Showing 87001 words to 90000 words out of 134888 words

Chapter 30 - Tantiriya Agidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

1226

Wanda aka kira gogaggu ne,Naila Shadda ta saka irin kalar hula da takalmin spark dark milk hand bag kuma da takalminta kalar shaddar Spark milk,sai sheki suke yi,Mohsin ma yazo tare da Abba sai Jauro Abba ya gayyato Jauro sunzo yiwa Spark Kara dangin matarsa ga Chika Kuma kawar Naila.

Ana idar da Sallah aka daura Auren Misam Ahmad da Suhailat As Saddiq akan sadaki dubu Dari biyu,Khalid yace sadaki yayi yawa Misam ya tsokane shi,Misam yace mata sunyi tsada yanzu,Jauro Yana zaune a gefe yace lokacin mu Habiba Matata dubu daya sadakinta a haka ma sai Dan gata sai da aka siyar da Sa Kato sabo da gata Kuma tafi dubu Dari biyunku daraja a yanzu,ai ba wani kokari kayi ba Kai da zamu ji Million daya amma har wani baza hanci kake yi Kai kayi bajinta,wata Daya ma zaka cinye dubu Dari biyun ka bare Akai ga ciki da haihuwa ga wahalhalun gida ga rashin mutuncinmu na Maza da zaka bude mata shafi shafi nan gaba,Misam yace da Jauro a'a Baba Banda ni,Abba yace karya kake Kai dalla yi mana shuru,matasa suka dinga dariya,Wanda basu sansu ba har tambaya suke su waye ne wannan,har Spark Bai San Jauro ba amma Abba suna hada Ido da Spark yace surukinka ne abokina ne friend ne wai harda turanci Yana jona yatsunsa biyu irin so close yake nufi.

Rafeeq yace kuje kuyi pics mu wuce Abba kamar ance da shi yace karku dauke ni hoto na daina yi bazan dauka ba,Mohsin yace Abba kayi shuru Dan Allah,yace Kai ai nasan rawar kafar da kake burinka kaje kaga matarka,Jauro yace kazo ka hanamu sakewa ni nace karka je ne? Sai kallo na kake yi, jeka ka ganta ko a samu yau ka iya bacci, Jauro da Abba sun sa ana ta kallon Mohsin,Shidai Mohsin ya Mike dama hanya yake nema yabi angwaye suka tafi sai video suke kowa da waya a hannu za a samu na status.







AsmaBaffa
[1/24, 9:55 PM] +234 806 252 6950:
BOOK 2
~YARAN JAURO~

66-70

Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM


Page naki ne

'Yar Gold



Ango Misam har da cewa ku sani a gaba na fara tozali da Amarya ta farin gani,sanyin raina, gidan iyayen suka fara shiga aka gaisa da su Spark da dukkan matasan Misam ko kunya yana gaba,Suna fitowa suka nufi makwafta Inda Amarya Chikar gayu take,irin kyan da tayi ba a magana, sai kida suke ji Dj ya bar musu kayan kidan ya tafi su suke saka abinsu,Naila ita ba rawa take ba wata ce me kula da kidan, Yan mata ana ta fitsara,Beauty ta shige cikin yan gidan yarinsu sai chashewa suke a compound duk iri daya suke yi kowacce rawa da sunanta, kawai sabo da an daura aure suke ta faman rawa.

Yau Amarya ta tsaya tana kallo kawai duk rawarta taki yi yau, Naila har ta hango nata hannu ta daga Masa,yayi dariya, Naila tace yau na karbi Chika ni tunda ta kasa mu bara muyi, tasowa tayi tana rawa a hankali da rangaji da cup a hannunta cike da fresh yo har ta isa gaban Spark Wanda ganin abinda take ya ja gefe Yana mata video, Rafeeq yace baza kuci lokacinku kuci namu ba fa ato,mutane suna dariya Arham wajen Amarya ya nufa shi yana rawar yace Naila ma tayi bare mu,duk lalacewa irin ta Naila a rawa ta iya yinta yau,dariya ake tayi,Misam ya jawo Arham baya yace matarka ce wai da kake rawa kana tafiya wajenta ,ana ta yiwa Chika tsiya yau taki yin rawa,kujera ta jawowa Ango ya zauna durkusawa tayi a gabansa tare da dora kanta a Saman cinyarsa.

