Showing 3001 words to 6000 words out of 134888 words

Chapter 2 - Tantiriya Agidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

902

wanka yace bazan iya ba sai an Sha ruwa yunwa nake ji ya kwanta a doguwar kujera yayi shanana,ga yunwa ga Sha'awar Naila Yana ta daurewa kar azumin ya balle,Naila Kuma taje taci gayu ta sa kana nan kaya na daukan magana duk ta sake ruda shi.

5pm ya tashi ya kinkimo agogon bango ya ajiye kusa da shi,Naila ta dinga Masa dariya,yace ji agogo baya tafiyar kirki,Agogon ya ajiye a Saman kansa ya kwanta yace agogo bazai yi sauri ba haba tun dazu a 5pm muke,Naila ta fito daga kitchen tana Masa girkin Shan ruwa dariya ya bata,ya kalleta kamar Dan maraya bashi da dauriyar azumi shi,gashi sai kallon Naila Amarya yake a banza tana ta zamanta bai more ba,Naila tace an kusa ai,yace Ina wani kusa agogo baya tafiya yaki tafiya tun dazu,a gefensa ta zauna yace tashi kiyi sauri ki gama girkin Nan ki ajiye min a gabana Ina shakar kamshinsu a gabana.

Naila ta zauna ya ture ta ta fado kasa suna dariya yace Jamilu ba karfi,tashi tayi zata wuce kitchen Mima ta shugo gidan ta Sha shadda,tana zuwa Naila tace sannu da zuwa,Mima ta daure fuska tace ke dalla wuce ki bani waje ba wajenki nazo ba gidan Dana nazo ko gidanki ne? Spark ya mike ya zauna yace Mima gidanta ne mana,kin taba Jin namiji yayi gida yayi aure ana cewa gidan wane? Ai sai dai gidan wance,sabo da haka gidan Nailan Spark,ko gidan Naila ai yafi dadi ma,amma gidan Spark tsura ai sai a zaci wani tsohon tuzuru ne a gidansa Wanda ya shahara a tuzuranci sai dai gidansa,Yana zaman kansa,ni yanzu ba zaman kaina nake ba,Naila dariya ta kamata ta boye,ta wuce kitchen ta kawo wa Mima kayan Sha,Mima ta gasa mata harara tace duk an mallake min yaro,Spark yace Baby sauri ki gama girkin nan na kaiki Shan ice cream.

Mima tace wato ni na tsufa baza ka kaini ba sai matarka,idan matsala ce ai kazo ka kirani amma Dake Jin dadi ne sai matarka wannan yarinyar,wai Dan Allah Spark baka Jin kunyar kanka,Kalle ka duk kudinka duk kyan ka sai ka kare a wannan abin, ta nuna Naila tana yatsina kamar taga Kashi,Spark ya Kalli Mima yace ice cream din zanje Sha Dake? da na taba zuwa Dake ne? ga Mijinki can ya kaiki mana kema, Naila da sauri tace Spark tana hararsa,Kuma kunyar me zan ji? Ki kalleta fa ai ban fita kyau ba,Kuma wannan duk tafi family dinmu wayewa da ilimi da hankali wlh,Dan Allah ku dinga Jan girman ku,talaka ta na gani ita nake so ba me kudi ba,kusan kullum sai kunzo min gidan Kun Bata mata rai,sabo dani fa take kyalewa tana daga kafa,ku dinga Jan girman ku dan Allah,bana so a Kai gabar da zata gajiya ta fara ramawa nima bazan ji dadi ba duk Dan Halak bazai so ya auro mace ta zagi iyayensa ba ko wacce ta rike shi,sannan Kuma na raba yarinyar da iyayenta na kawota Nan kullum sai Kun zageta,ita haka iyayenta suke min,kuje kuga yanda suke tarba ta kamar su goya ni, ai abin kuji dadi ne.

