Showing 33001 words to 36000 words out of 134888 words

Chapter 12 - Tantiriya Agidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

913

gari.

Inda Spark yake birge Naila duk saurinsa tsayawa yake sosai a hankali sai ya gama wasa da ita duk wani Jin dadi sai ya bata ya motsata sosai da sosai yanda zata gamsu sosai shi yasa take tsoron fushinsa,bama ta iya dogon fushi da shi,bai ma fiye mata laifi ba itace take Masa sabo da mata tunaninsu da banbanci dole sai mutum ya Kai zuciyarsa nesa haka kawai ma takalarsa fada take yi,sarrafa juna suka fara a nutse a hankali,Naila yanzu bata kunya abinda taga dama fada takeyi,dama gata fitsararriya sai abinda kunnen Spark yaji,idan kuwa ta haukace da dadi har fulatanci yi take har ya fara tsintar wasu words din da take fada idan ta zauce, ai shi Spark da yaji Fulatanci to yasan Naila taje karshe Kuma,Naila za a canja salo tace dole na dinga Exercise sabo da ko Ina na dinga lankwasa jikina,wani kafin na iya wahala nake sha,yace ai kina kokari sosai na taba zaton ma zaki koma haka yanda kullum Baki da aiki sai kukan zafi,yanzu kuwa a wajenki ma nake ganin Style,Naila tace Kai ai da kusan kullum sai mun Kalli Bf,haba ai tunda na Saba kakarka ta yanke saka salo salo zan dinga baka,dariya Spark yayi Yana son kurin Naila idan aka yabeta sai kuri sai Kuma ta sake dagewa,shi yasa sai ya nuna mata ta fishi iyawa da sani ga yawan yabonta da yake yi,ko ba dai dai tayi ba cikin hikima da wayewa yake nuna mata, Naila ce tace yau sau uku zaka min yini zamuyi,sai nace na koshi ,sai naga karshen Hallare yau,dariya yayi Yana Jin dadi shi ai yau ta gama Masa komai tace zata ga karshen Hallare ba lokacin dainawa sai dai a huta a koma bakin aiki.

Ikhram kuwa Rafeeq ta samu a palo yana Ganinta da akwati ya mike tsaye ya Sha swagg sosai,yace kema tafiyar ce? tace ae wlh ai gwara na tafi,Rafeeq yace babu wani gwara ,ko banza ana dan lasa min gaskiya zanyi rashi,Murmushi tayi duk ranta a jagule idonta kamar tayi kuka yace kalau kike kuwa? Kai ta girgiza Masa tayi kasa da kanta kuka Yana so ya kwace mata,yace baza ki magana ba? tana kokarin Maida kukanta ya matso gab da ita yace kunya kike ji ne ko me? yatsa yasa tare da dago kanta a hankali hawaye ne ya zubo mata,yace me ya faru baki da lafiya? Murmushin dole tayi tana tunanin boyewa tace ba komai, yace ya zaki ce ba komai ga hawaye Yana zuba Kuma kina murmushi? Tafiya tayi da sauri zata fita ya ruko hannunta tare da dawo da ita baya yace tell me what's going on? tace ba fa komai,yace Alright tunda kince haka bazan takura ki ba,zan kiraki a waya wai ke inane garinku ma ne? tace kano,kauye ko birni ta Harare shi tace na Maka kama da Yar kauye,to a kauye ai akwai Yan birni a birni akwai Yan kauye,tace hakane a birni nake to yace shike nan zamu yi wata muje na kaiki airport,tace ni a mota zan koma bani kudin jirgin ya min amfani,Rafeeq yace to muje na kaiki tasha,tace to suka tafi ya kaita har Tasha ya sata a mota ya biya kudin motar ya tura mata kudi a waya kyauta Yana tsaye a saitin window dinta suna ta hira har mota ta tashi,ta window tace Rafeeq....ya kalleta ta glass da sauri,tace I like you,bafa Ina nufin I love you ba,like nace....wani takaici ya kama Rafeeq yace ita da zata ce Rafeeq I love you sai ta wani ce like,Rafeeq da baya so wata tace tana sonsa yau shine ke neman wata tace tana sonsa a duniya,tana tafiya ya juyo kamar maraya duk sai yaji garin ya daina Masa dadi,gidan su ya tafi sabo da ya samu ya rage damuwa.
Yana zuwa gidan Mamansa ya sameta a kujera a zaune ya kwantar da kansa a cinyarta yace I'm in love ku taimaka min,tace wlh tunda na ganka ni ko a kusa dani baka taba zama ba yau Rafeeq a cinyata nasan da matsala,yace wa'azi budurwata tayi min,Dariya Mama tayi.