Misam yace zan sawa Amarya Albarka ya dafa kanta sau uku yace Allah ya miki albarka,aka saki shewa,Spark Yana Shan fresh yo dinsa da Naila ta bashi,Chika mayafinta ta bude a gabansa ya dinga mata liki Yana ta shigewa mayafinta kawai rapa yake farkewa ta Yan dubu dubu Yana liki,ya sake balle wata ya watsa sama,Yana ta uban liki yace sai Kun rike ni in ba haka ba yau sai dai jari ya karye ,ya zaro wata su Arham suka rike shi,yace ku barni,uhm uhm Yaya suka ce,dariya ake ta yi yace to na gama ya watsa last sama 'Yan mata suna ta tsincewa ,Chika taje ta juyewa Beauty kudin tace shirya min abina,ta dawo suna ta pics,Naila tace wlh nima sai ka min liki har rawa nayi,Spark yace kwantar da hankalinki bari su gama,sun shiga duka anyi pics iri iri da videos,Spark ya ja kujerar Ango ya zauna Naila ta tsaya a gabansa aka sa mata kida,dollars Spark ya balle shi baya ma lika mata a jikinta kafarta ya duka kamar Yana gyara mata takalmi ya dinga farfar da kudin,Mohsin sai dauka yake Yana dariya shi kanshi sai yau ya taba ganin Naila tayi rawa,Ana ta dauka Naila sai dariya take tana rufe fuska sabo da bata rawa, harda yiwa Chika gwalo,Misam ta kalla tana Yar rawarta ta Masa gwalo,dariya sukeyi yanda Naila take musu gwalo ko Ina sai ta juya tayi musu gwalo,Arham Yana gefe yana ta rawarsa, Kamal Yana ta dauka shima sai da Naila ta dafa Spark tace na gaji sannan ya tsaya da likin,Su Chika suka kwashe mata kudinta itama.

Abinci kuwa fried rice ta Sha hadi da quarter din kaza ga lemo ga ruwa shi aka rabawa duk wani Wanda yaje daurin auren,su Abba kuwa Naila ce ta Kai musu nasu suka gaisa ta dawo,ko mayafi basa sawa,Spark yace shi bai yarda ba sai ta sa mayafi,haka ta dakko ta yafa karami,Mohsin ya makale can gefe shi da Beauty suna ta hira cike da nishadi,yace kina iya cin abincin kuwa? tace Naila tana min girki na,yace kin huta,abincinsa ta bude tana bashi a baki,Jauro su sun cinye nasu,Abba yace Mohsin ya fito mu tafi, Jauro yace kyale shi ya gama Dan Allah,Abba yace Yar Inna yau Sakwara take min bana so ta huce,Jauro yace wai baza muje zancen bane Abba yace gobe sai muje Inshaallah amma ai kawai zuwa zamuyi a matsayin ba zance muka je ba sai an daura auren sai ta San da Kai aka daura,yawwa dan gari haka nake nufi cewar Jauro,iyakaci idan an daura taga nine mijin ta fara Dan hawayen gulma tana shagwaba ni..ni..nii...Habiba kawata ce faaaa...Jauro harda gwadawa, Abba yace Kai Kam ka tabe Jauro harda komawa dan Daudu?,kana nemafa kayi a asara a rayuwa wanne irin Abune sai surukina ya ganka ka kunyata mu.