Sabo da sun ga kana da kudi ne cewar Mima,to ni dai bana so wlh gaskiya indai haka ne ku daina zuwa gidana,Mima ta bude Baki tace akan wannan tambadaddiyar? Yace ae ita nake so ni dama irinta nake so,fitsararriyar? Yace ai tafi dadi kashe arna,ni da tana da kunya ma bazan so ta ba,nafi son tsagera wacce idonta a bushe yake in zuba iskanci na yanda nake so ta biye min muyi ta yin abin mu,dama na tara shi da yawa" me tayani nake nema sai gashi na samu,amma abinda kuke yi ba tsari sama,shi yasa ni kuka ga bana shiga safgar family.

Mima tace ae lallai ka lalace Spark,dama can ni a lalace na nake,tarbiyya aka yi min? Dan Kunga bana magana shine kuke tunanin ni wani Ustaz ne? Miciji ma ya yake? Kunga Yana magana? Amma tsiyar da yake shukawa fa? ai duk iskancin miciji baya magana bai taba ba Kuma idan yayi abu sai a Sha mamaki to ni haka nake.

Mima dariya tayi tace Allah ya hore Maka magana Spark wlh kana bani mamaki in ka Fadi Abu kamar ba Kai ba,Kuma a nutse Allah ya shiryeka,yace Ameen,matarka Kuma bazan so ta ba,Spark yace tunda Ina son abata ai ta haye,dama soyayyar Miji ake bukata Kuma ta samu sai yanda tayi dani,Maza su dinga wani cewa no body can control me,ba Wanda zai fada min abinda zanyi amma Yana shiga bedroom matar tace lock the door haka zai kulle Yana sauri,ke fa dangin mijinki basu miki haka ba Mima,Mima tace kaga ya isheka Kuma daga fadar magana biyu uku ka fada min taka tafi talatin,ka kyale ni Kuma wlh warning nazo yi Maka idan ka goyawa Misam baya yaki auren Wahida tamu ce ni da Kai,Spark yace wai ita Wahida nan Gold ne a tsakanin cinyoyinta ko kuwa AC ne a wajen,a likawa wannan a likawa wannan,matar duk da an gama lalubeta komai ya saki,to a Hakan Dan ubanku dole ko Misam ko Rafeeq sai ya aure ta,Spark yace Rafeeq? Ai dama Rafeeq kika bawa ita shine bai da budurwa,Mima tace da nayi wannan tunanin sai naga sunfi shiri da Misam.

Spark yace wa ya fada miki ai har ziyara take kaiwa Rafeeq school,rannan ma a gidansa ta kwana da Allah yasa Rafeeq Dan iska ne da tuni kinyi Jika a waje,ta Allah ba taka ba cewar Mima, wai da gaske kake? Nasan fa baka karya Spark,yace ki tambayi Rafeeq din kiji,Mima sai ta yarda tace to shike nan amma dai dole Misam ko Rafeeq wani ya aure ta,Spark yace ni fa? Kafi karfi na kai,cewar Mima ta mike zata tafi ya mike ya rakata har Mota sannan ya dawo.

Har magriba ta kusa wanka yayi a gurguje ya fito cikin jallabiya fara,Naila ta fito da milk a glass cup me Sanyi,da fruits a bowl,a Palo suka hadu tace anyi kira ma fa Yankan kankana ya dauka yayi Bismillah sannan yayi adduoi ya ci sannan ya dauki madarar ya shanye ya wuce masallaci da sauri.

Ana yin sallah ya dawo gida an shirya Masa girki daban daban ya zauna yaci,Yana murmushi yace mashaallah so delicious,Naila tana Jin dadi itama tana ci yace je ki shirya,au da gaske kake yi? Yace ae mana makwaftanmu zan kaiki ku gaisa,Naila ta wuce tayi wanka ta shirya cikin turkysh Abaya maroon ta Sha kyau sosai ta fito,yace Larabawa Yana mata video har ta karaso,bakinsa ya kuskure tare da sake gyara sumarsa sannan suka fita a kafa ba tare da sun hau abin hawa ba,suka je makwaftansu har gidaje biyar sauran Kuma yace sai jibi zai kaita,sannan Kuma zai kaita dukkan gidajen Yan uwansa kaf.
Ice cream suka siyo da kayan makulashe,Naila tace Ina na Mummy? gaskiya baka kyauta ba kace wani mijinta ya siya mata ba daidai bane,Spark ya kalleta Ledojin suna hannunsa Daya hannun Kuma ya rike Naila,suna tafiya yace sorry,bani zaka ba hakuri ba gida zaka je ka bawa Mima hakuri,shike nan zan ce tayi hakuri Inshaallah shike nan? Naila tayi murmushi tace ko kaifa.
Suna komawa gida tun a Palo ya dauki Naila sai bedroom ya bajeta suka fara Kwalbewa.

