Showing 72001 words to 75000 words out of 134888 words

Chapter 25 - Tantiriya Agidan Yari Book 2 Complete Hausa Novel

03 Feb 2025

914

fara ce, farare ai sai mu,Jauro yace da kaina zan daura,kaina na zaba mata ai tayi ganganci da tace na zabo mata wallahi da Kai zamu je ka tsara ta,Banda tone tone Kuma,Abba yace nine shugaban masu tsara Mata ai cewa zanyi tayi dace an samo na kirki,kayi addua dai kar ranar tazo min a me fadar gaskiya na tona asirinka billahillazi,Jauro yace ka rufa min asiri Dan Allah.

Abba yace kace Allah na yarda idan ango yaje sai taga Kaine,Jauro yace iyakaci tayi kuka ta share hawayenta daga Nan Kuma taci kaza me 'ya'ya,Abba Yana ta dariya yace lallai kuwa me 'ya'ya.
Abba Yana wayarsa a rumfa kawai sai ga mota hadaddiya tayi parking,Naila ce ta fito Spark ma ya fito,yace ba sanarwa,Naila tace ai dama nace bazan fada ba idan zanzo,Abba Baki ya rike yace Naila Allah ya yarda.

Wannan kiba haka ai sai ace balarabiya ce,Naila tayi dariya,Spark yace Abba gaskiya sana'ar Nan a canja me kyau,ba Wanda ya isa ya canja min sana'a a Nan zanyi arziki,arzikina a Nan yake sana'a kusa da gida Ina gajiya na fada gida abina na kwanta, Yar Inna ta kawo min girki Ina zan iya Nisa da gida,ai ni sana'a indai ba a kofar gidana ba bazan yi ba wlh,baza a sani tattaki ba,Spark Yana sani yace to Abba Allah ya Kara girma,Abba yace girma wanne irin kake so nayi Kuma? Ko Dan bakin ciki ne Kai? so kake Yar Inna ta daina so na tace na tsufa da yawa,duk girman da nayi bai isheni ba sai Kace Allah ya karo min wani,rannan haka kace Allah ya Kara sutura a fakaice fa zagina kake yi wato bani da sutura ni takala kake so kace.
Naila suna ta dariya tace Abba bafa haka yake nufi ba,ai yanzu kinfi son miji da kowa me yake fada miki ne a daki Naila? Naila tace Abba rada yake min,Abba yace uhmm muje to gidan yau Yar Inna bata Jin dadi komai na gidan nan ni nayi.

Naila gabanta ya Fadi tace Allah yasa ba ciki bane,Abba yace Ina ruwanki da ciki ne ko ba shi ba,baki da kunya fa ke,me yasa ke mijinki baiyi kokari ba,Naila tace ai laifin kwayaye ne,Abba yace ki zauna yarda da likitoci ki Sha wahala bazan bata lokacin yi miki addua ba akan haihuwa sai ta karbu kin fara na jiki a asibiti kin tafi Family planning kice a dakatar da ita,Spark yace ai kuwa kamar mun je,Naila tace Spark muje,Abba ya kalleta yace ba kyau fadar sunan miji kasa girgiza take in aka Fadi Sunan miji,Naila tace ya bamu ji ba to,ai ba a ji Dan ubanki,wani Spark,to Ina alawar taki da kike kiransa da shi ko har an tsotse alawar ta kare? Spark ya dinga dariya yace da saura tana Nan Abba kwali kwali,kuka ta fara min sai na kawo ta,Abba yace rainaka tayi,Kai kayi sake mace ta rainaka ba Rancen kudi take baka ba sannan ba kyauta take Maka ba,babu komai da take baka ka zauna ta rainaka,ai Wanda mace ke bawa Rancen kudi shi ake rainawa me matacciyar zuciya.



A Watso sharhi


TIKTOK
ASMABAFFA

AREWABOOKS
ASMABAFFA 1





AsmaBaffa
[1/22, 7:08 AM] +234 806 252 6950: PAID GROUP 300

ACCNT NO
0175487861

YAN NIGER
+22790795939

A GIDAN YARI

BOOK 2
~YARAN JAURO~

56-60

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM


PAGE NAKU NE
Umu Afrah
Fiddausi Yaro
Queen=?Q?