Arham anga yan mata sai faman baza Ido yake yace Yaya Spark Nima na zaba? In kana da kudinka zabi mana,ba Wanda zai sake aure yanzu a gidanmu sai Nan da 4yrs uban waye zai rike muku matan,Arham yace wai na fara soyayyar Nima,sanda kake yi shawara kake dani duk kwailayen da kake kulawa,yaro ka nemi kudin tukun,Arham yace Ina da Uba Allah yasa ba maraya bane ni,Misam ne ya kira Naila yace ba wani Palo Wanda ba mutane kin gane ai ki turo min Amarya zan fada mata wata magana,Naila tace babu sun kulle dakunan su sun tafi gidan bikin,Misam yace to anji jeki tunda ke Baki iya hada harkar Lada ba,dariya tayi tace ae sai da suka yi sallar La'asar sannan suka wuce Kano,Shaheed yace Naila ta fito su tafi,Rafeeq ya matsu shi ya ganshi a Kano ma,Naila,Beauty har wasu matan kaf Yan gidan yari an tafi wajen Malama,Chika aka bari da kawayenta Yan Kd ba damar zuwa.
7pm suka dira a masaukinsu can hotel,mata kuwa suka yi gidan Malama,Yahuza Donation ya kwaso karuwai da masu kida wai sun zo Masa murna zai aurar da Yar uwarsa,suna ta tambada a kofar gidan Yahuza,kida ne na gasken gasken kamar zai fasa layin,kidan ko baka so sai kayi nishadi,Su Naila suna zuwa suka ce ai mu bi sahu kawai,Amarya taci kwalliya cikin fitted gown na Bride material wani blue an zuba mata make up,tana zaune ana ta cashewa a gabanta,ya zata yi ance dole a gabanta za ayi,Naila ta kira Spark tace ai ku taho a Nan ake biki ku taho da kudin liki,yace hmm na gaji ni bacci zanyi,Naila ta dame shi ni wlh sai kazo.

Arham su dama ko masaukin basu je gidan Amaryar suka taho sai suka iske Inda ake badala,kowa ya rike baki gidan su Malama guda,Arham yace lallai a Nan ake biki,duk fitsarar su sai da suka tsaya kallo yanda Yan mata balagaggu ke barin mazaunai da kirji,Kuma tare da Maza,Stella ta jawo Amarya dai dai lokacin angwaye sun zo,Ikhram tace tun kafin a daura bazan iya jurewa ba dole na chashe,tana farawa aka dauki shewa da guda aka bata fili,Naila tace Ango ga ranarka kace zaka chashe,Rafeeq yace anya bazan iya ba yana dariya,ba irin rawata bace, Malama kida ya mata yawa ba ruwanta da kowa,Rafeeq tazo ta jawo ciki tace idan baza ka iya ba just watch ta juya Masa duwaisiyya tana girgizawa,Misam da sauran suka dinga dariya,Misam yace akwai abin ai dole kiyi,Ango ya fara zuba ruwan kudi Yana liki, Ku bani tamburan Ikhram harda tamke baki,akan yana liki ga rawa ana Masa yaga kaya.

Su Naila suka shugo suma suna ta liki,masu kidan karuwai suka Kara dagewa,suna cewa mu yau a nan zamu kwana,yau kwana nan,anyi liki sosai,Yan gidan yari suma sajewa suka yi da karuwan,sai wurin 1am,Spark Yana zuwa yaga abinda ake ya ja Naila mota suka zauna ciki suna tsotse tsotse,sai da angwaye zasu tafi masauki Kamal yazo yace Madam a bar mana mota,Naila fitowa tayi ta barsu suka tafi ita Kuma ta koma ciki,Amare nan ma masu kwana tattarawa suka yi suka koma kusa da gidan Yahuza Donation wani gida me kyau da Dan fadinsa ya Sha tiles matar yare ce me shegen tsafta,da aurenta ma da Mijinta shima yare,four rooms ne agidan da Parlo.

Naila suka baje a gidan,Beauty tace Naila banci abinci ba fa tun safe,Naila tace ke na gaji ki fadawa Amarya,Ikhram tace me zata ci a dafa mata yanzu,tace taliya da manja da yaji,Naila tace kullum dan masifa taliya,wata ce a kawayen Ikhram ta siyo taliya,tace naje gida na karbo mana,Ikhram tasan halin su Asabe tace a'a shafa'atu ga kudi siyo mata.