Bayan Hashimu ya zo gidan Jauro da kwana biyu kullum sai Hashimu ya bugowa Jauro waya akan lallai ya fadawa yara matsayinsu, yau ma da sassafe ya dinga kiran Jauro a waya,Jauro ya daga suka gaisa,Hashimu yace Yaya kuwa ka fada musu? Jauro yace iKon Allah wai yau nake Jin masifa yaranka ne wai ko Kai ka samo min su? bazan fada ba ban shirya ba,Hashimu yace wlh nazo da kaina na fada musu ni bazan iya Ganin wannan abin tausayi ba yara samari da Yan mata sun Isa aure an aurar da wasu amma basu San su waye su ba,wlh ko ka fada ko Kuma inzo har gida na fada musu ni bazan iya jiran wannan Abu naka ba Jauro wannan ba rayuwa bace,Jauro yace to zan fada ubana,Hashimu yace karka ka fada ma ka gani wlh zanzo na fada ni ya kashe waya,Jauro yace Ina murnar haduwa da Hashimu ashe masifa na hadu da shi,yabi ya ishe ni haba.

Na'ima tana can Station an bada bailing ko wacce mata amma Banda ita duk ta rame ta fita hayyacinta,kullum Dan sanda ke kawo mata abinci in yazo sai yace mijinta yazo Yana ta kuka amma Oga ya hanashi shiga,Na'ima tace Allah sarki ni San Jauro Yana so na wlh bazai iya kyaleni a Nan ba,Allah ya isa tsakanina da ku Yan sanda da kuka Hana mijina ganina.

Sai yau Allah ya kawo Jauro zai ga Na'ima matarsa,Jikin cail din yazo ya tsaya Inda Na'ima ke tsare hannunta rike da karfen jiki me raga,Jauro Yana zuwa yace Na'ima....Na'imatuta kece kika dawo haka?yanzu Na'ima kece wannan? Yan sanda sun cuceni sai ya fashe da kukan karya,Na'ima ma sai kuka harda yi da karfi na gaske take yi taci wahala, abinci sai anga dama ake bata,Kuma duk da sa hannun Jauro,Jauro kukan karya yake Wiwi harda fyace majina,yace yau zaki fita Na'imatu,na Sha wahala ta rashinki naji jiki,kwanciya ba dadi gida ya zama kango,na sani wlh cewar Na'ima tana share hawaye.

Baseeru kuwa har kwana biyu bai je ganin Mummy ba,kullum sai ta kirashi a waya,Chika itama Baseeru ta kira tana Masa warning tace wlh dai karka sake Kaci abinta,karka yi bacci a gidanta ko da rana ne,yace Ina sane ai,yau zanje domin a matse nake zanje na karbi hakkina na fece.
Waya ya yiwa Mummy yace zaizo yau da yamma,Mummy ta sa Yan aiki suka gyara gida kamar wani Gomna zaizo,itama taci gayu ta hade cikin material sky,tana zaune da yamma ko Ina Yana uban kamshi.

Baseeru ne ya shugo gidan shima anci gayu fes da shi,yana zuwa Mummy harda yin tsalle ta fada Jikin Baseeru,Baseeru ya rungumeta fuskarsa tana kallon bayanta Yana ta zuba gwalo ko uban wa yake wa oho,Mummy sai faman goga Masa kirji take,Baseeru yace yawwa nanika min su,manna su,tace Dear abinci fa? Baseeru yace an samu matsala wlh daga gidan abokina nake matarsa ta nace sai naci abinci na cika cikina ko bangaren ruwa a cike yake taf ba waje,Mummy taji wani ba dadi tace ba komai next time,a ranta tace ai sa guba kauyenci ne yanzu ai na canja salo zaka ci ubanka sai duniya ta San a gidana kake tukun zan gama da Kai,baza ma ka mutu a gidana ba,bare a tuhumeni nasan ta Inda zan kaika lahira.