Washe gari Naila ce ta kira Chika ta daga tace Chika ni Mummy anya kuwa baza a kyaleta ba taci darajar Spark,Kinga Mamansa ce,Chika shewa tayi tace to yar dadi miji matar da tayi kisan Kai sannan ta miki sharri karki manta har yanzu bata San kece Jamilu ba,sannan dangi ma basu sani ba,sannan ki tuna fa ba a wanke ki daga zargi ba kowa ke ya sani da kinyi kisan Kai tunaninsu kina gidan yari,ai ba batun wani daga kafa wlh tunda na fara sai na idar da aikina ko kina so ko bakya so,ke a dole dadi miji.
Naila tace shike nan Allah ya bamu sa'a ,Chika tace Ameen nima Ina da case da me Unguwa zan koma kansa.

Misam ne ya kira Chika Bata San Ina ya samu number dinta ba,muryarsa ta tsinta taji Yana makyarkyata kamar ba shi da lafiya,tace lafiya? da kyar yake magana wai ki....zo...bani da lafiya,Chika ta rude tace kana Ina? Wani sabon hotel din ya fada mata ta nufi can direct,harda cewa kiyi sauri yanzu za a tafi dani gida,Chika da sauri taje a taxi ta wuce room din Kai tsaye,kofar ta bude da sauri ta shiga a rude,Saman bed ta hango shi yayi wani ranga ranga.

Chika ta karasa gaban bed din da sauri tace Ina ma Ina da saurin kuka da nayi kuka yanzu,amma tsiyar ni sai naga mutuwa kiri kiri nake iya kuka,Nishi ya fara Yana furta ashhshsh...Chika dukawa tayi a kansa tana kokarin cire bargon da ya shige ciki,ba zato taji ya fisgota ta fado kansa ya Maida hannayensa tare da rungumeta,Chika tace wai mene haka Dan Allah ka sake ni,nifa ba Yar iska bace,Misam yace ni kuwa shine ya zaka yi soyayya da bazawari sai hakuri akwai mu da sakin layi sannan mu bama jira sabo da mun San kan komai.

Chika tana kokawar kwatar kanta ta karfi amma ya hana hakan,yace tun yaushe nace Ina sonki kinki bani amsa kin barni sai jira nake, Chika ba shiri tace indai akan wannan ne Ina sonka nima na amince zan aure ka Dan Allah ka sake ni,murmushi yayi Yana karewa fuskarta kallo Ya furta saura Tabesting,Kinsan Tabesting Yana Kara dankon kauna,Chika ta ce mene Kuma Tabesting? yace Tabe ,na dan tattaba kayan dadi,sai kin min Uzuri sabo da soyayya da bazawari dole sai anyi hakuri damu,shi yasa da nazo zance kawai Tabesting shine zaman lafiya idan ba haka ba wata ta taba miki miji.

Chika dariya tayi tace ba zai yuwu ba kuwa a dinga Tabesting Dina ta kwace kanta da kyar,ya fisgota again ta fado kansa,bakinta ya laluba ya fara tsotsa,Chika ta kasa tashi daga Jikinsa amma cewa take ka kyaleni ka bari please Bata da niyyar tashi,shi Kuma ba rike ta yayi ba,sai da taji hannayensa a cikin rigarta a Saman Boobs dinta" sannan ta dawo hayyacinta da kyar ta kwaci kanta a hannun Misam ta fice da gudu,ta bar shi jikinsa a mace gaba daya.