Naila tace a dafa Dani,Ikhram tace wlh Baku isa ba ga Abinci za a kawo mana wa za a barwa shi, Shafa'atu ta karbi kudi ta siyo taje dakin Ikhram ta dakko yaji ta soya manja a gas dinta sannan ta dafa taliyar ta kawo,Beauty ta ja gefe da taliya guda a dafe tana ci kadan ta rage,Naila tace naci wannan tace a'a da safe zan dumamata,Ikhram tace ki bata taci da safe a dafa miki wata wannan masifar cikin naki ke tab,Beauty tace yarinya rai dai Allah ya nuna mana naki,Naila cikinta ta shafa tace kwai na? Kwai ya kuke haka ne ku karbi Abu kun ki karba ku,ana ta abun nan ya Ilahi kunyi likimo,Ikhram tace wai ya kuka ji da zafi ne karya ake mana a gidan yari? First night,wata a ciki itama tana da aure tace wlh da za...da sauri Naila ta katse zance tace wani zazzafan dadi Ikhram,ai karki ji komai ko Beauty? Beauty tace wow da ba dadi Kya ganni da ciki,Ikhram tace Kai zan yarda da ku kuwa? to zauna Karki yarda cewar Naila.
Suna ta hira Beauty da Naila suna ta zuga Ikhram ta bada kai ba wani zafi.

Bayan sunci sun koshi bacci suka yi abinsu,washe gari da asuba bayan sunyi Sallah bacci suka koma suma angwaye haka,sai 9am suka tashi suka fara shiri,gaba daya mazan family din kaf har Misam farar shadda suka saka iri daya,Ango ne kawai ya buga wata Arsh dinkinsa ma ya banbanta,Motoci lafiyayye suka shiga sai kallon su akeyi sabo da irin suturarsu da motocin da suka zo da su,gidan Amarya suka nufa,Yahuza yace baza ayi a masallaci ba shi a kofar gidansa za a dora, Inda aka Bada order abinci sun kawo wajen da uniform dinsu na aikin mata da Maza girki ne iri iri sai abinda kake so zaka karba,komai anyi na Yan gayu tsarin ya birge kowa.
Yahuza ya Sha shaddarsa Sky harda rambadawa jan idonsa kwalli kana ganinsa ka San dan bariki ne, Misam yace au ba a masallaci za a ayi ba ga masallaci kusa,Yahuza yace banga dama ba,an baza tabarmai mutane dai an taru ga Yan bariki abokan Yahuza,Yahuza yace wai Ina Liman ne yace gani na karaso,idan baza ka daura ba sai ka fada mana,ai kasan ni ba iya khudubar Nan nayi ba da nasan yanga zaka mana da tuni ni na daura da kaina haba sabo da kana da addini da ilimi sai kayi mana yanga, Anji to kana Jan Sallar masallacin juma'a ana biyanka albashi ai ba kyauta kake Jan Sallar ba,gomnati biyanku take,Kuma duk kudin da ake biyanku harda na al'umma idan an kiraku radin suna ko daurin aure gomnati ta biya ku.

Liman yasan hali ya share Yahuza ya samu waje ya zauna mutane da yawa a tsaye suke,dangin Papa na kauye da su aka zo sai Baban Misam Wanda shima Yana ja gaba,Abokan Papa duk sun wakilci Papa gasu Nan da yawan gaske,taro yayi taro,haka na Misam ma an Sha mutane,Yahuza sai wulakanta Ikhram suke suna nunawa bata da gata,haka bangaren mata kowa yazo wajen sai ya gane Ikhram bata da gata,dangin Ikhram da suka zo mutum biyu ne rak suma ba wani dangi na kusa bane,Ikhram tana ganin wulakanci tunda bikinta ya matso,matan Uncle suyi mata shima haka,Rafeeq ya bawa Spark labarin Ikhram tun a gidan kafin biki, tausayi ta bashi,ance a yanke sadakinta Yahuza yace ai ba tsada zata yi ba ku Bada dubu Hamsim ai tunda aka zo tsaida rana na fada muku, kamar ma a make yake baya hayyacinsa bakin cikinsa sadaki bazai ci sisi ba shi yasa ya Fadi kudi kadan.

