Showing 12001 words to 15000 words out of 170905 words

Chapter 5 - Captain Ahmad Junaid 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

658

wife yanxu son" murmushi yyi ya mike yace "Allah ya kawo lkci mumyna" tayi murmushi tace "Toh Ameen" yace "Bari in kai ma su Umma kudin Mumy, daga can xan wuce" Mumy tace "Toh Allah ya tsare kar dae ka yi dare plss Ahmad" yace "In'sha Allah mum" daukan wayarsa yyi ya fita daga falon, gun Umma ya fara shiga ya samu Muhibba ce da wata kawarta a falon, ya wani hade rae ba tare da ya damu da amsa gaisuwar da suka yi masa ba ya mika mata 15k din yace "Gashi ki ba ma Umma" juyawa yyi ya fice daga falon, Kawar Muhibba me suna Salima tace "Kai amma wllh kina bada mata Muhibba, har wannan dan karamin alhakin ne xaki dinga barin yana walakanta ki don yana da kyau, ubansa kuma na da dukiya, sae kace ba gogaggiyar 'yar jami'a ba?" Muhibba tayi murmushi tace "Baki san Ahmad bane Salim, ya fice tunanin ki wllh...." Salima ta katse ta tana kalle kalle tace "Da'alla banxa tsaya ki saurareni, mu je daki in baki wani plan ki ga ko baxae yi aiki ba" mikewa Muhibba tayi suka yi daki da kawar tata cike da xumudin jin plan din. Junaid na fita bangaren Hajiya ya nufa ita ma ya bata kudin, tana jujjuya kudin tace "Duk kudin da Alhaji ya bari Ahmad ka rasa abinda xaka kawo min sae wani shegen dubu sha biyar, wato sauran kuma ka ba uwar ka koh, toh wallahi ka ji tsoron Allah don hakkinmu baxai bar ka ba" Junaid ya daga kafada yace "Ni Abba bae bar min kudi ba, kawae gani nayi hakan ya dace shi yasa na kawo maki na kai ma Umma don ko mahaifiyata ban ba kudi ba gidan nn, gobe ko jibi ae Abban xae dawo, in kina da wani bukatar da ya wuce na wannan idan ya dawo sae ki tambayesa" yana kai wa nn ya fice mata daga palo, ta bi sa da kallo baki bude, idonta ya kankance don bacin rai, rufe bakin tayi tana gyada kai tace "yaro yaro ne" kwafa tayi ta juya ta koma don ci gaba da abinda take tana wani murmushi. Karfe shidda saura Junaid ya isa gidansu El-Ameen sanin ya baro clinic yanxu, Mum din sa ya samu falo, bayan sun gaisa yace "Ummi El-Ameen ya dawo koh?" Hajiya Maryam da ake kira da Ummi tace "Ehh ya dawo daxu amma ya fita yanxun nan, ka kira sa kaji inda yake don nasan baya asibiti" Junaid yace "Toh shknn Ummi xan kirasa, ni xan koma" Ummi tace "Toh ko ruwa baxa ka sha ba Ahmad?" Yyi murmushi yace "Alhmdllh Ummi" Ummi tayi murmushi tace "Toh ka gaida min Hajiya Amina" yace "Xata ji Ummi" fita yyi daga falon yana tunanin inda El-Ameen ya tafi, sae da ya shiga mota snn ya kirasa, bugu daya ya d'aga Junaid yace "Kana ina ne?" El-Ameen yace "Au! ai nayi xaton xuciya kayi ka bar ni da mahaukaciyar taka" Junaid yyi tsaki yace "Kana ina nace?" Dariya El-Ameen yyi yace "Kai dae duk abun ka baxa ka iya xuciya da ni ba wllh, come over ina gidana, na samo mai gadi, ya kuma min hanya an samu wata dattijuwa, we are ol there 2gether ynxu, mind yhu duk wata xaka dinga biyan mai gadin dubu 30, ita kuma warce xata tsaya da mahaukaciyar xa'a bata dubu 50 monthly, coz its not an easy job, ga kuma risk din dake tattare da job din, and yhu make sure ka shiga kasuwa ka siyo mata kayayyakin da xata dinga sawa including inner wears" Junaid yace "Ni ban san inda ake sai da kayan mata ba" El-Ameen yace "So? Ba sae ka ce a raka ka ba, ko ka shiga kasuwar kayi tambaya" tabe baki Junaid yyi ya katse wayar ya kama hanyar gidan. A waje yyi parking ya shiga, sabon mai gadin da ke xaune compound din ya gaishesa da ladabi, Junaid ya amsa ya nufi kofar shiga palo, daga bakin kofar ya tsaya yana kare ma palon kallo, duk an share barnar daxu ko ina yyi fess, kallon El-Ameen dake xaune kan daya daga kujerun falon yana danna waya yyi snn ya karasa shiga falon, El-Ameen ya kallesa yace "Kayan fa, ni fa I can't put her under medication da suturan jikinta, it's very irritating, na dae yi mata