Showing 36001 words to 39000 words out of 134888 words

Chapter 13 - Tantiriya Agidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

923

suke yi su bari lallai su dawo gida,kafin kace me sun hallara,kowa yazo ya samu Iman tayi zaman Yan bori hannaye a Kai,ga Annoor a gefe ransa bakikirin fuska kamar hadari,Abba da Jauro a zaune,Habiba ta zauna a kasa itama tayi jugum,tunaninsu kaf ko Annoor ne da Iman aka kama su suna iskanci sabo da kullum suna manne kowa yasan alakarsu in ance hakan ma baza ayi mamaki ba.

Haidar yace Innalillahi shike nan Annoor da Iman sun ja mana abin kunya a family,dama ni wlh naga rashin dacewa kusancinsu yayi yawa,Annoor yace da nayi me? ubanka nayi mata,Nabeel yace Uhmm Dan Allah ayi mana bayani Annoor ya jawo mana,Rahma tace an barmu a duhu,Iman kuka take Wiwi ta cika palon shi yasa aka yi zargin Annoor ne ya mata wani Abu shima gashi ransa a bace,tace cikin kuka wlh indai har uwata karuwanci tayi nima sai nayi....yiiiiihihihiiii ....Annoor ne ya gwada yanda Iman tayi yace nima hakaaaaakakakaaaaa......ke dalla rufe mana baki tun yaushe kika yi karuwancin kin dame mu,ki barmu Muji da abinda ya damemu,Kai Haidar ba Kawu ne Baban mu ba dukka mu Tara yaran Shegu ne ba Yan sunna ba,ma'ana Yan gaba da fatiha,Rahma tace na'am?????.....Iman da kuka tace Eiiiiiiiiii......Kuma ma an saki Aunty Na'ima.....sabo da itace ta fadaaaahhhhhhh....taci gaba da kuka.

Nabeela tace Innalillahi wayyoooo ubana ya cuceni ya saka Aliyarsa ba a muhallinta ba aka sameni,Nabeel akwai rago bashi da juriya kamar mace ya dinga hawaye,Haidar yace kaji dadi ma Kai kayi kukan ni da zanyi kukan ma da naji sauki,Sajid yace Allah ya rufa min asiri nayi aure ba a sani ba lokacin,da dangin matar sun sani bazan auru ba, Karima da Laila suka ce wlh Allah ya tsallakar damu har da yaran mu mun Haifa.

Jauro yace hmm kowa ya nutsu na baku tarihinku tunda duk nasan cikinku Kun San Iyayenku mata amma Baku San mazan ba Kuma Alhmdllh dukkanku nasan Iyayenku Maza nasan Inda suke Baban Annoor ne kadai sai dai Mamanka ta fada Maka tasan Inda yake ita yanzu.
Abba yace Dan Allah ku nutsu ke Iman zan karyaki idan baki daina mana kuka ba,Annoor ya jawo Iman Jikinsa zo ..Abba ya daka Masa tsawa saketa dan ubanka ba muharramarka bace,ke ma Habiba kina da laifi wlh baki iya tarbiyya ba ace a gabanki yara suna haka kina gani sabo da ba naki bane.

Jauro ne ya dakatar da Abba yace karka yiwa Habiba haka bani da kamarta suma basu da kamarta itace duk taci Kashi da fitsarinsu har suka kawo haka,Habiba tana da Sanyi bata da zafi bata iya fada ba shi yasa take kyale su in tace su bari sai dai tace Allah ya shirya haka take Kuma Allah ya shirya tunda aka tsaya a iya haka.
Abba yace madalla ayi a Fadi gaskiya ni Ina sauraro,Jauro yace ah ko Kaine dai aka sameka ta haka ai iya damuwar da zaka yi kenan, Hashimu ka isheni fa,wai sanda na samo su kana nan ne,Abba yace yanzu mun hadu Ina nan kayi bayani sauri muke,nazo gidan Nan a sa'a yau Inama ma sunana Sa'adu sabo da Sa'a ta.

