Showing 63001 words to 66000 words out of 134888 words

Chapter 22 - Tantiriya Agidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

924

rike,bazan iya kula wata ba ko wace ko me zata bani,ke da mace ta bani Badon ta gwara nazo ki min kiss,Chika harda Jin dadi,ya zubo karya yace jiya Mima ta turo min Wahida wajena wai mu daidaita kanmu, nace Ina da ke,wai yarinyar nan ta dinga turo min kirji nace inyi me da shi gani da Chika nata ma fresh me kyau mu dan jiiii....Chika lusara har ya gama da ita sabo da tasirin so ta tsaya ta kyale shi,ya lalubi bakinta a hankali cikin salonsa na Yan bariki ya dinga tsotse mata baki,muryarsa na rawa yace ki tausaya min kar wata taje ta min na yarda da nata,Chika tace to karka je kaji ta dinga tayashi ana gaba gaba tun Yana shafe wuya ya zuge zip,ya zauna Saman kujera tare da dorata a Saman cinyarsa ya ja zip dinta kasa ya zura hannaye tare da janye bra din sama ya fara wasa da dukiyar fulaninta Chika sai dadi itama take ji,Wata yarinya ce ta taho da gudu kanwar Chika da suke Uba Daya,Chika da gudu ta mike tare da fadawa Daya kujerar,Misam ko a jikinsa ya dinga dariya yace matsoraciya bafa Nan ta yo ba fita zata yi waje,Chika tace ta ya ka sani? Yace daga sautun taku ake ganewa ai,Chika bra dinta ta gyara da zip dinta ta dawo daidai,yace ya haka? tace ka gama na yau.

Misam yace kira min kanwar nan taki data wuce da gudu ta cuceni Yar kundun Uba,kira min ita,Chika tana dariya ta mike ta fita taje ta kawo Masa kayan ci da Sha,ta koma ta tambaya a gidan tace wace ta fita a gidan Nan da gudu yanzu? Sukace Mubeena ce,sai ga Mubeena ta sake shugowa da gudu,Chika tace zo Mubeena ana kiranki,tace to tabi Chika suka shiga ciki.

Chika tace gata Mubeena ce ta wuce da gudu ko Mubeena? Yarinya tace ae nice nan wasa nake yi nice Super man,Misam hannu ya rike mata ya jawota gabansa yace sai na zaneki yau tunda kika tsorata ni,baki san anyi Bako ba?
Idan aka yi bako nutsuwa akeyi,Mubeena tace ni ba ruwana ai da Bako washa na nake yi,Misam kamar gidansu harda bata rai yace rufe min baki bakya Jin magana ko,zan zane ki a gidan nan,Mubeena tayi shuru,yace je ku tafi makaranta,tace yau ba makaranta,yace to sai Kun je School,dariya Mubeena tayi tace gwara ma nayi bacci,yace yawwa je kiyi bacci ku kwanta da kannenenki ku duka tace to,ya bata kudi yace gashi kuje ku raba amma duk Wanda bai kwanta bacci ba kar a bashi, tace to tace an gode Allah ya saka ta fice da gudu.

Tana fitowa da karfi Misam suna ji tace Bako ne yace muje muyi bacci a bawa kowa kudi,yaran gidan da gudu suka fada daki suna ihu da murna kowa sai rige rigen kwanciya suke,wannan ya tuntsira ta baya ya baje waccan ta wantsalo kafafu gefe,Mubeena kudin ta mikawa mamansu tace nima na tafi bacci idan mun tashi Mama a raba mana yeeee...ta fada daki,dariya uwar tasu tayi Dan gaba daya basu San dalilin bako ba har Mama.
Allah sarki yara daga baccin wasa sai na gaske ya kwashe su su biyar suka rushe da bacci gida yayi tsit,Chika ce tazo tace wai Ina yaran? Mama tace wai daga Bako yace suyi bacci leka ki gansu,Chika ta leka tana ta dariya ta koma ta bawa Misam labari,shi kansa dariya yake,yace yaro yaro ne.
Zama suka yi suna shirye shiryen auren su yanda zai kasance,ana yi ana soyewa.