Spark suna shiga gidan Abba suka samu Yar Inna a zaune tana ninkewa yara kayan wanki,Abba ya kalleta yace Yar halak taji sauki,Naila Sallama ta kwala dan aji itace Umma Amarya tazo ganin gida gani,Kubra murmushi tayi tace to sannu da zuwa amma shine baza ki fada ba, Spark rike da Yar akwatin Naila da alama za a kwana biyu.
Abba yace Naila harda akwati ke bazai yuwu ba zaki asarar ladan gidan miji har na kwanaki,

Spark ya furta to ta matsa min Abba sai tazo gida ta dade bata zo ba har kusan 4months,Abba Yana ji yace a zamanin mu ai sai ta Shekara guda a dakin miji,Yar Inna ma sai da tayi Shekara guda da wata biyu bayan guje guje da ta sha fama a dakin miji dama kafar ta karye a lokacin an huta,Spark suka dinga dariya,Abba yace Allah in ba lalacewa ba ta Fulani a kawo Amarya Kuma kullum ta gudu sai ta kwashe watanni,Abba yace na huta siyo lemo munyi arziki Mohsin yanzu zuba mana yake a freezer Naila ebo muku harda maltina,kafin kuwa Naila ta tare da kazo na kashe kudi wajen siya Maka lemo,Kuma ka shanye ko ragewa ku dai dama Baku hada jini da Fulani ba,hasken ku ma bana Fulani bane shi yasa ba Kara babu kunya,tun lemon da Abba ya siyawa Spark yake ta faman zancensa.

Naila tashi tayi ta ebo musu lemo,Abba yace dai daya kowa daya,Naila tace Abba mune fa lemo, naku ma me araha ne yanzu mineral sai manage,yace me yasa Baku taho da abinku ba,Mohsin ya kira a waya Yana dagawa yace kanwarka tazo Naila Bata kawo mana komai ba ko gishiri,Spark yayi dariya kamar me,yace Abba mun kawo suna mota yanzu zaka ga driver ya bawa Almajirai sun shugo da su,waya yayiwa driver ba a dade ba Almajirai suka dinga shugo da kayan arziki,Abba ya tashi yace yace yanzu zan koma rumfa ta.

Naila tace Ina yini Umma,Kubra ta amsa tana furta Naila anyi hankali,Spark ya gaisheta sai ga Mohsin da Beauty sun shugo,Naila da gudu zata mike ta rungume Mohsin Spark ya rike mata kafa yasan hali,Umma tace Ina zaki je ne haka Mohsin din gashi ya shugo bana son shiririta ke bakya girma ne,Naila sai ta Kalli Spark ta harare shi ta zauna,tayi shuru taki magana,Mohsin yace sis ba magana Kuma? ance kar na kula ka na daina Maka magana gaba daya" ya zanyi, murmushi suka yi,Beauty ce tazo ta fada Jikin Naila da gudu ta,a zabure Beauty ta mike ta fice sai amai a gindin pampo,Mohsin yace turare taji a jikinki Naila bata son turare,tashi yayi yabi bayanta,Umma bata ce kala ba tace bari naje kitchen ta fice ta shiga kitchen.

Beauty sai da ta gama amanta Mohsin yace Kinga duk abincin ya zube dama da ya aka ci,bakinta ta wanke ya wanke wajen tas suka koma ciki ta zauna can nesa,Hira suke sosai har Umma ta kawo abinci,Spark ya dan ci kadan yace tafiya zaiyi Yana da meeting,amma a jirgi zaka Koma? Umma ta tambaya yace ae Inshaallah,100k ya ajiyewa Umma ya yiwa transfer na 200k yace na Abba ne sannan yayi musu sallama