alluran barci daxu don ban ga alaman tana yi ba" Junaid ya xauna gefensa yace "Toh don Allah ka raka ni mu siyo kayan mana, serious ban san ina xan samu women wears ba" El-Ameen yace "Nace idan ka shiga kasuwar kayi tambaya mana sae kace ba wayayye ba" shiru Junaid yyi yana kallonsa, wata yar dattijuwa ce da baxata haura sittin ba ta fito daga kitchen da alama ita ce ta yi gyaran gidan gaba daya, gaishe da Junaid tayi, yyi murmushi yace "Sannu da aiki mama" mikewa El-Ameen yyi ya haura sama ba a dau lkci ba ya sakko rike da sabulan wanka tsadaddu da sponge, sae toothbrush da toothpaste yana kallon dattijuwar yace "Mama ga wannan, wanka xa ki taimaka kafin mu dawo, xae kai maki ita bayin yanxu," Matar tayi shiru tana kallonsa sae dae da ganinta kasan a tsorace take, El-Ameen yyi dariya yace "Babu abinda xata maki wllh mama, bacci ae take kuma baxa ta tashi ba yanxu, mu je ki ga" bin bayansa tayi suka haura sama, Junaid ya bi su da kallo kafin ya shafa kansa, El-Ameen ne ya fara shiga dakin snn ita ma ta shiga, tana nan kwance yanda ya bar ta bayan yyi mata allura, idanuwanta duk a rufe, kallon dattijuwar yyi yace "Kinga bacci take ko mama, kuma na gaya maki baxa ta tashi ba sae bayan awanni takwas," kai kawae ta gyada masa, bayi ya nufa ya hada ruwan dumi da yawa snn ya fito dakin ya dauketa ya nufi bayin da ita ya kwantar da ita kasan neat bathroom din ya fito yana kallon tsohuwar da ya sa ma Mama yace "Gata can na kai maki bayin, don Allah ki wanke mata wannan gashin da kyau mama, nasan baxa kiyi wahalan fito da ita ba idan kin gama don bata da nauyi, xan fito maki da bargo kawae ki lulluba mata har mu dawo da kaya" tace "Toh yaro" juyawa yyi ya fita ta nufi cikin bayin. Siyayya ba kadan ba Junaid yyi ma Mahaukaciyar, tun daga kan normal English wears wato dogayen riguna, xuwa mayyukan shafawa, turarruka, da inner wears da jallabiyoyi, har man gyaran gashi da combs duk sae da ya siya da takalma sae huluna da 'yan kunnaye, shi dae El-Ameen bin sa kawae yake yana dariya, ganin har xa ayi magrib yasa El-Ameen yace "Kai koh kayan lefe kake hadawa fa sae haka Junaid, for God's own sake kayan nan sun isa haka it's time for magrib" Junaid ya kallesa yace "Ohk" Karfe bakwae da rabi suka isa gida, shi ma don sun tsaya hanya sun shiga masallaci sun yi sllh snn sun tsaya eatry siyan abinci, xaune suka samu dattijuwar a falo kan dankwalinta alamar sllh ta idar, tayi masu sannu da xuwa, Junaid ya ajiye kayayyakin hannunsa, El-Ameen ya bude wani leda ya fiddo doguwar riga da man shafawa da na kai sae inner wears da turare ya mika ma matar yace "Gashi mama ki taimaka ki sa mata" ta mike tace "Toh" sannan ta karbi kayan ta haura sama, durkusawa tayi gabanta ta yaye bargon da ta rufe ta da shi ta bude tsadadden man da aka bata ta shiga shafa mata jikinta, cikin mintuna da basu fi goma ba ta gama shiryata, ta debi hair cream me yawa ta shafa mata a dogon gashinta sannan ta shiga taje gashin a hnkli saboda tsantsin sa, tana yin haka hawaye na xuba idonta kmr daxu da take mata wanka, rayuwa kenan duk yanayin da ka tsinci kan ka ka gode Allah, Coz he knows best, shi kadae yasan dalilin barin wannan Baiwar Allah haka, ba wae kuma don baya sonta ya bar ta a hakan ba, har ta gama tufke mata dogon gashinta da ya kusa bayanta hawayenta bae tsaya ba, gyara mata kwanciya tayi ta rufa mata bargon ta fito tana kallonsu El-Ameen tace "Na gama" El-Ameen ya mike yace "Kin sa mata komae dae koh mama" tace "Na sa mata" yana 'yar dariya yace "Kin tabbata mama" murmushi tayi tace "Na sa mata komai yaro" kallon Junaid yyi sannan ya nufi stairs, Junaid ya mike ya bi bayansa, El-Ameen na shiga dakin ya karasa gabanta ya durkusa ya yaye bargon dake jikinta a hankali, rike breath dinsa yayi yana kallonta ko kiftawa bae yi har Junaid ya shigo ya same sa a hka, shima ya durkusa a hankali nan gabanta yana kallonta.