Washe gari Chika ta wuce katsina tana zuwa a wajen mamanta ta yini suna hira,tana yi tana fitowa ko zata ga me unguwa,har tayi wanka ta canja kaya tasa riga da wando ta tsuke ta Sha kyau ta daura mayafi a kanta,Babarta bata San ta fice ba tace yau zanyi tijara wallahi shi yasa nasa riga da wando yafi ganina da kyau,kofar gidan me unguwa tazo tace Ina me unguwa Dan Allah? ta tambayi yara,suka ce Yana wajen Liman gasu can a majalisa.
Wajen ta nufa Kai tsaye tana taku dai dai tana zuwa tace salamu Alaykum,Ina yininku,suka ce lafiya, a Chika kece haka,Liman yace Subhannallah wannan ba tsari bane ga Yar musulm....dakatar da shi tayi tace ba abinda ya kawo ni ba kenan munafukan unguwa ka bari kaje can masallaci ka fara wa'azi,har Ilimi ne dakai,kiran sallah ma sai anci gyaranka,me ka sani Dan tsubbu,kana bawa mutane maganin tsubbu kana Jan Sallah,kana raba auren mutane,kana hada makwafta fada,kana sa kishiya ta yiwa kishiya asiri har kana da bakin wa'azi,Bakinka ai sai dai Kaci goro ba dai kayi wa'azi ba.

In banda lalacewar ma musulmai wa zai bika Sallah Kai mashirki irinka,mata suna zuwa kana amfani da su kace zaka shafa musu magani su tube,kayi amfani da mace mene bamu sani ba kana Nan ana kiranka Malam Liman kana washe baki,Liman mukus yayi yasan an San sirrinsa,Me Unguwa yayi tsumu tsumu,Chika tace tsohon munafuki,tsohon banza, Dan shege,wani Dattijo Wanda shima tsohon munafuki ne yace haba Suhaila,Chika da karfi take magana ta tara musu mutane karka sake min magana tsohon banza Kaine ka Kori Yar kaninka sai kauye ta koma zulaiha ko ba Kai bane?, karka sake min magana yanda kake ganina Ina cikin bacin rai tunda nake cikin garin Nan,Ina cikin Jidali,tsuma nake adey vibrate,ko na samu farin ciki bana jinsa bana nishadi,tana magana har haki take tana jijjiga

Tana nuna Me unguwa da yatsa tace Idan na fito Maka da rashin mutuncina dana fito da shi daga gidan yari,idan na fara Maka tijara da wulakancin Dana fito da shi daga gidan yari,bala'ina Dana fito da shi daga gidan yari wallahi sai gangar jikinka ta fita ta bar ruhinka

Liman yace ke ko kin haukace ne,Kan Liman tayi kamar zata dake shi tace Kai yane ta Masa maganar Yan daba Ina magana kana magana kana fada min burkutu,ta nuna Me Unguwa tace a fada Masa zan saita Masa zama,sai na hanashi Shan ruwa a kasar nan,sai na maka wanka da ruwan kwata,kayi min sharri kayiwa uwata sharri ka kashe mata aure Dan uwarka, ta ebo kasa ta watsawa Me unguwa a kansa,ya mike yace keee ni...

Chika tace uban me zaka iya matsiyaci,Babar Chika ce ta fito da gudu tana kuka tace yau na shiga uku wai baza ki hakura ba, dattijai ne da girman su,ai suci darajar tsufa, dazu fa nace ki hakura,bazan hakura ba sai ya Fadi gaskiya wlh sai ya tonawa kansa asiri zan hakura, matsiyaci haihuwar asara Allah ya isa me shedar zirrrr,kasa ta ebo ta watsa musu ku tashi ta fisgi tabarmar ,Suka mike da gudu,ta dakko dutse Kato suka arce da gudu ana ta musu ihu,sabo da kowa ya tsane su a garin sabo da gulmarsa da bakin halinsu,sun buwayi kowa a garin,Chika birge mutane tayi dama an rasa me yin haka kaf garin sun hana mutane sakewa.