Hanan ce zaune a Dan kurkubullin tsakar gidansu tana wanke kayan fitsarin yaran gidan su,gefe Kuma ga Mamanta tana dama Koko,Hanan ta Kalli kokon ta tabe baki tace kullum Koko tunda na dawo ban Sha shayi ba, Maman Hanan tace ai kina yin idda ki samu kiyi auren kisan wuta ta karfi,ko Idi KwarKwar ki samu a biya shi kudi ki aure shi Yana sakinki ki koma gidan Mohsin,Hanan tace tab wlh bazan koma ba ni burina tunda a sanadin Amaryarsa ya sake ni wlh itama sai ya saketa,sai na Hana su zaman lafiya,Kuma indai Ina raye to Naila baza ta haihu ba har abada,wlh bazan kyale su ba,yanda suka sa min bacin Rai na rasa Mohsin har abada...Baban Hanan ne ya shugo Dan Koli ya tsinci me take fada yace Allah ya Kara da kin San kina son mijin naki me ya hanaki biyayya,Kun dauka rubutun ku zaiyi amfani,bari kiji ko wajen uban wa zaku je wai ki Hana wata haihuwa ke din banza idan Allah ya tsaga yaro sai yazo duniya ke wacece da zaki Hana,wacce bata San kanta ba,Ina nan Ina jira naga yanda zaki bar gidan nan Jahila marar Ilimi,a'a a'a dakata karka yiwa Yata baki akan wasu yan iska, Dankoli yace Uwar banza wlh muna Nan sai kunyi nadama watarana" ya ja tsaki ya shige dakinsa.

Basiru Kusa complain yaje ya yiwa Chika akan halin da yake ciki,yace Chika ki min rai ayi a gama aikin nan Tsohuwar nan tafi karfina,zata kashe ni billahillazi da ace zaki iya Ganin tsaraici na da na nuna miki ita kin gani taji jiki tayi ja ta dawo abar tausayi,Chika dariya take kamar ba gobe tace ba Nollywood kake bukata ba,uhm uhm Chika yanzu ko Nollywood sunyi hankali sun gyara film dinsu yanzu,wannan ta maidani kamar doki ba hutu ba komai,Chika tace ai kuwa lokacin gama aiki baiyi ba kwana nawa kwata kwata ba a Kai sati ba fa ai yanzu aka fara bari dai a canja Maka magani.

Basiru yace Dan Allah ku agaza da sauri matar nan fa so take taga bayana,ni matata ba haka take ba,ke ni duk iskancin da nayi ban taba cin karo da irin Mummy ba,yanzu dalilin haka ta sa iskanci da mace wani neman mace duk dadinta ya sire min bana kauna.
Yanzu Dan neman matan ma Basiru dainawa zaka yi? Tun yaushe Kuma mata sun fita kaina ko wacce ta je da jikakken gabanta bana so,Ina naga lafiyar neman wasu ma wannan matar duk ta fatattaka ni.

Chika kuwa Naila ta bugawa waya lokacin Spark yayi Bako Kamal yazo suna tare,tace magani fa baya yiwa Baseeru sosai,Naila tace amma wannan Baseeru ba karamin rago bane,ai duk Wanda maganin nan bai Masa ba to a ragon ma na gaske ne,yanzu Kinga ni ba fita zai barni nayi ba bare naje wajen kaka,Chika tace ni aikin me nake sai na wakilce ki naje turo kudi na tafi,Naila tayi dariya tace ni fa aikin Nan ya ishe ni wlh bana so muyi abinda Spark dina zai ji haushi,Mamansa ce tafi wacce ta haife shi a wajensa haka yace min jiya itace komai dinsa,yanzu idan har ya ga nayi Masa haka fa,kiyi tunani Chika wlh da shine indai mutum ya shafe ni to ya hakura ko mene bazai Masa ba,Baseeru da rannan zaginsa yayi amma sabo da Mummy duk rashin mutuncinsa ya kyale shi,ni dai gaskiya Ina tsoron aure na kar ya gurgude haka kawai Hallare ta available ki cuce ni,Chika tace au cutarki ma zanyi? Naila tace a'a amma ai dai ai....ai.....

