace "Nuna min hoton matar ka" da mamaki ya kalleta yace "Really" bai jira cewarta ba ya dauko wayarsa ya bude ya shiga gallery ya nemo hoton Hafsat ya mika mata, mikewa tayi ta karasa kusa da shi ta karbi wayar ta dawo ta xauna, kallonta kawai take sannan ta kallesa tace "She's... She's beautiful!" Murmushi yayi yace "Ohh tnxx" kallon hotunan ta shiga yi, can ta mike da sauri tace "Ohh this is me" mikewa yayi ya koma kusa da ita yana kallon wayar ya ga hoto ne da yayi masu ita da Hafsat, gyada mata kai yayi yace "Yea, ke da Hafsat" a sanyaye ta ci gaba da kallon hotunan taga duk hotunanta ya fi yawa a wayar, ajiye wayar tayi ta koma ta xauna ta lumshe ido, yana kallonta yace "What?" Bude ido tayi ta girgixa masa kai cikin sanyin murya tace "Have you taken breakfast?" Gyada mata kai yayi yace "Yea" bata kuma cewa komai ba can kuma tace "Ban san sunanka ba!" Wara ido yayi yace "I am El-ameen Ahmad..." Gyada kai tayi tace "You have the name of my dad" murmushi yayi yana kallonta, ta mike tace "Xan je gun Abba yanxu" bin ta yayi da kallo har ta fita. Karfe goma saura sarki da tawagarsa suka shirya tsaf domin tafiya kt, shiga ce yayi na alfarma irin ta sarauta, da farko bai amince Zahrah ta bi su ba sbda b'akin dake ta xuwa masarautan dominta amma yayanta na sa baki sarki ya amince su je tare, don har da shi xa'a, rungume yayan nata tayi tace "Thanks bro" Ummanta ta tafi tayi ma sallama sai a sannan Umma ta rungume 'yar tata ta fashe da kuka, jikin Zahrah yayi sanyi ita ma hawayen ya shiga sakko mata da kyar ta fita daga dakin ta je yi ma step mum dinta sallama, Ummi ta gani ita ma ta shirya tsaf, Ummi na ganinta tace "Zahrah tare xa mu je fah" Kilishi ta kalleta tace "Mai martaba ne yace tare xa ku" bata fuska tayi tace "Yanxu xanje in gaya masa, Mumy bana son ta kara tafiya ita kadai ne...." Kilishi tayi murmushi tace "Toh Allah yasa ya amince" daga haka Ummi ta kama hannun 'yar uwar tata suka fita, basu sha wahalan shawo kan Abbansu ba ya amince xa ta bi su, motoci biyar ne xa a tafi katsinan da, mai martaba kuma flight xai bi da Zahrah da El-ameen da Ummi, Abdul kuma xae bi tawagar Abbansa ta mota sai su hade a masarautan kano daga can kuma su dau hanyar katsina.
Karfe daya motocin tawagar sarki El-ameen suka iso masarautan Kano, ko minti talatin basu kara a Kano ba suka dau hanyar katsina, Zahrah da Ummi suka shiga mota daya da Mahaifinsu, El-ameen bai yarda ya shiga motar sarki da ya sa masa takwara ba ya hau motar gaba, uku da wani abu suka shiga garin kt, duk da El-ameen ya san ba lallai junaid na gidansu ba, can ya sa suka nufa gaba daya, hudu da minti goma suka iso kofar gidansu Junaid, El-ameen ne ya fara fitowa, sannan dogarawan sarki, kafin sarki ma ya fito tare da aminansa, Sarki na kallon El-ameen yace "Masallaci mafi kusa, xa muyi la'asar!" Masallacin kofar gidan ya shiga da su bayan sun daura alwala, su Zahrah dai na mota a xaune, hudu da minti ashirin duk suka fiffito daga mosque din, Sarki yace "Shiga kayi mana sallama da masu gidan, El-ameen ya shiga compound din, bbu kowa tsakar gidan sai Khadija dake xaune balcony din Mumy, ya karasa har inda take, ta gaishesa da fara'ar yake, amsa kafin yace "junaid fa?" Ta girgixa kai tace "yana can gidansa!" Yace "Abba fah?" Ta kalli bangaren Abba tace "Yana ciki, amma yana da baki" El-ameen yace "Su waye?" Tace "Hajja na ciki, kawu Abbakar ma na ciki sai Abokansa biyu" ya d'an bude ido yace "Meeting din me ake" shiru tayi bata ce komai ba, a hankali yace "Junaid koh?" Gyada masa kai tayi, yace "Su Hajiya fah?