Kwana biyu Mummy kwaya ta saketa ta bude idonta ta mike ras da ita ba wani alamun ciwo ko wani Abu,Malaman suna ta karatu aka ga ta mike suka ce Alhmdllh Alhmdllh sun fita sun saketa, inshaallah ta rabu da su kenan baza su sake dawowa jikinta ba Kuma ai anyi arziki,Yan uwa sai rungume Mummy suke,Spark ma ya rungumeta Yana mata sannu,sabo da rainin hankali tace me nayi? Me ya faru dani? Ina Baseeru na? Ina Mero Yar aikina Dan Allah kar ta tafi, ban San me ya hau kaina ba nace na koreta,ku fada min me ya faru Dani ne,su Mima sune masu Bata labarin komai.

Mima tace kika Fadi kina dafara,Mummy tace Subhannallah,muka kaiki asibiti Abu dai yaki,Yaya yace a dawo Dake gida,muka dawo dake aka Nemo malamai suka dinga karatun Qur'ani a kanki ayoyi masu zafi suka dinga karantawa,Mummy tace shedan a gidan nan Kuma tasa ta kare,suna ta bata labari yanda Spark ya damu,Mummy taji dadi tace ashe dai Yana son uwarsa,suka ce ai munga zahiri,duk son shegiyar Matarsa Naila da yake yi sai gashi a kanki ya watsar da Yar iska,a nan yake yini,da asuba yake fitowa sai dare,Wahida tana wajen tace mayyar har nan take biyo shi ai,tana iyayin banza ita me miji.

Naila Kuma Allah sarki kullum sai ta yo soye soye na sha'awa ta kawo musu amma basa taba gani,yanzu ma sallama tayi ta shugo da basket dinta na abinci,suka ce gata nan jaraba an dafo kayan tsafi za a mallake mu,Mima tace baza mu mallaku ba kuwa Ubanta yayi karya,Naila shugowa tayi ta durkusa ta gaida iyayen, Yan matan kuwa sai harararta sukeyi ana mata kallon banza,duk da haka tace sannun ku ya me jiki? Mummy tace kin ganni ai naji sauki na maye na tambaya Kuma,tace to Allah ya Kara sauki suka ce Ameen a fusace,zata mike kenan suka ce dauke Abincinki ki kaishi can Palo baki saci,ko Kinga Jikin mu da yunwa?cewar Anam da wata kanwar Mima.
Dauka Naila tayi ta fito ta shiga kitchen ta juye a flasks din Mummy ta tattara nata a basket din ta fito ranta yana mata suya sosai,tunawa tayi da maganar Abbanta fadan da yayi mata tayi hakuri kawai ta zauna ita kadai,lokacin Spark ya fita Yana waya.

Tana zaune suna ta zirga zirga suna jefar mata da magana,Anam ta fito tace wlh Ina Nan sai na rama dukan da kika Sa Yaya ya min,shegiya Yar gidan Dolo,ubanki Hashimu dolo to Munji labari KwarKwar ne ubanki,ashe ma wani bi ta can ne wani shagiri girbau ne ubanki.

Naila kasa jurewa tayi tace ke Ubanki fa waye shi kakanki ma nasan asalinsa manemin mata,Dan bariki,gwara ubana halitta ce ta Allah,talauci Kuma ai ba Wanda yazo duniya da arziki,haka Yayanki ya gani yace yana so,Kuma dole a zauna dani ba yanda za'ayi,sai ma na fara zube muku yara tukun,ke dalla talakawa,ai duk mun kwakwulo komai naki,marar asali dama da Gani Yar kauye ce,wata ce cikin Yan matan budurwa tazo tace Yar gidan Hashimu Dolo da Kubra suka kwashe da dariya suka yi gaba.

Mero tana zaune a daga wajen kitchen a bayan kujera tana ta recording basu sani ba,tace kamar na kunnawa mijinta yaji,Naila ji tayi cin mutuncin yayi yawa tana magana Kuma zasu yi mata duka ta mike zata tafi,budurwar ta fisgo hannunta tana cewa wa kika cewa Kakansu Manemin mata?,Naila tana Juyowa ta sharara mata Mari,wai wai wai ai duk fitowa sukayi,Yan matan suka tararwa Naila suna dukanta kamar Allah ya aiko su,ga Naila ba karfi,hancinta ne ya fara fitar da jini ta fara habo sosai, Spark ne ya shugo Yana can Yana waya.