✍🏻
*Haske Writers Association*💡
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓



_By Khaleesat Haiydar_✍🏻

7.....

Fara ce sosai ba kadan ba don kamar ka latsa ta jini ya fito, dama ashe wahala ce ya maida kalanta baki, ko kadan bata da jiki sai tsayi, bakin gashin kanta ya rufe kusan rabin fuskarta sbda yanda tayi kwanciyar, d'an karamin bakinta me kalan baki da ja Junaid ya kalla yyi murmushi yace "Uhnn! Kamar me hankali koh? Da xata tashi ynxu duk sae mun yi bayani ryt?" murmushi El-ameen yyi ya mike yace "Yea! Exactly!" Juyawa yyi ya fice daga dakin Junaid ya bi sa da kallo sae gashi ya dawo da wasu alluran har uku, ya dawo gabanta ya durkusa, Junaid na ganin haka ya mike ya fita daga dakin, ya sakko palo ya dauki ledan abinci daya ya ba Mama, tayi masa godiya yyi murmushi kawae ya xauna, bayan kusan minti goma El-Ameen ya sakko falon ya xauna gefen junaid yace "Kana ji na, akwae drugs din da xa'a siya har biyar, kuma duk pack daya kusan dubu 40 ne kafin ayi diagnosing dinta...." Junaid yace "Ohk xan maka transfer ltr" El-Ameen ya mike ya dauki ledan abincin da ya rage da ruwa ya nufi sama, ajiye mata yyi bayan ya bude snn ya fito ya sa ma kofar key, ya dawo palo yana kallon Junaid yace "Let leave!" Mikewa Junaid yyi, El-Ameen ya kalli dattijuwar da ke xaune yace "Mama za mu tafi sae gobe, duk buge bugen da xata yi kar ki bude mata kofar" tace "Toh Allah ya tashe mu lfya, yayi maku albarka," duk suka amsa da Ameen suka fita palon. A bakin gate El-Ameen ya tsaya yana kallon Junaid yace "ka ba mai gadi kudi ya siyo ma tsohuwar abinci da safe ya kai mata ciki don am not coming here da safe" Junaid ya ciro dubu uku aljihunsa ya mika ma mai gadin snn suka fita, Suna isa gun motocin su El-Ameen yace "Gobe kuma foodstuffs xaka siya idan xaka xo" Junaid bae ce komae ba ya shige motarsa ya tada ya bar wajen, El-Ameen ya bi sa da kallo yana murmushi, snn shima ya shiga tasa motar. Karfe takwas da wani abu Junaid ya isa gida, bangarensa ya nufa yyi wanka snn ya dauro alwala ya fito yyi isha yana xaune kan darduma ya ji an bude kofar palonsa, bae motsa daga inda yake ba har aka bude kofar bedroom, ya daga kai don ganin waye, Mumy ce ta shigo dakin, yayi murmushi ganinta yace "Yanxu fa xan shigo d'a Mumy" ta xauna gefen gadonsa tace "Sae ynxu kake isha Junaid?" Yace "Mun hadu da traffic ne sosae a hanya Mumy" ta tabe baki ta mike tace "Toh taso mu je ka ci abinci" ba musu ya mike ya linke pray mat din ya ajiye ya bi bayanta, Mai aikinta ce ta dauko abincin nasa daga dinning ta ajiye nan tsakiyar lallausan rug din falon da ya ke xaune, Mumy ta sakko gefensa ta bude warmern dake dauke da Shinkafa fara ta dauki plate ta