Shi kuwa Baseeru Mummy ya fara sarrafawa gata itama an kwana biyu kadan ake jira ta zurma ya kwashi gara yau ma sosai tun yamma sai magriba ya hakura,tace dole sai ya kwana,Baseeru yace to bari naje Sallah na dawo Yana fita ya fece gidan Daddy Inda yake gadi ya bar Mummy bau tana jiransa.
Tunda taga bai dawo ba ranta yayi mugun baci tace wato ya maidani sex machine yazo ya kwasa ya tafi.

Wayarta ta dauka ta kirashi,bugu daya ya daga yace Me gidana nane ya kira ni ki rufe gidanki bazan dawo ba,Mummy takaici yasa cikin bala'i tace zaka ci uban babanka Baseeru,wlh dani kake zance,Baseeru yace zaki ci uban Babarki surayya kike ko Yusra wlh zan tsine miki ki San tsinuwar miji Kuma,Yar iska marar mutunci,Mummy tace kaiii wato idan na zageka sai ka rama kana me gadi? Tsaki ya ja yace baki da hankali zanzo gidan sai na ci mutuncinki ya kashe wayarsa,Mummy ta Kalli wayar tana girgiza Kai tace eyyaaaaaa Basiru baza kayi karko ba,baza ka Dade a duniya ba,baza kayi tsawon rai ba,mutum ya lallabani da Yaya ya kare ma.

Spark kuwa sabo da haushin Mummy da yaji ta hanashi bincike gashi me gadi ne ya aureta wannan yasa yace nima wallahi ta Abba suruki na bazan boye gaskiya ba, Hakan yasa duk Wanda ya tambaye shi a dangin su ya Mummy Dinka? yace tana gidanta lafiya Lau ai sun rabu da Abban nawa na biyu, yanzu gidanta ya dawo da zama,me gadi ne ashe,da ance a garin ya? Yace kuje wajenta kwaji zancen ba a gulma dani.

Yau ma yaje gaida Mima tace Ina Mummyn taka kuwa? Yace hmmm ai ni yanzu na koma Kuma abin tausayi,ya kamata ki tausaya min ni da Naila mun koma yaran talaka, to uban namu na biyu me gadi ne,yanzu ma uwar tamu tana gidanta ya koma zuwa gidanta,Ashe gadi yake yi ba gidansa bane,Auren dauki sanda muka koma mu ai,Mima tace ban gane ba? Yace kije kyaji tushen zancen.




Ayi min afwa tunda kuka ga shuru akwai uzuri ne.

Masu Sharhi Ina godiya wlh Allah ya bar kauna

Mrs chief My love har naga kira>?#?>?#?>?#?>?#?

Kar ku ce AsmaBaffa wai ko nima na zama Abba Dolo ne yau.




AsmaBaffa[1/12, 9:48 PM] +234 806 252 6950: Arewabooks AsmaBaffa1
https://www.arewabooks.com/locked?id=65759f207c65b397e88b84b3

A GIDAN YARI

BOOK 2
~YARAN JAURO~

26-30

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM


PAGE NAKI NE
MOM SANI




Jauro ne ya dawo da Na'ima gida,yace Maza shiga yau sai kin yini a toilet kina dirje jikinki idan ba haka ba baza ki hau gado na ba,Annoor ne ya fito zai fita ba aiki,Jauro yace uhm kaga Maza wai Annoor ya kake da Yan mata ne a waje da kallo? Annoor yace me zan musu kuwa Kawu wata gadara nake na Kara doro,Jauro yace Allahu Akbar Dan gidan Larabawa,dariya Annoor yayi.

Nabeel ne ya fito da sauri dauke da cup din shayi Yana kurba shima fita zaiyi,Jauro yace ga Kuma Dan Amerika ya fito ruwa biyu hancinsa kadai ya isa budurwa ta kware Masa,Nabeel baiyi niyyar dariya ba sai da yayi a lokacin.