Suna ganinsa suka gudu iyayen suna kallon yaran basu iya tsawatarwa ba.
Spark yaga Naila a kasa tana ta habo duk da Bata ji rauni ba sai iya habon,dagata yayi da sauri kamar zaiyi kuka ya dakko tissue ya bata yace jeki wajen mota, ya leka wajensu a daki yace ni wannan ai ba so na kuke ba,wlh bakwa kaunata ban sani ba ashe,yace duk iyayena ne ku da kannena ashe ni ba kaunata kuke ba, shike nan gwara da aka yi yunwa halin kowa ya fito.

Mummy tace tab an tabo tsiya wlh shike nan duk Yan matan Nan sun shiga uku wlh ko a hanya kuka ganshi ku gudu,mu Kuma ya daina zuwa wajen mu,Mima tace gashi kuwa da iya daukan mataki,Spark ficewa yayi ya koma Inda Naila take Jikin fanfo ya hangota ta kafa kanta ruwa me Sanyi yana zubo mata,Mero da gudu ta fito tace bari kaji abinda suka mata, ta dannawa Spark recording ya karba duk yaji,ya goge daga wayar gaba daya,ransa ya baci,habon Yana tsayawa ya riko Naila ya goge mata ruwan ya sata a mota,tace da mota nazo yace bari zan sa a kawo motar gida,suka shiga sai gida.








AsmaBaffa[1/19, 9:28 PM] +234 806 252 6950: PAID GROUP 300

ACCNT NO
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK

YAN NIGER
+22790795939

A GIDAN YARI

BOOK 2
~YARAN JAURO~

51-55


Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM

PAGE NAKI NE
UMMU KHINAL



Naila kawai takaicin ta Bata rama ba,ga ba su Chika ba kowa bare ta sa a daukar mata fansa,a ranta tace Ina ma Chika Na nan nasa sa azo har gida a zane su,takaici ne ya ishe ta wai Ubana KwarKwar,nawa iyayen ma da sunfi nasu hankali,tace wai Abba ne shashasha,Spark Yana driving Yana kallonta,yace kiyi hakuri please,Naila tace ba komai hawaye ya zubo mata,duk abinda kaga ya sa Naila kuka kasan yayi Muni bata kuka.

Hawayenta ta goge da mayafinta wani yana sake fitowa,parking yayi a gefen titi,yace baza ki hakura ba kenan mu koma a rama miki? Naila ba kunya tace ae,murmushi yayi yace sarkin ramuwa,ni kike aure ba su ba me zai dame ki,nine idan na miki zaki ji haushi amma su mene su,Naila tana kuka tace amma ubana aka zaga wlh sai na rama zan hakura,kawai dan Ina shuru sabo Kai kawai nake kyalewa,ba Wanda ya isa ya sani hawan jini sai na tafi gidanmu bazan iya zama a dinga zagin iyaye na ba,muna da rufin asiri ba Wanda zai dinga ce min talakawa tunda ci, sha da sutura basu gagare mu ba.

To kiyi hakuri please my love,Naila tace wlh bazan hakura ba sai sun zo har gida sun durkusa sun bani hakuri ko Kuma kaje can su baka Bado,murmushi Spark yayi yace ni din? tace da waye to? ta dauke Kai ta Kalli Jikin window can,hannunta ya ruko ta fisge hannunta,Kuma bazan sake zuwa gidajen danginka ba ko wace bazan je ba ko su waye tunda babu mutunci,Spark shuru yayi Naila tana ta faman Cece kuce,yanzu laifin ya dawo kaina kenan bafa ni nayi laifin ba,Kuma kin San ko waye ya miki Ina rama miki fa sai in ban sani ba,Naila tace yo Kuma dai wannan na baya ne ya wuce magana ake a yanzu,ba wani batun yaji a daina shiga safgarsu ai Anji tsoro, su zo su bani hakuri,ba ruwana da Wahida bata dameni ba nasan kishi take,kannenka nake magana su zo har gida su bani hakuri.