dibar masa iya yanda tasan xae cinye snn ta bude miya ta xuba masa k'adan a gefe don bae fiye son miya da yawa ba, sae cow meat da ta cika masa a abincin, spoon ya dauka yace "Thanks sweet mum" snn ya fara cin abincin ita kuma ta dauki wayarta da ke ring, ganin Abba ne yasa ta nufi daki. K'asa cin abincin Junaid yyi ya kuma rasa dalilin hakan, ya lumshe ido ya jinginar da kansa jikin kujera, ya kusa minti goma a hka sanin Mumy na fitowa sae ta sa shi ya cinye abincin yasa ya kira mai aikinta, yarinyar ta taho daga dakinta da sauri, ya dauki abincin ya mika mata yace "ina fatima?" Tace "Ta kwanta" yace "Ohk tafi daki ki ci na koshi" ba musu ta koma dakinta da abincin, juice ya diba ya shiga sha a hankali, a hka Mumy ta fito ta samesa tace "Har ka cinye?" Yace "Eh Mumy" ya ajiye cup din hannunsa yana lullumshe ido yace "Nafara jin bacci mumy" tace "Toh Allah ya tashe mu lfya, kayi alwala kafin ka kwanta, don't forget to pray also" ya mike yace "In'sha Allah mum" wayarsa ya dauka ya fita ya nufi side dinsa, sae da ya dauro alwala yyi shafa'i da wutr snn ya kwanta ya ja bargo. Washegari yana office yayi ma El-Ameen transfer din dubu dari da hamsin, yana barin office dama kasuwa ya shiga ya siyo food stuffs sannan ya wuce gidan El-Ameen, mai gadi ne ya shiga da kayan abincin palo, Junaid ya xauna bayan sun gaisa da mama yace "El-Ameen din ya xo ne mama" tace "Eh ya xo da safe, ya kuma xuwa daxu, bae dde da tafiya ba amma yace xae dawo" Junaid yace "Ohk, bacci take ne?" Mama tace "A'a gskya, sae dae yace kar a bude kofar makullin na jiki ma" Junaid yace "Tana cin abinci kuwa?" Girgixa kai tayi tace "Gskya ban sani ba don kifarwa take duka, bana gane ko ta ci ko bata ci ba" Shiru yyi bae kuma cewa komae ba, yana son ganinta amma shi gskya tsoro yake, dama El-Ameen na nan ne, can ya kalli agogo ya ga har biyar yayi, mikewa yyi yace "toh ni xan tafi mama, bbu matsala dae koh?" Tana murmushi tace "Babu komae wallahi" xae yi magana aka bude kofa El-Ameen ya shigo, ya d'an kyabe baki ganinsa, shi dae Junaid bin sa da kallo yayi har ya karaso cikin palon, ledan hannunsa na magunguna ya ajiye yace "Ba dae har xaka tafi ba, kuma kama duba mahaukaciyar taka kuwa?" Junaid ya dauke kai bae ce komae ba, El-Ameen yace "Ehh Lallai ma, wato ni xaka yi ta bari da wahala koh, daxu da safe ma sae da na xo nan kafin in tafi clinic nasan kai ko tashi kila baka yi ba lokacin" yana kai wa nan ya nufi sama, Junaid ya sauke ajiyar xuciya ya bi bayansa, El-Ameen ya bude kofar dakin da key ya tura kofar a hankali, tana xaune ta rakube waje daya bayan ta kuma cire labulayen dakin gaba daya kamar yanda ta saba, doguwar rigar kanti ne jikinta ja da ya