Haidar Yana fitowa Nabeel yace kace zan fita da Kai Kuma Ina jiranka kayi sauri,Jauro yace wannan Dan India ne shi ai Ina motarka Haidar? Haidar yace aro na bayar,wa ka bawa aro Kuma? Yace abokinane yace zai je Katsina na bashi tun jiya,zai je karya wajen Yan mata kenan,dama motar taka ma ta kwana biyu ya kamata a canja Maka,Annoor yace shi bazai iya siya ba sai ka canja Masa,Haidar yace to ni na kaika kudi ne Kai da kake da mota uku fa ka hau wannan ka hau waccen.

Jauro yace kyale shi zan canja ma kaima,Nabeel yace Nidai Banda ni zan karo wata da kudina,Haidar yace ni a canja min da ubana na dogara,Jauro yayi dariya,suka yiwa Na'ima Allah ya kiyaye gaba Dake basa shiga harkarta,sai wani share su take yi,sun san dama a banza take kallon su basu san dalili ba.

Na'ima bayan tayi wanka Habiba ta kawo mata abinci taci ta koshi tana dakinta waya ta dauka ta kira kawarta Hajiya Luba suna ta hira da gulmace gulmace dai dai zata fara gulmar yaran Shegu Iman tazo shiga dakinta zata mata Allah ya tsare gaba taji tace Jauro wa cab ai ya Hana a fada musu,wallahi abinda yake wa yaran nan ko shi ya haife su iya abinda zaiyi kenan,na tsane su ka tara yara tara yaran Shegu a gida,wai Annoor ne kawai Dan sunna,sai ma Iman na tsani yarinyar nan iyayi a cikinta ya baci wai ita ta gari,wa ya sani ma ko Annoor din Zina yake da ita,yo yarinya kullum tana jikinsa.

Luba tace tunda yace a bakin aurenki ai bai dace ki fada ba kamar fa aurenki ya mutu kenan wlh,Na'ima tace tab Kuma fa kenan auren nawa ya mutu? Yace duk Wacce ta fada shike nan ya saketa ko wani aka fadawa wai ya sake ta,bama iya yaran ba,Luba tace aure ya mutu,Na'ima tace wace zata bar daula Ina kallon kudi zaman zinata zanci gaba da yi kiyi shuru kawai,Luba tace ke dai ki tambayi malamai ta kashe wayarta,Na'ima tace tab ai wlh sai sunji labari gwara ma auren ya mutu da hujja ta fito fit waje taci karo da Iman a labe.

Dukan Iman ta fara Dan ubanki munafuka shegiya ashe labe kike mana Yar Zina duk baku da Uba yaran cikin shege ta fara jibgar Iman,Annoor ne ya dawo daukan wata Allura yana zuwa ya samu Na'ima ta rufe Iman dinsa da duka tana ce mata Yar Zina,da sauri ya karasi ya janye Iman dake kuka,Na'ima tace ni zata yiwa labe Yar iska shegiya yar zina,Annoor ya kwashe Na'ima da mari,sai ga Jauro ya fito daga bangarensa yace kayi dai dai ko baka mareta ba dama in nazo ni zanyi da kaina.

Na'ima tace Annoor ni ka mara? Ai ba matar ubanka bace ni dole ka mare ni,yayan Zina Jauro ya kasa fada muku gaskiya amma wallahi wallahi ba shi ya haifeku ba,yaran Zina ne ku,yayan Shegu,ni dama ba sonka nake ba Jauro kudinka nake so Kuma na samu bakin rabo,tunda na mallaki gidaje har biyu Ina da kudi a accnt sai me,yaro matashi zan aura Kuma na haihu,me zanyi da Kai juya marar amfani Wanda baya haihuwa,baka da masu Maka addua.

Jauro yace kije dai na sakeki ko me zaki ce kice Allah shine yake son ganina haka,akan a bani yara su zama ajalina gwara ban haifa ba,a bani yaro ya zama Dan kidnapping ko Dan ta'adda,Dan daba,Dan giya,me jawo min magana mene amfaninsa gwara ban samu yaro ba.