Rafeeq yace ni na Kara Sadakin matata dubu Dari biyar zan bayar,Rafeeq ya tara kudi sosai sabo da Iyaye mata me dubu Dari biyu,me dubu Dari me dubu Dari da hamsim etc Mima dubu Dari uku ta bashi tace ko baida kudin sadaki lallai ayi bajinta,Yahuza ya rude yace to kawo sai a boye mata ko wani abin sai a siya mata,Rafeeq ya zaro waya Nan take yayiwa Ikhram transfer a accnt dinta ya nunawa shedu kowa ya sheda yace an bawa Amarya abinta,Yahuza ya fara zare Ido Yana Jin haushi yace wato ni ba'a yarda dani ba to ta fito ta daurawa kanta auren na fasa a tashi a watse a bar min gida,Spark yace Kai Malam saurara karka mana kwaya a nan mun fika hauka Liman daura mana aure Ina dangin Ikhram? wasu Dattijai suka ce gamu Allah sarki yarinya, Spark yace ku mana walicci ai Kuma danginta ne ya halatta Liman daura muje,Yahuza ya mike Yana masifa wallahi ba a kofar gidana ba,Spark yace gidan haya ba har gidane da Kai,idan ban bugaka da kasa ba shege nake wa zaka mayar Yan iska,Yahuza yace Allah? Arham yace Dan anga bamu sako kakin sojoji bane,Khalid hularsa ta manyan sojoji ya dakko ya buga,sai Yahuza yayi mukus ya koma gefe yace bazan sheda ba to wlh,Yana gefe Dattijai aka daura aure sharrr, ana daurawa yaga motocin sojoji suna ta dira a gidan Wanda basu zo da wuri ba,bataliya bataliya,harda escorts din Khalid Dana Spark,Nemar Uncle aka yi aka rasa ya fece,ana ta cin abinci ana shagali,Rafeeq sai washe baki akeyi yana amsa Ameen Ameen,makadan karuwai sake dawowa suka yi suka saki Dan asharalle yau kuma, Rafeeq yau dai yayi rawa shi daya aka rufe shi da liki,kawai Dan yaji Dan Asharalle Yana wake Ikhram Yana kiran sunanta a wakar ya fara rawa dama shi dancer ne,Amarya ta fito da tawagarta ko wacce ta ci wanka aka sake sabon shagali su Stella ana ciki ana takawa,Ikhram harda shiga suyi iri daya da Rafeeq, rada ta Masa a kunne sai tasa hannu ta matse babbar rigarsa ya dinga murga duwawu,Kamal idonsa ya rufe ya juya yace ana abin kunya a wajen nan,Spark yace bazan iya kallo ba kunya zata kashe ni,Naila ta dinga dariya,Misam kuwa cewa yake ana zubar da mutunci a wajen nan yau.

Su Mima ana can ana shagali suna ta faman zuzuta Amaryar Rafeeq,Sai gani suka yi videos na tashi a sama,social media ana ta watsawa duk Wanda yaje da kalar nasa,wayar ta kashe wai kar ta ganowa kanta Amaryar Misam bata so ma ta ganta, bangaren Chika kuwa suna kusa tuni anje daukan Amarya da motoci biyar sabo da kawayen sai an gama na Rafeeq zasu taho,11am aka tafi da Amarya Abuja,ana gamawa Yahuza yace da su Asabe lallai yau su dauke Amarya baya son bikin,washe gari aka yi za a kaita amma yace Sam ba a isa ba,Spark yace masu Kai Amarya su shirya ba damuwa,Asabe tace dole muje muga gidan Ikhram ko karyar kudi aka yi mana,suka shirya ita da Amarya yaran suka zubewa Yahuza su suka fito,Amarya Ikhran tace ni ba sai gobe akace ba kayana ma ban hada ba,Kuma yau na gayyaci wasu duk zasu zo min biki,Kun San fa sabo da sana'ata Ina da mutane,Asabe tace to su koma gidan ubansu mu yau zamu kaiki idan Kuma kece da kanki to ki bayani.

Ikhram ta zuba uban gayya yau zata yi shagalinta ta kashe kudin komai amma ance dole a kaita yau ta saka kuka,Asabe tace in zaki shirya ma ki shirya,Naila tace ke dalla daina kuka shirya mu tafi can ma fa dinner za ayi ta Misam,Yau ta Misam za ayi,duk wani tarkacen Amarya Naila da Beauty sun hada komai an zuba a mota Daya,kayan Lefenta ma a mota daban ba abinda suka bari nata,ta shiga wanka tana ta kuka ta fito ta shirya a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login