Spark yace zasu zo indai wannan ne kiyi hakuri kinji Baby, Naila taki dariya Sam,yace my love,taki kula shi, sweetheart,Babyna,my Apple? Bata kula shi ba,a haka suka koma gida ko gama parking baiyi ba ta fice tayi ciki, direct Bedroom dinta ta wuce bata ma shiga dakinsa ba,Spark yace ikon Allah ni ba da laifi ba yara sun jawo wlh sai kunci burar....bari na fito,wanka ya shiga yayi har da yin shiga ta musamman kamar zai je daurin aure, kace wani ango ne ya Sha shadda fara tas,harda yar hula,duk dan ya birge Naila ta daina fushi.

Kitchen ta fito ta shiga ta fito dauke da cup na juice a hannunta ta zauna tana kallo tana Sha,fitowa yayi taji kamshi na dabam ba Wanda ta Saba ji ba,wurin Steps ta kalla ta ganshi yayi masifar kyau kamar ta lashe shi,idonta ta dauke taci gaba da kallonta,tunaninta ma fita zaiyi sai taga yazo ya zauna yanda zata kalle shi,suna facing juna ya tsura mata Ido,a hankali ya furta yunwa nake ji fa,ba tare da ta kalle shi ba ta mike ta shiga kitchen ta kawo Masa abincinsa ta jera a gabansa ta koma ta zauna,yau ba mutunci ko zuba Masa baza ayi ba.

Kallonta yayi yace zan danna phone Dina a zuba min,tace bazan zuba ai an iya zagin iyayena,Babana bai bada ni dan a zage shi ba,Spark gefenta ya dawo ya zauna, zata mike ya rike ta yace bafa ni na miki ba Naila me yasa kika kasa ramawa? In sun miki ki rama shine kawai,ba Kya ganin Mero ramawa take yi,in kika tsaya jiran Yan gidanmu baza su gane ba,Naila ta kalle shi tace ni da Mero daya muke? tana auren wani ne a dangi,Kai kanka ka sani da bana aurenka wlh basu Isa ba duk bani da karfi kasan Ina da hanyoyi,wlh tunda aka zagi iyayena bazan yarda ba, Spark yace rama to zagi nawa,shuru tayi tace dan kasan bazan iya bane ai har abada bazan zagi Iyayenka ba,yace to Kuma mene na fushin?

Indai hakuri ne kamar sunzo sun baki har gida,Naila tace yawwa Kuma sai sun gyara min gidan nan tas ayi sauri kar ya huce a hakura gwara yanda suka min na rama da duminta,suyi min wanki da guga,yace to shike nan? Wanne shike nan ai sai na gani a kasa,yau ko bed baza mu hada ba,Spark yace uwarku su Anam Yan iskan yara sun jawo min masifa,saura kadan Naila tayi dariya tace nidai na fada Maka ehe,Spark abincinsa ya ci ya kalli Naila yace zanyi kuka,kayi na jini ma haka nake so.

Yana gama ci ya tashi yace zan fita yazo ya mata kiss ta boye fuskar ta da sauri,tace aje wlh a Nemo min hakkina idan ba haka ba zaka dade kana bacci kai daya,ya fita kawai,tace haka kawai a dinga zagina,Saida taji fitar motarsa tace Dan uwanki yana more ni,Mima nan wlh da ace ba mijina bane danta sai na bata fitsarina ta shanye lutuwar banza.

Spark gidansu ya wuce direct ya tambaya Ina Papa? Me aiki tace Yana part dinsa yanzu ya dawo,part dinsa ya nufa ya shiga ciki,Yana Shirin shiga wanka Spark yayi knocking,come in ya furta,ya shiga tare da sallama,Papa yace Spark wannan suna naka to shike nan da wani ya fada a banza ai gwara Nina na fada ni da na haifi abina,dariya Spark yayi yace General,yace gidanku ka rainani,Spark yace kune Mazaje Papa,Allah ne yasan muguntar da kayiwa mutane tun Kana yaron Soja zuwa yanzu,Papa yace bayan Kai ka gudu,Misam ma kamar abin arziki daga zuwa training ya gudu,Arham ne kamar zai iya,amma shashasha Rafeeq shi ko gwadawa ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login