Naila mikewa tayi ta tafi rakashi,a kofar gida suka tsaya yace 2days na baki,Naila kamar tayi kuka Dan Allah ka Kara min kwana ko daya ne ya zama uku,murmushi ya sakar mata yace shike nan 3days na cika kin gama,tace na gode tana murna ya tafi ya koma ciki,tana mamakin kokarin Spark yau.
Tana dawowa ta zauna a gefen Mohsin tace to Yaya,kallonta yayi yana dariya yace aure me gyara mutum,Nan muka damu akan a dinga aiki ana gyara gashi kika ji a banza kin canja,Naila tace Yaya na Isa ni yanzu girkin da na koya ma ko matarka Albarka,Beauty tace akwai labari fa Naila ki gama dai,Mohsin yace ni wajen aiki ma zan koma,zan dawo da yamma yaci abincin a gurguje ya Kalli Beauty yace madam na wuce ni,Naila ya mikawa Hannu suka tafa yace na tafi,tace Allah ya tsare sai ka dawo.

Yana tafiya Beauty ta turawa Naila abincin tace kici ni bazan ci ba bana son shi,Naila tace me zaki ci to? Taliya da Mai da yaji nake so manja Kuma,Naila tace ai sai na dafa miki ta mike ta shiga kitchen,Umma tace me zaki yi ne? Beauty zan dafawa taliya da manja da yaji,dariya Kubra tayi tace ikon Allah wai Naila kece kike haka babu kyuya, da fa tsinke baza ki dauka ba,wanki sai dai ayi miki in ana so a ganki fes,Naila tace tun yaushe yarki tayi hankali Kuma Yar Inna,Umma tace zanci ubanki sa'arki ce ni,Dan kiji Abbanku na fada ba sunan kowa bane,Naila tace Yar Innan? tana dariya sannan tace

Abba yace baki da lafiya? Uhm dan ciwon Kai fa kawai nayi shine yace bazan yi aiki ba shi yayi komai ma da kike Gani girki kawai na karasa,Naila tace soyayya tana dariya,Ya ranki kiyi fata Spark din naki ya Kai kamar shekarun Abba Yana miki so haka,Naila tace zai yi ma Umma,sai kin dage kuwa kina sauke hakkokin da Allah ya gindaya miki,da Kuma siyasar zaman aure sai kin koyeta dole,komai ace baki da matsala ko aure ya Kara zaki zama on top amma mu mata wasu suna Kara girma suna sake zama boss a gidan miji suna bude rashin mutunci da rashin kunya,maimakon ana girma ana hankali mata da yawa su haukacewa suke,a haka muke zubar da mutuncinmu a gaban Mazaje,miji zai iya zagin mace ta uwa ta uba sabo da ta wulakanta kanta,karki sake kice Kun zama daya ai mene be sani ba a jikinki, ki dinga kin yin tsafta da kwalliya ko ya kika ga dama ki zauna a gida sabo da kawai ya sanki yasan komai Maza yawanci da abinda suke gani da shi suke amfani.

Bana so ace kayan unguwa daban na gida daban,a gida a zauna da kodaddun kaya wulakantattu ko a sa skirt din atamfa da tshirts kullum a gida,ko a daura zani da Tshirt kullum a gida, miji bazai ga kwalliya ba sai za a fita,Maza suna son tsafta da kwalliya,suna son kulawa Kuma,kar kice ko kinyi 'ya'ya zasu dauke miki hankali kullum kina wajen yara Baki da lokacinsa,ai dai Kinga Ina kamantawa ni,na sanki da rashin karfin tsiya...