Jauro yace Kun riga Kun san sunana Kun San asalina da iyayena,muna zuwa kauye da ku,amma zaku ga tunda kuka fara wayo ban sake kaiku kauye ba,nayi hakane sabo da gudun kar Yan uwana ko wasu a gari su fada muku ko ayi muku gori,shi yasa tun Kuna yara rabon da ace kunje kauye ku mazan kenan matan ma basu taba zuwa ba dan ban bari sunje ba,kunyi kunyi har kuka hakura,sannan ko mazan ma bana yarda su kwana tare muke zuwa mu dawo tare,haka a kauyen ma bana bari su fita ko kafar gida daga gida sai mota duk ba komai bane sai wannan dalilin.

Sannan zaku ga bama zama a gari daya, Kun sani farko a Katsina muka zauna,muka koma Jibgawa,na dawo da ku Minna yanzu muka dawo Kano,bana so a San wani Abu a gari bare ma Yan unguwa suyi muku gori shi yasa ban bari mun ta zama a wajen Daya ba tunda Kun sani Allah ya azurtani Kuma Kuma kowa na bashi Ilimi boko Dana addini sannan Kuna da aikin yi ai Alhmdllh.

Farko gata Ummin ku Habiba ita na fara aure Kun sani tunda na aureta ban taba haihuwa ba gashi Allah ya sa min masifar son yara,Ina so ace yau ga wannan a karkashi na suke amma Allah bai bani ba,dangina kaf sun tsani Habiba akan cewar itace juya Bata haihuwa,ba zagi da wulakancin da basu yiwa Habiba ba tun Ina kauye lokacin bani da kudi har Allah ya azurtani na dawo da ita birni.

Iyayena sun tsani Habiba har cewa suke lallai sai na saketa ko na Kara aure,Hakan yasa tace na rufa mata asiri na Kara auren kawai ko ta huta da gori,ana haka na auri matata ta biyu,itama shuru shuru bata haihu ba tace baza ta zauna ba haka na sallameta, tana tafiya ta auri wani ta samu ciki ta haihu yanzu yaranta shida Kunga ya tabbata daga ni ne rashin Haihuwa,haka na sake auren wata itama ta dinga yi min wulakanci iri iri ko Shekara bata yi ba na saketa taje ta auri wani itama tana nan da yaranta yanzu ta haihu.

Na sake auren wata wann???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?an kuwa kullum a zagina take juya marar haihuwa,taimakonka nayi Dana aureka,babu masifa kamar ace mace ta dinga ganin dan ta auri mijinta ma taimakonsa tayi ya shiga uku,ta zageni babu irin cin mutuncin da bata min ba,rabuwar mu da ita shine zagin Habiba da tayi,babu wacce ta isa na aureta ta zagi Habiba na kyaleta,sabo da Habiba nayi nayi akan ta amince na saketa taje ta auri wani ta haihu taki yarda,tace tsakani da Allah take so na, rashin Haihuwa bazai sa ta juya min baya ba,Habiba matar rufin asiri ce,ta karbeni a duk yanayin da nake ciki,talauci,arziki ga rashin Haihuwa duk tana zaune dani,sannan na Tara mata yara ta rike min Kuma bata taba musu kallon banza ba bare gori,ta rike kowa kamar ita ta haife shi.

Abba yace Dan Allah tsaya Jauro bakina Yana kaikayi,Jauro yace Ina ji sarkin shishigi,Abba yace Kuma duk Habiba adalcin da ta Maka baka hakura da yi mata kishiya ba ka Kara auren Na'ima? Allah ya rubuta min ya zanyi,Kuma idan namiji ya Saba da mata biyu baya iya hakura,idan Allah yayi zan Kara idan Allah baiyi ba Habiba for ever Habiba for life inji bature,Habiba harda Jin dadi ta gyara zamanta.

Jauro yace lokacin da na bar kauye na koma katsina muna zaune akwai wata yarinya me suna Asiya a makwaftanmu,tana yawan zuwa gidana jininsu ya hadu da Habiba,kullum in ta dawo daga tallan gyada to tana gidana,Iyayen Asiya wasu masu mugun son Abin duniya ne duk da basu da kudi amma wai Asiya da tallan gyada zata ciyar da su,gyadar da gaba daya bata fita dubu daya ba a lokacin wai da gyada zasu ci su Sha,Kuskuren iyaye kenan wasu,Babar Asiya a lokacin tace indai Asiya Bata yi tallan gyada ba to baza ta samu kayan daki ba idan aurenta yazo,sannan bata kauna Asiya ta dawo mata da gyada ba tare da ta siyar da ita ba.