Sannan karki tunanin dan wani ya haifi yaro kice wai kansa ya haifawa maybe yaron da ya Haifa har makwafta da Al'umma sai sun amfane shi,akwai yaron da za a haifa iyayensa baza suci moriyarsa ba amma Wanda basu hada ko gari ba sai su amfane shi,Ashe baki San maganar da ake nufi da Da na kowa bane, Kinga wannan yaran da na rike sunfi min kowa a wajena wlh,ban rike su da wata manufa ba face naga ni bana haihuwa naga me zanyi na tallafi wasu yaran, shi yasa naga irinsu sunfi bukatar taimako Kuma nayi Alhmdllh, ban taba Jin kamar ba ni na haife su ba,wlh ba Wanda bana so a cikinsu,Kuma yanda nake jinsu sunfi yaran Yan uwana a wajena,ai Yan uwana suna da yara idan so nake zan iya zuwa na karba amma ban karba ba sai su,banza wawiya tattara naki ki Kara gaba.

Suna tsaka da haka Abba yayi sallama ya samu rikicin,Jauro yace ka huta fada ta rigaka mahaukaciyar ta fada,Abba yace Alhmdllh amma naji dadi,Na'ima ce ta dakko mayafinta zata tafi Abba yace sabo da me? Tace ya sake ni sai Kuma ta fashe da kuka,Abba yace akan kawai ta Fadi gaskiya haba Jauro baron mata,Kai da matan Kuma,Kaine fa bawan su,Jauro yace wlh bazan dawo da ita ba na tsaneta tunda tasan zan fada musu ai ba da haka nace zan fada ba,ta ya zata dinga fada musu yaran Zina wlh har abada bani ba ita na cike na uku ma na sakeki saki uku wlh bani ba ke.

Abba yace Subhannallah aiki ya lalace Kinga tafi gida kukan me zaki yi Kuma da katon Kai kamar kin dakko botiki a kanki, kince yara yayan Zina sai kinyi sheda a gaban Allah ,ni ai sai yanzu na gane ma Ashe Na'ima ce naga tayi baki,Jauro yace manta ne ya kare,Body leshon suke cewa ko body Leshun,Abba yace kaji Dan kauye Body lotson ake cewa,Jauro yace yawwa shine ya kare ta Dade a wajen Yan sanda babu na shafawa a can asirinta ya tonu,Abba yace irinsu ake aurowa yanzu su dinga haifo Maka yara bakake ka rasa dalili ashe suma bakake ne,Jauro yace kaga laifin mata? Ai mu muke jawowa da son farare,Abba yace su shafa abinsu safi auruwa da wuri ko akan layi fara ta wuce ita ake Kallo,ni kaina Ina daga runfa Ina kallo,Jauro yace baren ma ni,gwara ta tafi na auro sabuwa dama kullum Ina ganin wata Hajara sonta nake na rasa Yaya zanyi yanzu na samu fili.
Abba yace Ina son auren nan Jauro amma Kubra ta kankane ni,da nace zanyi sai kuka,ga Kubra da kyau duk Wacce na dakko ko kama kafar Kubra baza tayi ba,Kai da Kubra zata fita daga gidana samari sonta zasu yi ba ruwana ni dai,Jauro yace Kara aure ai sai mu bayin mata,ai da zaka yi Kuskuren rabuwa da Kubra wlh zuwa zanyi nayi wuff da ita,sai dai mu daina abota har abada,Abba yace karka sake shigar min gida daga yau ashe kallonta kake yi kana yabawa.

Annoor da Iman suna tsaye kamar gumaka Annoor yace aji damu Nan mu,Jauro ya juyo da kalar tausayi kamar ba su suke hira ba,Abba yace kuyi hakuri ku kwantar da hankalinku,Iman tuni kuka take ita ta zauna tayi zaman Yan bori ta Dora hannaye a kai,tace Allah ka dauki raina na huta,Annoor yace wlh ki daina adduar nan yar iska kina zuwa lahira ubanki zaki ci, kin San dai abinda kika aikata ko tom.
Abba yace Dan Allah ku nutsu a baku tarihinku yau,Jauro duk ya kira yaransa a waya har masu aure yace duk abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login