Abba ne ya shugo ya leka kitchen yace Kubra an San 'ya a gaba ana koya mata Dan hali,Naila idan baki gaji Kubra ba ke Kam kin rako mata duniya,dariya suka yi Abba yace Allah kuwa nasan ma kin gajeta ko? Naila tace ae na gaje ta,Beauty ya hango yace suruka ma ta gaji surukarta,Beauty tace Abba na gajeta,yace shike nan danmu Kuma an shanye shi Ina Tausayin Mohsin,shi da Kara aure Kuma shike nan,shi yasa bana so ki dinga zuwa gidan Nan akai akai kar ki dinga course wajen Yar Inna an gama da uban Dan ma ace babu,Dariya Beauty ta dinga yi,tace Abba waye a rumfar ne yanzu ka taso da rana?
Yace na gaji rana ta kwallare bazan iya ba na hada tarkacen kayan Miya na sasu a store, na fasa siyarwa kwanciya na dawo gida nayi tunda nayi sallah me zanyi anjima abokina Jauro zaizo,Beauty tace kafin Naila ta koma kuwa zamuje gidan Kawu Jauro muma mu gaisa shi,Abba yace Kun kyauta yara,da samari baligai zagada zagada a gidan idan zaku je ku zurma katon hijabai.
Taliya Naila ta dafawa Beauty ta kawo mata da yaji da Maggi ga Kuma manja ta soya mata,Abba yace ko gobene Naila ki shiga makwafta duk ku gaisa ko,tace to ai dama zanje,dakinsa ya shiga Yar Inna ta shirya Masa abincinsa kamar wani Gomna flasks din na musamman komai na daban ne kayan Abba,butarsa ma babu Wanda yake taba ta, tashi dabance har cokali na Abba kalarsa daban me gida ran gida,Beauty sai gulmar Umma suke yi suna dariya,Naila tace Kinga Umma ko kunya,Ga surukarta ga yarta amma ta wuce.

Beauty tace Kai muna kallon love,Abba Yana kwance a gadonsa yasha gyara ko Ina Yana kamshi yace me wanki Bai min wanki bane? Kubra tace wai bashi da lafiya ai na wanke su tun jiy???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a na goge tunda naga basu da yawa,Abba yace Kubra kin dauki makatin Hanawa ayi miki kishiya ta ko wanne ganni, na hakura,shiryuwar nan taki tayi yawa, nidai Kubra duk kin gama dani Kuma sai dai zawarawa suyi hakuri babu rabon Hashimu a jikinku Zawarawa.

Beauty suna ta hira da Naila,tace Naila kin samu time sai kiyi gyaran jiki sosai kafin ki koma,Naila tace ban mu Sha" suka tafa" tace ai sabuwar Amarya zan koma wlh so nake idan na koma na gigita Spark yaji sabuwa,Beauty tace akwai sabon harka wlh wata matace har skin dinki komai in and out amma zaki kashe kudi,Naila tace ba komai Inda Spark yake ba daga kafa ai dole sai da gyara,a yau zamu je amma,Beauty tace ai ba sanya a yau din nan kuwa,duk abinda zaki yi kiyi da wuri kawai ba time.
Daga wannan hirar suka fada hirar bikin Chika da ankon su da komai,suka kira Chika a waya.

Sai yamma Mohsin ya dawo suka kebe da Naila suna ta hirarasu ta zumunci,zasu tafi ta dauki jaka da mayafi tace muje Beauty mu dauki motarki,Umma tayiwa sallama ta bisu.
Spark ta kira taji yaje gida lafiya,lokacin Yana meeting ma bai picking ba text ya mata yaje lafiya meeting yake.
Tun a ranar Naila ta fara gyaran Skin da Bado,Umma ma da dare ta bata wasu tsumin da take hadawa da kanta.

Spark Yana komawa gida da magriba gidan ya dawo Masa wani kango ba kowa a ciki shuru matar gida bata Nan,yace mace itace darajar gida,da haka nake rayuwa ashe Kai na Sha wahala,gida ba dadi haka ko Ina shuru ya dawo kango,sama ya haura yace da yanzu an min Oyoyo harda zazzafan hug amma yau shuru,zama yayi gefen bed dinsa yayi shuru shi kadai yace Kai Naila ta zan iya kwana uku nan gaba kuwa babu ke a kusa,wanka ya shiga ya fito bayan yayi Sallar Isha kamal ya shugo gidan,Spark yace Alhmdllh na samu dan tayen hira,kasa ya sakko yace Ina matar gidan Ne?
Spark yace ta tafi unguwa tana Kano fa,Kamal ya saki baci yace you Spark ka iya barinta ta tafi,kwana nawa? Yace 3days na Bata Kuma ni na kaita da kaina,Inda kasan an min asiri ni ban ma San wannan gigi ne da iyayi yasa na barta har 3days, wlh nayi dana sani Ina laifin yini Daya.