Asiya suka takurawa da uban tallan gyada ba dare ba rana,daga nan Kuma suka koma yi mata funkaso da Miya tana kaiwa tasha,to Kun San dai Tasha tana da shugaban ko,to shugaban tasha a katsina wani me Suna Zubairu Dan yayi shi yaga Asiya yace yana sonta,Asiya yarinyar kirki ce wlh me addini da hankali,ta fada son Sarkin Tasha Zubairu Danyayi,shima da gaske aurenta zaiyi suna soyayyar su me tsafta,to gaskiya Zubairu Dan shaye shaye ne shi sosai, sai iyayen Asiya suka ce Sam baza su bashi yarsu ba,har yayi alkawarin in ta aure shi zai daina shaye shaye sabo da son da yakewa Asiya,amma suka ki yarda,Asiya tayi kuka sosai,Baban Asiya sai ya samo mata wani Dattijon mutum tsoho zai mata auren dole,Zubairu Dan yayi sai ya sace Asiya suka gudu,sai bayan watanni biyar Asiya ta dawo gida da ciki kato.

Babanta suka mata dukan tsiya suna tambaya waye ya yi mata ? tace gida ,zubairu ya kama musu a Zaria suka zauna abinsu,tace wallahi Kuma akasi aka samu sau uku kacal ya taba amfani da ita duk wannan watanni da suka kwashe,Kuma duk da tana da cikin itace ta gudo amma Zubairu Yana son abarsa.
Ya dawo Yace ai Yana sani suka yi haka so suke dole sai an bashi Asiya,Asiya tace nice nan nace yayi min ciki idan aka ganni da ciki dole a daura mana aure, shi kuwa Zubairu ya Shole abinsa,ni kuwa lokacin naji labarin Asiya,iyayenta sun koreta,ni da Habiba muka fita neman Asiya muka sameta a kasuwa take kwana tana tashi ga ciki,ta bani tausayi ace ga ciki mace ta dinga kwana a rumfar kasuwa kamar mahaukaciya sai na dakko Asiya na dawo da ita gidana,tayi zamanta muna kula da ita,Bata da matsalar ci da Sha da sutura har tazo haihuwa na kaita asibiti ta haifo Danta namiji santalele.
Na Nemo Zubairu yazo ya dauki dansa yayi Masa Addua Yana ta kuka sosai,a wajen nace Dan Allah ni idan ta yaye Dan Ina so,Asiya da sauri tace mun bar Maka sabo da suna gudun abin kunya.

A nan dai ranar suna yaro yaci Suna Sajid na yanka raguna har biyu,duk wani kayan barka na jariri nayi,muna zaune abinmu da Asiya,lokacin na samu iyayenta suka yafe mata sannan suka amince zasu aurawa Zubairu ita,bayan ta yaye jariri aka daura mata aure da Danyayin ta,ya gina musu gida me kyau aka Kai Masa Amarya Kuma a dalilinta wallahi ya daina shaye shaye ya shiryu suna zaman su lafiya da yaransu uku Yasmin,Mufeed da Aryan sai kai Sajid babba,Na sha kaika Kuma kana zuwa da kanka amma tunaninka Zubairu ba mahaifinka bane kawai na auri Asiya na saketa Zubairu ya aura, to kaji daga yau Zubairu shine mahaifinka,Kuma Ina so ka sani kaddara ce babu ta Inda bata zuwarwa mutum,Dan Adam bashi da wayo ko dabara,Iyayenka sunyi kuskure na biyewa son zuciya,Asiya kuruciya da giyar so ce ta kwashe ta,Zubairu Kuma yayi ganganci ya biyewa zuciya,wannan ba wani Abu bane akwai ciwo dole amma ai baza ka kashe kanka ba,ka fawwalawa Allah.