Chika tace Okay bari a fada mata gaskiya kawai,Naila tace ae nidai a fada mata ba wani donkey monkey da zai kashe min aure,Chika tayi dariya tace wato nice Donkey money din kenan,Naila tace da wai ae haka nake nufi,dariya suka yi,Chika tace baza a fasa aikin ba wlh sai Baseeru yaji dadi kafin a hakura bari ni ai nasan address din kaka zanje na karbo,Naila tace Bada yawu na ba babu hannuna a ciki,Mijina kawai Ina Jin dadi na ku jawo min tunda na fito daga gidan yari Alhmdllh Allah ya hadata da Gamonta itama na barwa Allah,Chika tace wato yau Tantiriya tasan ta barwa Allah ikonsa kenan,Naila tayi dariya tace aurena nake ji ko Bai sake ni ba idan yaji haushi na fa,ko Yana Sona Kashi Dari nazo nayi abinda zaiji so na ya dawo Kashi Hamsim ko arba'in fa,ke da baki aure ba Chika kina da chance kiyi komai ni kuwa wannan ta shafi Spark,kar nazo nayi aikin da na sani,Chika tace dalla rufe min baki wlh sai Baseeru yaji dadi,Baki isa ya Sha wahala ya hakura ba,to ai nace kuyi ba hannuna sisi bazan bayar ba,Chika wayar ta kashe ta kira Beauty ta fada mata yanda suka yi da Naila,Beauty tace dalla share ta dole Baseeru yaji dadi in yaso a hakura gaba daya,Kai amma Naila ta zama sallamammiya,Chika tace hmm sai Kinga ma Yan uwan Spark yanda suke mata bata iya ramawa,duk rashin kunyar ta sai dai Spark ya tare mata da kansa.

Beauty tayi dariya tace tayi dai dai ai dole ta hakura tunda Yan uwan miji ne da iyayensa tunda shi dai baiwa nata dangin ba ai bai dace tayiwa nasa ba,Chika tace Allah ya kaimu na auri Misam su gani wlh wlh ba shegiyar da zata zo gidan mijina ta ci min mutunci ta tafi babu ita wlh sai na rama, Tantiriya fa ta fiki rashin kunya Chika tunda kika ga tana kyale su kiyi hakuri kawai aure ba komai kake yi ba,Chika tace ta fini dai fitsara a baki amma wlh nasan nafi Tantiriya masifa ita ai bata da karfi bata fada Kuma sai zallan iya shege da shi take tsorata mutane,nasan yanzu abinda Naila zata iya fada a bainar mutane ni bazan iya ba amma fadan da za ayi dani ita Baza ta iya ba wlh wane mutum,Beauty tace na sani ai ko ni nafi Tantiriya fada,Kin dai iya Munafunci cewar Chika.

Dariya suka yi Chika tace Malama Ikhram fa har yau tana Abuja Kuma wlh tana gidan Rafeeq,zata aikata, wai ni Kam ko Baban Malama ya mutu ne ko shima naga ta kara lalacewa ne,dariya suka yi Beauty tace dama Malama Yar iska ce matar da take iya zigidir a gaban Yan daki,kin San da fa dakinsu Daya da su Azima masu kwana ba wando,Malama wlh a gidan yari ma an San da zamanta ita fa ta fara bullo mana da gasar girgiza Nonuwa ko kin mata,duk Wanda yaci Naira Biyar,Wai wannan wa'azin shine sana'ar da ta samo a gidan yari dama tace sai ta fita da sana'ar da zata dinga cin abinci,Rafeeq bai San Malama bane zata iya tubewa a gabansa ita dama bata saka sutura Indai ba Sanyi ba,gidan yari take zagewa da pant da bra yini kwana da Pant da bra idan ana zafi,Ke badan karatun da tayi me zurfi ba fa shine ta daina amma da tare muke Shan Wiwi cewar Chika,wai Ina Wiwin ne Chika kin daina Sha kuwa,Ina shayinta abina idan nayi aure ranar da za a kaini zan Sha ta karshe shike nan Inshaallah nayi alkawari,Beauty tace yanzu tuban baza ki tuba ba sai ma ranar da za a kaiki dakin miji,Ina laifi da bance sai na samu ciki ba,idan fa za a kaini nace,Beauty tace idan?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? kin auri Misam ki rama iskancin da dangin Miji suke yiwa surukata Naila kici uwar su sannan a wajen miji kiyi lakwas,Chika tace haba Bata bakinki kike mune fa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login