Kamal yayi dariya yace kayi hakuri Dan Allah ka barta ta huta da danginta ai ya dace ma kace tayi 1week,banyi mamaki ba Dan ka Fadi haka ai Gwauro ne Kai baka San komai ba,yanzu ma da kyar na daure ban kira ta ba bari nayi ta dan sarara da danginta,Kamal yace ka kyauta gaskiya,kaga Dan iskan yaron nan zai riga ni aure ko? Spark yace wai Misam? Ae mana nayi mamaki fa wai gobe Chika zata tafi hado lefenta,su Mima idan suka ga itace ya kenan,Mima ta nace sai taje gidan su Chika wai tasan wacece matar Misam,Kuma fa Baba yayi bincike wlh basu da mummunan hali suna da asali me kyau,ita nasan so take taga masu kudi ne ko talakawa,Misam Kuma yaki yarda sam,Rafeeq dinma gobe za a Kai kudi bata sani ba Kuma sai anzo daurin aure taji an daura da Rafeeq,Kamal suna ta dariya ,yace ni nawa 5mnths aka saka rana wai gidan su Siyama basu shirya ba,normal ne ai suna da hali su Siyama cewar Spark.
Sun dade suna Hira da Spark har 11pm sannan Kamal ya tafi gida.

Naila ta sa waya a gaba taki bacci tana ta jira Spark ya kirata,ta kira Kuma bai daga ba yace Yana meeting zai kirata back bai kira ba,shi Kuma barinta yayi ta samu ta shakata,wayarsa na hannunsa sai pics din Naila yake kallo da videos dinta Yana so ya kira kar a dame shi ya fiye naci a haka bacci ya kwashe shi,Wayarsa tana silent Naila tana ta kira ba a daga,ta kumbura ta cika fam tace lallai an samu matsala Bado yayi Sanyi,haba ai ni nasan tunda naga Spark ya barni har 3days Kuma ya kawoni da kansa nasan da matsala badan Allah bane,Ashe gajiya yayi Dani,dama Abba yace love zai ja baya gashi Nan tun ba ayi Nisa ba sai ta fashe da kuka uban kowa sai da ya tashi a gidan a firgice an zaci wani abin ne ya faru.

Tana ta rusa kuka Hidaya ta fito tayiwa su Abba Knocking suka bude tace Aunty Naila ce ta hanani bacci tana ta rusa kuka,Abba yace dama kukanta nake Juyowa na zaci ma Malam Sahabi ne ya rasu shine yau naji ance Yana zazzabi,tace Aunty ce Kuma tace kalau take,Abba suka je dakin Kubra tace lafiya Naila Baki da lafiya ne? Spark ne.....Abba yace ya rasu la'ilahaillallahu tafiya Abuja ta kamamu cikin dare,dazu dazu aka rabu Kai duniya Abba ya fashe da kuka,Naila sai tayi sauri tace wayata fa yaki dagawa sai text ya min sau uku kalau fa yake,Abba yace amma ke dai Naila anyi Jikar Uban Kubra,Allah ya kwashe miki zunubinki tas Naila, yanzu ki dinga kuka haka sai kace mutuwa akayi,Kubra tsaki ta ja ta koma daki,Abba yace so kike ki kashe kanki da soyayya ai shike nan,Hidaya ya kalla ta tsaya yace wuce ki kwanta Kwaila ke har abada baza ki kiba bane idan ni kika gado kin shiga uku kuwa mijinki ya tanadi Sha ka fashe Kawai kullum tsilai tsilai sai iyayi,aure zan miki na yi miki miji,Hidaya ta kwanta yace ga kanwarki Nan Zarah sai girma take tana ta faman irgar dangi, kullum sai irga su Malam Hallai take Yana kabari,kunya su Naila suka ji suka yi shuru,yace ke Naila in Kinga dama ki kwana kina ihu watakil ma ya manta dake.

Naila tana jin haka tace ni dai gobe zan tafi na fasa kwana uku ni dama wlh gidan nan ya ishe ni,gwara Ina gidana da yanzu Ina abinda naga dama,Abba tafiyarsa yayi ya barsu .
Spark da asuba ya tashi babu Naila babu sex na asuba jaraba Kuma ta motsa,ya jawo wayarsa yaga kiranta yafi ashirin,ya kirata back tana ta bacci bata sani ba.
Masallaci Yana zuwa a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login