Daga Kai sai Sajid ana yayeka sai Nabeel,watarana akan harkar sufuri na naje Jigawa birnin kudu,Ina mota Ina tafiya wata yarinya budurwa tana ta gudu a titi da sassafe fara ce tas Yar Fulani jikinta furu furu,tana ihu tana a taimaketa da sauri na tsaya tazo ta fada motata tana haki lokacin ban tambayeta komai ba sai da ta huta sannan nayi parking nace wacece ke? tace sunanta Sa'ade ita Yar asalin jigawa ce Birnin kudu,marainiya ce iyayenta sun rasu a hannun kanin Ubanta take,tace wani ne yake sonta sunansa Suffiyan akan bata sonsa ya saceta ya boyeta a wani gida a jigawa dutse kwananta ashirin kullum sai yayi amfani da ita har Allah yasa yau ya manta kofa a bude ta fito ta gudo shine tace na taimaka mata,har gidansu na mayar da ita,amma a lokacin Dake Suffiyan me kudi ne Wanda ke rike Sa'ade kanin Ubanta sai yace karya take yi ya zaneta yace karuwanci ta tafi dama,ai shi dama Suffiyan ya fada Masa tana zuwa gidansa,bayan na tafi da wata biyu ciki ya bayyana a Jikin Sa'ade,Kanin Ubanta yace karya take Suffiyan bazai lalata ta ba,shi da matarsa suka dinga gana mata azaba har watarana lokacin cikin ya gima ta kusa haihuwa naje garin na nemi gidan su Sa'ade,Ina zuwa naga ana dukanta ga tsohon ciki tana ta kuka na karasa nace cikina nane ni nayi cikin Ina son abina,ita kanta tayi mamaki amma na dage nace cikina nane,a garin sai da aka cika ana kallona ana tsine min,Kanin Ubanta yace to wallahi sai an daura min aure da ita,akace haramun ne aure da ciki nace ba komai a daura
Na bada sadaki aka daura na taho da ita gida,tun a mota na saketa nace ba aure tsakaninmu,itama taji dadi.

Haka na kawota itama suka zauna tare da Habiba ta kula da ita har ta haifo Danta santalele kyakyawa gashi nan ranar suna na yanka Masa rago, na rada Masa Nabeel,kayi hakuri Nabeela kai rago daya na yanka Maka.
Haka na dinga sintiri da Sa'ade muna neman Suffiyan Wanda ya mata ciki Allah ya taimake mu muka same shi kuma Nabeel sak mahaifinka kayi a kamanni kyakyawa ne amma sai ka dakko Dan hasken mamanka ka sirka da duhun ubanka sai ka zama ruwa biyu ga ka nan rass da Kai,Kuma Alhmdllh da muka je ya karba domin lokacin yayi nadamar Halayensa ya nemi yafiyar Sa'ade ta yafe Masa,haka kanin Ubanta suka daidaita ya gane gaskiya na maidata gida,cikin ikon Allah ta samu miji na gari me kudi ya aureta a ta biyu a Nan Jigawa kaima ka Santa Nabeel kana zuwa kaji asalinka,tana da yara shida yanzu da Mijinta,Kuma itama ni na mata kayan daki da komai,babanka yanzu ban San me yake ciki ba amma dai nasan ita mahaifiyarka ta sani tunda ta fada min.

Sai ke Laila Mahaifiyarki Zahrau,yaren Edo state ce,ba musulma bace a lokacin tayi aure a Lagos Bata taba haihuwa ba,kasuwanci ya kawo mijinta Arewa Kano,ya Dade a Kano katsam sai ta musulunta wannan yasa ya mata duka ya saketa,ya fadawa iyayenta suma suka ce basu ba ita kar ta dawo wajen su,akwai wani malami babba Malam Yusuf a unguwar da suke shine ya musuluntar da ita,bayan abinda mijinta yayi mata sai ta koma ta fadawa Malamin,ya lallasheta yace ta dawo gidansa ta zauna,haka ta koma can da zama sun Saba da matansa,tana sha'awar namiji amma kowa a musulmanmu sunki aurenta da ta samu saurayi sai iyayen saurayin su hanashi aurenta suce ai Tubabbiya ce sabon musulunta ce,kowa ai ta cewa Tubabbiya ce ana kyararta ana ganin ma kamar ba wani addini take ba,to yare sun Saba da saka kaya damammu,tana yin shigar da taga dama Malamin ya koma sha'awarta sabo da rashin Imani ya fara nemanta har ya dirka mata ciki,Kuma bayan zance ya fito yace karya take,naje unguwar lokacin wani uzuri ya kaini na harkar siyar da mota naji matasa suna labarin ance Malamin ma yace korarta zaiyi,Ni Kuma sai ta bani tausayi