haska farin fatar ta, duk ta birkita dogon gashinta kmr ba da safe Mama ta kuma daure mata ba tana bacci, kayan ma da gani ta kasa cire shi ne don duk ta yamutse shi jikinta, El-Ameen ya balla mata harara yace "Wai ke wace irin mutum ce, wllh kika sake cire min labule sae na gaura maki mari, baki da aiki sai barna" Junaid dae na d'aga bakin kofa yana leko dakin, El-Ameen ya kallesa yace "Da'alla matsoraci shigo baxa ta ma komai ba" kin shigowa junaid yayi yace "Nan ma ya isa" El-Ameen ya hade rae yace "Ohh wato ni ne ban san ciwon kai na ba da nake shigowa koh, sae in daina shigowa nima in dinga tsayawa daga bakin kofa in ga ta ynda xa ayi maganin" a hankali Junaid ya d'aga kafa ya shigo dakin yana kallonta sae shishshigewa jikin bango take a tsorace, El-Ameen ya kalli Junaid dake tsaye shi ma duk a tsoracen, Junaid bae ankara ba sae gani yyi El-Ameen ya fixgosa ya tura sa har sae da ya fada kanta, a tare suka kwala ihu daga shi har ita, El-Ameen ya dinga kyakyata dariya har da rike ciki, da kyar Junaid ya mike, ita ma ta yunkura ta mike, tsorata junaid yyi ya nufi bayi da sauri, ita kuma ta wawuri d'aya daga karafunan labulen dakin tayi kan El-Ameen dake dariya har lokcin, xaro ido yyi ya hadiye dariyarsa ganin haka, ya juya da sauri xae fita ae da hanxarinta ta bi bayansa, me Junaid xae ban da dariya, ya dinga kyalkyala dariya ya bi bayansu, har downstairs ta bi El-Ameen, mama na ganin hka ita ma tayi waje da gudu, El-Ameen ya dinga cewa "Junaid wllh ka xo ka riketa, junaiddd" Junaid ya durkusa nan stairs ya dinga dariya ganin yanda El-Ameen ya rude yana xaga palon, ita ko sae binsa take xata buga masa karfen, Hadiye dariyar Junaid yyi ganin El-Ameen ya shige kitchen ya sa key ya barsu su biyun a palon, ta dade tsaye bakin kofar kitchen din, kafin ta juyo tana bin ko ina na palon da kallo, k'asa motsi Junaid yyi daga inda yake xuciyarsa na bugawa, ta jefar da karfen hannunta ganin kofa a bude ta nufi kofar da sauri, Junaid bae san lkcn da ya nemi tsoron ya rasa ba ya bi bayanta cikin hanzari ya riga ta isowa kofar ya rufe gam, juyawa tayi tana kallonsa tana maida numfashi, sae kuma ta fasa wani ihu tayi kansa ta fixgosa, rungumeta yyi ya riketa gam, ta dinga fixge fixge ya ki saketa, Sosae suka jigata daga ita har shi, don kin saketa yyi, ita kuma bata fasa kokuwa da shi ba, daga karshe tayi lamo jikinsa bata sake yunkurin kwatar kanta ba, a hankali ya saketa ta sulale nan kasan palon, hawaye yaga kwance fuskarta, jikinsa yyi sanyi ya durkusa gabanta yana kallonta.

✍🏻
*Haske Writers Association*💡
⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓




Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login