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Mumy fa?" Kallon kofar parlon tayi tace "Tana ciki" yace "Ohk pls ki gaya min taron me ake a parlon" ta tabe baki tace "Humainah ce ta gaya ma Hajja abinda ya sa ya saketa daxu da safe" El-ameen ya d'an bude ido yace "Ta basu labarin mahaukaciya kenan" gyada masa kai Khadija tayi, El-ameen yace "Toh me Abba yace?" Hawaye ya cika idonta taki cewa komai, ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh bai xo ba junaid din" hawaye na sakko mata tace "Tun daxu ake kiransa ya ki ya xo" El-ameen bai kuma cewa komai ba ya nufi parlon Mumy, xaune ya ganta da ganinta ba karamin kuka ta ci ba, kasa karasawa yayi cikin parlon ya juya ya fita kawai, kofar gida ya koma ya ba sarki hakuri sannan ya ce su shigo, Fitowa Zahrah tayi da 'yar uwarta suna daga gefen mahaifinsu suka shiga gidan, har parlon Abba yayi musu iso, tuni Khadija ta mike tana kallon ikon Allah ganin jama'ar dake shigowa gidan, El-ameen ne ya fara shiga parlon da sallama ya gaida Abba da ladabi, Hajja tace "Alhmdllh kun ga babban munafukin abokin nasa nan, ae wllh sai Allah ya mana hisabi da ku...." El-ameen bai ko kalleta ba yana kallon Abba yace "Abba baki kayi daga masarautan Bauchi, mai martaba sarkin bauchi ne da kansa" Abba da ya wani xaro ido tun kan yace komai Sarki El-ameen ya shigo parlon da sallama Aminansa biyu da Zahrah da Ummi ma suka shigo sai Abdul sauran dogarawan sarki suka yi cirko cirko bakin kofa, da farko tsaye sarkin yayi ganin yanda ake kallonsa da mamaki barin Abba ya sa shi samun kujera ya xauna, parking Junaid yayi kofar gida ya tsura ma manyan motocin dake Parke a jere ido, mamaki ne ya cika sa sosai lokaci daya yaji gabansa ya fadi ya bude motar ya fita da sauri ya shiga cikin gidan, uniform ne jikinsa sai hula dake kansa, ko lura da dogarawan da suka cika compound din bai yi ba, shi dai burinsa ya ga Mumynsa, hankalinsa bai gama tashi ba sai da ya ga jerin takalma dake kofar parlon Abba, da part din Mumy xa shi kawai ya fasa ya nufi parlon Abba da sauri ya shiga.
*Haske writers association*💡
[3/19, 9:36 PM] El-hajj💥: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
76......
Tsaye yayi bakin kofa yana bin kowa na parlon da kallo irin na mamaki, ido hudu suka yi da Zahrah dake kallonsa ko kiftawa babu, hade rai yayi ya juya xai fita El-ameen dake tsaye har lokacin ya kama hannunsa yana kallon Sarki da shi kansa kallon Junaid yake yace "Ahmad junaid kenan, kuma dominsa ku ka taho katsina." Mikewa Hajja tayi da sauri tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Me yayi? Yaron da ko hanyar bauchi na san ko xa a kashe sa bai sani ba, ashe kai mugu ne Aminu ba mu sani ba..... Meye hadin jikana da masarautar Bauchi can kace ko ina?" Abokin Abba ne yace "A'a Hajja ba tashin hankali bane, ae ba mu jira mun ji me ke tafe da su ba, kuma ko gaisawa fa ba a yi ba, sannan ance sarki ne nan gabanmu ba fa waxiri ba....." Wani kallo ta watsa masa A fusace tace "Yo ni ina ruwana da sarautarsa, ka gan ni nan ban tsoron kowa sai Allah, kuma bbu irin fitintinun da ban gani ba a duniya, ya fadi me jikana yayi masa in ji, Ahmad da ko titin da xai kai sa Bauchi bai sani ba" Abba dai kasa cewa komai yayi, don shima jiran jin me only son din nasa yayi kawai yake, Sarki kam banda murmushi babu abinda yake sai dai ba lallai ka gane murmushin ma yake ba sbda turban din kansa, Aminin sa da shi ma ya samu gu ya xauna gefensa cikin kaushin murya yace "Mind you all, ba fa karamin mutum bane xaune a gaban ku, sannan mu alkhairi ne ya kawo mu in'sha Allah, Mai martaba sarkin bauchi kenan da kansa don haka a samu nutsuwa don Allah....." Hajja tace "Ina xa mu samu nutsuwa ba ku fadi me ke tafe da ku ba, ni dai nasan Ahmad ko cinnaka baxae iya kashe wa ba...." Sarki ya kalli Junaid yace "Toh karaso ka xauna Ahmad" tsaye junaid yayi kamar baxai karasa parlon ba gashi gabansa sae faduwa yake ya rasa dalili, sarkin bauchi kuma, is she related to the royal family? Abba ne yace "Ka kasa tahowa ke nan?" Da kyar ya d'aga kafa ya karaso ya xauna nan tsakar parlon Hajja ta xauna gefensa tace "Kwantar da hankalin ka Amadi bbu wanda ya isa ya cutar da kai matukar ina raye a doron kasa, su fadi me kayi in ji" tana magana ne tana matsar kwalla, Abba ya kalli El-ameen yace "Tafi ka kira Amina" juyawa yayi ya fita ba a dau lokaci ba ya dawo parlon tare da Mumy, k'in xama Mumy tayi ta kalli junaid ta kalli Sarki sannan Abba,