Naje nan ma nayi
shishishigi nace cikina nane,dama Malam Yusuf mufita yake nema sai ya kebe dani gefe yace na aureta,yasan fa haramun ne amma ya aikata nace bazan aureta ba ya nace, to ni ba wani jajirtacce ba kawai nace a daura Allah ya yafe min,aka daura aure na tafi da ita gidana,Satin latifa biyu na saketa Kuma ban taba ma shiga dakinta ba,bayan ta haihu ta zabi suna da kanta aka sa miki Laila,bayan ta yaye ta barni ke ta Samu miji Isa na aurar da ita na mata komai,Laila kina zuwa Kuma ke sai da na miki aure muka je da Latifa wajen Malam lokacin cuta ta kamashi yaga mutuwa da wuri ya amsa cewar ke yarsa ce Kuma ya Sanarwa danginsa kaf suka yafi juna da kyar,amma iya mamanki kika sani kawai.
Sai Kai Haidar tunda still ka girmi Annoor daga Laila sai Kai tsiranku ba yawa,Annoor yace nine karami ma kenan,yace kwarai kuwa,Abba yace mu aci gaba sauri muke ka tsaya surutu,Dan Allah Jauro mene haka haba komai sai kayi kunbiya kunbiya.

Mummy kuwa ta Kai sati guda Baseeru kullum sai dai yazo ya kwashi harka ya fece,Hakan ba karamin Kona mata Rai yake ba kullum da karyar da yake shirgawa ko ruwanta baya sha,yau Mummy ta gama girki tace yau dole sai Baseeru yaci abincinta,tana kitchen ta bude abincin tana zuba Masa magani a ciki,me aikinta ashe tana labe tana kallo tana dauka a wayarta,Mummy Bata sani ba Baseeru ya hada baki da Yar aiki tuni ya biyata wasu kudi,ficewa tayi da sauri bayan ta gama dauka ta kira Baseeru a waya yace Mero ya akayi? Mero tana kasa da Murya tace shegiyar ta zuba Baseeru,dama kace yau zaka zo? Baseeru yace Mero Ina hanya ma tasan zanzo,Mero tace to wlh Yana nan flas ruwan hoda Alqur'an karka ci,billahillazi zata kaika kiyama Baseeru,aradu na Gani da idona,kwarankatsa dubu ta dakko he zubawa take he zubawa take yi a ciki,ai kuwa na dauka a waya hine nace bari na fada Maka,Baseeru yace Na'am Mero to he aka yi Yaya? shima yayi mata irin hausarta ya tsokaneta shi a dole wayayye,Mero tace hine hine nace uhmmm....Dama....ta rankwashi kanta tana sosawa taci gaba da magana Hine nace dama uhmmm...abin nan...abin Nan.......................

Ina son Dan Hajiya Spark mijin wannan me kyau din, Ina gani suna zuwa tare wajen Mummy wallahi ni hi nake so,na fasa karbar kudin kayi min hanya ya Soni ya aureni wallahi Baseeru Ina sonsa tunda kaga Kai mijin uwarsa ne ko? Baseeru ya sheke da dariya yace Mero Ina laifin kice kina so na ai nine daidai ke,Mero tace cabdi jam hummm uhmm wallahi ni Spark nake so jikinsa me kyau so nake nima na dinga rungume hi,rannan matarsa haka ta dinga rungume hi suna ta wani umhmaahchacha da Baki yana tsotse mata kumatu na gani a Jikin mota suna ta yi,Nima ina son irinsa gahi Yana ta kamhi kullum wallahi Allah ni hi nake so,ko Kuma idan bazai so ni ba ai akwai kaninsa wannan yaron Arham ko Rafeeq Ina sonsu a bani Daya.

Baseeru yace Misam fa tace kuturun Uba wallahi hima Ina sonsa na ma fi sonsa a kan Arham sabo da su suna da kudi,hi kuwa Arham din nan agogo ma siya Masa akeyi gahi ya dinga zazzago wandonsa duwawunsa a waje, Allah ya kiyaye amma ko hi na samu Ina so zan karba da hakuri,amma dai ni tsakani da Allah Spark

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login